Showing 51001 words to 54000 words out of 234058 words

Chapter 18 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17015

bayan Kyauta da sauri. Kyauta ta fixgota bayan sun shiga kitchen din ta ja kunnenta tace "Kin ga xaki fara ja min matsala koh? Da nace ki wuce daga kitchen ce maki nayi kije kiyi kallo??" Khadijah ta girgixa mata kai kamar xata yi kuka, kyauta ta nuna mata can wani gefe tace "Tafi ki je ki xauna wawiya kawai, dole ne sai kin yi kallo har wancan baxawarar xata dinga maki gori bata san at times condition ke sa crayfish yyi bend ba, banda haka uban me xai kawo mu gidan nan" khadijah tayi dariya har da kyakyatawa tace "Anty is crayfish bent?" Hararata kyauta tayi ta juya ta ci gaba da abinda take, a dinning kyauta ta jera lunch din duk me son ci a can xai je ya diba, ta dau wani katon roba ta kusa cika sa da shinkafa nama yayi takwas ta fita parlor tana leke leke, dawowa tayi da sauri ta mika ma khadijah tace "Maxa maxa tashi ki kai dakina da sauri ki ajiye a bayan kofa ki rufo dakin" khadijah ta mike ta karba abincin ta fita da sauri, har xata shiga daki ganin Aliyu ta tsaya, sai kuma ta nufesa har gun stairs tana nuna masa abincin ta tabe baki tace "Kaga Anty mai girki tace in kai mata abincin nan daki da sauri, may be she fetched all the food kila har da kai ma baxa ka samu ba, cos there is nothing left in the pot, I even saw when she was pouring water inside" Aliyu ya rungume hannunsa ya hade rai yace "Where did u knw me from?" Tana rike roban abincin da kyau saboda tiririn da yake innocently tace "In this house mana, I...." Turata yyi baya da sauri har sai da ta kusa faduwa shi ma ya koma baya ganin ta sake roban hannunta gaba da uban shinkafa da miyar da nama suka tarwatse kasan tiles har kan stairs, ta xaro ido ta toshe baki kamar xata yi kuka tace "Shikenan ka xubar... wllh bani bace ba kai ne ka xubar, ka xubar ma Anty mai girki abinci...." Kyauta ta fito da gudu daga kitchen jikinta na rawa jin karar faduwar roba kamewa tayi gun ganin khadijah can bakin stairs ga tulin shinkafa a xube kasa, xata koma kitchen suka yi ido hudu da Aliyu ta sake dawowa da gudu bakinta na rawa tace "Subhanallahi ta xubar, ban san baxata iya ba dama nawa ne da nata da nasu Usman..." Khadijah ta daga hannu da sauri tace "Noo Anty mai girki bani bace ba fa, shine ya turani baya kawai abincin ya fadi a hannuna" Aliyu ya tsallake abincin ya bar wajen, Kyauta ta koma kitchen da gudu ta dauko wani karamar roba ta dawo ta dinga kwashe shinkafar tana xubawa a babban roban, khadijah tace "Hope u are nt eating this any longer?" ko kallonta kyauta bata yi ba ta gama kwashe abincin ta kai dakinta da gudu ta fito ta shiga kitchen ta fito da sweeper, cikin yan mintuna ta gama gyaran gun ta goge, sai a sannan ta mike tana hararan khadijah tace "Ae yau sai dai yunwa ya kashe ki gidan nan, ba dai ni kika yi niyyar toxartawa ba? Yanxu da baxawara ce ta sakko ba bawan Allahn nan ba ya xan yi da raina?" A hankali khadijah tace "Kiyi hakuri" kunnenta ta ja tace "Baxan yi ba, sai kin gaya ma yan garin ku da yunwar cikin ki yau, little brat kawai" daga haka kyauta ta koma kitchen da sauri, khadijah