Showing 135001 words to 138000 words out of 234058 words
da babu abinda xai hanasa jawota jikinsa tayi bayanin abinda take nufi, dariya kawai khadijah take tana kallonsa, khaleel ya kasa cewa komai, kawai ya 6uge da shafa lallausan bak'in gashin kansa, ta sata kallonsa ta sake kyalkyalewa da dariya, yyi murmushi ya cire glass din idonsa murya can kasa yace "Xa ki yi bayani ai xa mu koma UK din" ta hade rai tace "So?" Yana murmushi yace "Nothing, ki gaya ma Umma xa mu je shopping da su sudais plss har da ke" khadijah da bata sake kallon fuskarsa ba tace "Noo ban da ni" yace "Plss" tace "Ni baxan je ba da gaske, su dai ka tafi da su" da kyar da kyar khaleel ya lallabata bayan ta sa ya rufe idanuwansa da glass din da ya cire sannan ta yarda xata bi su, amma bayan ta gaya ma Umma idan xata yarda, ganin tare da su sudais ne Umma ta yarda suka tafi bayan tace kar su dade, front seat ya bude ma su Shureim suka shiga, ganin haka ta bude back seat ta shiga, sai da suka yi nisa khaleel yace "Mu je ki gaida mum dita nima, it's just malali here ba nisa...." Da sauri khadijah tace "Noo plss, sai in je a wa?" Yana kallonta murya can kasa yace "A surkarta to be" shiru khadijah tayi ta na kallonsa da mamaki, ya mayar da dubansa kan titi yana driving, da sauri tace "Noo, sae dai a matsayin friend dinka, and am not ready for that Dr don ban ce ma umma xan je ko ina ba daga inda kace xaka kai mu" a hankali yace "Ohk then, amma xa mu biya gidansu jawaheer mu dauketa, I think she wants to shop also" kallonsa Khadijah ta tsaya yi ta ma rasa abinda xata ce masa, ai ko suka isa anguwarsu jawaheer din yyi parking ya dau waya ya kirata yace yana waje, khadijah tayi karfin halin cewa "Toh su sudais su dawo baya" Khaleel yace "Noo xata xauna baya ita ma, no probs" Ba a dau lkci ba jawaheer ta fito, she is a real definition of black beauty, kyakkaywa ce ita din ta karshe, ta bude front seat tace "Sweetheart ashe da gaske xaka xo din" ganin su sudais da Shureim ta wara ido tace "Waoww cuties, ina ka samo su swthrt? They are so cute" gaisheta yan biyun suka yi, duk ta yi masu kiss a goshi, Khaleel dake kallonta yace "Yarana ne" dariya ta yi tace "Kai dear, don Allah waye su, sun min kyau wllh" ya kalli khadijah ta madubi yace "Ga Aunt dinsu a baya nan" sai a sannan jawaheer ta kalli baya da sauri tace "Ohh ban lura ba, hello" Khadijah tace "Hi" jawahir na murmushi tace "You've got sweet siblings" murmushi khadijah ta kirkira, kamar baxa ta ce komai ba sai kuma murya can kasa kamar ana tilastata tace "Thanks" jawahir ta bude bayan motar ta shiga ta rufe khaleel ya ja motar suka bar wajen, ta madubi yake ta kallon khadijah da ta kauda kai tana kallon waje, ita kuma jawahir na ta basa labari da siririyar muryarta da ya cika motar. Farouq dake ta kallon Aliyu da d'an mamaki yace "Ko meye dalilin da yasa kake son sanin sa Dr?" Aliyu ya hade rai yace "Idan xaka gaya min ka gaya min" Farouq yace "He is my good friend, tare muka yi karatu a England degree and masters, his mum from Saudi Arabia, the most simplest woman I have ever known, his dad a Nigerian from kano, shi kadai ne namiji gidansu with 4 siblings duk mata, Dr Ayman ba shi da matsala, he is free with everyone sai dai he don't make friends easily, he is a genuine... He was among those that graduated with d best result during our time, yanxu haka PhD dinsa yake a Uk..." Katse sa Aliyu yayi yace "Am not asking you about his life history or how intelligent he is, ina gidansu yake?" Farouq ya dinga kallonsa da tuhuma kafin yace "I don't think i wil tel you that Aliyu" murmushi Aliyu yyi yana shafa beard dinsa.
