Showing 99001 words to 102000 words out of 234058 words
baki tace "Though I knw when you are saying the truth and when u are lying, and duk da nasan karya kake coz I saw it in ur eyes, ni kam sai dai ince Allah tayi jagora, ya kuma yaye maka abinda ke damun ka, wnn ramar kuma da kayi, kayi kkrin ganin cire ko ma ke damun ka plss, it's better you pray to ur God" Sudais ya dauke kansa daga kallonta da yake ya mike a hankali yace "Toh nagode Mami sai na dawo" tace "Allah ya tsare" daga haka ya fita. Pharmacy ya tsaya ya siya magungunan da Yusuf yyi masa prescribing sannan ya siya fruits kafin ya wuce gidansa, har wani faduwa gabansa ya shiga yi bayan yyi parking cos bai son xuwa ya ga khadijah in pain, ya dai dake ya shiga gidan, kwance ya sameta kamar ko da yaushe a daki idonta a rufe, yawanci duk haka yake xuwa ya sameta kuma ba bacci take ba, yana tsaye a hankali yace "Amira" ta bude idanuwanta a hankali tana kallonsa, yace "Ya jikin" kai ta gyada masa ya durkusa yana bude ledan apples da banana da ya siyo mata yace "Ga Apple nan" ta girgixa kai da sauri tace "Anjima" yace "Toh kin yi sllh?" Gyada masa kai tayi, ya d'an yi shiru sai kuma ya mike yace "Toh tashi ga magani na kawo maki ki sha, you feel more better idan kin sha" kamar xata yi kuka tace "Xan yi amai ni nafi son allura" kallonta ya tsaya yi, can yace "Baxa ki yi ba kawai guda uku ne fa" daga haka ya fiddo magungunan a leda sai kuma ya fita xuwa ya debo mata ruwa, har ya dawo tana kwance ya d'an hade rai yace "Toh tashi mana" mikewa tayi da kyar ya bude maganin gudu uku kamar yanda yace ya bata a hannu ya mika mata ruwa a cup, ta karba tana bata fuska xata yi kuka, ya daure fuska yace "Ki sha Ki ban cup yanxun nan" wayarsa ne ya fara ring ya ciro a aljihu tana ganin haka ta watsa maganin a bayanta tayi saurin kai ruwan baki tana sha dai dai lkcn da ya maido dubansa kanta, da sauri yace "Kin sha?" Ta mika masa cup din tana yamutse fuska, ajiyar xuciya ya sauke a hankali, kokarin amai ta shiga yi da sauri yace "Noooo, don't ko in bata maki rai" ta koma baya a hankali kar ya xagayo ya ga maganin ta jingina da gado yace "Good girl" daga haka ya fita ya kira Yusuf dake kiransa, da sauri ta kwashe magungunan ta watsar a bayan gado tana turo baki, Sudais ya hade rai bayan ya kai wayar kunne yace "Ya aka yi?" Yusuf yace "Ya ta sha?" Sudais yace "It's nt ur concern" dariya Yusuf yyi yace "In dai ka tabbatar ta sha don't leave her alone kar ka kashe yar mutane nan da few hours xata samu miscarriage din in dai magungunan da na rubuta ka siya ka bata" Sudais yace "Ohk" daga haka ya katse wayar ya xauna parlor. Haka Sudais yyi ta xama gidan har magrib amma shiru kke ji, ya duba ta yyi sau ashirin kafin magrib amma banda bacci bbu abinda take hankli kwance, yana fitowa masallaci ya kira Yusuf yace "Kai ni da ina ta xaune gidan har yanxu shiru" Yusuf yace "Bata sha ba toh" Sudais yace "Ya xaka ce haka, a gabana fa ta sha ni ma na bata maganin da ruwa" Yusuf yyi shiru jin haka, sudais yyi tsaki ya katse wayar. har washegari shiru kake ji bbu alamar miscarriage gashi Yusuf yace kar ya kara bata wani, duk ran sudais ya baci, da yammacin washegari Yusuf ya xo gidan, Magungunan ya dauka yana ta kallonsu kamar yanda Sudais ke hararansa shi kuma, can ya balli wasu ya mika ma sudais yace "Bata ta sha" Khadijah dake kwance tana kallonsu kamar xata yi kuka tace "Ni maganin wani iri yake min bana so plss" Sudais ya daure fuska yace "Karba my friend" mikewa tayi hawaye ya cika idonta ta amshi maganin ya mika mata ruwa, daga shi har Yusuf suka kafeta da ido, ta daga gefen Hijab din jikinta tana share hawayen idonta hakan ya bata daman sakin maganin gaba daya a Hijab din cikin dubara sai kuma tayi saurin dage kafarta kamar xata daura kanta bisa kneel dinta, har lkcn kuma hannunta na dunkule kamar tana rike da drugs din, Yusuf yace "Baxa ki sha ba?" Bude