Showing 66001 words to 69000 words out of 87750 words

Chapter 23 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13353



&&&&&&

?arfe kusan huWu su Ahmad suka iso cikin garin kano, ya jigatu sosai saboda tafiyar dare sukayo, tun a tasha sukai sallama da Nura da shima yazo ganin gida, ya loda kayansa a napep Win da yay shata suka nufi gida.
?ammatane dan?am da ?ofar gidansu, ga galla-gallan motoci sun jeru domin kwasarsu zuwa wajen kamu.
Mai napep ya samu Wan wajen ma?alewa yay fakin.
Kallo Waya Ahmad yayma motocin ya Wauke kai, dan koba a faWa masaba dai yasan ?an bikine.
Yana fitowa idon Mudan dake Winki a shago ya sauka kansa, cikin matu?ar mamaki ya fito, dan babu wanda yasan da dawowar Ahmad Win sai baba.
 Yah Ahmad! Abu ya faWa da ?arfi shima tare da sakin butar da ya Weboma Mudan ruwa daga cikin gida, she?awa yay da gudu ya koma dan kai rahoto.
Kafin kace mi yara sun zagaye Ahmad anata murnar ganinsa suna kwasar kaya zuwa cikin gida, hakan ne ya sakashi farin ciki, inda kuma hankalin ?awayen Samina ya dawo kansa, dan kuwa su Nafy tuni sun fara rattafo labari akan da shine zai auri Samina ai.
Da yawansu ?yawunsa ya Wau hankalinsu, sai dai sunce rashin ?an canji ya kwafsa masa.
Ahmad da baisan mi sukeba tuni ya nufi cikin gida ri?e da hannun Mudan suna dariyar tsokanar da mudan din ke masa akan yayo ?iba kamar ba shiba.
A ?ofar soro sukai karo da Samina da taci ado cikin wani arnen farin les, ?awayensu kusan biyar na tare da ita, da alama dai zasu fita ne domin a kaisu wajen kamun.
Kallo Waya Ahmad yay mata ya Wauke idanunsa yana cigaba da murmushinsa da ya ?ara haska choco color Win fatarsa mai ?yalli ta asalin rumawa.
Haka kawai Samina ta samu kanta da faWuwar gaba, tuntuSe tayi zata faWi ?awayentan sukai saurin tarota, da kallo ta bisa har suka Sacema ganinta, sosai taga ya canja mata duk da ma babu kwalliya tare dashi, dan wandon jeans ne da t-shert mai gajeren hannu a jikinsa, duk rigar ta yamutse alamar sunsha zaman mota.
Siririn tsaki taja tana faWin,  ?an wahala kawai a fili.
Mutum biyu a ?awayen nata da sukasan komai suka kwashe da dariya kuwa, suma idonsu a kansa, sai daifa harga ALLAH sun yaba da wannan ?ya?y?yawar halittar.
A cikin gida kam an rikice da dawowar Ahmad, harma ya rasa sannu da zuwar wazai amsa, ?an uwansa da yaran anguwa duk sun zagayesa, kunsan yaro dason adawo daga tafiya a bashi tsaraba koda ta biredi ce=??.
Fahimtar hakan da Ahmad yay ya sakashi jan ledar biredi Waya ya mi?ama Sadiya data ajiye masa ruwa yace ta raba musu.
Aiko kowa yana samu aka bashi sai ya fita cike da Woki kai rahoto gidansu.
Bakin Ayyah gaba Waya ya?i rufuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, Gwaggo kuwa babu mai cewa ga yanayinta, sai dai cikin ranta ita kaWai tasan sanyin da takeji na dawowar Ahmad Win.
Bayan yasha ruwa suka gaisa da mutanen da suka shigo ?an biki masa sannu, wasuko dai ?an son ganin ?wa?waf ne.
Bayan an gaggaisa suka fita, shima sai ya samu gaisawa da nasa iyayen da ?annensa.
Yana shirin kishingiWawa a tabarmar da aka shimfiWa masa Ayyah tace,  ?an albarka badai anan ba, maza tashi ka wuce wajen matarka ka huta acan .
Cikin shagwaSa ya narke murya yana faWin,  Kai Ayyah na, nifa kamarma kin daina sona nake gani?, yanzu abincimafa kince bazaki bani naci ananba .
 Aiko wlhy ban baka, gashi dai zan zuba a kwano auta tazo ta bika dashi gida kaci acan, maza tashi, baiwar ALLAH ai tayi ha?uri ?arnan .
 To Ayyah zan tafi, amma ki bari mu gaisa da baba to .
 A'a idan ka dawo anjima kwa gaisa, dan malam ma baya nan kusa yaje Dawanau ne .
Dole Ahmad ya mi?e domin bin Umarninta, jakkar kayansa kawai da jakka Waya da leda ya Wauka, sauran kayan kuwa duk nan aka barsu a Wakin Ayyah kamar yanda yace su Sadiya su shiga dasu.
Shi kuma Mudanseer ya Wauka kayan ya fito ?ofar gida domin tarar napep.
Su Samina amare har an wuce, sai abokan Ahmad dake jiran fitowarsa.
Nanma fa wata sabuwar murnarce ta sake kacamewa a tsakanin abokan amana tun ?uruciya, da ?yar Ahmad ya ?waci kansa akan zaije ya kimtsa ya dawo.
Ya shiga napep Win da mudan ya saka masa kayansa suka wuce.

