Showing 78001 words to 81000 words out of 234058 words

Chapter 27 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

16994

yi. Washegari da sassafe Anty khadijah ta shirya har da kwallarta take ce ma Mumy xata Abuja an kirata wai Yusuf d'anta ba lafiya yana asibiti, mumy jikinta yyi sanyi har da bata dubu goma ta hau mota, ta karba ta yi mata godiya ta bar gidan. Karfe goma saura Mumy ta tafi aiki gidan ya rage khadijah da baby sai Iklima don su siyama sun tafi makaranta, Aliyu ma na sama a dakinsa, tun bayan abinda ya faru tsakanin khadijah da Aliyu ta rage xaman cikin gidan sae Mumy na nan, always a baya xaka ganta xaune ita kadai, yau ma xaune take tayi nisa a tunanin da take kamar ance ta juya taga Aliyu tsaye d'an nesa da ita, mikewa tayi a tsorace tana komawa baya, ya dauke idonsa daga kallonta yace "Iman" hawaye ya cika idonta ta kasa amsawa, karasowa yyi kusa da ita ya tsaya tana komawa baya a hankali, yace "Za ki gane gidan step mum din ki?" Khadijah sai kallonsa take xuciyarta na bugawa, ya hade rai yace "Am asking" a hankali tace "Kila in gane" yace "Ohk... Am coming back now" daga haka ya juya ya koma ciki, ba a dau lkci ba ya dawo, envelope ne rike hannunsa ya mika mata taki amsa gabanta sai faduwa yake, yace "Collect it" hannunta na rawa ta karba, yana gyada kai yace "Go Iman, go back to ur step mum, I can't continue my life the way I want living with you in the same roof, you are now a barrier to my happiness pls ki tafi Iman go anywhere, leave our home, bana son Ina ganinki ina jin haushin kai na cos nobody is above mistake, just go plss" A hankali ta juya masa baya hawaye na sakko mata tace "Ohk xan tafi... thank you very much for all what you've done to me throughout my stay in your home, Allah saka maka da alkhairi duk hidiman da ka min, but ina neman alfarmar ko xan iya yi ma Mumy sallama kafin in tafi, don ban mata hallaci ba idan na tafi bata sani ba" a takaice yace "Noo, just go Iman" ta fashe da kuka sosai tace "Ohk nagode" juyawa yyi ya nufi cikin gida... Sai kuma ya juya da sauri yana kallonta yace "And one more thing... Forgive me plss" ta juyo hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that already" yace "Thank you" daga haka ya juya ya shiga ciki ya rufe kofa. Share hawayen idonta da ya ki tsayawa ta dinga yi, dama Hijab ne jikinta kawai ta nufi gate ta fita gidan, da kafa ta karasa bakin titi ta samu napep tana kallonsa a hankali tace "Tasha xaka kai ni" yace "Toh" daga haka ta shiga napep din, har suka isa tasha bata sani ba tayi nisa a tunanin da take, mai napep din ya dawo da ita duniyar tunanin da taje, sai a sannan ta tuna kudin da xata basa, da sauri ta leka cikin envelope din da Aliyu ya bata taga kudi ne me yawa a ciki ta xaro dubu daya hawaye na sakko mata ta shiga tashar ta nufi inda taji ana kiran kano, dama mutum daya ake jira tana shiga motar ta bada kudinta bbu bata lkci suka dau hanyar kano.

