Showing 171001 words to 174000 words out of 234058 words
3qtr ne jikinsa da sweater mai hula yana tsaye bata dai ga abinda yake ba, kallonsa kawai take, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, takowa yyi har gun windown yana kallonta yace "Ina kika je?" Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta Sauke idonta kasa a hankali tace "Market" yace "What did you get?" Ta hade rai tace "Ina ruwanka" yyi murmushin sa mai kyau ya sauke hular kansa yace "Ohk then" daga haka ya juya ya bar wajen, Irish ta soya da kwai sai ruwan Lipton da ta dafa da kayan kamshi, har xata fita kitchen din ta dawo, ta fi minti biyu a tsaye kamar mai contemplating abinda xata yi, kawai daga karshe ta dau wani warmer ta debi Irish din da kwai ta xuba ruwan Lipton din a wani karamin flask ta ajiye su a gefe ta fita kitchen din, Bedroom dinta ta wuce ta tada Shureim dake bacci ta wuce bathroom da shi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta sa yayi alwala suka fito, sai da ta gama shiryasa sannan ta shimfida masa darduma tace "Idan ka gama sllhn meet me at the parlor" daga haka ta fita, ba a dau lkci ba ya fito yace "Anty na gama, good morning" tace "Morning dear" kitchen ta tafi ta dauko flask din Lipton din ta mika masa tace "Ka kai ma uncle sai ka dawo ka karbi dayan" yace "Toh" ta bude masa kofa ya fita, ta danna bell din apartment din khaleel sannan ta juya ta koma ciki da sauri, Shureim na tsaye bakin apartment din khaleel ya bude kofar, dukawa yyi yana kallon yaron murmushi dauke fuskarsa yace "Good morning handsome" Shureim yace "Good morning uncle, Antyna tace in kawo maka" karba yyi yana kallon flask din sannan ya jawo yaron ciki, Shureim yace "Uncle tace it's remaining one" rufe kofar yayi yace "Kyaleta xata kawo da kanta" Khadija tayi ta jiran dawowan Shureim amma shiru, mikewa tayi ta bude kofa ta leka waje a hankali taga kofar apartment din nasa a rufe, kiran Shureim ta shiga yi, Shureim dake xaune yana cin bread and butter da khaleel ya basa da shayi ya mike da sauri yace "Uncle Anty is calling me" xaunar da shi yyi yace "Don't worry she will come in now" Khadija ta gaji da tsayuwa amma Shureim bai fito ba, komawa ciki tayi ta rasa yanda xata yi da Irish da ta dibar ma khaleel, daga karshe ta wuce kitchen ta dauko ta sa hijab ta fito waje, tsaye tayi tana kallon baturiyar dake bakin apartment dinsa, baturiyar ta mata murmushi tace "Good morning" dauke kai Khadija tayi kamar ana tilastata tace "Morning" xata koma ciki sai gashi ya bude kofar, Kallon Khadija yayi kafin ya dubi baturiyar dake masa murmushi tace "Good morning Dr Ayman...." Juyawa Khadija tayi ta shige apartment dinta ta rufe, Khaleel na kallon baturiyar yace "Morning Lydia, hw did u knw I am back?" Tace "I just met with Dr Ahmad, he told me you are back" shafa kai khaleel yayi a hankali yace "Ohk, we will meet later in the day, I am about going out now" tace "Ohk do you mind dropped me?" Ya girgixa kai yace "You get a taxi" daga haka ya rufe kofarsa, yana ta tsaye bakin kofa bayan kusan minti biyar ya bude kofarsa ya ga ta wuce, fitowa yayi yana kallon kofar Khadija, a hankali ya murda ya ji a bude ya shiga parlorn.
