Showing 3001 words to 6000 words out of 234058 words
murmushi tace "But he said I can hand it over to you, I just gave him a call now..." kallon litattafen na tsaya yi gabana na faduwa, Clara tace "Yeah, i am travelling today, and i can't go with his material" Khadijah dai ba don ranta ya so ba ta karba, Clara ta mata godiya ta juya ta wuce, Khadijah ta rufe kofarta, nan kan kujera ta ajiye books din a parlor. Ta fito daga wanka misalin karfe takwas da wani abu aka danna bell, tsaye tayi da mamaki tana tunanin to waye kuma wannan, jin an sake dannawa ta xura Hijab ta fito parlor tace "Who?" Ba a ce komai ba hakan yasa taki karasawa, ga xuciyarta da ya fara bugawa, aka kuma danna bell din, dakewa tayi tace "Who's there?" A takaice taji muryarsa yace "Somebody, open right away" mamaki ya cika ta sosai har lkcn kuma xuciyarta bai daina bugawa ba, tayi karfin halin cewa "So? What did you want from me?" Yace "Open now" A fusace tace "Did you miss ur road!" Yace "Did you knw I can open the door my self?" hankalinta yyi mugun tashi, kamar xata yi kuka tace "And did you know I can also report you to the police right away" cikin tsigar rainin hankali yace "Ohh really? ohk then, let me get the door open for u so you can have ur way to d police" baya ta koma da sauri cikin rawar murya tace "Plss stay away from me, I don't knw you" hawaye cike idonta ta kare maganan, shiru bai ce komai ba, har ta fara tunanin ya wuce ne tana nan tsaye dai kamar an dasa ta don ta dade bata shiga tashin hankali irin na lkcn ba, can cikin husky voice taji yace "Then.... I want to get my reading materials from you" da sauri ta kalli textbooks dinsa da ta ajiye daxu, gaba daya ta mance da su, ta hade rai kamar yana ganinta tace "Sorry, i can't open my door now, you'll get it tomorrow at ur door step" yace "You must be joking, wil u get that door open and hand over my property to me" mamaki ya cikata tace "Sorry I can't" yace "This is serious" juyawa tayi ta koma kan kujera ta xauna, sai dai fa gabanta faduwa yake, bayan kusan second talatin yace "Look I am having exams, and I need those books" banxa tayi masa, a hankali taji yace "Alryt... Plss" shiru ta yi tana naxari d'an ita gaskiya tsoro take, can tayi tsaki ta kwashi books din ta nufi kofa, gabanta sae faduwa yake ta bude a hankali tana karanto addu'o'i a xuciyarta, tana bude kofar taji ya cafko ta, ta yi wani ihu ta saki books din hannunta jikinta na rawa, ya rungumota firmly har tana iya juyo numfashinsa, turasa ta shiga yi hankali tashe ta dinga cewa "Let go of me...." ya ki saketa yana kallon kwayar idonta fuskarsa daure yace "Isn't this what you're afraid of?" Yatsine fuska yyi ya turata yace "I am waiting for the police" daga haka ya duka ya kwashe books dinsa, tuni ta shige ciki dai dai lkcn da ya mike tayi banging kofarta ta sa lock, ya ja baya da sauri yace "Damn it..... What a f**k... I will get you" Da gudu ta koma daki kamar ya biyota din nan, ita kadai tasan irin tsoratan da tayi. Gaba daya ta kasa bacci har kusan karfe daya gashi ko wanka bata yi ba balle ta sauya kaya xuwa na bacci, duk kamshin turarensa ya cika ta tun rikon da ya mata, ko ta ya ta juya kamshin kawai take ji, a hankali ta tashi kamar mara laka ta cire kayan jikinta ta shiga toilet, wanka tayi ta fito ta xura rigar bacci ta kwanta bayan ta feshe jikinta da turarrukan ta, sai a sannan bacci ya dauketa. Sai kusan karfe bakwai ta tashi washegari ta mike da sauri ta shiga toilet tana salati ganin ynda ta makara, karfe takwas da rabi ta fito shirye cikin doguwar rigar kanti kamar ko da yaushe, blue ne rigar mai stones baki, sai white veil da ta daura kanta, takalminta ma fari ne haka karamar jakar hannunta sai handouts dake hannun, kana ganinta kasan a tsorace take, ta rufe kofarta da sauri ta nufi gate dai dai nan suka kusa cin karo xai shigo, sosai gabanta ya fadi ta juya kamar kiftawar ido har ta bar bakin gate din, can gun da aka tanada domin parking space a gefen apartment dinta ta nufa sannan ta juyo tayi iya kkrin ganin ta boye tsoron fuskarta tana kallonsa tayi kicin kicin da fuska, lkci daya ta karasa kofarta ta ga ya nufo wajen, tsabar