Cikin barci naji muryar Zainab na faWin,  Yaya Rumana ki tashi ga Yah Ahmad ya dawo .
Da ?yar na iya buWe idanuna saboda ba ?aramin barci nayiba ashe, ganin Zainab zaune kusa dani ya tabbatar min da ba mafarkin dana saba yi bane.
Tashi nai zaune sosai, sai kuma na mi?e zumbur jin muryar Yah Ahmad dake amsa gaisuwar su maman Ama.
Kasa ha?uri nayi, na nufo ?ofa domin tabbatarma kaina.
Sai dai ashe ya kawo jiki zai shigo sai mukai karo harna bige kaina a ?irjinsa, nai baya zan faWi yay saurin ru?omin hannu..............
'


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* =؋?d'?NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* =؋?d'?NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* =؋?d'?SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* =؋?d'?NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* d'?=؋?NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN=?G?=?G?_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin=?G?=?G?
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*=?G?=?G?

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuWi gida masoyan asali=? ?=?;?>?p?>?p?=?
?=?
?=??=??=?L?

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN=??=?I?




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O?

*_GDW_*



*(27)*


..............Jini sosai ya Sallema Samina, abinda ya tsorata su Ma'aruff kenan suka Wauketa zuwa asibiti, gaggawar fara ?o?arin shawo matsalar Aliyu ya farayi, da ?yar aka samu komai ya dai-daita bayan ba?ar wahalar da yasha.
Ma'aruff sai jan tagwayen tsaki yakeyi, ya kasa zaune ya kasa tsaye har sai da Adam ya fito sannan.
Kwantar masa da hankali yayi akan an samu dai-daiton komai, yanzu haka zasu kai Samina Wakin hutune.
Numfashi ya sauke a hankali, sai lokacinne ya tuna da batun aikinsa, waya ya ciro yay kira Mama gaje ya sanar mata akan tazo asibitin ta samesu.
Hankalinta ya tashi sosai, da yake batasan ina zata gano asibitinba saboda private ne sai ta tasa ?anin Rumana gaba Kamalu suka tafi dan ya rakata, bata sanarma kowaba saboda a ?ofar gida ta gamu da Kamalun ta iza ?eyarsa suka tafi.
Koda suka iso suna gaisawa da Ma'aruff ya kaita Wakin da aka kai Samina sai yay mata bayanin Sari Samina tayi, daga haka yay musu sallama ya tafi akan shi zaije Office ne saiya dawo.
Yanda Samina ta rame ya tadama mama gaje hankali, amma data tuna Sari akace tayi saita danganta ramar da kwaikwan ciki, sai dai a ?asan ranta tana mamakin miyasa Samina bata taSa sanar mata ta samu cikiba koda wasa? Yanzu kuma auren sati uku ne har an samu cikin da zai iya zubewa?.
Batai zurfi a wannan tunaninba ta watsar da shi gefe kawai ta Wakko wani.
Kamalu shine ya koma gida ya sanar musu Samina na asibiti babu lafiya, kowa yasha mamaki, amma da yake ba biyema shirmen mama gaje sukeba sai sukai shirin zuwa su dubata.
Yayinda yaran gidan suka fara tafiya kaima yayyensu na ma'auri labarin.

