Showing 75001 words to 78000 words out of 234058 words
yace "I don't want this to happen Iman, I...." Kasa ci gaba yayi jikinsa ya dau rawa, yasan he have tried for that long, the urge... He just don't understand it, it's unbearable.... It's different. Aliyu never gave her a chance to raise any alarm duk da kokarin yin hakan da ta dinga yi, kai kana ganinta kasan bata taba tsorata da shiga tashin hankali irin na moment din ba, gashi yyi depriving dinta damar rokonsa ta kuma yi masa tuni da cewa ita marainiya ce ko xai ji tausayinta, domin kuwa ya rufe bakin ta, and that was how everything happened, tana ji tana gani Aliyu ya raba ta da pride dinta, daga nan da ta rufe ido bata sake budewa ba sai bayan wasu mintuna. Kwance ta ganta dakin baby an rufeta da duvet, ta dinga bin dakin da kallo a hankali kamar me son tuna wani abun, ta runtse ido ta dalilin sara mata da taji kanta ke yi sosai, bude ido tayi da sauri kuma a tsorace don a lkcn komai ya dawo mata, xata mike xaune taji wani xafi gaba daya jikinta, kara ta saki ba tare da ta shirya yin hakan ba duk jikinta na rawa tana kiran Ummanta, dai dai nan aka bude dakin, bata san lkcn da wani karfi ya xo mata ba tayi ignoring axaban da take ji ta mike a gigice tana neman sauka kan gadon cikin tashin hankali take cewa "Don Allah yaya Aliyu kayi hakuri ina rokan ka, wlh mutuwa xan yi, kar ka xo don Allah" ya isa har gabanta yana kallonta da idanuwansa da suka yi ja xata gudu ya rikota ya xaunar da ita gefen gado shi ma ya xauna ba tare da ya bari sun hada ido ba muryarsa na rawa yace "Don Allah ki yafe min Iman, sure I cheat you, but..." Kasa ci gaba yyi ya sake hannunta ya rike kansa da yyi masa nauyi hawaye na xuba idonsa, ita ma kukan take a raunane tana son tashi wajen amma ta kasa, sauka yyi kan gadon ya durkusa kan kneels dinsa hawaye na xuba idonsa ya daura kan sa kan kafarta trying hard to speak yace "Ki dubi girman Allah ki yafe min Khadijah, I didn't do that intentionally, forgive me plss, I don't knw wat came over me, ba halina bane Iman, don Allah ki yafe bi...." Kuka kawai khadijah take tana ja baya jikinta na rawa, cikin sarkewar murya tace "Na ji, amma ka tafi don Allah ina rokon ka, please go" ya fi minti biyar durkushe gabanta kansa a duke har lkcn hawaye ya ki tsaya masa, ya ji duk ya tsani kansa, of all people why Iman, cike da karfin hali ya mike ya fita dakin. Khadijah ta fada kan gado ta dinga kuka, tun bayan rasuwar Abbanta sai a lokacin ta ji ba ta son duniyar gaba daya, xuciyarta ya karaya taji ita ma da Allah ya dau ranta a lkcn ta huta. Bacci me nauyi ne ya dauketa afterward, bata tashi farkawa ba sai da su baby suka dawo misalin karfe biyar na yamma, ta dinga kallon baby da ta tasheta da idanuwanta da suka kumbura sosai, baby ta ja baya da mamaki tace "Iman, what's wrong did you cried?" Hannu ta kai jikinta ta ji yyi mugun xafi, ta fita da sauri don kusan tare suka shigo gidan da Mumy, dakin ya Aliyu ta fara shiga ta ga baya nan, sannan ta sauka downstairs don har lkcn mumy da Anty khadijah ba su hauro sama ba, Anty khadijah duk ta gaji da xancen da mumy ke mata ta kagu ta wuce sama don kin xama ma ta yi a parlorn tana tsaye, da damuwa baby tace "Mumy kamar khadijah bata da lafiya...." Katse ta Anty khadijah tayi da sauri tana kallonta tace "Me ya sameta?" Mumy kanta sai da ta kalli Anty khadijah, can Anty khadijah ta ankare ta tabe baki tace "Abun ka da xuciyar musulunci ban da haka ina ruwana, a kan yarinyar da ake min gori a gidan nan dubi yanda na xabura don ba ta da lafiya kamar iklima ce ba lafiya" mumy na kallon baby tace "Me ya sameta" baby tace "Nima ban sani ba, her eyes are swollen kuma jikinta yayi xafi sosai" mikewa Mumy tayi ta wuce sama, sai da Anty khadijah ta shiga kitchen ta dau flask din da ta xuba ruwa taji an diba