rikicewa ta kasa bude jaka ta ciro makulli sae rawa hannunta yake, ta fashe da kuka ganin ya kusa wajenta tace "Am begging you stay away from me plss, I don't know you.... Stay outta my way" har ya karaso gun bata iya ta motsa ba, kawai ta durkushe kasa ta rufe ido, jin ya bude kofar sa ta dago da sauri, suka hada ido yace "I only have ur time at night" daga haka ya shiga ciki ya rufe kofarsa ta mike a sanyaye tana kallon kofar, da sauri ta fice compound din gabanta na faduwa. Suna gama lectures ranan tace da Vanessa a gidanta xata yi spending night din, don haka tare suka wuce gidan Vanessa dake Round church street, Vanessa tayi masu girki suka ci bayan Khadijah tayi sallah, karfe shidda saurayin Vanessa ya xo gidan Khadijah ta shiga bedroom ta bar masu parlorn, har ta fara bacci Vanessa ta tada ta wai Richard xae kai su shopping, duk yanda Khadijah taki amincewa aje da ita sai da Vanessa tayi convincing dinta suka fita tare, turarurruka kawai ta deba a mall din, sun yi kusan minti sha biyar kafin Vanessa ta gama siyayyar da xata yi suka bar mall din, gun siyar da ice cream suka tafi daga nan, Suna tsaye cikin Aromi ba a kai ga siyar masu cold stone ice cream din da xa su siya ba kamar ance ta juya suka yi ido hudu da neighbor dinta, xaune yake da wata kyakkyawar baturiya da baxata wuce ashirin ba ga kayan ciye ciye a gabansu yarinyar na rike da hannunsa cikin nata, tun daga sama har kasa yake kallon khadijah, ta hade rai tayi saurin dauke kai ta amshi ledan ice cream din da Vanessa ke mika mata, Richard ya siya masu har da pizza ya biya bills din, tuni ta yi hanyar fita Vanessa na biye da ita, ta d'an saci kallonsa taga kallonta yake yana wani murmushi ta jefa masa harara suka fita wajen, motar Richard suka shiga ya mayar da su gida. A gidan Vanessa tayi weekend din gaba daya, ranan lahadi ta shirya ta koma gida ba don ranta ya so ba, duk da a xuciyarta dama niyyar dawowa ta kwaso kadan daga kayanta ta dawo gidan Vanessa tayi, tunda taxi ya ajiye ta gabanta ke faduwa kamar mai tausayin kasa ta dinga tafiya tana waige waige duk da bata ga motarsa ba hankalinta ya ki kwanciya, tana kkrin bude kofa taji an bude nasa kofar a gigice ta sakko kasa dai dai lkcn da yarinyar da ta gani a eatry ranan ta fito daga parlornsa, yarinyar tace "Hello, seems I frightened you" banxa Khadijah tayi mata da farko can kuma tace "Never mind" daga haka ta shige apartment dinta bayan ta bude, bin parlorn ta dinga yi da kallo ganin ya d'an yi k'ura, kawai tayi deciding ta gyara ko ina kafin ta bar gidan, ta tsaftace ko ina ta goge, sannan tayi wanka ta canxa kaya ta fito parlor, kitchen ta shiga jin tana jin yunwa, cikin mintuna kalilan ta hada ruwan jollof din cous cous da yaji nama ta dawo parlor ta kwanta, har bacci ya dauketa ta farka da sauri don ko cous cous din bata xuba ba, ta dawo parlor bayan tayi hakan bacci ya sake saceta, cikin bacci ta dinga jin k'auri, ta shi da sauri ta nufi kitchen din, turus tayi komai nata ya tsaya ganin wanda ke tsaye bakin gas, wani ihu tayi ta juya cikin rikicewa xata fita ya fixgota, ya matse ta jikinsa ya rufe bakinta, kasa kwakkwaran motsi tayi ta kuma kasa freeing kanta, hawaye ya cika idonta taji kafafuwarta sun kasa daukarta, yana mata wani kallo cikin husky voice nasa yace "Kin gama gudun kin dawo?" Xaro ido tayi tana kallonsa da mugun mamaki, bai damu da hakan ba yace "All this while kina gidan boy Friend din ki right?" Takaici ya rufe ta dake tace "Yess" yyi wani murmushi yace "Kina me?" Tace "Abinda kke kawo yan mata suke yi a flat din ka...." Ko rufe baki bata yi ba ya hade bakinsa da nata, ta rude ta dinga kokuwa da shi amma ko gezau, don kansa ya saketa yana kallonta da lumsassun idonsa yana murmushin rainin hankali yace "Haka kenan" ta fashe da kukan takaici ta durkushe a wajen xuciyarta na tafarfasa, yace "Next time ba sai kinje gidan saurayin ki ba, you need it... Ki sameni a flat dina kawai" daga haka ya nufi kofa, sai kuma ya juyo yace "Mind you, I hate smell of burnt foods" yana kai wa nan ya fita gidan gaba daya cike da kasaita, ta mike da sauri ta na kallon kofar don a tunaninta ta rufe da ta shigo.