Tun da suka shiga shopping mall din Khaleel ke kallon khadijah ganin yanda ta daure fuska, duk yanda khaleel yayi da ita ta dauki abubuwan da take bukata nuna masa ta yi bata bukatar komai, Jawaheer da twins suka dinga daukan abinda suke so a gun, khaleel dai na biye da su a baya, xagawa Jawaheer tayi gun chocolates da biscuits duk wanda yaran suka dauka ita ma sai ta dauka, khaleel dake ta kallon khadijah bayan jawahir ta bar wajen yace "Wait, wai me yasa baxa ki dau komai ba Khadijah, or did I offend u in any way plss?" Khadijah ta tabe baki ba tare da ta kallesa ba tace "To lallai ne sai na dauki abu a mall? Kuma don ban dauka ba sai ya xamanto anyi offending dina? Am not just interested" Shiru yyi yana kallonta, a hankali ya juya ya bar ta tsaye gun ya koma gun twins da jawahir, nesa da su wani mutum ne tsaye yana dauke da wata yarinya da baxata wuce shekara uku ba an mata kitso irin na yara gashinta har kusan bayanta, kusa da shi kuma wata mace ce rike da trolley tana xuba kayan da ta dauka, kallon su Shureim kawai yake ko kiftawa babu, har sai da matarsa dake gefensa tace "Barrister mu je mana" sai a sannan yyi saurin dauke idonsa kan yaran ya bi bayan matarsa, ya sake juyawa yana kallon yaran da khaleel ke rike da hannunsu har ya bar wajen ya daina ganinsu, khaleel ya biya kudin abubuwan da suka siya yana kallon khadijah da ke bakin kofar fita tana jiransu, ganin kallon da yake mata ta dauke kai da sauri dai dai lkcn da idonta ya sauka kan barrister sudais dake tahowa rike da kyakkyawar daughtern sa, matarsa na biye da shi tana rike da ledan siyayyar da suka yi, still Khadijah tayi a gun da take tsaye taji komai nata ya tsaya cak, yanda take kallonsa shi ma haka yake kallonta ko kiftawa babu har ya iso dab da ita ya sauke idonsa kasa ya mika ma security dake bakin kofar receipt din kayan da ya biya aka mayar masa sannan ya fita mall din, matarsa na biye da shi.
Khadijah ta bi sudais da kallo cikin shock sosai, fita tayi da sauri tana ci gaba da kallon sa xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya juya bai san ta fito ba suka kara hada ido yayi saurin dauke kansa, motarsa ya nufa ya bude, matar ta bude back seat ta ajiye ledan hannunta sannan ta bude seat din gaba xata shiga ta dakata da sauri tana kallonsa tace "Lahh Barrister na bar masu wayata a counter..." Bata jira cewarsa ba ta juya da sauri ta koma mall din, Sudais ya kara daga kai ya kalli khadijah, bata san lkcn da ta nufesa ba tana kallonsa ta fashe da kuka sosai cikin raunin murya tace "Why are you pretending you don't knw me? Did I deserve that Sudais.... Me yasa kake yin kamar baka taba sanina ba" sosai hawaye ke xuba idonta, Ya kasa kallonta ya kuma kasa cewa komai ba, ganin Jiddah na fitowa mall din ya sa ya shiga motarsa ya rufe, gwiwa a sake Khadijah ta koma baya tana kallonsa ko kiftawa babu kai kana ganinta kasan she is over shock, Tun daga nesa jiddah ke kallon khadijah da tayi saurin share idonta, har ta iso tana mata wani kallo daga sama har kasa tace "Baiwar Allah, do you have any problem? Tsayuwar me kike a nan" Khadijah bata kalleta ba ta juya da sauri ta bar wajen ta koma can jikin wani mota xuciyarta na mata xafi, ta fashe da wani matsanancin kuka, me yasa ko da yaushe a cikin mall take haduwa da abinda ke mugun daga mata hankali, yau ga ta ga sudais yyi kamar bai taba sanin ta ba, me tayi masa xai mata haka, ta sulale wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, bata yi deserving yyi mata haka ba da ya bari ko godiyar abinda yyi mata a rayuwa ta kara masa don tasan baxa ta iya biyansa ba kuma ba lallai su sake haduwa ba. Jiddah na shiga motar ta kalli sudais fuska a murtuke tace "Wacece ita Aliyu?" Buda hannu yyi alamar bai sani ba, ganin kallon da take masa yace "Kawai ce min fa tayi in ara mata waya xata yi making call, ni kuma nace bani da airtime, that's all madam" tsaki jiddah tayi cikin bacin rai tace "Da ta fada a gabana in koya mata hankali yau wllh, irin yan iskan matan nan ne masu bin maxajen mutane a titi, banda haka ta baka ajiyar kati ne xata ce ka ara mata waya?? dear idan baka son matsala da ni wllh ka bar ko da responding wa ennan mutanen, idan xa su shekara suna ma magana kar ka ko da kalli inda suke balle ka bude baki ka basu amsa ka xama kamar deaf and