Tun da suka iso kano Khadijah ta fito daga cikin tashar kanoline take ta kalle kalle tsaye a bakin titi, duk mai adai daitan da ya tambayeta inda xata sai dai ta kafe sa da ido nan kuwa tunanin da take daban, hadarin da ya shiga haduwa a garin ne yasa ta dawo reality, da kanta ta tafi gun wani mai napep a hankali tace "Tudun yola xan je" yace "Dai dai ina a tudun yola" tace "Idan mun je xan gane" Bata damu da kudin da ya kira mata ba ta shiga adai daitan suka dau hanyar anguwar da ta kira masa, tun suna hanya aka fara yayyafi har suka kawo Tudun yola, ita dai ta san ranan da suka taho daga katsina da ummanta taji ta ce ma mai napep Tudun yola to amma bata san ina a Tudun yola ba, tun mai napep na biyeta suna xaga anguwar har yyi parking yace "Bani kudi na ki sauka, ke da baki san inda xa ki ba kika sa na dauko ki" sauka tayi daga cikin napep din ta basa kudin da yace daga cikin envelope ya bata canjinta ya ja adai daitan sa yyi gaba, hawaye ya cika idonta ta saka kai gabas tana ta tafiya, to ina xata ga gidan ummanta, jin ruwan ya taho da karfi yasa ta samu yar rumfa ta tsaya, ta kusa minti talatin tsaye karkashin wajen, kowa ya shige gida, wasu kuma sun shiga shagunansu saboda ruwa hanyar kamar anyi shara, ita kadai ce a waje ga wani sanyi da ta dinga ji, an dau fiye da awa daya ana ruwan kafin ya tsagaita sai yayyafi, fitowa tayi daga inda take tsaye ta ci gaba da tafiya a gajiye, bata yi wani nisa tana tafiya ba taji ance "Lahh Mama dubi yarinyar nan mai kukan kitso" Juyawa tayi taga wata mata ce da 'yar ta da suka hadu a saloon ranan da Umma ta kai ta gyaran gashi, uwar ta rankwashi yarinyar da baxata wuce Khadijah ba tace "Toh ina ruwanki salon tsokana" matar tace "Sannu yan mata" Khadijah ta gaisheta ta amsa ganin xata wuce tayi saurin cewa "Anty don Allah ban san hanyar gidanmu bane, ko xa ki kai ni gun mai saloon din nan ta san ummata" matar ta saki baki tace "Baki San hanya ba kuma, daga ina kike haka?" A hankali khadijah tace "Daga kano nake na mance hanyar gidan ne" Matar dake ta yi ma khadijah kallon mamaki tace "Ikon Allah, sai dai saloon din da nisa daga nan gashi da sauran hadari, amma mu je mu hau adai daita sai in ajiye ki shagon" Khadijah ta d'an risina tace "Nagode Anty" daga haka ta bi matar da 'yar har suka isa inda masu adai daitan suke, ta fadi inda xa su sannan suka dau hanya, kamar yanda matar ta fada bbu laifi tafiyar da nisa, suna isa saloon din suka tarar mai saloon din ta fito xata rufe shago ta wuce gida saboda ruwa, Matar suka gaisa da mai saloon din sannan tayi mata bayanin Khadijah, mai saloon din tace "Tab, to ai gidan Hajiya Amina da nisa daga nan, cikin ruwan nan yaushe mutum xai fara takawa xuwa gidan ai sai dai adai daita" Matar tace "Toh don Allah ki taimaka ki dau adai daitan ki kai ta gidan idan ya so mamartata sai ta baki kudin adai daitan da kika biya" mai saloon tace "Sai dai haka" daga hakan suka yi sallama da matar Khadijah tayi mata godiya, wani adai daitan mai saloon ta samu suka shiga har kofar gidan Umma, a nan hankalin khadijah ya kwanta ta dinga kallon kofar gidan, khadijah ta sauka tana murmushi tace "Anty nagode xan je in karbo maki kudin napep din" daga haka khadijah ta shiga ciki da sauri, bbu kowa tsakar gidan saboda ruwan da aka yi, Khadijah ta kwankwasa kofar parlorn Ummanta a hankali, Bude kofar Umma tayi tana tambayar waye? Umma ta xaro ido hade da bude baki tace "Khadijah??" Rungumeta khadijah tayi cike da farin ciki tace "Ummata" Umma ta ja ta suka shiga ciki da mugun mamaki tace "Daga ina kike haka" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma" Umma tace "Ke da wa?" Khadijah tace "Ni kadai Umma ki ban kudi in kai ma mai adai da ita a waje, mai saloon din nan da kika kai ni ranan ce ta rakoni, ban san gidan ba" Umma ta dau kudi ta fita da sauri, Godiya tayi ma mai saloon din ta ba mai adai daitan kudin kawo ta da yayi da mayar da ita da xai yi sannan ta koma ciki. Umma ta dinga kallon khadijah tana share hawayen da ya ki tsaya mata a sanyaye bayan Khadijah ta gama yi mata bayanin duk abinda ya faru tun daga ranan da ta bar ta gidan yakumbo har ixuwa yanxu da take gabanta, abu daya ta boye mata a labarin da ta bata shine kuma abinda ya