*Haske Writers association*💡
*Haske Writers Association*💡
✨ *Noor-Al-Hayat*✨
_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
4......
Ta fi minti biyar a tsaye duk jikinta a mace, tunani daya ya xo xuciyarta a lokacin and that is ta bar apartment din ta koma gun Vanessa da xama gaba daya har ta samu wani gidan, ta juya ta kalli gas din kitchen din taga ya kashe, kamar mara laka ta fito parlor ta karasa kofa ta sa key, xaunawa tayi parlor har lkcn tana ganin abun kamar a mafarki, ita fa yanxu bata ga namijin da ya isa ya takura ma rayuwarta, ba ayi namijin nan ba ko waye shi kuwa, tunanin hakan yasa ta yi murmushin takaici hade da jan tsaki ta mike ta wuce daki, nan ma dai xaunawa tayi gefen gado ta kasa daina mamaki, kiss kuma? how dare him kiss her? Haka nan kawai yayi kissing dinta kuma ta kyalesa, hawaye ne ya cika idonta tuna hakan da tayi, ca tayi masa ita gantalalliya ce? Ko kuma xaman kanta take a k'asar? ta xamo kasa ta jinginar da kanta da gado xuciyarta na kuna, to yanxu wa xata kai ma kukanta a kasar nan, nobody in particular, Vanessa won't take this as anything ko ta gaya mata ma dariya xata mata, Yusuf?? ji tayi ranta yyi wani mugun baci da ta tuna yaren da yyi mata, wai a hakan shi bahaushe ne ko kuwa Hausa kawai ya ji, abinda ta kasa ganewa kenan, ta kuma jan tsaki a xuciyarta tace ai sai dai kawai ya ji Hausan don in har dai shi Afuno ne he is nothing but a disgrace to Hausa and Hausa land as a whole, infact ta ma san ba bahaushe bane.... har kusan goma tana xaune kamar mara abun yi, xuciyarta dai ya kasa dawowa dai dai, ta Dade ranta bai baci ba irin na yau, can dai ta kuma jan tsaki for the countless time tace "Sai nayi maganinka kafin in bar gidan nan in sha Allah, you can't just put ur filthy mouth in mine and go scot free...." daga haka ta mike ta shiga bathroom, wanka ta yi ta dauro alwala ta fito ta yi shafe shafenta ta xura doguwar Riga ta tada sallahn Isha, ko da ta idar ta shafe addu'o'in da tayi ta jawo wayarta don sau biyu ana kira tana sallan, Vanessa ce ke kiranta, ta shiga kiranta baya, Vanessa na dagawa tace "Hey love, you are still nt yet back" Khadijah ta kalli agogo a hankali tace "It's late Vanessa, I will come over tomorrow" daga haka Vanessa tayi mata sai da safe ta katse wayar, sai a sannan taji ta fara jin yunwa, ta mike ta fita xuwa kitchen don duba girkinta na daxu, tsaye tayi ta kasa kunne jin kamar muryar mace a kitchen dinsa da yake ko ina was very silent, a hankali ta karasa jikin window ta kafa kunne, nan ko ta kara tabbatar da hakan, muryar mace take ji, ta rike ha6a da mamaki k'ana ta kyabe baki ta dau plate ta debi abincin da xata diba ta fita kitchen din, tana gama ci ta tafi daki ta hada gaba daya kayan sawanta a jaka biyu, tana shirin kwanciya wayarta yyi kara, ta dauka tana kallon screen din sannan ta xauna gefen gado ta daga kiran hade da sallama, a hankali tace "lafiya lau Umma ya gida" Daga daya bangaren warce ta kira da Umma tace "Alhmdllh, na ma yi tunanin kin kwanta, ya karatun" tace "Alhmdllh Umma, yanxu xan kwanta" Umma tace "Toh Allah ba mu alkhairi, a dai dinga kula sosai kinji" cikin sanyin murya tace "Toh Umma" daga haka suka yi sallama ta katse wayar, kwanciya tayi hade da rufe duk jikinta da duvet har lkcn ranta ba dadi. Tun da ta idar da sallan asuba bata koma ba kasancewar da safe take da lectures, ta yi wanka ta wanke bathroom dinta sannan ta fito xuwa kitchen don tsaftace sa shi ma, wanke duk utensils da ta 6ata jiya tayi sannan ta hada bin din gaba daya a kwandon da aka tanadar don haka, Hijab ta koma ta xura kan yar rigar jikinta ta dawo kitchen din ta bude kofar ciki ta fita don disposing sharan dustbin, still tayi ganinsa a wajen, ya ajiye weight din hannunsa tana ganin haka