dumb, domin kuwa yawancinsu da asiri suke xuwa, ni dai na gaya maka kada a fara jin kan mu kuma" "Toh" kawai Sudais yace ya tada motarsa ya bar harabar mall din tana ci gaba da mita, Khadijah taji xuciyarta ya mata nauyi ta dinga kuka ko xata samu relieve amma kamar ana kara mata ciwon da take ji, babu irin neman da khaleel bai mata cikin mall din ba amma bai ganta ba, jawahir ma sai dube dube take tana neman ta, atm dinsa ya mika ma jawahir yace "Dear gashi you pay the bill" tace "But the pin?" Fada mata yyi ya fita mall din ta bi sa da kallo a sanyaye, little Sudais na kallon jawahir yace "Anty ba mu ga Antynmu ba" jawahir ta duka tana masu murmushi tace "Yanxu Dr xai nemo mana ita cuties" daga haka ta mike ganin an xo kanta a gun biyan kudin. Tafiyar few minutes sudais yyi ya tsayar da motar, Jiddah dake kallonsa ganin yanda ya ja tsaki tace "Ya aka yi Abban Amira?" Ya d'an dafa kansa yace "Wannan matsalar dai da nace maki motar ta bani last week, I don't knw what's wrong with this car" tace "Yanxu baxai tashi ba kenan?" Yace "Sai wani ikon Allah, gashi ban san ko Ahmad na garage ba da na kirasa ya taho yanxu... Am just bored of this car" ta hade rai tace "Toh ni ya xa muyi yanxu ga ranan yamma" ya kalli cute angel dinsa me suna Khadijah yana kiranta da Amira ya ja hancinta ganin yanda take kallonsa da kwala kwalan idonta yace "Kar Amirata ta sha wahala bari kawai in tsayar maku da adai daita ku wuce gida ni xan taho daga baya" Jiddah tace "Wai to ka kara gwada tada motar mana, ba girman ka bane barrister a gan ka bakin titi mota ta lalace" Murmushi yyi ya bude motar ya fita ya tsayar da adai daita ya gaya masa sunan anguwar su sannan ya xaga ya bude motar yana kallon jiddah yace "Ki fito ku wuce yanxu xan taho nima in sha Allah" ta hade rai tace "Aa mu je gaba daya kawai, ai babu me satar motar idan ya so sai Ahmad yaje gida ya karbi makulli ya lallaba ya kai motar gareji" kallonta ya tsaya yi kafin yace "Plss be a good wife and humbly come down kinga na tsayar maku da d'an sahu, you don't worry about me I will be okay sai kace ba namiji ba" da kyar ya lallaba ta ta sauka ta shiga napep din ya mika mata Amira da kayan da suka siya a supermarket, yana tsaye har napep din ya sha kwana sannan ya shiga motarsa da sauri ya tada yyi reverse ya koma mall din at high speed kamar xai tashi sama. Babu irin duban da khaleel bai ma khadijah ba a haraban Shopping complex din, har yyi give up a xaton sa gida ta wuce sai dai kuma haka kawai ya ji ransa ya baci, ya juya kenan xai koma ciki ya hangota durkushe bayan mota, da mamaki ya dinga kallonta lkci daya ya isa gabanta ya durkusa yace "Me ya faru Khadijah me kike yi a nan?" Ta kasa cewa komai sai shessheka take hawaye na sakko mata, a rikice yace "Ki min magana don Allah khadijah, me ya faru" ganin ba shiru xata yi ba ya daga ta ya nufi gun motarsa bai damu da mutanen dake kallonsu a gun ba ciki har da jawahir da ta fito da su shureim ya bude back seat ta shiga ya rufe, Sudais ya taho gun khaleel da sauri hankalinsa tashe yace "Uncle what's wrong with my Anty" Daukan sa Khaleel yayi yana murmushi yace "She is having a headache" kokarin sauka ya shiga yi a jikinsa kamar xai yi kuka yace "Uncle ina son in xauna kusa da ita I don't like d front" bude masa bayan motar khaleel yyi ya shiga sannan ya rufe, shi dai shureim na tsaye can kawai ya fashe da kuka, jawahir ta duka tana kallonsa da mamaki tace "Me ya faru handsome" Khaleel na ganin haka ya karasa ya daukesa shi ma ya bude back seat din ya xaunar da shi sannan ya rufe, jawahir dai na tsaye tana kallonsu ya bude mata front seat ta karaso ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver, Khadijah ta hadiye kukan da take da kyar ganin yanda yan biyunta suka rikice su ma suna kukan tana yin shiru su ma suka yi shiru, khaleel sai kallonta yake ta madubi duk ya ji ba shi da nutsuwa kamar ya jawo ta jikinsa ya lallasheta, Jawahir ma sai kallon khadijah da yaranta take, Khaleel na fita mall din da motarsa sudais ya shigo shi kuma da tasa motar, ko parking din kirki bai yi ba duk da maganar da securities din gun ke masa ya wani rikice ya dinga duba nook and cranny din wajajen yana nemanta har ciki sai da ya shiga amma babu khadijah, ya fito jikinsa a sanyaye ya hade kansa da motar sa.
