Showing 210001 words to 213000 words out of 234058 words

Chapter 71 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

16975

"Mijin ki, mu xa mu wuce yanxu Iman, Allah ya bada xaman lafiya" khadijah ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku, me yasa baxa ku kwana ba don Allah kar ku tafi, ki bani wayar xan masa magana" dariya ta ba baby amma bata yi ba tace "Gobe fa da safe xan xo Iman" cikin kuka sosai Khadijah tace "Don Allah ki rufa min asiri ki kwana" Baby tace "In dai gidan nan ne wllh baxan kwana ba, gwara ki hakura gobe in dawo, idan kuma kika ban haushi in ki xuwa goben ma, ko a kauye an daina haka kina abu kamar wata yarinya..." Dariya kawai Hafsa take don khadijah ta bata dariyan, Baby ta mike ta hade rai tace "Mu je Hafsah, ji wani abu da take fa kamar yar yarinya, ko yara sun daina haka, balle ita wayayya" Da haka baby ta samu fa fita Hafsat na biye da ita, Ban da kuka babu abinda khadijah take tana kallon kofar har suka fita suka rufe, Baby ta ji tausayin ta har ranta, amma tasan idan ba haka ta yi mata ba sai ta iya ma biyosu, A waje ta tadda Aliyu tare da Sudais a tsaye jikin motar sudais din, da alama su suke jira, Baby tayi kasa da kanta tace "Ina yini yayanmu" yace "Lafiya lau" Hafsat ta gaida Sudais sannan ta gaida Aliyu tayi masa fatan alkhairi a aurensa, murmushi kawai yyi bai iya yace mata komai ba, Sudais yace "Alryt, sai da safe Dr" Aliyu ya kallesa a hankali yace "Baxa ka shiga ba?" Ya bude motarsa yana d'an murmushi yace "Gobe xan xo in sha Allah" Aliyu bai iya yace masa komai ba, can ya kalli Baby yace "Ku shiga xai yi dropping din ku gida" Ta d'an buda ido, Aliyu ya matso kusa da ita da damuwa yace "Did she know...." Baby ta girgixa masa kai a hankali, sauke idonsa kasa yyi, Hafsat ta bude back seat ta shiga, Bayan few seconds ya kalli baby yace "Don't keep him waiting, ki shiga motar ku wuce, sai da safe" A hankali baby tace "Yayanmu wllh kunyarsa nake, daxu da safe na gama tsigale shi a waya I never knew makirci matarsa ta hada masa" Aliyu ya bude ido yana kallonta, ta marairaice tana kallonsa, yace "Ki basa hakuri idan kin shiga motar" shiru tayi, ya gyada mata kai yace "Yea, do that" a hankali tace "Toh sai da safe yayanmu" daga haka ta xaga ta shiga front seat ganin Hafsat baya ta shiga Aliyu ya bi ta da kallo, Tana shiga motar ta rufe ta kasa kallon Sudais, bayan ya tada mota ba tare da ya kalleta ba yace "Good evening" sai a sannan ta kallesa dai dai nan shi ma ya kalleta, Murmushi tayi cike da jin kunya tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" a hankali tace "Am soo sorry for what I did daxu da safe don Allah kayi hakuri" kallonta yayi da kyau, sai kuma yyi murmushi yace "Wai dama ke kika kirani?" xaro ido tayi ganin ashe ita kadai ke ta haukanta shi bai ma san wa ya kirasa ba, wani murmushin ya kuma yi yana shafa kansa ya ja motar yace "I bet da muna kusa har duka sai kin kai min" sauke kanta kasa tayi bata ce komai ba. Tun da Aliyu ya shiga gidan gabansa ke faduwa, ya kashe wutan parlorn da kyar ya haura sama, ya fi minti daya tsaye kafin ya bude kofar bedroom din da khadijah ke ciki, tana xaune can karshen gado ta hade kanta da gwiwa tana shesshekar kuka, ya kasa karasawa cikin dakin, a hankali ya kai hannunsa kan switch dake jikin bango ya kashe wutan dakin, da sauri ta dago kanta, ya rufe kofar a hankali, cikin rawar murya tace "Barrister ka kunna plss..."

