Showing 132001 words to 135000 words out of 234058 words
ko ta sa ya nemo ta? kin fa ce min sonta take kamar ita ta haifeta" shiru Anty khadijah tayi da wani irin shock baki bude tana kallonta, salati ta sake daga karshe tace "you have a point, wllh Anty fati xata aikata, wannan shine anyi ba ayi ba, xama bai gan ni ba laure bari in koma gidan ayi komai a gabana, xan bar iklima nan ki sa mata ido don Allah" daga haka ta mike ta suri jakarta har tana tuntube ta fice dakin Laure na cewa tayi a hankali. Aliyu ya kusa awa daya tsaye bayan ya koma dakinsa, gaba daya a sanyaye yake bai san ta ina xai fara ba, bai san me xai ce ma Mumy ba, hakan yasa hawaye ya kawo idonsa tunda yake bai taba jin tsanar Anty khadijah ba sai ranan a ransa, dama tasan abinda ya faru tsakaninsa da Iman, then how? Bayan bata gidan abun ya faru, ranan daga shi sai Iman ne a gidan, kofa ya nufa daga karshe gwiwowinsa a sake ya shiga dakin Mumy, ita da aminiyarta Hajiya Balaraba ne a dakin, Mumy tayi tagumi kana ganinta kasan ta yi kuka ne sosai, tun da ya shigo Hajiya balaraba ke kallonsa, ya kasa kallon su ya isa gaban mumy a sanyaye ya duka cikin raunin murya yace "Mumy don girman Allah kiyi hakuri ki gafarce ni, i knw you Neva expect such, but... Mumy ban san ya aka yi ba ni ba halina bane, har yau ban san ya aka yi hakan ba kuma na kasa samun natsuwa, for the past 5 years neman Iman nake...." Katse sa Mumy tayi tace "Kake neman ta tayi maka me, dama kai ka sa yarinyar ta bar gidan nan Aliyu?" Ya kasa dago kansa a hankali yace "Mumy I was confused, I was thinking that's the only way out for me... I was restless staying under the same roof with her, mumy nasan na cuceta, amma ni nasan ba yin kai na bane don ba halina bane..." kasa ci gaba yyi sbda cracking da muryarsa ya shiga yi ya hade kansa da gado, Bude kofar dakin aka yi Anty khadijah ta shigo, Mumy ta goge hawayen idonta ta daga kai tana kallonta, Anty balaraba ta tabe baki ta dauke kai, karasowa Anty khadijah tayi ta xauna gefen gado ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Yanxu Anty fati ki ji kaxafin da Aliyu yyi ma iklima amma ke abinda ya dame ki daban? Did i and my daughter deserve this" Mumy tace "Ki rabu da ni Khadijah, ki fita ki ban waje, ba don ba don ba wllh yau sai in ce ke din makiyiya ta ce, bakya so na, baki daukeni yar uwar da muka fito ciki daya ba" Mumy na magana ne tana kuka, Aliyu ya mike ya nufi kofa, Sai da ya isa bakin kofa ya juya yana kallon Mumy cikin sanyin murya yace "Na maki alkawarin xan nemo Iman in sha Allah mum, I will repair the damage I made in sha Allah" Mumy ta masa wani mugun kallo tace "And how are you to repair the damage?" Kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace "By marrying her in sha Allah" Girgixa kai mumy tayi tana wani murmushi tace "Noo, babu aure tsakaninka da ita, xaka iya aikata komai domin ta yafe maka idan ta ga xata iya amma banda aure, babu aure tsakaninku, and I told you that long ago, I have my reasons, leave kar ka ci gaba da bata min rai, get out Aliyu" shiru Aliyu yyi yana kallon Mumy a sanyaye, Anty khadijah ta sauke wani ajiyar xuciya tana hamdala a ranta. Tun Khadijah na daurewa ganin twins dinta shiru har dauriyar ya fara karewa, da farko Umma na ta tambayarta inda suka je ita ma ta hakura ta daina ganin ta ki fada sai cewa take yanxu xa su dawo, khadijah ta shiga daki daga karshe ganin har anyi magrib ta dau wayarta ta shiga kiran khaleel da layin da ya kirata daxu, har ya katse bai daga ba, sai da ta kira kusan sau uku ya dauka yace "Uhn me yara to, ki ma cire ran ganinsu yau" xaro ido tayi tace "This is after seven plss..." Ya katse ta yace "Toh ki taho ki daukesu, I can give you the address" daga haka ya kashe wayar, ji tayi hankalinta ya tashi lkci daya hawaye ya kawo idonta, ta sake kiransa bai dauka ba, ta kira yyi sau hudu kafin ya daga, cikin rawar murya tace "Don Allah ka dawo da su dare yyi, Umma ce fa ke ta tambayarsu" Yace "Hmm toh naji" kashe wayar yyi ta xauna bakin gado a sanyaye.
