Showing 69001 words to 72000 words out of 87750 words

Chapter 24 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13340

tsakar gidan shiru kamar babu mutum, dama dagani sai Kausar ne, mai raya gidan maman Ama ce kodan saboda ?iriniyar yaranta.
Bayan na idar da salla na Wauki waya na kirashi, amma harta yanke bai Wagaminba, na kuma kira ban gajiba, sai da na jera masa kira goma sannan ya Waga.
A hasale yace,  Ke wai bakisan ina kasuwa bane? Idan kika takura min da maganar nan zan Sata miki rai wlhy .
Bai jira ma mizan ceba yanzun ma ya sake yanke min wayar, hawaye masu Wumi suka shiga rige-rigen fitowa a idanuna suna silalowa bisa kumatuna, ni bansan lokacin da ya farama Yaya Samina irin wannan ba?ar tsanarba? nima dai na shagala wajen mantawa murWaWWen halinsa ne, darajar aurenmu yasa na fara ganin ha?oransa a waje, suma Win a wannan zuwan.
Zamewa nai na kwanta ina cigaba da hawayena.

Sai bayan isha'i yau su Salima sukazo, dan sune ke a gidan saboda su Ammi sunje duba Yaya Samina a asibiti.
Yanda suke bani labarin halin da Yaya Saminar take ciki sai tausayinta ya kamani, na mata addu'a dan nasan tunda yace bazan jeba to bazanje Winba, dan sunan ?anwar Maman Ama da yace bazanjeba jiya gashi banje Winba.
Sai da zan kwanta ne danaga har lokacin bai kiraniba nai masa text message na ban ha?uri da kalamai masu sanyi na tura masa.
Haka na kwanta cikin damuwa, da ?yar barci ya Waukeni kuwa, dan ya sabamin duk dare ko bazamuyi hira mai tsaho ba dai zamu gaisa yaji lafiyata naji tashi kafin na kwanta.

Da safe ko da su Fa'iza sukace na shirya muje dubota, canai musu suje kawai banajin daWi, danma karsu zargi wani abu sai nace jiri nake gani.
Sannu sukaita jeramin kafin su wuce, nace suce ina gaisheta dan ALLAH.
Bayan wucewarsu na Wauki wayata na sake dubawa, a zatona ko zanga reply Win Yah Ahmad, amma sai naga wayam, tagumi nayi na zubama wayar ido kawai.
Duk da motsin Kausar da nake jiyowa a tsakar gida ban fitaba sai da zanyi sallar zuhur, dan kafin su Salima su wuce komai sunmin har Wibar ruwa.
Banga Kausar a wajeba yanzun, ta shige tuni, na laru dai batajin daWi kwana biyunnan, Wakinta na nufa nai sallama, sai da nayi kusan uku sannan ta amsa min, ban damuba na shiga ciki, kwance take a ?ofar Waki, Wakin kaca-kaca babu gyara, na zauna a kujera ina mata sannu da tambayarta yaya jikin?.
Nanma da ?yar ta amsamin cewar da sau?i.
Duk da nima ba ?arfin nakeji ba haka na tashi na fara kimtsa mata Wakin, dan yayi datti da yawa, da alama dai tama daWe batai gyaransa ba, wanke-wanke kansu cike da babbar robarta ta tara, bayan na gyara gadon nace ko zata koma can.
Bata musaba ta yun?ura zata tashi amma ta kasa, taimaka mata nai ta mi?e ta koma saman gadon, nikuma na ?arasa kimtsa Wakin harda morping duk nai mata, na kwashi wanke-wanken na fita dasu.
Har la'asar ina ma Kausar hidima, sai da naga komai yayi fes sannan nace mata ta daure tayi wanka zataji ?arfin jikinta, kanta ta Wagamin kafin ta fara jeramin godiya.
Nai murmushi da faWin babu komai karta damu, koda na fito nai alwalar la'asar Waki na koma, ban sake fitowa ba sai da Maman Ama ta dawo gab da magriba.
Sannu da zuwa nai mata tare da ALLAH ya raya, na kuma bata ha?uri akan rashin ganina da bataiba.
Ta Wanyi dariya tana bina da kallon ?urulla,  Babu komai Amarya, ai dole nai miki uziri tunda ban saniba ko ogane ya murWa kambunsa, dan ba kasafai suke son yawan fitarba .
Murmushi nai nace,  A'a bama shi bane, kawai dai jiya na yini ne da ciwon kai wlhy .
 Ayyah, to UBANGIJI ya ?ara lafiya .
Da Amin na amsa ina tsokanar Amatullah dake cin biscuit.