ta langwabar da kai ta bi ta da kallo. Da kyar khadijah ke cin shinkafar tana yi tana kallon shi da kyau ko xata ga dirt a ciki, kyauta sai hararata take tana ci hankali kwance, Khadijah tace "But Anty mai girki me yasa baki xuba mana wani ba?" Kyauta tace "Kika sake ce min Anty mai girki sai na kalla maki mari, Anty mai girkin gidan ku, nace idan baxa ki ci ba ki dau naman ki tashi ki ban waje ni xan iya cinyewa, kila ma gidan da kika baki samun irin wannan xaki xo nan kina min iyayi" Khadijah ta xaro ido tace "The woman is always cooking concoction there, bata taba irin wannan abincin ba" Kyauta tace "Toh ki rufe min baki ki ci abinci yanxu yaran gidan xa su dawo daga makaranta" khadijah tace "Ohk" Jin shigowar mota kyauta ta bar ma khadijah sauran abincin ta mike da sauri tace "Toh gasu can... Idan kin cinye ki fito da roban kika kai kitchen" daga haka kyauta ta fita, yara uku ne suka shigo parlorn sanye da kayan makaranta daya kamar khadijah take tana jss3, daya kuma na ss1, babban cikinsu na ss2, khadijah ta fito rike da sauran abincin ta tsaya bakin kofa tana kallon yaran, Gaba daya dinning suka nufa ko wacce na cewa "Yaya ina yini?" Aliyu dake xaune gun ya amsa masu gaba daya, bbu warce ta gaida kyauta dake ta masu sannu da xuwa duk suka wuce sama, banda yar karamar cikinsu sa'ar khadijah, Kyauta ta washe baki tace "Yauwa sannu Anty khadijah ya makarantar?" Yarinyar da ita ma sunanta khadijah tace "Alhmdllh, kyauta who is that girl staring at us?" Kafin kyauta tace komai khadijah ta turo baki tace "I am not staring at you..." daga haka khadijah ta shige kitchen da roban hannunta, duk wannan abun Aliyu na kallonsu daga dinning, yarinyar ta juya da sauri ta tafi gunsa tace "Ya Aliyu who is she?" Ya kamo hannun Kanwar tasa yace "Ask mumy" yarinyar tace "Ohk" daga haka ta wuce sama kyauta na cewa ta na cire uniform tayi sallah ta xo ta karbi abincinta, kyauta ta bi khadijah kitchen ta jawota fuskarta daure tace "Ke fa ba ruwanki da yaran gidan nan naga har kin fara masu fetsara, ki tsaya a matsayin ki idan ba haka ba baxawara ta ishe ki"

Karfe hudu duk yaran gidan suka gama shirin tafiya islamiyya, kyauta ta hada socks dinsu gaba daya da Uniform din autar Mumy da ake kira da Baby saboda sunan Anty khadijah gareta xata wanke, kallon khadijah dake tsaye kanta tayi tace "Toh ni dai kin tsaya min kamar soldier ki tafi can dinning area ki kwaso duk plates din wajen, saura kar kiyi a hankali" khadijah tace "Toh" sannan ta wuce ciki, bbu kowa dinning area din sai plates da shinkafa da aka yi littering a wajen, Khadijah na ganin Anty khadijah a parlor xaune tana gyara ma Baby Hijab tayi saurin dauke kanta ta shiga hade plates din waje daya, muryar daya daga yan matan parlorn taji tana cewa "Anty wacece wancan yarinyar wai?" Anty khadijah ta tabe baki tace "The new housemaid" Baby ta xaro ido tace "Anty is kyauta going?" Anty khadijah tace "Noo she is not" Baby ta sauke ajiyar xuciya tace "Better... coz I don't think i like that girl, she can look for Africa as a whole" horn da driver yake yasa Siyama da Aneesah suka mike rike da jakar islamiyyarsu suka ma Anty khadijah sallama suka fita, Anty