Not edited.🤷🏻♀
Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta inda xata fito amma bata fito ba, karasawa yayi kan kujera a hankali ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe manyan idanuwansa, bayan wani lkci sai ga ta ta fito daga daki da hijab a jikinta, mikewa yyi yana kallonta amma bai ce komai ba, Babu yabo babu fallasa tace "How may I help you?" Yana shafa lallausan gashin kansa a hankali ce "Where is.... the food?" Tace "Wani abincin? I didn't cook with you ai" ya d'an kalleta na few seconds sai kuma ya nufi kitchen cikin takunsa na kasaita ta bi sa da ido, rike da warmer din Irish din ya dawo yana dubanta yace "This" daga haka ya bude kofa ya fita ta bi sa da harara ta ja tsaki. Khadijah na ji suka fita gidan da Shureim wajen karfe goma, kafin sha daya ta gama duk abinda xata yi a gidan ta kwanta duk da ta so tafiya makaranta amma ta bari gobe kawai, ganin bacci ya ki xuwa mata ta dauko kayan karatun ta ta shiga yi, tana ta xaune har azahar yayi, ta mike daga karshe ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta kwanta, lkci daya bacci ya dauketa. A hankali khadijah ta bude idonta bayan wasu awanni ta mike xaune cikin sanyin jiki tana tunanin mafarkin da tayi, bell taji an danna wanda hakan sai da ya d'an tsorata ta, bayan wasu yan dakiku ta mike tsaye da kyar har lkcn mafarkin ya kasa fita a xuciyarta, jin an kara danna bell din ta sa hijab ta fita kamar mai counting steps dinta, tana isa gun kofar ta bude a hankali, Vanessa da Angela sai Maryam ta gani bakin kofar, sosai gaban Khadija ya fadi ganin Maryam bakin kofar, da farko kallonta ta dinga yi, sai kuma ta kirkiri murmushi tana masu sannu da xuwa ta basu hanya suka shigo parlorn, mamaki ta dinga yi a ranta, me ya kawo Maryam gidanta, after all she isn't her course mate nor her frnd, bayan sun gaisa suka mata gaisuwar Sudais, khadijah ta mike ta wuce kitchen don kawo masu ruwa da cakes din da ta siyo daxu da safe da ta fita, Maryam na kallonta tace "Mumy tace da daya twin din kika taho koh?" Ba tare da Khadija ta kalleta ba tace "Ehh tare muka xo" Maryam tace "Yana Ina?" Khadija tace "Ya fita ne" Maryam bata sake cewa komai ba, Khadija suka dinga hira da su Vanessa, sai dai hirar duk ta makaranta ce bayan kusan minti talatin suka ce mata xa su koma, har waje ta rakasu inda xa su samu cab, wani cab ne yyi parking dai dai su, aka bude cab din khaleel ya fito tare da Shureim da wani leda hannunsa, kallonsa kawai Maryam take, ya wara ido ganinta yace "Isn't this Maryam?" Yar dariya tayi tace "A nan anguwar kake dama Dr khaleel?" Yace "Sure, me kika xo yi nan?" Ta nuna masa Khadija tace "My frnd, mun xo mata gaisuwa ne yaron ta ya rasu" ya kalli khadijah yace "Ohh that's nyc, a schl kika santa kenan" Maryam tace "Eh a schl na santa" yace "Good" Maryam ta karasa gun Shureim tana kallonsa a hankali tace "Hello boy" gaisheta yayi, ta amsa tana murmushi jin muryarsa kamar na Aliyu, Su Vanessa ma suka taho gunsa duk ya gaishe su da turanci, ita dai Khadijah na tsaye, Khaleel na kallon Maryam yace "Alryt bari in shiga ciki Maryam, sai anjima" tace "Yauwa Dr, ya mutuniyar fa?" Har ya fara tafiya ya tsaya yace "Wai jawahir?" Tace "Ehh" yace "Haba ai ke ya kamata in tambaya, kun fi kusa" Maryam tace "Au haka ma xaka ce" Yace "Yes, nasan yau ma baxa ku rasa waya ba ni kam bata kira ni ba" Maryam tace "Lallai ma, ita ce ma xata kira ka kenan, soon ma xa su xo hutu nan da yayarta ar" Khaleel ya d'an kalleta yace "Really?" Girgixa kai Maryam tayi tace "Dad dina naji ya fadi haka nima" Ya dauke kai ya nufi cikin gida yana rike da Shureim yace "Allah ya kawo su lafiya" Taxin da Khaleel ya sauka suka hau Khadija ta daga masu hannu tace "We'll meet in school tomorrow, thank ya all" daga haka ta wuce ciki. Khadija na kitchen tana girkin lunch khaleel ya taho ya tsaya gun window yana kallonta yace "Ya kike?" Dauke idonta tayi daga kallonsa tace "Lafiya lau" Shureim dake kusa da shi a tsaye yace "Anty I am missing you" Khaleel yace "Bude masa ya shiga" kallon Shureim tayi