Showing 12001 words to 15000 words out of 234058 words

Chapter 5 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

16977

you guys meet him" Sudais yace "Shuraim will make u understand Anty" dai dai nan Shuraim ya shigo tare da Nanny, ya taho da gudu ya hau kanta, yace "I missed you Anty" ta daura lips dinta a forehead dinsa tace "but I've warned you to stop talking to strangers times without number.. I mean that man u were greeting outside" Ya xaro ido yace "I never knew he was a stranger, sorry Anty" tayi murmushi tana shafa kansa tace "But you don't knw him, so he is a stranger"

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨







_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻






8......

Sai a sannan Khadijah suka gaisa da Nanny tana tambayarta hanya da Umma, kitchen Nanny ta nufa xata daura masu ruwan wanka khadijah tace "Na riga na sa ruwan Nanny, bari xan masu" daga haka ta mike ta ja boys din xuwa Bedroom dinta. Wanka ta yi masu ta wanke masu baki ta sa duk suka yi alwala sannan suka fito, ta saka masu kayansu ta sa suka yi sallah, a tare suka ci abincin da tayi serving dinsu, Nanny da ita ma ta kintsa a daya bedroom din ta fito ta tarda su parlor ta dau abincinta da Khadijah ta rufe mata, nan su Shuraim suka dinga bata labarin abubuwan da ya faru a makaranta, ita dai ta tallabi chin dinta tana kallon kyawawan yaran with interest, Nanny ta shiga ciki ta kwanta ta bar su a parlorn, Shiddah saura Sudais ya 6ata fuska yace "Anty ba mu ci indomie ba fa yau" dariya tayi tana kallonsa sanin irin soyayyarsa da indomie gashi har da speaking din Hausa, which is rare kaji sun yi, ta mike tace "Toh bari in dafa maka Prince, in yi maka frying egg din or I shud cook it" yace "Cook" tace "Toh" Shuraim yace "No i prefer fried egg" tace "Alryt duk xan maku" daga haka ta wuce kitchen ta bar su suna kallon cartoon a parlorn, ta gama dafa indomien kenan tana xuba masu a plate kamar ance ta kalli waje ta tagar kitchen ta hango Shuraim tsaye kan study table din khaleel, khaleel din na tsaye gaban sa yana murmushi yana kallon sa, shuraim kuwa sai demonstrating yake da hannunsa yana masa magana, ta wani hade rai ta bude kofar kitchen din ta fita a tsawace tace "Me kake a wajen nan Shuraim, with whose permission ka fita" sosai yaron ya tsorata ya shiga kkrin sauka kasa, Khaleel ya saukesa ya juya yana kallon ta calmly yace "With my permission madam" ta wani kara hade rai, Shuraim ya nufo ta da sauri kamar xai yi kuka yace "Kiyi hakuri Anty" hanyar kitchen din ta nuna masa tana kallonsa sternly, ya shiga ciki da sauri, Khaleel ya shafa beard dinsa yace "Toh sannu me k'anni.. sai ki jira ki haifa naki tukun" ko kallonsa bata yi ba ta shiga ciki ta rufe kofar ta ta dau plates din indomie din ta fita parlor, duk a tsorace Shuraim yake, ta ajiye abincin hannunta tace "Zo nan" tasowa yyi ya nufota yace "Kiyi hakuri" tace "Wa yace ka fita?" ya girgixa mata kai yace "Ball nake nema" ta kara hade rai strictly tace "Ka taho da ball ne?" Nan ma ya girgixa kai a tsorace tace "Toh me mutumin yake gaya maka?" Yace "He is asking me my name and Sudais name, shine kuma yace wani class muke" kamar xai yi kuka ya kare, tace "Idan ka sake fita gidan nan I will flog you mercilessly, why can't u be like ur brother Sudais?" Sudais dake kwance yace "Na ce masa kar ya fita but he refused, I don't knw what's wrong with him" Ta ce "Ka dai ji me nace maka, ka sake fita kaga abinda xan maka" ya gyada mata kai, ta dau indomie dinsa ta basa sannan ta dau na Sudais ma ta mika masa. Ana magrib ta ja su suka wuce daki bayan sun gama waya da Umma, suna yin isha duk suka kwanta saman gado suna ta mata labari tana biyesu har bacci ya daukesu