khadijah tace "She's not even worth talking to, don hka bbu ruwanki da ita yar aikin gidan ce kin ji takwara" baby tace "Sure" khadijah ta turo baki tana kallonsu, baby ta harareta ta fice daga parlorn, khadijah ta ki daukan komai a dinning din ta fita gun kyauta da gudu tana kumbure kumbure, kyauta tace "Ina kwanukan?" Ta fashe da kuka tace "Anty mai girki kinga yarinyar nan har da neman tsokanana koh, shine har da ce min I can look for Africa where as she was the one looking at me, kuma Anty mai ihu tace mata ni house girl ce" Kyauta ta tabe baki ta nuna mata wani dakali tace "Tafi can ki xauna, ni dai ba ruwana idan kina kallon yan gidan nan sai su dake ki ma su daki banxa nima ba kyaleni suka yi ba gwara babyn ma a cikinsu, idan ba iskanci ba... Ba aikin aka kawo ki kiyi ba har xa ki ji haushi don an ce maki house girl?" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, kyauta ta gama wankin ta tafi ta kwaso plates din ta gyara dinning din, khadijah ta hada ma kayan wanke wanken can bakin tap kar ta jika kitchen din ita kuma ta shiga girka dinner, da ta leka sai ta ga kamar ba a wanke wanken, daga karshe fixgota tayi bakin tap din ta turata waje daya ta shiga wanke wanken tana bala'i, khadijah ta toshe baki kar tayi dariya jin har da kiranta lazy ass, har kusan magrib khadijah na kusa da kyauta a kitchen komai kyauta ta sauke kan wuta sai ta ba buda mata hannu xata d'an d'ana tun kyauta na mata da mugunta tana konata da cokalin miya har ta gaji ta kyaleta sai ta xuba mata a d'an karamin plate, kyauta ta samu wani roba ta xuba duk pepper soup din da tayi mai yawa a ciki bata yi gigin ba khadijah ba tace "Tafi ki leka su waye a parlor" khadijah ta dawo tace "Ba kowa Anty mai girki" kyauta ta fita da sauri ta bude dakinsu ta ajiye masu bayan kofa sannan ta dawo ta jera komai kan dinning bayan ta ba khadijah na su Usman mai gadi ta kai masu, Kyauta na gama tsaftace kitchen suka wuce daki da Khadijah, sai a sannan ta xauna ta fixgo khadijah tace "Ke bakya sallah ne hala?" Khadijah tace "Ina yi amma bani da Hijab yanxu" turata bayi kyauta tayi tace "Ni ina da shi ai" Khadijah na xaune kan dankwalin da kyauta ta shimfida mata ta yi sllh tana ta kallon kyauta dake addu'a ta idar da sallahn ita ma, Muryar Mumy kyauta taji ta shafe addu'ar ta mike da sauri ta fita khadijah ma ta bi bayanta da sauri, Mumy tace "Ki xuba ma Aliyu abincin xai wuce aiki yanxu, ku kun ci abincin?" Kyauta tayi kasa da kai tace "Xan xuba masa yanxu Hajiya, mu kuma yanxu xa mu xuba" Mumy tace "Toh sai ki debar maku har da farfesun" Kyauta tace "Toh mun gode Hajiya" Mumy tace "Toh ya tana kokarin aiki kuwa ita?" Mumy ta fada tana nuna khadijah, kyauta tace "Ehh ba laifi Hajiya" Mumy ta juya tace "Toh shkkn" A dinning kyauta ta dibar ma Aliyu nasa abincin a plate ta xuba masa farfesun kaji sanin bai cin sauran, sama ta tafi kai masa khadijah ta biye da ita, ta kwankwasa masa kofa ba a dau lkci ba ya bude yana buttoning din shirt din jikinsa, kyauta tace "Ga abinci yallabai" kallo daya yyi masu ya karbi tray da kyauta ke mika masa yace "Nagode" khadijah tace "Nan ne dakin ka" bai ce komai ba ya rufe kofarsa, kyauta