shiga tsakaninta da Aliyu kawai dai ce mata tayi yace ta tafi saboda Anty khadijah bata sonta, Khadijah ta share hawayen dake sakko mata ita ma cikin rawar murya tace "Umma me yasa baki son in xauna a wajen ki, don Allah kada ki sake kai ni ko ina, let me stay with you plss" ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Umma da ita kanta ba karamin rama tayi ba, Umma tayi gathering courage ta jawota jikinta a hankali tace "Khadijah ba laifi na bane kinga kishiyoyina ba kirki ne da su ba saboda su ya sa na kai ki gun yakumbo amma ta ci amanata ko don ba uwar mu daya ba, da wani mugun gidan ta kai ki haka xa a cutar min ke ina nan ban sani ba, har kadunan naje kwanaki in duba ki aka ce ai ta tashi a gidan, gashi bbu wanda yasan inda ta koma, haka nayi kwana biyu kafin in dawo nan kano, duk layukan ta basa xuwa har na gaji na daina kira, kullum fatana shine Allah yasa kuna lafiya ashe abinda ta maki kenan, to Allah ya saka maki, ita kuma wannan baiwar Allah da ta rike ki a gidan ta har na wnn lkcn Allah ya saka mata da alkhairi" Khadijah dake ta sauraren ta a hankali tace "Ameen" Umma ta mike tace "Bari in karbo maki abinci a makwabta bani nayi girkin gidan ba" daga haka Umma ta fita parlorn, khadijah ta jinginar da kanta da kujera a sanyaye, kadan ta ci shinkafa da miyar da Umma ta amso mata ta sha ruwa sannan ta fita yin alwala don ta yi sallah, Shafah da fitowarta kenan ita ma ta saki baki tana kallon khadijah, can ta kwalo ma Hasana kira, Hasana ta fito ita ma, Shafah tace "Kin ga ashe bak'i muka yi a gidan yau" a hankali khadijah ta gaishesu, dariya Hasana tayi tace "Lallai kam bak'i" daga haka ta juya ta koma bangarenta, Shafah ma ta wuce ciki tana dariya. Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da sallah, Umma dake yankan alaiyahu alamar dai ita xata amshi girki tace "Kina ji na khadijah, babu ruwan ki da mutan gidan nan ki rufa min asiri kinji, duk me xa su maki kar ki tanka su, ko don Alhaji ya bar ki ki xauna gidan nan" Khadijah ta gyada mata kawai, mikewa Umma tayi ta fita da alaiyahun waje sai da ta shiga kitchen ta kira Abban fadila, yana dauka bayan ta gaishesa tace "Alhaji dama alfarma nake son tambaya gun ka" yace "Ina ji" tace "Dama khadijah ce xata xo ta d'an kwana biyu nan, sun yi hutu idan ba damuwa don Allah" Yace "Toh kin gaya ma su Shafah?" Shiru Umma tayi bata ce komai ba, yace "Sai ki sanar da su don bana son abinda xa a xo ana min tashin hankali a gida" daga haka ya katse wayarsa, Umma ta ajiye wayarta a sanyaye , ko wace irin rayuwa ce wannan ta fada yanxu ita kam, tun da tayi auren nan bata da kwanciyar hankali sannan kamar warce aka daure kafarta a gidan tana xaune a hakan har lkcn. Fita tayi ta tafi dakin Shafah ta samesu tare da Hasanar daga nan bakin kofa ta tsaya tace "Sannun ku, Khadijah ta xo daxu daga kaduna nace in gaya maku..." Shafah ta mata wani kallo tace "Au haba, to ta sha kabo..." Hasana tace "Lallai kam, sannunta da xuwa" juyawa Umma tayi ta fita ta koma kitchen ta daura girkin tuwo a gas, ko da Umma ta koma parlornta dauko maggi bacci ta tarda Khadijah na yi kan kujera, ta tasheta ta shiga daki ta hau gado, abu daya yasa ta jin hankalinta ya kwanta game da Khadijah, kuma shine yanayin da ta ganta, kowa ya ganta yasan bata tare da wahala sai dai 'yar ramar da tayi. Sosai Khadijah tayi kokarin ganin bata kula duk yaran gidan ba kamar yanda Umma ta yi mata huduba duk da irin cakalarta da suke yi a satin ta daya a gidan, ita kanta Umma hakuri take da kowa na gidan don kamar warce aka rufe ma baki komai suka mata bata tankawa duk ta yi sanyi kamar ba ita ba, Shafah da Hasana wani mulki na musamman suke xubawa a gidan, sai abinda suka ce ayi ake yi ga ikon bala'i... A can Kaduna kuwa, kamar wasa aka nemi Khadijah a gidan aka rasa har yamma, Mumy da farko ita a tunaninta ko Aliyu ne ya fita da ita don har ta tanadi rashin mutuncin da xata yi masa amma tana kiransa yace mata shi bai fita da ita ba, na hankalinta ya tashi sosai ta dinga tambayar baby ko iklima ta yi mata wani abun ne don Anty khadijah bata nan balle tace ita ce, shi kam Aliyu dama yana tabbatar da Khadijah ta tafi ya wuce clinic, ganin yanda mahaifiyarsa ta ishesa da kiran ba a ga Khadijah ba