________________________________

?angaren Samina kam sai washe gari ta farfaWo cikin hankalinta, ta?i magana wa kowa sai hawaye, hakan ya saka Inna mari fara mata masifa akan ai ba kanta aka fara Sarin ciki ba, idan tayi ha?uri ALLAH ne zai bata wani.
Ita dai batace uffan ba, sai da taga ?an dubiya nata zuwane sannan ta daurema ranta ta daina kukan, sai tsoro ya kamata sosai da lamarin mutane, dan wasu idan akace Sari tai sukan jinjina maganar, harda masu cewa ikon ALLAH, yanzu cikin sati uku har yakai ai Sarinsa?.
Wannan furuci da mutane ke yawan yi sai ya fara Warsama mama gaje da inna mari shakku suma a ransu, ga mamakin rashin dawowar Ma'aruff asibitin, tun daren jiya daya fita cikin fushin abinda Aliyu yay masa su kuma suka Wauka damuwar halin da matarsa ke a cikine, sai kuma rashin ganin danginsa da basu zo duba Samina ba.
Koda mutane suka tsagaita zuwa yamma inna mari kasa ha?uri tai sai da tai maganar rashin dawowar Ma'aruff Win da rashin zuwan danginsa.
Uffan Sanina dake kwance bata ce ba, duk da kuwa taji mi Inna Mari Win ta faWa sarai.
 Wai Samina bakiji mina faWa bane halan? .
Kallo Waya Samina tai mata ta janye idanunta gefe,  To idan najiki mizance Inna mari? Naga dai kwance nake anan ta yaya zansan lafiya ko saSanin hakan .
 Kefa dama baki da kunya Samina, daga tambaya minene namin ba?ar magana dan rashin arzi?i .
Shareta nanma Saminar tayi, saima ta rufe ido kamar mai shirin barci.
Har suka kwanta babu Ma'aruff babu dalilinsa..........
'

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* =؋?d'?NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* =؋?d'?NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* =؋?d'?SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* =؋?d'?NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* d'?=؋?NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN=?G?=?G?_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin=?G?=?G?
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*=?G?=?G?

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuWi gida masoyan asali=? ?=?;?>?p?>?p?=?
?=?
?=??=??=?L?

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN=??=?I?



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O? [7/28, 1:22 PM] Haleemat M Musa: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(22)*



...............Da asuba Ahmad ne ya fara farkawa, ya buWe idanunsa da ?yar saboda nauyin da sukai masa na rashin samun isashshen barci, Umm-Ruman na kanannaWe a jikinsa, sai dai su duka zazzaSin ya sauka.
Wayarsa ya lalubo ?asan filo ya kunna fitilar, gaba Waya Wakin ya gauraye da haske, ya shafa kan Rumana dake lafe saman ?irjinsa a hankali, komai na daren jiyane ya shiga dawo masa, ya sauke sassanyan numfashi yana faWin,  ALLAH yay miki Albarka akan laSSansa.
Cikin rashin son ya tasheta ya ?o?arin zameta daga jikinsa, tako sake ri?eshi dan sanyin da takeji bataso ta rabu da koma miye ta ma?al?ale.
Murmushi ya sauke a hankali tareda busa mata hucinsa cikin kunne, Wan sautin hucinne ya sakata motsawa kaWa.
Ganinfa da gaske ba tashin zatai ba sai ya kai bakinsa saman kunnenta ya fara magana,  Ruman kibar Yayanki ya tashi lokacin salla yayi .
Sarai Umm-Ruman taji maganar Ahmad cikin kunnenta, dan tunda ya kunna fitila ta farka, amma kunya ta hanata koda motsin da zai gane.
Sake shige masa jiki tai tana faWin,  Uhm-uhm .
 Uhm-uhm ko? to ai nasan maganink......
Kafin yakai ?arshe tai azamar raba jikinta da nashi, ta matsa baya tana juya masa baya.
Sosai abin ya bashi dariya, dan haka yay murmushin da har take jiyo sautinsa.
Bargon ya yaye yana zura ?afarsa ?asa da faWin,  Matsoraciya da ki tsaya mana .
Ita dai batako motsaba harya buWe Wakin ya fita bayan ya zira doguwar riga.
Har lokacin ana Wan yayyafi, shiyyasa Ahmad da yayo alwalan sai ya dawo Waki.
 Wai bazaki tashiba? yay maganar idonsa akan Umm-Ruman da har yanzu take naWe akan gadon, ita duk wayonta sai ya tafi salla zata tashi, amma jin ya dawo Wakin ya bata tabbacin anan zaiyi shima.
Tashi tai da ?yar, dan har yanzu gaSSanta ba daina mata ciwo sukaiba, ga Wan zafi har yanzu tanaji, bata yarda tama kalli sashen da yakeba koda wasa, shiko yana tsaye saibin ta da kallo yake sabida ganin yanda take tafiya da Wan Wingishi, duk da ya lura da Wunbin jarumtar da takeson nunawa dan ganin tafiyar ta tafi dai-dai.
Sai da ta ficene ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa da buWewa lokaci Waya.