Khaleel ya fara ajiye jawahir a kofar gidansu, yana lura ranta bai so ba ta bude motar ta fita da kyar ma ta dau ledan siyayyar da tayi kamar baxa ta dauka ba, ko sallama bata yi masa ba ta dai daga ma su sudais dake kallonta hannu ta wuce ciki abun ta, ya lumshe ido ya bude sannan yyi reverse ya bar layin, yana isa kofar gidansu khadijah ya bude motar ya fito sannan ya bude back seat yana kallonsu sudais da suka yi jigum kamar xa su shige jikin uwarsu, yyi murmushi yace "Toh ku fito" da taimakonsa suka sauko kasa ya basu ledojin yace su shiga ciki, Khadijah xata fito khaleel ya dakatar da ita, sudais dake lekanta yace "Uncle Anty bata sakko ba" khaleel ya shafa kansa yace "Xata sakko yanxu ku shiga ku kai ma Umma chocolates din ku ta ajiye maku" yaran suka wuce ciki suna yi suna waiwayowa, khaleel ya shiga motar yana kallonta da damuwa yace "Ki gaya min plss me ya sa ki kuka khadijah, is it me?" Girgixa masa kai tayi a sanyaye wasu hawayen na gangarowa idonta, ya kasa daurewa ya rungumeta yace "No plss I don't want to see you cry, it hurt me, don Allah ki gaya min meye matsalar ki, me ya sa ki kuka a supermarket?" Tayi lamo jikinsa taji ta kasa kukan kuma, duk kamshin sa ya cika ta, murya can kasa yace "Khadijah" a hankali tace "Uhn" yace "Kukan me kike yi?" Ta lumshe ido cikin sanyin murya tace "Sudais" still khaleel yyi na kusan 10 seconds kafin ya dake cike da karfin hali yace "What about him?" Har lkcn idonta a lumshe tace "I saw him" dagota khaleel yyi da sauri yana kallonta at first a bit shock, sai kuma ya hade rai yace "Where?" Ta ki kallon kwayar idonsa tace "A inda muka je shopping" da kyar ta ci gaba wasu hawaye na taruwa idonta tace "He shunned me, he pretend he don't knw me...." Kasa ci gaba tayi ta fara kuka a hankali, khaleel ya lumshe ido, jin ta a jikinsa kuma yasa tayi shiru, a hankali yace "Khadijah..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" dai dai kunnenta yace "forget about sudais plss, forget him...." Sai kuma yyi shiru, Khadijah taji kamar an xare mata radadin da take ji a xuciya, taji ta samu relieve, hankalinta ya kwanta fiye da xaton ta, murya can kasa tace "Toh, nagode" ji yayi kamar yyi kissing dinta but yyi controlling kansa bai yi hakan ba, har lkcn idonsa a lumshe yace "I... I know I love you from day 3 of our encounter....." Duk da yanda gaban Khadijah yyi mugun faduwa don bbu Wanda ya taba fadi mata wannan Kalmar duk tsawon rayuwarta hakan bai hanata fara tunanin me ya faru a rana ta uku da suka fara haduwa da khaleel a UK ba.
Khaleel ya dago kanta yana kallonta, tayi saurin rufe idonta, murmushi yyi murya can kasa yace "Kin tuna ko in tuna maki" dauke kanta tayi xata bude motar yace "Wait" still tayi a wajen bata yi motsi ba, yace "promise me baxa ki sake kuka a kan hanya ba, sannan you wil forget your past and face the future" shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Khadijah" ta gyada masa kai kawai, yace "Noo, say it out" bata san lkcn da tayi murmushi ba a hankali tace "Ohk" yace "Ohk kadai" kamar bata son ya ji ta tace "I promise" yyi murmushi yace "Yauwa baby" ta turo baki tace "Tana can kayi dropping dinta a gida" wara idanuwansa yyi yace "Wai jawahir?" Khadijah ta ki dago kanta, murya can kasa yace "Ita daban ke daban..." Daga haka ya bude side dinsa ya fita ita