gaba daya, tayi murmushi sanin karfin hali ne irin na yaro kawai banda haka uban tafiyar da suka yi tun yamma ya kamata su yi baccin ma. Washegari bayan sun yi sllh brush kawai ta masu suka fito parlor da pyjamas dinsu misalin karfe goma ta kunna masu cartoon, tana kitchen tana girka breakfast taji duk suna kiranta, ta fito parlorn da sauri jin irin kiran, khaleel ta gani tsaye parlon ya daga Shuraim dake turjewa yana kiranta tare da d'an uwansa dake kkrin ganin ya sakkosa duk da hannunsa bai kai ba, Shuraim yace "Anty kinga xai tafi da ni, nace masa A'a...." Khadijah ta daure fuska ta dai rasa abinda xata ce, Daya hannun Khaleel ya sa ya dauki Sudais da ke jan sa ya sauke masa d'an uwa shi ma ya daga sa sama ya juya ya nufi kofa da su suna kwala mata kira, Nanny ma ta fito tana kallon ikon Allah, har ya fita da su Khadijah bata ce komai ba, Nanny tayi murmushi tace to fa sai kace dole, ita dai khadijah na tsaye har lkcn, bayan wani lkci taji duk sun yi tsit, komawa kitchen tayi ta ci gaba da abinda take bbu walwala. Ta kalli agogo yafi a kirga don kusan awa biyu kenan da ya tafi da su har yanxu shiru kuma ko motsinsu bata ji, kasa daurewa tayi ta mike ta yafa mayafinta ta fita waje, a hankali ta murda kofar parlorn, xaune ta gansu gaba daya a parlor sun sa shi a tsakiya yana game a laptop, Shuraim na kwance kusa da shi bakin nan har kunne yana cin Burger yana nuna masa direction din da xai bi a game din, Sudais kuma na daga gefensu yana cin indomie da kwai yana kallon game din shi ma, duk suka juya suna kallonta, Shuraim ya bata fuska ya mike da sauri yana cewa "Antyyyy.... Ya ki ya bar mu mu wuce" Sudais ya jefa masa wani kallo a hankali yace "Stop lying pls" Hauri Shuraim ya kai masa da kafa yace "u re calling me a liar" Sudais ya ajiye abincin hannunsa ya mike kamar jira yake, Khaleel yyi saurin janye Shuraim, hakan kuma bai hana Sudais kai masa naushi a baki ba, tana ganin haka ta karaso da sauri a rude ta durkusa tsakankaninsu ta rike Sudais tace "Fadan xa ku fara yanxu..." Cikin kuka Sudais yace "He started 1st, why will he kick me" Shuraim dake nasa kukan shi ma yace "Why calling me a liar" Kamar xata yi kuka take kallonsa tace "Ba kai ka fara kick dinsa ba shuraim" Duk wannan abun Khaleel dake rike da Shuraim din yana kallonta, bai san lkcn da yyi murmushi ba ya jawo Sudais yana kallonsu a hankali yace "Toh ku yi hakuri" Duk suka ki cewa komai sai kuka, ya rungumesu gaba daya yace "Ohk, I don't want to hear u both cry anymore" Sudais ne ya fara yin shiru sannan Shuraim, khaleel na kallonsu yace "To waye senior cikin ku?" Sudais ya nuna masa Shuraim, yace "Good, tell him u are sorry now" a hankali Sudais yace "I am sorry" Ya kalli Shuraim yace "Say it also" yana kumbure kumbure yace "But ai shi ya fara" Khaleel ya hade rai yace "Ba shi hakuri yanxu" a hankali Shuraim yace "Okay kayi hakuri" Khaleel yace "Good...." Kallon Khadijah yayi yace "You can't just come into my apartment babu notice bayan ke ma ba son a shiga naki kike ba malama" wani kallo tayi masa ta mike ta fice daga parlorn. Har yamma tana ta xuba ido ta ga shigowarsu amma shiru, ta rasa yanda xata yi, Nanny ta tura ta dauko su wai xa su yi wanka, ba a dau lkci ba Nanny ta dawo tace "Kinji wai sun yi wankan" shiru Khadijah tayi don ta rasa abun cewa. Tana kitchen tana girkin dinner ta hango boys din a waje gun da yake xama yayi karatu da alama tare suka fito ya koma ciki shi, don ga textbooks dinsa da eye glasses a ajiye, kofa ta bude da sauri ta fito tana masu wani kallo tayi masu alamar da su xo su shiga ciki, tahowa suka yi ta shigar da su kitchen gaba daya sannan ta shiga ita ma ta kulle tana hararansu, Shuraim ya nuna mata wayar hannunsa a hankali