Lumshe ido Aliyu yayi jin sunan da ta kira lkci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya bude idanuwansa ya taka a hankali har ya isa gabanta, ja baya ta dinga yi xuwa lkcn ta daina kukan da take tsoro ne fal xuciyarta, ya xauna dab da ita har suna jiyo numfashin juna xata mike da sauri, yyi hanxarin rikota ta fashe da kuka jikinta na rawa, a hankali ya jawota jikinsa ya rungumeta lkci daya ta hadiye kukan da take, ya dinga jin yanda xuciyarta ke bugawa a kirjinsa kamar xai fito, lumshe ido yyi hawayen idanuwan sa suka xubo, cikin rawar murya tace "Barrister ka kunna wutan bana son duhun plss, switch the light on" Murya can kasa yace "Imannn" Ta fi second talatin muryar da taji na kai kawo a kanta, a hankali ta xame jikinta daga nasa tana kallon fuskarsa cikin duhun dakin kamar yanda shi ma yake kallonta a sanyaye, hannu ta kai fuskarsa tana masa wani kallo da kyar tayi gathering courage din cewa "Aliyu?" Rungume ta yayi kamar xai mayar da ita jikinsa cikin rawar murya yace "Yes Iman, I beg you... don't say no to me plsss, this our fate... na sha wahala kan ki a rayuwa Iman, na sha wahala fiye da tunanin ki, kashe ni ne kadai son ki bai yi ba, for good six years bani da kwanciyar hankali bani da walwala, forgive and forget the past plss, Barrister Aliyu..." Kasa ci gaba yyi bayan wani lkci ya ci gaba voice dinsa na breaking "I owe him... he gave up for me.... Ya bar min ke Iman, don girman Allah ki ji tausayina kar ki bani wahala...." Kamar warce aka yi moulding haka khadijah tayi stiff jikinsa maganganunsa na mata yawo a kai, she's still trying her best to apprehend all what he is saying, Jin tayi shiru ya dago kanta jikinsa na rawa, hawayen dake makale idonta suka xubo tana kallonsa, ta fashe da wani matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma wa da sakon mutuwa, sauka yyi saman gadon a rikice ya durkusa kan gwiwowinsa kusa da ita yace "Iman kiyi ma girman Allah kada ki wahal da ni, I have already had enough, don't say no to this marriage, kar ki ce A'a Iman...." Kasa ci gaba yyi.... A hankali tayi baya ta fada saman gadon, ya mike da sauri ya riketa yana kiranta amma tuni idanuwanta suka rufe, ya dago ta ya rungume ta hawaye na sakko masa yace "Why Iman, kin yi saurin mance alkhairin da na maki a rayuwa, sharrin kawai kika bari a ranki, ba laifina bane, ba yin kai na bane, ni ba maxinaci bane, duk xaman ki gidanmu ban taba tunanin akwai ranan da xai xo in cuce ki ba...." Kasa ci gaba yyi ya runtse ido yana rungume da ita har sannan. Sai kusan karfe hudu saura na asuba khadijah ta bude idanuwanta a hankali, Aliyu da ke xaune kan darduma ya mike da sauri ya iso kusa da ita yana kallonta da damuwa, mikewa take kokarin yi tana kallon jikinta, riga ce mara nauyi jikinta maimakon atamfar da ta sa tun a gida, Aliyu ya xauna gefen gadon a sanyaye yana kallonta, kokarin sauka ta shiga yi daga kan gadon yana son riketa amma yana tsoron abinda xai biyo baya, cike da karfin hali yace "Iman you are not strong ina xa ki, Wait..." Bai san lkcn da ya riketa ba ganin tayi baya xata fadi, xai kwantar da ita ta kwace kanta tace "Let me" Dafe kansa yyi, ganin xata sake tashi ya kara rikota, tura hannunsa tayi muryarta na rawa tace "Dole sai ka rike ni ne, nace bana so" ko saurarenta bai yi ba ya ki saketa, ta fashe da kuka tace "I want to use the restroom ka kyalenii...." Tashi tsaye yyi ya dagota ya nufi bayi da ita, suna isa bayin ta kwace kanta ta shiga ta rufe kofar, a hankali ya koma gefen gado ya xauna duk jikinsa a sanyaye, tana fitowa ta nufi kofar fita ya mike da sauri yace "Iman" ganin ko juyowa bata yi ba ya karasa da sauri kafin ta isa kofar ya rufe ya marairaice yana kallonta, Xaunawa tayi nan bakin kofar ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka xuciyarta yayi rauni ga wani xafi da yake mata, yanxu dama duk yaudararta Sudais yake, me yasa xai ci amanarta ya sa a aura mata Wai Aliyu?? Of all people why Aliyu? The beginning and end of her problem, the person that shattered her life, me yasa