Cikin dauriya da ?arfafa kanta take taku saboda ruwan da akasha, danma tsakar gidan nasu duk sumintine, alwala itama tayi bayan ta shiga bayi ta fito.
Lokacin data dawo Wakin yana zaune yana jiranta, mi?ewa yay idonsa a kanta, itako ta?i yarda yanzun ma ta kalli ko sashen da yake, baice da ita komaiba harta kimtsa tazo inda yake tunda taga alamar jiranta yake ya jasu sallar.
Hakan kuwa akai ya jasu suka sallaci asubahi, bayan sun idar yaja dogayen addu'oi a garesu da al'ummar musulmi baki Waya.
Koda suka shafa Rumana na zaune a bayansa batako motsaba, kanta dai a ?asa tana wasa da yatsun hannunta.
Zamansa ya gyara ya jingina da jikin hado yana mai fuskantarta, sai dai baice komaiba kallonta kawai yake tamkar ya samu tv.
Ai sai jikin mutuniyar taku ya nemi fara tsuma, cikin sal?ewar halshe ta fara gaishesa,
 Uhm u..hm Yaya ina kwana, ya gajiyar tafiya? .
Guntun murmushi yayi yana Wora dukkan hannayensa saman gadon cikin mi?ar dasu, har sannan kuma idon nasa a kanta yake.
 Lafiya lau Amaryar Ahmad, ya ?o?ari? .
Shiru tai dan bata fahimci ?o?arin mi tayi ba.
Ya sauke hannayensa tare da kai na damar ya Wago haSarta,  Kalleni nan yay maganar babu wasa.
Dolenta ta Wago idanunta a hankali ta saka cikin nasa daya kafeta da su.
 Bakin ya mutu ne? .
Yay maganar yana matso da fuskarsa daf da tata.
Itakam ta rasa yaya zatai da Yah Ahmad, shi baisan kunyarsa takeji bane halan? Tun daga dawowarsa jiya ya koma mata tamkar bashiba a komai.......
Iskar daya busa mata saman idanu ya sata lumshesu sosai tsigar jikinta na tashi, ya jawota gaba Waya jikinsa, ya cire mata hijjabin tare da faWin,  Yaya jikin? .
Baki taWan kumburo masa kaWan da faWin,  Nidai lafiyata lau fa Yaya
 Oh ALLAH? Shike nan kinga to bara mu maimaita .
A zabure tace,  Yah Ahmad mi? .
Yanda tai maganar hawaye na zubowa lokaci Waya saman kumatu ne ya sakashi yin dariya, yaja hancinta kaWan tare da dungure mata kai yace,  Mai raki kawai, iya tasan har ita kika kira saboda ragwantakarki saita miki dariya .
Cusa kanta tai a jikinsa tana murmushi, jiya kam a ?an gidansu ai babu wanda bata lissafo ba, har Tahir dake shan nono bata mantaba, yo taji azaba, ashe abun da gaske babu sau?i........
Ahmad ya katse mata tunani da faWin,  Kinga tashi kije ki kwanta, wannan barcin da muka Wau bashi idan bayinsa akaiba zai haddasa ciwon kai .
Da ?yar Rumana ta bar jikinsa ta mi?e, bata yarda ta kallesa ba taje ta haye gadon ta kwanta, shima da yake binta da kallo tashin yay yacire rigarsa ya hau gadon.
Jinsa a jikinta ya saka sabon tsoro bijiroma Rumana, ta lafe tamkar mai barci tana sauraren mizai biyo baya, sai bataji komaiba, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ahmad daya jita ya murmushi kawai.