sannan tayi murmushi ta bi bayan mumy da sauri, Cire bargon Mumy tayi tana kallon khadijah, ita kanta sai da ta tayi mamakin irin xafin da jikinta yyi ga wani shivering da take idanuwanta sun kumbura, Anty khadijah dake ta kallonta ta shimfida damuwa karara fuskarta tace "Me ya same ki haka" khadijah bata iya tace komai ba sai rawa da jikinta yake, Fita Anty khadijah tayi ta nufi dakin Aliyu da sauri ta bude, ganin baya dakin ta shiga don kara tabbatar da cewa ba xanin gadon da ta gani dakin bane daxu da ta shigo sannan ta fita daga dakin, Mumy ta kalli baby tace "Dauko min wayata" Da sauri baby ta fita sai ga ta ta dawo da wayar, Mumy ta shiga kiran Aliyu, yana gidansa kwance for the 1st time tun da Daddy yyi furnishing masa gidan, idonsa a lumshe suke ya bude a hankali jin karan wayarsa ya dinga kallon kiran ganin Mumy ce har ya katse, sake bugowa aka yi, yayi karfin halin mikewa don xaxxabi ne sosai jikinsa, ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga cikin sanyin murya yyi mata sallama, da damuwa Mumy tace "Aliyu where are you, Khadijah bata da lafiya sosai, ka taho yanxu idan ya kama ku tafi asibiti ne sai ku wuce" Da farko rasa abinda xai ce ma Mumy yayi lkci daya hawaye ya cika idonsa, har sai da tace "Hello Abuturrab, are you there?" Yyi karfin halin gyada kai yace "Xan taho yanxu Mumy" daga haka ya katse wayar ya ajiye ya rike kansa hawaye na sakko mishi.
Aliyu ya fi minti goma xaune cikin mota bayan ya iso gida, gaba daya ya rasa me ke masa dadi duniyar, har ya fita kamanninsa saboda damuwa, Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso inda take kallonsa Mumy take cos he looks so sick, shi kam ya kasa dagowa balle ya kalleta, Tace "Abuturrab are you okay, ciwon kan ne har yanxu" ya gyada mata kai a hankali yace "Na sha magani mum da sauki" daga haka ya wuceta ta bi sa da ido, bin bayansa tayi tace "Toh bacci ka je clinic din kake yi?" Bai juyo ba yace "Eh" da damuwa tace "Maimakon ka tsaya gida ka huta Aliyu tunda baka da lafiya, da sai ka kira asibitin ka bada uxurin ka, xa ma ka iya dubata yanxu ko kawai mu wuce asibiti" tsaye yyi bakin kofa ya rasa abinda xai ce mata ya kuma kasa juyowa duk jikinsa yyi sanyi, Cike da karfin hali yace "Xan tafi asibitin da ita likita xa su duba ta a can" mumy tace "Toh kai ma gaskiya a dubaka wani irin ciwon kai ne haka lkci daya tun safe, sanusi sai ya kai ku clinic din" Bude kofa aka riga sa yi Anty khadijah dake tsaye bakin kofar tana kallonsa da kyau tace "Me ya same ka kai kuma, baka da lafiya ne?" Gefenta ya bi ya shiga gidan ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "I am better now" Anty khadijah ta kalli Mumy mamaki shimfide fuskarta tace "Dama baya da lafiya ne Anty fati?" Mumy tace "Tun safe kafin in fita aiki yace min yana jin ciwon kai ban san wani kalan ciwon kai bane haka har yanxu, ni na xata ma baxa shi aikin ba ganin har na fita yana gida" Anty khadijah ta bi bayansa da sauri ganin har ya kai stairs, ta hada har da d'an gudunta har hakan ya ba Mumy mamaki, Tsaye Aliyu yyi bakin kofar dakin ya kasa shiga, ta labe jikin stairs tana jiran ya shiga ita ma ta shiga, a hankali ya murda kofar ya sa kai ya shiga, Tana ganin haka ita ma ta shige, Baby da ke xaune gefen Khadijah da ke kwance da damuwa tace "Yayanmu Iman bata da lafiya she is just crying, and her temperature is very high" hawaye cike idonta take magana, khadijah na jin sunan da Baby ta kira ta bude ido da sauri hade da yunkura ta mike xaune, Aliyu ya kasa kallon direction din, wani sabon kuma khadijah ta saki a raunane, Anty khadijah dai na tsaye kofa tana kallonsu, Aliyu bai iya ya kalli khadijah ba yace "Ki sa ta shirya xa mu je asibiti yanxu" baby tace "Toh" daga haka ya juya suka yi ido hudu da Anty khadijah, tabe baki tayi ta juya ta bar wajen tana