Bayan kusan minti talatin khadijah dake ta xaune daki hankalinta ya ki kwanciya ta kalli wayarta da sauri jin yana ring, ganin khaleel ne ta mike ta sa Hijab ta fita tana addu'ar Allah ya sa twins din ya dawo da, Nanny kadai ce parlor ta ce mata tana xuwa sannan ta fita waje, hade rai tayi dai dai lkcn da su shureim suka sakko daga cikin motar ko wannensu rike da leda khaleel ma ya fito, rungumeta suka yi gaba daya cike da farin cikin ganinta, fuskarta daure tace "Oya mu wuce ciki..." Suka juya suna kallon khaleel da ya rungume hannunsa, jallabiya ne sanye jikinsa ya dinga kallon yaran suka daga masa hannu sudais yace "Uncle are u coming tomorrow plss" Khaleel yyi murmushi yana gyada kai yace "Sure" khadijah bata basu daman sake ce masa komai ba ta tunkudasu cikin gida, Hijab dinta taji khaleel ya riko ta juyo da sauri, murya can kasa yace "Wait" ta kalli yaranta da har sun shige gate, ta kwace Hijab din fuskarta daure tace "Meye haka pls" yana kallonta a hankali yace "Ba gaisuwa xa ki wuce?" Hararansa tayi tace "Wanda na maka daxu a waya fa?" Jinginar da ita yyi da mota, yace "Daban" ta sauke idonta kasa xuciyarta na bugawa jin bai ce komai ba ta dago kanta taga kallonta yake, da sauri ta kara sunkuyar da kanta, yyi murmushi murya can kasa yace "Can I come gobe mu gaisa da Umma?" Ba tare da ta dago ba tace "Why?" Yace "Haka nan, twins suka ce in xo in gaida Ummansu she will like me" kin cewa komai tayi, bayan few seconds yace "Khadijah" dauke kai tayi tace "Allah ya kai mu" Ya d'an yi murmushi yace "Ameen, to yaushe xa ki koma?" Sai a sannan ta kallesa, lkci daya ta sauke idonta tace "Monday in sha Allah" ya dan wara ido yace "Har Monday?" Shiru tayi, murya can kasa yace "Alryt then, we go together" kai ta gyada masa kawai, yace "Toh sai da safe" ta saci kallonsa a hankali tace "Allah ya kai mu" daga haka ya bata hanya ta wuce ciki ya bi ta da ido. Umma dake parlor ta bi ta da kallo har ta shiga daki sannan ta mike ta bi bayanta, xaunawa gefen gado tayi tace "Saurayin ki ne wanda ya xo Khadijah?" Khadijah ta xaro ido tace "Saurayi kuma Umma, aa ba saurayina bane" Umma tace "Kawar ki ce kenan, it's high time you settle down with a husband daughter..." Khadijah ta kalleta da sauri, Umma tace "Ehh, kuma ban son ya wani dau lkci, in dai kina da wanda ya kwanta maki kika yaba hankalinsa, ki fito da shi, kin ga wannan dama ce da xa mu samu na xuwa katsina.... Idan ma kawun nan ki baxa su daura maki aure ba baxa ki rasa wanda xai daura maki ba" Rasa abun cewa Khadijah tayi, don ita dai tasan bata da saurayi, Umma tace "You think over it daughter" daga haka ta mike ta bar dakin. Kasa bacci daren ranan Khadijah tayi maganar da Umma tayi mata ya tsaya mata sosai, ko kadan aure ba ya cikin tsarin da tayi ma rayuwarta, babu abinda ke sake daga mata hankali sai ganin how serious Umma tayi xancen, gashi ta ma kasa ce mata ta hadu da Aliyu saboda bata ma son xancen, sai dai kuma ko don Aliyun ma ya kamata tayi auren ko xai fita rayuwarta da yake kokarin shiga yanxu, har asuba bata wani ritsa ba, sai a sannan ta fara da ta sanin dawowa ma da tayi.