yasa shi komawa gida, and he tried his best pretending he knws nothing about her disappearance. Islamiyyar da Umma tayi ma khadijah register ta ci gaba da xuwa a kano, abu daya ke damun Umma yanxu a kanta shine irin sanyin da tayi kamar ba lively khadijahr ta ba, sanyin kuma ne yasa ko kadan abinda ake mata a gidan bata kula wa duk da idan ta fita islamiyya tun safe sai yamma take dawowa gidan. Kwanan khadijah talatin da 'yan kai a gidan Umma ne ta fara fito da wani habit na bacci, ko me take yi sai ta fara bacci a kai, islamiyya ma idan taje duk bacci take, hakan yasa wani lkcn bata dadewa xata dawo gida, Umma da abun ya fara isarta ranan ta bar mata kaya ta linke tana shigowa taga tana bacci kan kayan, duka ta kai mata tace "Wai lafiyar ki kuwa Khadijah, wannan wani irin bacci ne?" Khadijah ta farka a firgice tana mitsika ido, Umma ta harareta tace "Tashi ki je kiyi sallah bana ma son linkin kuma, wani iskanci komai aka sa ki sai ki buge da bacci" mikewa khadijah tayi a hankali ta fita bayan ta dau butan Umma, Hasana dake tsakar gida ta cika gidan da radionta Shafah kuma na kitchen suka bita da harara a tare, babu abinda ke kona masu rai a gidan irin yanda Umma da khadijah ke kin kulasu a gidan, duk da ita Umma sun san ba banxa ba rashin kulawar, to ita khadijah fa, Hasana tace "Ohh daga Hutu dai sai kuma aka rashe" Shafah dake juya miyar ta na yakuwa dake kan wuta tace "Ke ma dai kya gani, dama yau nake son tambayar Alhaji dalilin da yasa xa a munafurce mu ayi mana karya, ai sai ace mana ta dawo nan din ne da xama ba wai a mayar da mu yara ba" Hasana tace "Yara ko dai shashashai, bari dai ya dawo din ma ji dalilin rainin hankalin" Khadijah dake durkushe kasa sai yamutse fuska take ta dalilin kamshin miyar Shafah da ya kauraye tsakar gidan, mikewa tayi da sauri jin cikinta na hautsinewa ta juya xata koma parlorn Umma taji amai ya taho mata, dawowa tayi ta durkushe wajen ta dinga kwarara amai Shafah da Hasana aka yi tsit daga mita da habaicin da suke suna kallonta.

Fitowa Umma tayi da sauri jin kakarin aman khadijah, ta karaso da ita ta duka tace "Subhanallahi.... Are you okay" khadijah ta kasa cewa komai duk ta galabaita lkci daya, Umma ta taimaka mata ta wanke baki sannan ta dagota ta wuce parlorn ta da ita, Khadijah ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi da kyar tace "Umma I don't knw what's wrong with me, I am always week" Umma tace "Sannu, ko malaria ne, bari Alhaji ya dawo sai mu tafi asibiti ni bani da kudi a gu na" Khadijah ta lumshe ido har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, mikewa Umma tayi ta fita don wanke gun aman, tana isa bakin kofa ta ji muryar Hasana tana cewa "Wllh fah, sai kace mai ciki, ji fa salon aman ma daban ne, idan ma malaria ne ba yellow shataf kalan aman ya kamata ya xama ba" Shafah tace "Haka fa shekaranjiya ina lura da ta shiga kitchen duba mata girki daga xama kan kujera sai bacci, daxu kuma da safe nan bakin kofa ta xauna da abinci a gabanta tayi bacci, ace baccin nan ba lafiya ne?" Umma dake tsaye bakin kofa har lkcn gabanta yyi mugun faduwa, fita tayi parlornta a fusace duk da ta fi wata uku bata tanka su a gidan tace "Sai dai ku ga ciki can kan 'ya yanku ko dangi, amma ba 'ya ta ba, tunda baku da kirki baku da Imani har ku yi ma yar mutum fatan wannan mugun abun, Allah ya isa wllh" Hawaye cike idonta ta kare maganar, Shafah ta mike tana huci ta kunduma mata xagi tace "Bakin ki ya sari danyen kashi, ba ma ga mugun abu ba a 'ya ya ko dangi, to wa yasan inda kika kai ta kwanki ko karuwanci kika sa tayi maki...." Umma ta juya ta koma daki hawaye na sakko mata sosai, kallon khadijah ta tsaya yi taga har tayi bacci, ta xauna duk jikinta a sanyaye a xuciyarta tana kara yi ma su Shafah Allah ya mayar masu mugun alkaba'in da suka yi ma 'yar ta. Har karfe tara Khadijah na bacci bata tashi ba, tada ta umma tayi hankalinta ya tashi jin irin xafin da jikinta ya dauka, da kyar ta lallabata ta sha shayi kadan sannan ta bata paracetamol ta rakata bedroom dinta ta kwanta ita ta dawo parlor ta xauna har lkcn xuciyarta ya kasa dawowa dai dai, khadijah ce ta fito da sauri daga dakin umma na tambayarta me ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login