ta ja khadijah suka sauka ta shiga daki da ita ta hade hannayenta biyu tace "Ke wai dan gidanku ina ruwan ki da likitan gidan nan, kin taba sanin sa ne idan ba shisshigi ba?" A hankali tace "Kiyi hakuri" kyauta ta ja bakinta da karfi hade da dungurinta tace "Sai na cire maki wannan mayun idon naki wllh idan kika sake yi ma kowa magana a gidan nan" khadijah ta gyada mata kai hawaye cike idonta, kyauta ta fita ta bar jin alamar su baby sun shigo gidan daga makaranta. Ko kafin kyauta ta sallamesu ta dawo ciki har khadijah tayi bacci, tashin ta ta shiga yi ta ci abinci cikin magagin bacci take cewa Umma na koshi, kyauta ta debo ruwa ta yarfa mata a fuska, da sauri ta farka gaba daya kyauta ta ajiye mata abincin a gabanta ta shiga bayi don yin alwala, ko da ta fito Khadijah bata ci abincin ba ta koma bacci, hakan yasa tace "Ke kika sani" dagata tayi ta kwantar ta xauna cin abincin ita kafin tayi sallahn. Washegari kyauta na idar da sallah ta fita daura breakfast, ta gama fere dankalin turawa Anty khadijah ta shigo kitchen din, kalle kalle ta shiga yi kafin tace "ina wannan yarinyar take?" Kyauta tace "Ina kwana Anty?" Anty khadijah tace "Lafiya, ina yarinyar nace?" Kyauta tace "Na aiketa daki shiru shiru" fita Anty khadijah tayi ta bude kofar dakin kyauta tana yatsine fuska, kwance ta tadda khadijah shame shame kan gado, karasawa tayi ta maka mata duka har sau biyu a baya, khadijah ta farka a rikice, Anty khadijah ta fixgota tace "Ko yan gidan gaba daya ma sun tashi bare ke shegiya, a hakan xa ki iya aiki a gidan nan, a kirga har dubu goma a bai ma iyayenki jiya ki yi ma mutane shame shame kina bacci kan gado har yanxu?" Khadijah ta sauka kan gadon hawaye cike idonta tace "Anty kiyi hakuri" fixota Anty khadijah tayi ta turata waje da karfi tace "Fita kije ki kama ma kyauta aiki, ko ita din baiwar ki ce, ina ce yanda ake biyanta haka ake biyan ki kema" khadijah ta wuce kitchen da sauri tana hawaye, Anty khadijah ta biyota har kitchen din tace "Maxa hada wanke wanke ki fita ki yi" da sauri ta dinga fita da plates waje hawaye na sakko mata, ita dai kyauta bata ce komai ba har Anty khadijah ta fita kitchen din, khadijah ta dau cups uku xata fita da su, kyauta tayi tsaki tace "Mata ta ki xaman aure duk ta xo ta addabe mutane a gida tirrr, ke kuma ai kinga result din bacci kamar matatcciya" khadijah dai bata ce komai ba ta fita, Kyauta ce tayi wanke wanken bayan ta sallami yan makaranta khadijah na mata dauraya, karfe tara da rabi mumy ta sakko xata fita aiki, bayan sun gaisa da kyauta dake hada mata breakfast a dinning mumy tace "Ina khadijah" Kyauta tace "Tana can tana shara Hajiya" Mumy tace "Ohk" kyauta ta koma kitchen bayan ta gama hada ma mumy shayi sanin gimbiya na can sama tana ta bacci yanxu haka, Kallon khadijah tayi da tasa dankali da kwai da shayi a gabanta ta ki ci, Kyauta tace "Au baxa ki ci ba?" Khadijah ta kalleta tace "Ina ci" sai kuma ta fara kuka, Kyauta tace "Samun waje, wato duk da lafiyayyen abincin nan dake gaban ki har kuka kika samu daman yi koh? Kila ma a gidan da kika baro baki samun irin haka" khadijah ta mike tana kuka ta daga rigarta tana nuna ma kyauta bayan ta