xai sa a aura mata shi, ta dinga kuka a raunane taji duk duniyar ya isheta, gaba daya ji tayi haushin kowa take har Umma don tasan ita ma ta sani amma ta boye mata, a hankali Aliyu ya sa key kofar ya cire a jiki, Jin haka ta mike a mugun fusace hawaye na sakko mata xuciyarta na bugawa tace "Malam ka bude min kofa in fita.... Bana son ganin ka, bana so...." Bai bari ta kai karshe ba ya jawota jikinsa ya rungume ta ya lumshe ido, duk iya kokuwan da ta dinga yi xata kwace kanta kasa wa tayi daga karshe ta hakura ta dinga kuka, a hankali murya can kasa yace "Plss, tell me how many days will it take you to finish this drama?" Dago kai tayi tana masa wani kallo xuciyarta na heaving, a sanyaye yace "I just want to get prepared... Just tell me for how long it will take you to finish it? And in sha Allah I will endure" fuskarta daure tace "Sake ni" a hankali ya saketa ta koma baya ta mika masa hannu tace "Bani makullin" ya mika mata makullin hannunsa, ta juya ta bude kofar ta fice tayi banging din kofar, Ya d'an tabe baki ya juya a hankali ya koma kan gado ya kwanta don har wani ciwo kansa ke yi masa baccin da bai yi ba, har aka kira Asuba bai bari bacci ya daukesa ba ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito don wucewa masallaci, kwance ya ganta kan 3 seater a parlor tana bacci ta dunkune waje daya saboda sanyin parlorn, ya kashe A.c sannan ya nufi kofa ya bude ya fita. Ko da ya dawo masallaci bai ganta parlorn ba kuma, ya wuce sama ya bude kofar dakinta a hankali yana leka ciki ya ga bata nan, juyawa yyi da sauri ya bude wani dakin, xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta jikin bango, tana ganinsa ta daure fuska ta cinno baki gaba, a hankali ya rufo mata kofar ya shiga nasa dakin ya kwanta, sai a sannan bacci ya daukesa. Sai da gari ya fara wayewa khadijah ta mike jiki ba kwari daga kan darduman da take xaune ta bude kofar dakin ta fito, dakinta ta bude a hankali tana kallon ciki, ganin babu kowa ta shiga ta rufe kofar, bathroom ta shiga tayi wanka ta fito, bayan ta shirya ta kwanta saman gado jin kanta na ciwo sosai, bacci ne ya dauketa daga haka, Bata farka ba sai da aka danna bell a kasa, ta mike xaune da kyar tana kallon agogo, har sannan kanta ciwo yake ba kadan ba, karfe tara saura ta gani, ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta sa ta fita, a hankali ta bude kofar ta ga Baby tsaye rike da basket din abinci tana murmushi tana kallonta, khadijah ta hade rai sosai ta juya ta koma parlor, Baby da ta bi ta da kallo a xuciyarta tace kya yi ki gama ne ma, A nan parlor ta ajiye basket din ta juya xata fita khadijah ta bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar sai a sannan baby ta fara dariya kasa kasa, khadijah da ta bi ta da kallo ta xauna kujera lkci daya hawaye ya cika idonta ta ji kamar ta bi ta ta mata magana amma ta kasa tashi, wato dai ita ma tasan wanda aka aura mata amma bata fada mata ba, tashi tayi ta wuce sama ta shiga daki ta fada kan gado tana kuka takaici, bayan wani lkci ta mike ta dauko wayarta ta shiga kiran Sudais, sau uku tana kira bai dauka ba, ta ajiye wayar tana share idonta ta kwanta xuciyarta ba dadi, ta jima kwance jin ciwon kai ya isheta tana son shan magani ta mike a hankali ta fito, downstairs ta sauka taga abincin da baby ta kawo na nan yanda ta ajiyesa, ta kalli agogo ta ga har sha daya ya kusa, sama ta kalla, ta fi minti biyar tsaye kafin ta nufi kofar da take xaton kitchen ne ta shiga ta dauko cup da spoon, shayi ta hada ta koma kujera ta xauna, kasa shan shayin tayi ta ajiye cup din hannunta a hankali ta wuce sama, dakin da take tunanin nasa ne ta bude a hankali, kwance ta gan sa kan gado idonsa a rufe, ta dinga kallonsa kafin ta karasa ciki kamar mai tsoron taka tiles din ta isa har kusa da shi ta duka, Bbu wanda ya fado mata a rai lkcn sai little Sudais, lkci daya taji jikinta yyi sanyi ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, lkci daya ya bude idanuwansa ta mike da sauri tana kalle kalle kamar mai neman abu duk ta daburce.....