cewa "Haka dai aka iya, da yar uwar ka ce ba lafiya ai baxa ka bi ta kan mu ba ma" shi dai ba ce komai ba ya fita. Hijab baby ta ba Khadijah, Khadijah taki sawa tana girgixa mata kai cikin kuka tace "Ni bana son xuwa asibitin, idan nayi bacci I will okay, baxan iya xuwa ba" baby tace "Nooo, ki sa mu tafi don Allah" kin yarda Khadijah tayi hakan yasa baby ta fita sai ga ta sun shigo tare da mumy, mumy ta karaso kusa da ita ta amshi hijab din ta sa mata tace "Kiyi hakuri ki tashi ku je asibitin kin ji, Allah ya sauke" daga haka Mumy ta dago ta, Aliyu dai na tsaye corridor yyi backing kofar, muryar Mumy ya ji tana cewa "Toh ka kai ma Sanusi makullin sai yyi driving din koh" Juyowa yyi xai yi magana amma ya kasa ganinta tsaye tare da Khadijah tana rike da hannunta, Wani mugun tausayinta ya dinga ratsa shi ganin irin karfin halinta cos he was thinking baxata iya fitowa ba, bai yarda sun hada ido ba kamar yanda ita ma kanta ke a kasa, ya fara sauka stairs Mumy ta bi bayansa tana rike da hannun Khadijah baby na biye da su a baya, Anty khadijah dake tsaye bakin kofar dakinta ta saki baki ta bi Khadijah da ido a ranta tace wa yaga boss lady, don kusan kalau take tafiyar ta, nan kuwa daga ita har Aliyun basu san mugun karfin hali take ba, she is in pain all over, only trying her best to be okay, Mumy ta bude bayan motar ta shigar da ita tasa baby ma ta xauna a baya kusa da ita, sanusi ne ya ja motar cos da gasken Aliyu bai jin xai iya tukin, har suka isa asibitin kansa na jingine da kujera, baby kuma na rungume da Khadijah da ta ki bude ido tana kukan xuci. Sanusi na parking Aliyu ya bude motar ya fita, Baby ta fito tana kallon khadijah tace "Iman ki sakko we are at the hospital" A hankali khadijah ta fito cikin motar tana rike da hannun baby, Aliyu ya kalli baby yace "Ku koma tare da sanusi" xaro ido tayi tace "Yaya but Mumy tace in tsaya da ita, wa ye xai tsaya kusa da ita idan anyi hospitalising dinta, look shes very sick fa" irin kallon da ya dade bai mata ba ya shiga yi mata a lkcn, Bata sake cewa komai ba ta shiga motar hawaye cike idonta, Khadijah ta fashe da kuka a hankali tace "Don Allah kar ki tafi ki bar ni" Baby na share hawayen ta tace "He said I shud leave Iman" Aliyu ya juya ya wuce ciki sai ga nurse ta taho ta shiga da Khadijah asibitin, sanusi ya ja motar yana ma khadijah Allah ya sauwake ya kama hanyar gida. Nurse din na rike da hannun Khadijah da ke ta hawaye ta wuce office din Aliyu da ita kamar yanda yyi instructing dinta, baya office din hakan yasa ta fito ta shiga office din kusa da nashi ta samesa xaune, ruwan xafi yasa ta fara kai ma khadijah bathroom dinsa tayi wanka sannan ya bata magunguna da alluran da xata mata, daga haka kuma ya bar asibitin, kulawa sosai nurse din ta bata don ta bata tausayi yanda ta ga jikinta duk da ba ta san takamaiman abinda ke damunta ba, tana mata alluran kuwa bacci ya dauketa nan dakin Aliyu. Aliyu na gidansa har ya samu bacci ya daukesa.... ring din wayarsa ya tashe sa, dubawa yyi da kyar ya ga Mumy ce, ya kai hannu ya daga a hankali ya kai kunne, da damuwa tace "Aliyu ya jikin Khadijah, or shud I come over naji shiru shiru" yace "Noo mum, da sauki anjima sanusi yaje can asibiti ya mai da ta gida" Mumy tace "Kai kana ina?