baki tayi ta yi kamar ta watsa su ciki sannan tayi saurin xuba ruwa bakin ta tana yamutse fuska har da kokarin amai, da sauri Sudais yace "Don't try that" ta hade kai da gwiwa suna ta tsaye suna kallonta har ta dago a hankali, Yusuf ya juya ya fita sudais ya bi bayansa, Yusuf yace "Toh sai kayi xaman gadi" daga haka ya bar gidan, Sudais na ta xaune har dare amma shiru, mamaki ya dinga yi anya ba yaudararsa Yusuf yyi ba, a fusace yaje har gida ya samesa don jin me yasa yyi masa haka, Yusuf dake dakinsa kwance yace "Toh ka kai ma wani likitan takardar maganin ka tambayesa na menene, I think that's all I can tell you" Bayan kwana biyu sudais ya sake komawa Yusuf office da rana, da damuwa yace "Dr ko xaka canxa wani method din ne, wllh I don't have rest of mind, am afraid kar Mami ta san abinda nake yi, gashi in few weeks time xan je UK, to ya xan yi da yar mutane?" Yusuf yayi dariya yace "Tunda taimakonta kake son yi ka tafi da ita mana" Yusuf ya watsa masa kallo yace "Ko matata ce ke wannan laulayin ina xa ni da ita balle wannan" Yusuf yace "In baka shawara Barrister?" Sudais yyi shiru yana kallonsa, Yusuf ya mike tsaye yace "Wllh ka kyale mata cikinta tunda ka ga haka, Allah kadai yasan me xata haifa, there is power in the baby, banda haka ban ga dalilin da xai sa ta sha drugs din nan har sau biyu ba amma shiru ake ji, just let her pls and idan son samu ne ka taho da ita clinic ko gobe da safe ayi mata scan cos this is almost a miracle" kasa cewa komai Sudais yyi can ya juya ya fita. Washegari kamar yarda Yusuf yace haka Sudais ya sa khadijah ta shirya suka je asibiti don a mata scan, gaba daya jikinsa yyi mugun sanyi bayan result ya fito, shi kadai da Yusuf ne a office din Yusuf din, ita kuma tana reception, Yusuf yace "You see, da haka xaka sa ayi wasting bayin Allahn da basu san komai ba, 2 souls barrister" Sudais bai iya yace komai ba. A hakan dai Sudais ya ci gaba da ba Khadijah kulawa yanda ya kamata, bai rage ta da komai ba a gidan sa, damuwarsa daya yanda ta ki kwantar da hankali har lkcn ga yawan koke koke, idan ya sa ta gaba ta fadi me ke sa ta kuka sai ta ce masa ita bata da kowa yanxu, hakan nasa jikinsa yyi sanyi, sannan hakan ke kara masa kwarin gwiwan ci gaba da taimaka mata, ganin saura yan kwanaki ya fita kasar ya sa ya shiga tunanin wanda xai bar ta da a gidan, idea ne ya xo masa yasa aka nema masa wata dattijuwar da xa su xauna tare da Khadijah a gidan nasa, hakan aka yi bayan matar da baxata haura shekaru hamsin ba ta amince duk wata xai dinga bata dubu arba'in. A yau Khadijah na daki xaune kasan carpet tana shan kunun da dattijuwar da ta dama mata, dattijuwar matar da a ranan tayi kwana uku a gidan duk tunaninta Khadijah matar Sudais ce, su biyu ne dakin Sudais yayi sallama bakin kofa, ta mike da sauri ta iso kofa ta bude tana cewa "Sannu da xuwa yallabai" Gaisheta yyi ta amsa cike da jin dadin yanda yake girmamata sannan ta fita, Sudais ya karasa cikin dakin yana kallon khadijah, wani mugun haske tayi da kyau sai kyalli take, lips dinta yyi pink colour, dauke kai yyi ya isa gefen gado ya xauna, a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya jiki?" Tace "Da sauki" shiru yyi na wasu yan mintuna kafin yace "Am traveling Amira" ta dago tana kallonsa, ya gyada kai yace "Yeah, gobe xan tafi" sauke idonta kasa tayi, lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Tafiya xaka yi ba bar ni" ya tsura mata ido kafin yyi murmushi yace "Aiki xan tafi yi can, in sha Allah xan dawo when am done" ta kallesa hawayen idonta ya sakko tace "Toh yaushe ne xaka gama" ya wara Manyan idonsa yace "Nima ban sani ba, but da na gama xan dawo ai" kai kawai ta gyada masa amma kana ganinta kasan jikinta yyi sanyi, murmushi ya sake yi yace "Ba ga mama ba xata dinga kula da ke xan bar mata kudi ta dinga siya maki duk abinda kike so, just promise me baxa ki dinga damuwa ba