ta juya da gudu ta koma kitchen ta rufe kofar da makulli hannunta na rawa, tsaye yayi jikin window din kitchen dinta yace "Ga Beast ko monster koh?" Ko kallonsa bata yi ba, ta kashe fitilar kitchen din ta fita parlor ta yi banging kofar da karfi ta rufe. Yayi wani murmushi yana share xufar forehead dinsa, Komawar da ba ta yi kitchen din ba kenan har ta gama shirin makaranta, Abaya ne baki da mayafinsa sanye jikinta, duk da yunwar da take ji haka nan ta dau jakarta ta nufi kofa, a hankali ta murda makullin ta bude ta leka waje sannan ta fito tana karanto addu'a a xuciyarta, ta gama rufe kofar kenan, wata baturiya da baxata wuceta ba ta fito daga apartment dinsa, ba karamin faduwa gabanta yyi ba don a tunaninta shine, 'yar riga ce iya cibi da wando jikin baturiyar sai yar karamar jaka da litattafai a hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba har ta sauka d'an stairs din dake wajen, taji yarinyar tace "Good morning" yi tayi kamar bata ji ta ba tayi wucewarta, taji yarinyar na cewa "Is she having difficulty in hearing?" sai a sannan Khadijah ta gane shi ma ya fito kenan, hakan yasa ta kara saurinta, taji yace "I think so" tuni ta fice daga gidan ta tsayar da cab ta hau ta gaya masa inda xa ta, ya ja cab din, a xuciyarta tace In sha Allah ma this is the end, ba lallai ma ta kwana gidan ba yau, don tana dawowa makaranta dama fiddo kayan ta xata yi ta yi wucewarta gidan Vanessa, but she promise before leaving xata koya masa lesson xata gwada masa cewar ba ko wace mace ce sha sha sha kamar sa ba, abinda ta lura da xaman k'asar shine gwara a hadaka da bature waje daya sau dubu a kan wanda ku ka fito k'asa daya. Xaune Khadijah take tare da Vanessa da wata course mate dinsu Angela, sai wata Maryam 'yar Nigeria kamar ta amma kuma a nan UK aka haifeta, ko kadan Khadijah bata yarda sun saba da Maryam ba, hasalima gaisuwan kirki bai hadasu, ita kanta Maryam bata sake da ita ba, amma kilan hakan na da nasaba da cewar ba course daya suke ba, duk da haka dama can yarinyar bata ma Khadijah ba, ba wai tana da wani aibu bane ko wani abu, kawai she just don't like her ta rasa dalili kuma, don so tari ma idan ta ganta sai taji faduwar gaba, sannan ganin ta na tuno mata da wani abu da ba ta son tunawa a rayuwarta gaba daya, yanxun ma su kadai suke hirar su, ita dai tana ta danna wayarta kanta a sunkuye, duk ta kagu Vanessa ta tashi su tafi, dama can Angela ba kawarta bace, don she is too lousy to be kept as friend, d'an gaisuwar da suke ma da ita ta dalilin course dinsu daya ne, gajiya tayi daga karshe ta mike ganin Vanessa bata da niyyar tashi da halshan turanci tace mata xata je can gidanta ta dau kayan da xata dauka sai su hadu a can gida, Wato gidan Vanessa din, Vanessa tace to sai sun hadu, daga haka ta fara tafiya, Angela tace "See yahh tomorrow Pretty" sunan da wasu ke kiranta da shi kenan a makarantar, Juyawa Khadijah tayi ta kirkiri murmushi tace "Sure" daga haka tayi wucewarta Maryam ta bi ta da kallo. Karfe biyu da yan mintuna ta isa gida, ta fito ta ba mai cab kudinsa, a hankali take jin faduwar gaba har ta shiga ciki tana kallon parking lot ta ga bbu motarsa, ajiyar xuciya ta sauke ta nufi flat dinta da sauri don ta yi abinda ya kawota ta bar gidan, da d'an mamaki take kallon farar matar dake tsaye b'akin apartment dinsa matar na rike da wata kyakkyawar yarinya kamar ta, lkci daya kuma tana kuma danna wayar hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba ta shiga kokarin bude apartment dinta, a hankali matar tace "Hi" sai a sannan ta juyo ta kalli matar, ita dai matar ga ta kamar fulani kamar kuma balarabiya, idanuwanta kuma kamar na neighbor dinta, Khadijah ta dauke kai tace "Hello" matar tace "Plss Dr Ayman, will he be back anytime soon?"