yace "Anty na shi ne" kwacewa tayi tace "Maza ku wuce daki, bana son ganin ku ko a parlor" obediently suka wuce kamar yanda tace, ta bude kofar ta fita don ajiye masa wayarsa, dai dai lkcn da ya fito waje, ta ajiye da sauri xata bar gun ya jawota, xaro ido tayi jin ta a jikinsa ta kalli kitchen dinta da sauri tace "Meye haka kake yi malam ka sakeni" a hankali yace "Me yasa kika kora su ciki" taki cewa komai, ya juyo da ita tana facing dinsa, kin yarda su hada ido tayi don ko kadan bata son idonsa, ta shiga kokarin kwace kanta, ya jinginar da ita da bango yana kallonta, turasa tayi da karfi tayi kitchen dinta da gudu ta tura kofar ta rufe, jingina tayi jikin kofar gabanta na faduwa, a xuciyarta tace "Wannan mutumin fa dan iska ne da gaske" Fita tayi kitchen din, ta sa Nanny ta karasa mata girkin, ta dawo ta xauna gefen gado a bedroom tana kallon yaran dake ta hada puzzles xaune kasan carpet din dakin, kallonsu take ko kiftawa bbu, lkci daya ta tafi duniyar tunani iri iri a xuciyarta, bata san sanda tayi wani murmushi ba wanda xa a iya kira da na takaici hawaye ya xubo idonta, ko kadan bata san yaran sun ga hawayen ba, duk suka taso Shuraim ya kamo hannunta da damuwa yace "Anty are you sick?" Da sauri ta girgixa kai tana share idonta tace "Noo, idona ke ciwo" Sudais da har idonsa ya kawo ruwa yace "Toh Anty me yasa" jawosu tayi jikinta jin wasu hawayen sun taho mata, ta rungumesu trying very hard to control her self tace "I will be okay soldiers, xae daina yanxu" shiru suka yi gaba daya, bayan wani lkci ta janyesu a hankali ta mike tace "Xan yi alwala" daga haka ta shiga bathroom tayi kukanta me isarta har taji xuciyarta yyi sanyi sannan ta fito, ganin duk sun yo kanta tace "Ku je kuyi performing ablution" ba musu duk suka shiga bayin. Da wuri duk suka kwanta bayan sun ci abincin da nanny ta kawo masu har dakin. Washegari da ya kasance Saturday, bata tashi da ko wani damuwa ba kafin karfe tara har sun yi breakfast ta yi ma su sudais wanka, ita ma ta shirya don so take su fita xuwa gidan Vanessa ta dau motarta ta xaga da su gari kamar yanda ta yi masu alkawari jiya kafin su yi bacci, tana parlor tana goge veil dinta aka bude kofar parlorn, ta dago tana kallon direction din, tsaye yyi bakin kofar ya rungume hannayensa idonsa a kanta, tayi saurin kauda kanta, ganin ita kadai ce parlorn yasa ta fara kame kame gashi kananun kaya ne jikinta, kofar kitchen ta kalla tuna su Shuraim da tayi, sai a sannan ta tuna tun daxu suka je ajiye cup din cornflakes da suka sha a kitchen shiru shiru basu fito ba, Nanny dama tana daki, ya karaso cikin parlon cikin tafiyarsa ta kasaita, ta mike da sauri xata shiga kitchen yyi hanxarin preventing dinta, ta daure fuska tace "Meye haka ni ka kyaleni" yana kallon lips dinta da lumsassun idonsa yace "You've got cute lips" xaro ido tayi xata fixge hannunta ya jawota jikinsa a hankali yace "Tafiya na xo yi da twins" ta hadiye abu da kyar cikin rawar murya tace "Stop it pls ka sakeni, ni bani kadai bace a gidan nan" yace "In tafi da su?" Kai ta gyada masa, duk da haka ya ki saketa, taji ta kasa tsayuwa, kamar xata yi kuka ta rufe ido tace "Ni ba yar iska bace na hadaka da Allah ka daina min irin haka" A hankali ya saketa yace "Nima ba d'an iskan bane, just living a free life, ko kin taba kamani da wata?" daga haka ya nufi kitchen ta bi sa da kallo xuciyarta na bugawa, Tare ya fito da su Shuraim, bai kuma yarda ta hada ido da su ba, don sai kakkaresu yake, su ma basu yarda sun kallo inda take ba sai shigewa jikinsa suke har suka fita ya kulle kofar, duk da bacin ran da take ji hakan bai hanata murmushi ba, tana jin fitar motarsa daga gidan ta tabe baki ta dau veil dinta ta wuce daki tayi kwanciyarta.