Harsu Ayyah sukazo duba Samina asibiti tana barci bata farkaba, kowa yayi mamakin ganin ramar da Samina tayi a sati uku da aure kacal, hakama zancen Sarewar ciki ya tsayama kowa a rai.
Ammi ce kawai data daWe da fahimtar Samina nada shigar ciki tun tana gida abun bai bata mamakiba, sai dai tana tausayin mama gaje akan ?arancin rashin kulawa da saka idanu akan yaranta.
Basu baro asibitinba sai gab da magriba, har zuwa lokacin kuma babu ko Waya daga dangin mijin Samina daya le?o, shima kansa Ma'aruff Win bai dawo ba, sai Inna mari da Iya da sukaje, sai ko dangi Wai-Wai irin na kusa da labarin yaje musu suma suka Wan lalle?o.
Har zuwa lokacin kuma Samina nata barci bata farkaba, su dai sallama sukai musu suka taho akan sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan malaman asibitin sun fara maganar sunyi yawa, da sun tsaya har sai Saminar ta farka suma.
Bayan dawowarsu gidane suma su Baba suka tafi duba Saminar, sun isa babu jimawa ne ta farfaWo.
Da ihu da fisge-fisge Samina ta farka, sai ambatar sunan Ma'aruff take akan itafa tanason cikinta karsu zubar mata, babu wanda bai shiga ruWaniba, su sam sunma kasa fahimtar mi Samina ke faWa.
Dr Adam yace duk su fita daga Wakin Please.
A daidai wannan lokacinne kuma Ma'aruff ya dawo, daka gansa zaka san hankalinsa kwance, kuma daga gida yake, dan bakayan Wazun da safe banema a jikinsa, babu tausayi ya wankama Samina dake cikin halin rashin sanin mi takeyi mari,
 K dan ubanki duniya kike faWama yanda aikai ne?
Da sauri Adam ya janyesa yana masifa,  Wai kai MJ mike damun kankane? Yarinyar dama batasan ina a hankalinta yakeba kakema wannan Marin? Kaji tausayin halin da muka sakata mana, wlhy badan tanada sauran shan ruwaba a Wazun zata iya rasa ranta, kai baka da wani abin birgewa sai dukan mace? Wannan fa matarkace ta sunna ba matan banza daka sabama wannan rayuwarba, Mtsoww, baka sha giyarba ma rasa hankalinka ake......
A fusace Ma'aruff ya dakatar da Dr Adam,  Malam karka faWamin babu daWi mana, bansan shishshigi kaima ka sani .
Banza Dr Adam yay masa, ya shiga ?o?arin ganin Samina da numfashinta ke fita da ?yar bama taimakon gaggawa, dole dai allurar barcin ya sake mata saboda sam bata a cikin hayyacinta, a ?asan ransa yana dana sanin biyema Ma'aruff akan wannan aikin.
Acan waje kuwa su mama gaje na iya jiyo hayaniyar su Ma'aruff, sai dai basajin mi suke faWa, tuninsu ma duk ruWewar halin da Saminar ke cikine ya jawo hakan, hakan yasa suma suka sake rikicewa ainun.
A fusace Ma'aruff ya fice daga Wakin, ko kallon su Baba dake wajen dasu mama gaje baiyiba balle su sami mutuncin a gaishesu, su duk ganinsu halin da matarsa ke cikine ya sakashi a ruWani>?z?.
Basusan ma yana fita daga asibitin zuwa yay ya tanaji giyarsa ba tare da tsaleliyar budurwa suka nufi gida, tunda yau babu Samina a cikinsa anan zai warwasa abinsa=?"?.