sannan ta ajiye wukar hannunta ta isa gun kofar ta bude, Khaleel ya shigar da Shureim ciki sannan ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, ya jawo kofar ya rufe gam, ya jinginar da ita jiki yana mata wani kallo murya can kasa yace "Ni kike daga ma hanci" A tsorace tace "Kaga bana son haka ka bari, ka kyaleni plss" Duk ta kasa kallon idanuwansa da ya tsare ta da shi ga kamshin sa da ya cikata, A hankali yace "Fushin me kike yi da ni?" cikin rawar murya tace "Toh Fushin me xan yi da kai Dr, don Allah ka sakeni" d'aga kanta yayi tayi saurin runtse idanuwanta xuciyarta na bugawa, ya dinga kallon lips dinta, a hankali ya saketa yace "Where did you know Maryam from?" Ta shiga kokarin bude kofarta da sauri, ya rike handle din kofar yace "Au Ina maki magana xaki wuce?" Ta juyo kamar xata yi kuka tace "Ni ban santa ba sosai fah, kawai ina ganinta ne a schl kawar course mates dina ce" yace "Ohk, don't frnd her for some reasons kin ji?" kallonsa tayi da sauri, lkci daya tayi saurin kauda kanta xuciyarta na bugawa, his eyes are always not encouraging, d'an murmushi yayi a hankali yace "Ki gaya min meye da idona Khadijah?" Ta hade rai tace "I don't like them" wani murmushin yyi kamar me rada yace "Xan koya maki son su" murda kofar yayi ya bude ta juya da sauri ta shige kitchen din ta rufe kofar da makulli fuskarta daure. Shureim na cin abincin da ta xuba masa bayan magrib yace "Anty uncle yace gobe xan fara xuwa schl, we even went to the schl, uniform din na gidansa, in je in karbo?" Khadija dake ta kallonsa tace "I didn't send you" yace "Ohk" sannan ya ci gaba da cin abincinsa. Washegari da asuba khaleel ya miko mata uniforms din Shureim ta kitchen, rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta karba tana kallonsa a hankali tace "Mun gode" ko kallonta bai yi ba ya wuce. Karfe takwas saura khaleel yayi dropping Shureim a makarantar da yayi enrolling dinsa, Khadija dake xaune bayan motar ta bi Shureim dake daga mata hannu da kallo har aka wuce da shi cikin makarantar, khaleel yayi parking in da ya saba ajiye ta a schl ya juya yana kallonta, ta bude motar a hankali ta fito,, bata ce komai ba ta kulle motar ya ja motarsa ya bar wajen, a sanyaye ta karasa department dinsu don saura few minutes a shiga lectures. Karfe sha biyu saura Khadija ta fito daga lectures, cafeteria ta tafi ita kadai ganin Maryam na tare da su Vanessa, tana xaune ita kadai a cafterian da lemonade a gabanta idonta a kan wayarta tana dannawa, kujerar dake kallon nata taga an ja ta daga kai da sauri, sosai gabanta yayi mugun faduwa bayan sun hada ido, tayi saurin dauke idonta, xaunawa yayi yana kallonta a hankali yace "Hi Iman" kasa cewa komai tayi ta kuma kasa dago kanta, bayan few seconds ta dago da kyar tana dubansa tace "Hello" Murmushi yayi yace "Ya boko?" Kasa amsawa tayi lkci daya little Sudais dinta ya fado mata, taji xuciyarta ya mata rauni, ganin tayi shiru ya fiddo wayarsa ya fara dannawa, a hankali tace "Ya su mumy" yace "Na baro su lafiya, how is Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Har kinyi enrolling dinsa a nan?" Tace "Ehh" shiru ya d'an yi, kafin a hankali yace "How much did you spend Iman?" Ta kallesa lkci daya ta hade rai tace "What about it?" ya girgixa kai da sauri yace "Ohk, I am sorry I asked" bata ce komai ba, ya mike yana kallonta yace "Alryt, I will be on my way now Iman, my regards to Shureim" da ido ta bi sa, har ya tafi ya dawo da sauri ya sa hannu a aljihunsa yace "I think I've got something here" Chocolate guda daya ya fiddo ya duka yana kallonta ya mika mata yace "Ki ba Shureim plss" a hankali ta sauke idonta daga kallonsa ta karbi chocolate din tace "Ohk" yace "Thanks" daga haka ya mike ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya bace mata, kallon chocolate din hannunta tayi ta bude jakarta ta saka a ciki, tayi tagumi tana tunanin me yasa in dai ta ga Aliyu sai little Sudais dinta ya fado mata, or is it because of the resemblance, jin wayarta na ring ta sauke kai a hankali tana kallon mai kiran nata.