Aliyu ya mike xaune yana kallonta yace "Did you come to check on me?" Ta tsuke fuska tace "Saboda kai Shureim ne?" Ya shafa kansa bai ce komai ba, ta juya da sauri ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice, sai a sannan ta ja tsaki taji haushin shiga dakin da tayi, parlor ta koma ta dau shayin da ta hada, da kyar take sha don gaba daya bakinta ba dadi, ji tayi kamar xata yi xaxxabi, ta mike ta dau sauran kayan kumallon ta kai dining ta ajiye ta wuce kitchen don wanke cup din shayin ganin baxata ta iya sha ba, xata ajiye bayan ta wanke taji kamar mutum bayanta ta juya da sauri suka kusa cin karo suna hada ido ta hade rai ta dauke kai, ya mika mata hannu a hankali yace "Bani cup din" tace "Saboda xaka amsa cup sai ka tsaya bayana toh" Bata jira me xai ce ba ta ajiye cup din ta fita kitchen din ya bi ta da ido. Har aka yi azahar bata kara fitowa daga dakinta ba, xuwa lkcn ta fara jin yunwa sosai amma ta kasa sakkowa, duk xaman dakin ya isheta, tana ta xuba ido taga kiran Umma amma shiru, ga kewar Shureim da ya cikata, duk abubuwan suka taru suka mata yawa, ta hade kai da pillow tana son yin kuka amma ta kasa. Aliyu na xaune parlor yana duba wasu articles bayan sun yi waya da Sudais yace masa suna hanya, saboda su ma ya dawo parlorn ya xauna, ajiye takardar hannunsa yyi ya dau pain reliever a center table for the second time in 2hrs ya balla biyu ya dau table water dake ajiye ya sha maganin ya mayar da ruwan ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, ya rasa me yasa bai samu relieve ba bayan wanda ya sha daxu, har ya fara bacci a haka ya ji an danna bell, ya bude ido ya mike ya isa kofar ya bude, Baby ce rike da lunch, ganinsa tayi murmushi tace "Yayanmu Ina yini?" Ya shafa kai a hankali yace "Lafiya lau" da damuwa tace "Are you sick?" Ya d'an bude ido yace "Me kika gani?" Tace "You look so" murmushi yayi yace "Am alright" Bata ce komai ba ta shigo parlorn cike da tausayinsa ta ajiye abincin hannunta ta juyo tana kallonsa tace "Ka ma yi breakfast kuwa yaya?" Yace "Nayi mana, ya su Mumy" Xaunawa tayi tace "Suna gaishe ku" ya xauna shi ma yace "Ki kai mata abincin sama" xaro ido baby tayi tace "Uhn ba ruwana, I don't want to imagine me going to her now" Aliyu bai ce komai, tana kallonsa a hankali tace "You just have to be patient ya Aliyu, soon nasan xata hakura... Kar ka damu kaji yayana, I know it's just for few days" Murmushi yayi yace "Toh Allah ya sa" cike da tausayin sa tace "Ameen" yace "Plss ki taho da Shureim idan xa ki xo anjima...." Tace "Ae yana can gidansu" yace "Ehh ki dauko sa can din, I am lonely..." Tace "Toh Yaya xan kawo sa" Wayarsa ne yayi ring ya dauka yaga Sudais ke kiransa, yyi pick din call din Sudais yace "Muna waje" Aliyu yace "Alryt ku shigo" Baby na kallonsa bayan ya katse wayar tace "waye yaya?" Yace "Barrister with Dr Ayman I guess" Baby tayi shiru bata ce komai ba, bude kofar parlorn aka yi khaleel ya fara shigowa kafin Sudais, Aliyu ya mike bayan sun gaisa gaba daya suka xauna, Baby na kallon Dr Ayman tace "Ina yini" yace "Lafiya lau ya kike?" Tace "Alhmdllh" kallon Barrister tayi dai dai lkcn da ya kallota shi ma, yace "Ina yini" xaro ido tayi sai kuma tayi dariya tace "Ina yini" yace "Ohk I was thinking baxa ma ki gaisheni ba" Khaleel yayi murmushi yana kallonsa ta gefen ido bai dai ce komai ba, Aliyu ya kalli baby don tsoron xuwa daki gun khadijah yake yace "Baby talk to her tana daki" Mikewa baby tayi ba don tayi niyya ba ta wuce dakin gabanta na faduwa, Khadijah dake kwance ta daga kai jin an bude kofa, ganin baby ce ta mike xaune tana kallonta, a sanyaye tace "Shine daxu baki min magana ba kika wuce ko Baby" Baby tace "Hmm tsoron ki nake ai ni Iman" Baby ta xauna kusa da ita, khadijah ta kamo hannunta a hankali tace "Amma baby kin san wanda aka aura min kika boye min, idan kowa ya boye min ke bai kamata ki min haka ba, Ni yanxu shkkn cikin kunci xan kare rayuwata, nobody is after my happiness...." Hawaye cike idonta ta kare maganar, a sanyaye Baby tace "Nan gaba xa ki gane ma'anar hakan da aka yi Iman, just give my brother a chance... Iman ki manta abinda ya faru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login