that's all" murya can kasa tace "I promise, amma yaushe xaka dawo?" Dariya ta basa ganin ta yi tambayar daxu yace "Duk sanda kika samu lafiya kika fara cin abinci sosai sannan bakya damuwa xan dawo" xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Yes" murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, sae ranan ya fara ganin murmushinta ya dinga kallonta ganin xata dago kanta yyi saurin dauke kai, tana wasa da dogayen yatsun ta tace "Toh naji" yace "Yauwa ko ke fa" wayarsa daya ya Ciro ya mika mata yace "Xan dinga kiran ki in sha Allah" karba tayi a hankali tace "Toh" yace "to tashi ki raka ni" Ba musu ta mike shi ma ya tashi ya nufi kofa sannan ta bi bayansa, a parlor ya tsaya yyi sallama da Dattijuwar ya kuma sanar da ita xai yi tafiya ta dinga masa addu'ar Allah ya tsare yace "Ameen Ngd mama, don Allah ki dinga sa mata ido bata son cin abinci" tace "In sha Allah kar ka samu damuwa" Dubu hamsin ya ba matar ta dinga siya ma khadijah duk abinda ta bukata, ya kuma sanar da ita komai babu gidan Dr Yusuf xai kawo masu, daga haka ya juya yana kallon khadijah dake ta kokarin ganin bata yi kuka ba yace "Toh mu je" har bakin mota ta rakasa kanta a kasa ya kara mata sallama ta kasa daurewa ta fara kuka, duk jikinsa yyi sanyi, a hankali yace "Look Amira ba dadewa xan yi xan dawo ba, ki daina kuka pls" kai ta gyada masa cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya tsare hanya" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da ido. Kamar kar Sudais ya bar kasar Khadijah ta fara samun lafiya sosai dattijuwar me kirki komai take so shi take mata kafin wani lkci duk babu ramar da tayi sai cikinta da ya fara fitowa, kullum a rana sudais xai kirata kusan sau biyar just to check if she is fine, idan bai kirata ba kuwa ta dinga damuwa kenan, a haka har watanni suka shude.
5 months later.
Yau tun da Khadijah ta tashi take ta murna ta rasa dalili, har hirarta ya fi na ko wani rana yawa har da dariyarta wanda da wuya ka ga tayi dariya, Dattijuwar mama suwaiba da take kira da Anty har ta lura da hakan tace "Wannan murnar yayi yawa khadijah ko dai mai gidan ne xai dawo yau" Khadijah dake hada fruits salad xata sha ta daga kai tana kallon mama suwaiba tayi shiru don kuwa gaskiya ne jiya da daddare da suka yi waya da Sudais yace mata yau xai dawo, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da abinda take a hankali, mama suwaiba tace "Toh gwara a tashi a san me xa a girka masa, ki fadi duk abinda kika San yafi so sai in shirya in tafi kasuwa yanxu" Khadijah tayi shiru don har lkcn bata san komai game da Sudais ba balle ta san abinda ya fi so da wanda bai so, hakan yasa jikinta yyi sanyi sosai. A cikin watanni biyar din nan khadijah ta warware jikinta yyi kwari, babu abinda bata ci har da wanda bata ci a da can, wato wake, taliya kai har da tuwo da miyar kuka, wani kyau na musamman tayi don hatta fatar jikinta har wani glittering yake yayi taushi, yanxu kam cikinta ya fito sosai don sai ayi tunanin at anytime xata iya haihuwa don da kyar take yin komai nan ko watannin cikin bakwai, tausayi take ba mama suwaiba ganin yarinya ce sosai wa ya sani ko xata iya haihuwa da kanta ma, hakan yasa in dai ta fita cefane ko siyo wani abun bata rabo da dawowa da magunguna irin na gargajiya da tasan mai ciki na bukata, duk ranakun alhamis kuma tare da mama suwaiba suke xuwa can clinic dinsu Yusuf domin Antenatal a bisa umarnin sudais, damuwar Khadijah daya a lkcn ummarta don ko cikin dake jikinta baya damunta ta kuma rasa dalili, gaba daya tayi kokarin ganin ta mance ta taba rayuwa gidansu Aliyu, amma duk sanda cikinta yayi motsi sai ta tuna shi Aliyun, duk wannan difficulties na rayuwa da ta shiga ko sau daya bata taba jin haushin Aliyu ba kuma har ranta take jin ta yafe masa a lkcn... ko don tana tare da yarinta har sannan ne oho. Khadijah ta kasa hakuri ganin har yamma bata ga sudais ba