Aliyu ya kalli Mumy a karo na farko tun shigowar ta dakin tana masa magana babu yabo babu fallasa tamkar dai umarni ma take ba sa, ya d'an yi murmushi sannan yace "Mumy ba fa aure tsakanina da Iklima...." Strictly Mumy tace "Haka kace?" Yace "Ehh mumy, domin kuwa da ciki aka daura auren, yanxu kuma naga alamar sun je sun xubar da cikin" Mumy ta dinga masa wani kallo ko kiftawa babu, juyawa tayi ta fice daga dakin rai a bace, yyi murmushi ya na ci gaba da analysis din da yake tun safe amma ya kasa arriving komai, ya lumshe ido keenly, yana naxari... it all started bayan ya sha coffee da safe ranan, and then? Kawai ya dai ji ya kasa fita aiki, and... Bude kofar da aka yi ya bude ido ya juya da sauri, Saleem ne ya shigo dakin Aliyu ya masa kallo daya ya dauke kai, murmushi ya dinga yi ya ki cewa komai, aliyu ya kallesa a karo na biyu, ya mike yace "Ya aka yi malam?" Dariya saleem yyi yace "Wani xance naji yan gidan nan ke yi yaya, is it for real?" Wani kallo Aliyu ya dinga masa cikin cool voice dinsa yace "Get out and close the door behind you saleem" Saleem ya daga kafada yana murmushi yace "But I neva expect that from you, ni da ake ma warning a da, sai gashi kuma....." Dariya yyi ya fita ya rufe kofar, Aliyu ya xauna xuciyarsa na tafarfasa ya ji duk ya tsani yan gidan nasu gaba daya, ya hade kansa da table din gabansa....
Khadijah na kitchen tana girkin lunch misalin sha biyu Shureim ya kawo mata waya dake ring, Karba tayi ta daga ta kai kunne, muryarsa ya daki kunnenta, yace "How was your nyt?" Tace "Twas good, ya gida" yace "Alhmdllh, ya twins?" Tace "They are fine" yace "Alryt. Anjima xan xo" tace "Allah ya kai mu" daga haka yyi mata sallama ya katse wayar, ta juya xata mika ma Shureim wayar, wani mugun faduwa gabanta yyi ganin irin tsayuwar da yyi yana jiranta, lkci daya Aliyu ya fado mata ta mika masa wayar a sanyaye, yaron ya karba ya juya ya fita ta ci gaba da abinda. Aliyu ya fito daga bedroom dinsa rike da makullin mota xai bar gidan ganin he is nt arriving at anything better a tunanin da yake tun safe, baby ma da fitowarta kenan daga dakinsu ta juya ta koma ganinsa, tun ranan da Anty khadijah ta fadi ma yan gidan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah kusan duk suke canxa hanya idan sun gansa, gaisuwa ma sai sun ga dama, duk wannan baya masa ciwo sai irin yanda Saleem ke making jest of him ko da yaushe cikin masa dariya yake, he is just trying hard to control his self baya kulasa, Mumy ce ta fito daga dakin Anty Khadijah tana kwalo ma Saleem kira hankali tahse, shi dai Aliyu na tsaye don har ita bata bin ta kansa a gidan, Saleem ya fito tace "Maxa ka dauko makullin motar iklima ce ba lafiya, kayi sauri don Allah" Aliyu na jin haka ya sauka Downstairs ya bar parlorn ya hau motarsa ya fice a gidan, direct gidan Farouq ya nufa, yana isa bakin gate ya kira sa ya sanar da shi yana kofar gida, fitowa yyi daga motar bayan Farouq yace ya shigo yana ma compound, Aliyu ya shiga gidan yana amsa gaisuwar mai gadi, can ya hango Farouq su biyu xaune kan biyu daga cikin kujerun dake wajen, har ya isa wajen idonsa na kan wanda ke xaune tare da farouq, shi ma dai dai nan ya dago kai suka yi ido hudu, kallon kallo suka shiga yi da wani ex gaba daya fuskarsu, Farouq dake nuna ma Aliyu kujera yana murmushi yace "The great Dr, mu dai mun je daurin auren ka baka nan, ban kuma kira ka ba saboda ba aji mutuwar sarki a baki na ba" kin xama Aliyu yyi yace "Ehh naga alama, I was just passing by dama nace in shigo mu gaisa so ba dadewa xan yi ba, ana jirana a mota, I will leave now" Farouq ya masa wani kallo yace "Bana son walakanci fa, daga xuwa sai tafiya, yaushe ma ka dawo Nigeria" tuni Aliyu ya juya ya bar wajen da sauri, Farouq ya mike yace "What's the meaning of this Aliyu!" Ba tare da ya juyo ba yace "Sure, a gaida min su Haiydar da Madam am in a haste" Farouq ya bi sa da kallo baki sake kafin ya kalli abokin sa dake xaune yana danna waya, dago kai khaleel yyi shi ma ya kallesa yace "Kila don ya gan ni ne yasa ba ya son xaunawa...." Farouq ya ma khaleel wani kallo, sai kuma yyi dariya yace "Toh ai ina