&&&&&&&&&&&


Ina bakin rijiya zaune ina wankin ?arfin hali saboda kaina dake mani wani azabar ciwo, gaba Waya kwanakinnan haka nake fama da wannan ciwon kai, abinda kawai nasaka a raina basir ne yaymin mugun kamu da malleriya, sallamar yaran gidanmu ta sakani Wago idanu na kallesu, ni kaWaice dama a gidan, Kausar taje asibiti wai yaron cikinta na dawo mata a ?irji, maman Amatullah kuwa tana gidansu sunan ?anwarta data haihu, su Fa'iza kuwa tun da safema suka tafi gida yau.
Sallamarsu ta amsa fuskarta dai babu walwala.
 Ku kuma daga ina? Da wannan tsakar ranar khadija? .
 Yaya Rumana daga gida mukefa, Yaya Samina ce bata da lafiya tana asibiti .
Ajiye hijjab Win danake cuWawa a cikin ruwan kumfar nai ina faWin,  Ya salam, miya sameta haka? .
 Muma bamu saniba, amma dai su Ammi ma duk sunacan sunje dubata .
 Wayyo, to ALLAH ya bata lafiya, zan kira Yah Ahmad kuwa nasamu zuwa anjima naje na dubata .
Haka Rumana ta cigaba da wankinta su khadija na tayata da hira, duk da ma ita ba saka musu baki takeba dan kanta dake ciwo, da yake wankin baida yawa dan danan ta kammala, tana share ruwan wajen Kausar ta shigo tana Waga ?afa da ?yar saboda ciki, duk da yanzu bata min magana hakan bai hanani mata sannu ba.
 Uhumm kawai tace min ta buWe Wakinta ta shige.
Ban damuba, nima na haWa robobin danai wankin na nufi nawa Wakin, muna shiga na bama su Khadija kantu daya rage a kayan sana'ata nace suje gida kar'a nemesu, dan nagaji da surutunsu nikam.
Da murna suka amsa suka wuce, nikuma na shiga duba magani dan nasha sai dai ma ashe ya ?are, ?aramin tsaki naja na haye gado na kwanta kozan samu sassauci.

Ring Win wayartane ya tasheta daga nannauyan barcin datai nisa a ciki, ta kai dubanta ga agogon Wakin tana ?o?arin lalubo wayar a ?asan filo.
?arfe biyar na yamma, agogon ya nuna, tashi nai zaune a rikice dai dai na gama ciro wayan, Yaya Ahmad ne, kafin na Wagama ta tsinke.
Ina ?o?arin sakkowa ya sake kira, dakatawa nai na Waga ina kaiwa kunne.
 Kina lafiya kuwa? Tun Wazun nake kira amma babu amsa .
Cikin yanayin wanda ya tashi a barci nace,  Kayi ha?uri Yaya, wlhy barci nake .
Daga can yace,  Barci kuma? Lafiya dai ko? .
 Lafiya ?alau, kaina ne kawai kemin ciwo dan wankima na gama ..
 Na rasa wannan ciwon kai na miye haka? Kusan kullum yanzunfa sai kinyi? .
 Wlhy kuwa Yaya, amma karka damu inaga basirne, zan aika iya ta bani magani .
 ALLAH ya ?ara sau?i, yanzu kinsha magani ko? .
 A'a maganin ya ?are, jira nake anjima idan Yah Mudan yazo sai ya sayo mani .
 Bara kawai na kirashi sai ya kawo miki yanzun, ina zama da ciwo yaga daWi .
 To Yaya na gode, itama Yaya Samina ma bata da lafiya .
Shiru yay kamar bai jitaba, hakan yasa tai tunanin baijinba ta sake maimaita masa.
Cikin halin ko in kula yace,  ALLAH ya ?arama kowa lafiya .
 Amin yaya, ammafa abin serious ne fa, dan tanama asibiti, na shirya naje na dubota dan ALLAH? .
A hasale yaja tsaki yana faWin,  Malama kiji da naki ciwon kinji, inada abunyi sai anjima ?it ya kashe wayarsa.
Shiru nayi a wajen tamkar ruwa ya cinyeni, na zame wayar a hankali ina kallonta kamar zan hangosa ta ciki, dama tun jiya nasan haushina yakeji saboda su Fa'iza sunce zasuje gidan Yaya Samina, nima saina tambayesa dan naje nagano Wakin amarya daga nan mu wuce gidan sunan ?anwar maman Ama da akeyi.
Aiko naci masifa, dan Yah Ahmad na asali dana sani ya komamin, tamkar zai jawoni daga wayar ya daka, daga ?arshe ya kashe wayarsa ma baki Waya, na gwada kira yafi sau hamsin amma switch up, ni kuma yanzu sam banyi zaton abin zai ?ara Sata masa raiba tunda dai ciwo akace.
Damuwa fal raina na tashi na fita, dan ko sallar la'asar banyiba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login