&&&&&&&

Basu farkaba har kusan goma, har lokacin kuma dai garin ana yayyafi irin yaf-yaf Winnan, hakan yasa garin Waukar shiru kowa yana cikin Wakinsa, sai irinsu maman Ama ?an gutsiri tsoma da ake yawan le?a waje aga wazai fara fitowa, dan ita dukda yayyafinnan tuni mijintama yabar gidan.
Kausar ma dake fama da ciki kusan tara ta fito Waura musu abin kari, ananne suka haWu da maman Ama.
 Waisu waWannan bazasu tashi bane? Garin ALLAH ya waye amma ?ofa a gar?ame? .
Dariya Kausar dake sauraren mama Ama tayi tana gyara buhun ledar data Wora saman kanta saboda kar yayafi ya ji?ata, tace,  Ke ko sai an nuna manafa miji ya dawo jiya ko .
Baki maman Ama ta taSe,  Saikace wata tsiya mijin ke iyayi matan .
Kausar ta sake yin dariya tana juye shayi a kofi mai murfi,  Ko baiyiba ai yaWan lalubi abinda zai iya, wlhy ni idan nice ita tuni zan tona maka asiri na kashe auren, banga amfanin namiji gareni bai iya taSukamin komaiba, ai ko ganga batason ajiya burinta kullum a kaWata ta bada sauti balleni da ?uruciyata da komai .
 Ke kika san dokar ai  Cewar maman Ama tana harar ?ofar Wakin su Rumana da basusan sunaiba ma .

Rumana ce ta fara tashi, ta janye jikinta da yay mata nauyi da?yar daga na Ahmad ta sakko, barcinsa yake sosai dan haka baiji saukarta ba, ?ofar ta buWe ta fita bayan ta cika buta da ruwan zafin daya ajiye a filas ta fita da brush a hannu, tsakar gidan babu kowa, dan sun gaji da le?e-le?en sun zauna waje Waya, hartayi brush Winta taje bayi tai tsarki sosai ta fito babu wanda ta gani, taji daWin yin tsarkin kuwa, dan sai taji kamar an mata gafara.
?akin ta koma, ta maido risho bakin ?ofa daga ciki ta kunna domin nema musu abin kari.

Tana cikin juye ruwa filas Win Ahmad ya farka shima, lalubawa yay kozai jita sai yaji wayam, ya buWe idanunsa yana tashi zaune, ganin tana aiki sai yaWanji sanyi a ransa, bata yarda ta kallesa ba harya sakko a gadon, ya Wauki brush da buta ya fita baice da ita komaiba.
Lokacin daya dawo harta gama kwashe ruwan ta kashe risho Win, daga bakin ?ofa ya mi?o butar ya ajiye ya juya ya fita.
Ganin hakanne ya saka Rumana ?o?arin fara gyaran Wakin, da yake aikin ba wani mai yawa bane dandanan ta kammala, tana shara Ahmad ya dawo ri?e da leda ?arama a hannunsa.
Matsa masa tai ya shige, ita kuma ta fita da sharar waje, koda ta dawo saita iske yana fito da kayan tea daga jakkar da yazo da ita, batace komaiba ta kawo kofuna kamshin ?wai soyayye dukya gauraye Wakin.
 A ledar nan akwai bired . Yay maganar yana cigaba da maida kayan daya fiddo daga jikkar.
Cikin sanyin murya Rumana ta amsa da  to .
Bayan ya kammala zama yazo yayi, da taimakonsa ta haWa musu shayin, ita dai duk ta?i yarda su haWa ido, duk da shi Ahmad yanata bu?atar hakan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login