*Haske Writers Association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨






_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻







9......

Sai kusan karfe biyar din yamma Khaleel ya dawo da boys din, da kayan wasa suka shigo mata ko wannensu baki har kunne, kana ganinsu kasan they are just happy, ta ajiye handout din hannunta tana kallonsu ta nuna masu hanyar bedroom alamar su wuce ciki, basu mata musu ba suka wuce, mikewa tayi ta isa kofa ta sa makulli sannan ta bi bayansu, tsaye ta samesu sun yi tsuru tsuru, ta hade rai tana kallonsu gaba daya tace "Ku gaya min daxun da ku ka je ajiye cup a kitchen me ku ka tsaya yi?" Duk suka ki cewa komai ko wannensu a tsorace, tace "Ba magana nake maku ba?" Sudais ya kalli Shuraim sannan yace "Anty mun ga uncle a waje shine ya xo wajen window yace mu fito, ni nace A'a, sai Shuraim yace xa ki mana duka" daga haka yayi shiru, ta kalli Shuraim strictly tace "Sai me ya far kuma?" Shi ma kamar xai yi kuka yace "Shine sai ya tambayemu inda kike sai Sudais yace kina parlor" shiru yayi shi ma, ta rungume hannayenta ta kalli Sudais tace "What now happened after that?" A hankali yace "He told us to remain in the kitchen he will come pick us.... And, shine kawai muka gansa ya shigo ya tafi da mu" tana kallonsu da kyau tace "Good... Next time baxa ku sake xuwa wajena ba kuma xan fadi ma Mumy duk abinda ku ka yi tunda bakwa ji" hawaye su ka fara yi suna bata hakuri, bata bi ta kansu ba ta yi fitowar ta parlor. Ranar lahadi Khadijah na kitchen tana dama masu custard kamar yanda suka bukata taji an danna kararrawa, kusan a tare da Nanny dake masu wanki a bathroom suka fito, ganinta Nanny ta juya ta koma, ita kuma ta sa hijab ta iso gun kofar, a hankali tace "Waye..." Yace "Kin sani" k'in bude kofar tayi tace "How can I help you?" Yace "In bude kofar kenan da kaina" shiru ta yi na 'yan sakwanni kafin ta bude kofar, da sauri ta bar bakin kofar ganin shigowa xai yi kuma bai damu da cewar sai ya bugeta kafin ya shigo ba, yace "Where are they" ta hade rai bayan ta bar gun tace "Breakfast xa su yi" lkci daya duk suka fito daga dakin suka tsaya cirko cirko, sakin baki tayi tana kallonsu, arms akimbo ya tsaya kallonsu shi ma yana murmushi, can a hankali yace "Good morning boys" suka washe baki a tare suka ce "Good morning Uncle" yace "We've got 2 more places to go... So..." A hankali Shuraim yace "Noo we won't make it up" ya buda ido yace "Why" duk suka kalleta, Khaleel ya kalleta shi ma sannan yace "What about her?" a hankali Sudais yace "Aunt was angry at us yesterday, she promise not to let us come over again for holidays" Buda baki tayi tana kallonsu, Khaleel yace "Ohk, haka kika ce masu" ta hade rai ta kallesa tace "Ni bance masu haka ba, they misunderstood me" yace "Ohk to fahimtar da su abinda kike nufi ynxu" ta kallesu tace "Oya ku bi sa ku tafi" Shuraim ya kamo hannunta yace "Sure Anty?" Ta dake tace "Yeah" rungumeta suka yi gaba daya da murna suna ce mata thank you aunt, Khaleel ya kama hannunsu suka fita yana murmushi, banging kofarta tayi bayan fitarsu rai a bace. Ba su tashi dawowa ba sai da daddare don ita har ta kwanta sbda takaici gashi gobe xa su koma, wato ba gunta twins din suka xo yin hutu ba wannan karan kawai, Nanny ce ta shigo daki da uban ledoji ta mike xaune tana kallon ledojin, rungume ta boys din suka taho suka yi da gudu ko wannensu na kokarin expressing kansa ya bada labarin abubuwan da ya faru, sai kuma suka sauka kasa suna bude mata ledojin, mamaki duk ya cikata ganin uban abubuwan da ya siya masu har da kaya da abubuwan makaranta, haka ta saki baki tana kallon ikon Allah, Nanny kam sai yabawa take tana shi masa albarka, ita dai bata samu bakin cewa komai ba har Nanny ta ja su ta masu wanka, bayan ta shirya su xuwa rigunan baccin su tayi masu tayin abinci suka ce sun koshi, daga haka suka kwanta bbu bata lkci bacci yyi gaba da su, Nanny ta wuce dakinta, sae a snn Khadijah ta samu kwarin gwiwar sakkowa daga saman gado tana kallon tsaraban cike da mamakin yanda ya san gobe xa su koma, bata kwanta ba sai da ta gama hada masu duk kayansu da za su koma gida da, taji har ta fara jin kewan yaran gashi bata samu lkcn su yanda take so ba. Washegari kafin karfe takwas har ta gama shiryasu nanny ma ta shirya, tana kokarin fita kira masu taxi aka danna bell, lkci daya kuma ya bude kofar yana mata kallon cikin ido a hankali yace "Morning" sauke kanta tayi wondering anya yasan abinda yace kuwa, don gaisuwa bai taba hada su ba, "Same to you" ta mayar masa, a takaice yace "Yaushe xa su wuce airport din" tace "Yanxun xa mu wuce" yace "Alryt, ina jiran ku" ta bi sa da ido bayan ya juya. Shi ya kai su har airport din a motarsa duk da bata so hakan ba amma twins suka gwaleta, suna isa duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login