alhalin yace mata in sha Allah yau yana Nigerian duk jikinta yayi sanyi ta tafi daki ta kwanta, Mama suwaiba kuma ta ki hakura tana ta girke girke a kitchen ita kadai. Sudais na sauka taxin da ya kawo sa har kofar gida ya shiga gidan yana rike da daya daga travelling bag dinsa guda uku da mai taxin ya dire masa a bakin gate, kai kana ganinsa kasan daga turai yake don wani fresh na musamman yyi da haske sai dai ya rame sai idanuwa da hancinsa da suka fito, sosai ya rage bak'in gashin kansa, yyi murmushi ya na amsa gaisuwar da mai gadi ke masa da fara'a yana masa sannu da dawowa sannan yace "Ka shigo min da sauran kayana bilyamin" tun a bakin kofa kanninsa suka rungumesa ko wacce na murnar dawowarsa bayan kusan watanni biyar, Mami dake parlor da Anty Maryam ma sai murmushi suke, lkci daya murmushin Sudais yyi fading ganin Jiddah da yayi xaune parlorn, ya karaso a sanyaye ya duka kasa ya gaida mami ta amsa tana murmushi tace "Sannu da xuwa Aliyu ya hanya?" Yace "Alhmdllh Mami, fatan mun same ku lafiya?" Tace "Alhmdllh" gaisawa suka yi da Anty Maryam sannan ya kalli jiddah yana kirkiran murmushi ta sunkuyar da kai tace "Sannu da xuwa ya hanya?" Yace "Alhmdllh mun same ku lafiya?" Tace "Sure" Rabi'ah da Humairah suka dau bags dinsa xa su kai daki yace "Noo don't worry sisters wancan kadai xaku dauka ku bar wa ennan, xan d'an fita yanxu" da mamaki Mami tace "Ka fita kaje ina daga dawowa, idan ma fitan xaka yi ina xaka da jaka kuma?" Ya sunkuyar da kai yace "Sakon wani abokina ne xan kai gidansu Mami" Mami tace "Ohk, to amma sai ka huta ka ci abinci koh?" D'an shiru yyi sai kuma yace "Mami baxan dade ba xan dawo yanxu" daga haka yasa kanninsa suka dau jakunkunan suka kai masa bakin motarsa sanin ko baya nan ana amfani da motar, ya mike yace "Toh sai na dawo Mami" tace "Toh don Allah kar ka jima ka dawo ka ci abinci ka huta" yace "In sha Allah" yana barin gidan bayan ya hau titi ya dau wayarsa ya shiga kiran khadijah, Khadijah dake kwance har lkcn a daki ta mike da sauri kamar jira take jin ring din wayar ta jawo ganin Sudais ne ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yyi sallama yace "Amira" turo baki tayi tace "Uhn" yace "How are you" a hankali tace "Fine baka dawo ba kuma" d'an murmushi yyi yace "I postponed the trip xuwa next month in sha Allah" wani irin faduwa gabanta yyi da har sai da ta ji a kirjinta da ya mata sauki kwana biyu sbda magungunan da Yusuf ke bata, hawaye ne ya shiga sakkowa idonta, yace "Hello are you there?" Kasa amsawa tayi ya dinga hello ta katse wayar ta hade kai da gado ta fara rera kuka, sake kiranta yyi ta ki dauka har ya katse ya kara kira, sai a snn ta dauka ta kai kunne taki cewa komai, murya can kasa yace "Amira" ta fashe masa da kuka a hankali, wara ido yyi hade da murmushi yace "Har da kuka kuma?" Ta ki cewa komai, murya can kasa yace "Cry no more, tunda kina son ganina kawai fito gate ki tsaya ni kuma xan taso daga UK yanxu, har kofar gida jirgin xai ajiye ni" mikewa tayi xaune da sauri tace "Don Allah ka bari, ka dawo pls?" yace "Da gaske fa just wait me outside xa ki ganni yanxun nan" katse wayar tayi ta tashi da sauri ta dau Hijab har Kasa ta sa sannan ta fita dakin, Ganin xata fita waje Mama suwaiba da fitowarta kitchen kenan tace "Ya iso halan" Khadijah bata iya ta ce komai ba ta kirkiri murmushi ta fita, a hankali take tafiyar har ta isa gate ta tsaya gabanta na bugawa, tsaye ta ga motarsa bakin gate din suna hada ido ya bude motar ya fito yana murmushi, tsabar farin ciki ta kasa cewa komai amma kana ganin ta kasan she is just happy, ita dai tasan yau da ace mace ce Sudais da ta tafi da gudu ta rungumesa, ya wara mata ido ganin kallon da take masa yace "Toh ko dai in koma tunda kallona xa ki tsaya yi" tahowa tayi ta tsaya gabansa ta sunkuyar da kai tana murmushi, murmushin yayi shi ma murya can kasa yace "How are you Amira" ta kasa dago