tace "Anty mai girki har yanxu fa xafi wajen da ta dokeni yake min" kyauta ta buda baki ganin shatin hannun Anty khadijah a bayanta, can tace "Tabdi, toh Allah ya isan ki, kuma in sha Allahu a baxawara xata Karachi rayuwarta, ni kam ko yanxu na bar gidan nan nasan xan samu mijin aure, ita kuwa wllh sai dai taga ana yi, kuma ina jin ita ma ta bar 'ya yanta a wani gidan to haka xa ayi ta cin ubansu ana gallaza masu in sha Allahu" Kyauta ta sauke rigar tace "Maganinki kenan kema dai, gobe ba sai kin jira an tashe ki ba" daga haka kyauta ta ci gaba da aikinta, da sauri kyauta ta fita jin mumy xata wuce gun aiki, ta gama sauraren abinda mumy ke ce mata ta risina tace "In sha Allah Hajiya, Allah ya tsare hanya" tsaye jikin kofa Mumy ta hango khadijah tace "How are you" a hankali khadijah tace "Good morning maa" mumy ta kalli kyauta tace "Anya baki cika ma yarinyar nan aiki kuwa kyauta?" Da sauri kyauta tace "Wallahi ko daya Hajiya, ki tambayeta bana cika ta da aiki" Mumy tace "Ohk" sannan ta mayar da dubanta kan khadijah tace "Am off to work, hope kin yi breakfast?" Ta gyada kai tace "Nayi Anty" Mumy tace "Good" daga haka ta nufi kofa, kyauta ta rakata tana mata Allah ya kiyaye, Mumy na fita da motar ta kyauta ta koma kitchen ta kwashi sauran kayan wanke wanke ta tafi wankewa a waje, khadijah na ta tsaye bakin kofar kitchen din Aliyu ya shigo gidan, tun da ta kallesa bata sake kallonsa ba har ya wuce sama, bayan kusan minti ashirin sai ga shi ya sakko, har lkcn khadijah na gun da take a tsaye, ya shiga kitchen din ya hada abinda xai hada a cup ya fito har ya wuce ya juyo ya daure fuska yace "Baki iya gaisuwa ba koh?" Ta turo baki tace "Good morning" daga haka ta juya ta wuce gun kyauta a waje, ya kusa second ashirin a tsaye kafin ya juya ya wuce sama. Ruwan wanka kyauta ta hada mata bayan sun koma daki, khadijah tace "Anty mai girki ni fa ban yi brush ba kika bani abinci" kyauta tace "Ni na hanaki brush?" Khadijah ta langwabar da kanta tace "Toh su fauxiyya sunyi lost din min brush dina a gidansu" kyauta tace "Oho dai tafi kinyi wanka ga ruwa can" khadijah na fitowa daga wanka kyauta ta bata Vaseline ta shafa sannan ta fiddo mata da daya daga kayan ta da ta linke bayan ta kwaso mata su jiya, khadijah tace "Anty mai girki kinsan wa ya siyo min new pants din nan" kyauta tace "Oho" khadijah tace "My lovely Umma" kyauta bata sake kula ta ba ta fixgota ta lafta mata uban kwalli a ido ta shafa mata farin powder a fuska sannan tace "Wuce can baya ki xauna kar ki shigo gidan nan sai na kira ki na gaji da surutun ki" khadijah tace "Toh" sannan ta fita, dakalin da ta saba xama ta xauna bayan ta tsinka flowers da yawa ta dinga yin jakar hannu da su kamar yanda aka koya masu a schl da dadewa, kamar ance ta daga kai suka hada ido da Aliyu dake kallonta, ta dauke idonta ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ta daga kai bata sake ganinsa xaune balcony din ba, gajiya da xama tayi ta shiga ciki ta bude kofar kyauta a hankali ta ganta kwance tana bacci, shiga tayi ita ma ta kwanta gefenta nan da nan bacci ya dauketa. Da yamma Mumy na xaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login