Sorry for the short chappy kilan in kara post around one na dare😦
A hankali khadijah tayi picking wayar ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Ya kike Amira?" Khadija tace "Alhmdllh ya aiki?" Yace "Lafiya lau, account number ki xa ki turo min yanxu" shiru ta yi na wani lkci kafin tace "Barrister.... Shureim fa yana da kayan sanyi, wllh you shouldn't bother...." Katse ta yayi yace "I am not asking for you opinion Khadijah" a hankali tace "Toh shkkn, ya Amira fah?" Sudais yace "Tana gun ummanta" bai karasa maganar ba ya ga jiddah tsaye kusa da dinning din da yake xaune tana kallonsa, ya dauke kansa yace "I will call you later Amira" katse wayar yayi ya ajiye, jiddah tayi dariya tana tafe hannu tana masa wani kallo tace "Cin amanar har cikin gidana Aliyu?" Sudais bai kalleta ba balle ya tanka ta, lkci daya idanuwanta suka kankance tace "Toh ko ma wace yar iskar ka samu wlh wlh sai tayi da ta sanin sanin ka a rayuwar ta, sai na nuna mata tayi kadan tayi kishi da ni, ba ma xai yiwu bane, mu xuba da ita sai dai idan ba mijina take cusa ma kanta ba" mikewa yayi yana kallonta yace "Wannan da kike gani wllh ta fi ki k'ima a idanuwana Jiddah, kuma kina nan xaki ga ta shigo gidan nan ta koya maki yanda ake kula da miji" bai sake sauraranta ba ya bar parlorn, jiddah ta kasa tsaye gu daya, ta ja kujera ta xauna da kyar xuciyarta na tafarfasa, lkci daya tayi wani murmushi tace "Babu boka babu malam, amma kai xaka bata shawarar ta rabu da kai, mu dai je xuwa, da kuluwa take xancen" Har khadijah ta iso gun motar khaleel idonta na kansa, shi kuma yana jingine jikin motar yana danna waya, bai san ta iso ba kawai kamshin ta ya ji, ya daga kai yana kallonta, a hankali tace "Good evening" ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ya lectures?" Tace "Alhmdllh, karfe nawa su Shureim ke tashi?" Ya buda ido yace "Ke fa yarinyar nan baki da kara" turo baki tayi tace "Toh me nayi, am just asking" yyi murmushi yace "Daga nan xa mu dauko sa, yanxu suke tashi su ma" ta karasa ta bude front seat ta shiga, shi ma ya shiga motar ya tada suka bar wajen, har suka iso makarantar shureim khaleel bai ce komai ba ita ma haka, ya bude motar ya fita, ba a dau lkci ba suka dawo tare da Shureim, xagayowa Shureim yayi ya bude inda khadijah take xaune ya rungumeta yace "Anty good afternoon" ta shigo da shi cikin motar ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa da murmushi tace "How you sweetheart?" Yace "Fyn Anty, I love the schl, I wish Sudais will come here also, am really missing him" Khadija bata ce komai ba, inda sabo ta saba, don bbu ranar da xai wuce Shureim baxai mata xancen Dan uwansa ba, he is always wishing Sudais is with him, lkci daya chocolate da Aliyu ya bata ya fado mata, ta bude jakarta a hankali ta fiddo chocolate din ta mika masa, karba yyi cike da jin dadi yace "Waow, Anty ke kika siya min?" Girgixa masa kai tayi tace "No" ya wara ido ya juya yana kallon Khaleel dake driving yace "Uncle kai ka siya min?" Khaleel ya kallesa yyi murmushi yace "No bani bane" Shureim ya mayar da dubansa kan Khadija yace "Toh Anty waye ya siya min" Khadijah tace "Idan baxa ka ci ba bani in cinye" Shureim ya bude chocolates din yace "Noo Anty ina so, ai irin wanda kind uncle din nan yake ba mu a gidansu maman nan ne, he told me his name is Dr Aliyu, Anty ina son a kai ni gidansu a Nigeria" Ita dai khadijah kallon yaron kawai take, ya gutsura ma khaleel ya mika masa yace "Uncle taste it" khaleel yyi murmushi yana girgixa kai yace "Noo thanks son, cinye abun, ko Anty kar ka ba" dariya yaron yayi bai ce komai ba, can ya kalli Khadija, alama yayi mata da ta bude bakinta, tayi murmushi ta bude masa bakin ya sa mata chocolate din a hankali yana satan kallon Khaleel. Suna isa gida bayan khaleel yyi parking khadijah ta bude motar ta fito tare da Shureim tana kallonsa murya can kasa tace "Thank you" fitowa yayi yana mimicking din muryarta yace "Thank you" daga haka ya rufe motarsa, hararansa ta fara yi sai kuma tayi murmushi ta wuce apartment dinta rike da hannun Shureim, ya jingina da mota ya rungume hannayensa ya bi su da kallo. Tun da Khadijah ta fito daga lectures yau take xaune cafteria ta rasa dalili, har lkcn lectures din karfe biyu yyi tana xaune gun bata tashi ba, Maryam ce ta shigo cafterian tare da wata kana ganinta kasa yar Nigeria ce, Maryam na ganin Khadijah tayi murmushi tace "Khadijah kina nan ashe, ya lectures?" Khadija tace "Alhmdllh ya naki?" Maryam tace "Alhmdllh" Maryam ta kalli yarinyar dake gefenta tace "Deejah meet ur namesake Khadija, tana studying pharmacy ne a nan, she is also a Nigerian from kaduna" Warce Maryam ta Kira da Deejah tayi murmushi tace "Its nyc meeting you namesake" Khadija tayi murmushi sosai tace "Nyc meeting you too" gun Khadija