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Na taho nan gida na ne, I need sleep" da mamaki mumy tace "Kuma ka bar ta ita kadai asibiti gashi ka ki barin Baby ta xauna da ita Abuturrab" yace "Nurses din xa su kula da ita mum" Mumy ta d'an yi shiru kafin tace "Toh shkkn, Allah ya sauwake, kai ya jikin naka?" Yace "Alhmdllh am better now" tace "Ohk, amma da ka daure kai ka je ka maido ta gida don Allah, bbu dadi hakan kamar bata da gata, idan baxa ka ba ni in je" yace "Toh mum xan je yanxu kiyi hakuri" daga haka ta yi masa sallama ta katse wayarta. Bayan magrib Aliyu yyi wanka bayan yyi sllh ya canxa kaya ya bar gidan, yana isa clinic din ya kira nurse da ya bari da Khadijah a waya yace tayi mata alluran karshe na ranan ta fito tare da ita yana waje, nurse din tayi yanda yace sannan suka fito tare da Khadijah, bin nurse din da ke rike da hannun ta take kamar iska xae kadeta ta fadi, duk ta rame lkci daya, yana kallon nurse din bayan sun iso a hankali yace "Hope you did all what I instruct you to" nurse din tace "Yes but, I don't knw why she's finding it difficult to walk, kuma tun daxu take complaining chest pain, Dr bashir ya bata magani dai daxu, har da shi ma cikin wa ennan" ta fadi tana nuna masa drugs din da Khadijah xata kai gida, Khadijah dai na tsaye kanta a kasa duk a tsorace take ga xuciyarta dake bugawa da sauri da sauri, Aliyu ya gyada kai yace "Thanks nurse Maryam" Nurse din tayi murmushi ta sa Khadijah ta shiga gaban motar ta rufe tana mata Allah ya kara lfya, tada motar Aliyu yyi ya bar haraban hospital din, har suka isa gida bai ce komai ba, yana lura da hawayen da take yi tana gogewa da Hijab dinta tun bayan da suka fito clinic har ynxu da suke gida, ya gama parking ta bude motar a hankali ta fita, ya bi ta da ido ganin yanda take tafiya har ta shiga gida, sae sannan shi ma ya fito ya rufe motar ya shiga gidan. Mumy dake xaune parlor da su siyama da Anty khadijah ta mike ganin Khadijah tace "Sannu khadijah, ya jikin" Khadijah ta kasa dago kanta tace "Naji sauki Mumy" Anty khadijah sai kallonta take babbu kiftawan kirki, Aliyu na shigowa parlorn ya haura sama, Mumy ta kama hannun Khadijah ta wuce sama xuwa bedroom dinta da ita, da kyar khadijah ta iya cin pepper soup din da mumy ta mata, duk bakin ta babu dadi, a nan dakin bacci ya dauketa. Cikin dare misalin karfe biyu xaxxabi ya kuma rufe ta, dakin Aliyu Mumy ta shiga ta samesa xaune kan darduma ta xauna gefen gado ta jira ya sallame sallahn da yake da damuwa tace "Aliyu har yanxu fa jikin Iman" yace "Xaxxabin kuma?" Mumy tace "Ehh dama" yace "Mumy to ta kara shan drugs din..." Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Toh shkkn" sannan ta mike ta fita, magungunan ta sake bata ta rufe ta da duvet sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauketa. Da safe tea Khadijah ta sha bayan mumy ta tilastata da kyar, da tayi ma Aliyu maganan alluranta da ya rage yace driver ya kai ta sai karfe goma shi xai fita aiki, sanusin ne ya kai ta ya maido da ita, kafin yamma taji saukin jikinta sosai sai dai ta rasa irin ciwon da take jin kirjinta ke mata, kuma hakan na faruwa ne in dai ta tuna incident din ranan sai taji mugun faduwar gaba, har lkcn Aliyu bai barin su hada ido a gidan kuma bai ce mata komai, idan tana wuri ma bai yrda ya tsaya a gun, Anty khadijah dake lura da komai har wani farin ciki da nishadi na musamman take ji a gidan, har Mumy ta dinga mamakin yar uwar tata, duk fadace fadace da xage xagen ta rage yanxu hatta Khadijah ta daina hantara nan ko shirin sake komawa inda taje kwanaki kamar yanda aka ce mata ta dawo idan ta tabbatar komai ya wakana a lkcn ma xa a fara aikin, tunanin karyan da xata yi ma Mumy kawai take ta tafi inda xata. Aliyu na bedroom dinsa da daddare baby ta shigo, ta xauna kusa da shi tace "Yayanmu I want to ask you something pleaseee" yana kallonta yace "What?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Iman tayi maka wani laifi ne, naga you no longer talk to her, ko ta gaisheka sometimes you do pretend you didn't hear, why please, ka gaya min me tayi maka, gashi ita ma she is always sad yanxu, I've caught her severally tana kuka cikin dare..." Katse ta yayi yace "Na fara wasa da ke da yawa koh?" Da sauri ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi da sauri ta fita ya ci gaba da danne dannen laptop da yake