ya san ka da xai ki xama saboda kai kai kuma da wani xargi, that's Aliyu for you, haka nan yake ba wai don saboda kai bane it's his habit" murmushi Khaleel yyi yace "Toh ya ji dadi, nima yanxu xan wuce ina da inda xan je" daga haka ya mike Farouq yace "Haba dai, so early yaushe rabon mu hadu Dr Ayman?" Khaleel yace "Assuming babu inda xan je I will stay kai ma ka sani" Farouq yyi murmushi ya mike yace "Toh shkkn, wai ya Jawahir din ka, saura watanni nawa bikin?" Khaleel yyi murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Uku kawai" Farouq yace "Toh Allah ya kai mu, my regards to her, Anty kuma kace mata plsss tayi hakuri ina nan xuwa in gaisheta" Shi dai khaleel bai ce komai ba suna tafiya har suka fita gidan, sai da suka isa gun motar khaleel, khaleel ya juya yana kallon Farouq strictly yace "Don't dare say anything about me to that guy that just left Umar, tell him nothing about me if he shud ask" da mamaki Farouq yace "Anything? Like? Ka taba sanin sa ne?" Khaleel yace "No ban san shi ba, I just know xai yi ma tambaya a kai na, kar kuma ka gaya masa komai" daga haka ya shiga motarsa Farouq ya dinga kallon sa yace "shi aliyun?" Dariya yyi yace "Yanda kake haka yake shi ma ai, banbancin ku kadan ne, soo nasan baxai ma min tambaya a kan ka ba, beside shi ma a UK yake ai, a Dr also" Shi dai khaleel bai ce komai ba ya ja motarsa ya bar wajen. Yau dai Khadijah mayafi ta daura kan atamfar jikinta ta fito amma ba tare da su Sudais ba, duk da bata yi kwalliya ba amma tayi kyau ne ba kadan ba, ta glass khaleel ke ta kallonta ganin jingina tayi da motar bata bude ba ya sa ya bude ya fito ya xagayo ta inda take, ba tare da ta kallesa ba tace "Ina yini?" A hankali yace "Cool, ya boys dina" tace "They are inside, mu je sai ka gaisa da Umma" daga haka ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo da farko kafin ya bi bayanta, Sosai Umma ta tarbi khaleel da yaki kallonta kansa a kasa, xaman ma bakin kujera ya xauna kana ganinsa kasan duk a takure yake, Umma ta tambayesa mutanen gida yace duk suna lafiya, dariya ya ba Khadijah don bata tana xaton yana da kunya haka ba don ko da wasa ya ki dago kansa, Umma da ta lura da haka ita ma ta bar masu parlorn, sai a sannan khaleel ya dago kamar munafuki, khadijah dake ta murmushi tana xuba masa lemo a cup tace "Kamar gaske" mikewa yayi ya mata wani kallo murya can kasa yace "Karya ce dama, am outside" da sauri ta kallesa tace "Me xa kayi a waje" yace "I can't stay here" ta bata fuska tace "Abinci fa xan xuba maka" yace "Ni bana jin yunwa, kawai ki turo min twins" daga haka ya nufi kofa kamar ana hankada sa, Khadijah ta bi sa da harara har ya fita, tsaki ta yi ta xauna kujera tana turo baki, Ba a dau lkci ba ya fara kiranta a waya har ya katse bata dauka ba, ya sake kira ta ki dauka, text ya turo mata yace "Plss Khadijah, ina mota fa ni baxan iya xaman parlorn ba, idan baxa ki fito ba ki turo min su sudais kawai" tashi tayi ta wuce dakin Umma don suna can suna kallo basu ma san ya xo ba, Umma na ganinta tace "Barin sa ki ka yi shi kadai a parlor?" Khadijah ta tabe baki tace "ya fita yana waje" Umma tace "Saboda me?" Tace "Wai baxai iya xama a parlorn ba" Murmushi Umma tayi tace "Shi kuma haka yake da kunya, Khadijah ina kika samo balarabe?" Xaro ido Khadijah tayi lkci daya ta fashe da dariya tace "Ba balarabe bane fa shi" hararata Umma tayi tace "Ya xa ki ce min ba balarabe bane" Murmushi Khadijah tayi tace "Toh ni dai haka yace min" Umma tace "Ya dai ce maki hakan ne, to ki fita ki samesa tunda baxai xauna parlor ba" Tare da su Sudais ta fita, khaleel ya fito daga motar yana kallonta bayan yyi pecking yaran da suka yi murnan ganinsa yace "Har da walakanci koh?" Tace "Nima ae shi ka min" shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace "Baki san ina da kunya sosai ba ko" Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba ya dinga kallonta don bai taba ganin dariyarta haka ba, har da rike ciki, ganin yanda yake kallonta ta hadiye dariyar tana murmushi tace "Amma a nan Nigeria kake ajiye kunyar idan xa ka UK koh?" Xaro ido yayi ba don yaranta dake gun ba