Showing 15001 words to 18000 words out of 234058 words
jikinta yyi sanyi, yanxu fa komawa yaran xa su yi su bar ta, su kansu sai bata rai suke suna shisshige mata, shi ya rakasu daga karshe don ita kam kasawa tayi, sae d'aga mata hannu yaran suke, kasa daurewa tayi bayan tafiyarsu ta hade kai da gwiwa a inda take xaune, bayan kusan minti goma Khaleel ya dawo, muryarsa taji yace "Heyy" ta dago kanta a hankali, ya d'an bude ido yace "Waow, kuka kike?" da sauri ta goge idonta don bata san ma tana yi ba, yyi murmushi yana shafa kai yace "Su ma kinga kukan suke, Ashe sun ji a jikinsu kina kukan ne" tashi tayi da sauri tace "Kuka suke?" yace "Yea but I made sure sun yi shiru before I left, the bond between u and ur Siblings is really amazing...." daga haka ya fara tafiya yace "let get home" bin bayan sa tayi a sanyaye har suka isa gun motar sa, a hankali ta sa hannu ta bude front seat ta shiga, babu wanda yace komai cikin su yana driving, tsaki yyi bayan wani lkci ya jawo wayarsa dake ta ring tun fara driving dinsa yyi silencing wayar ya ajiye, ita dai tayi nisa tunanin da take na su Shuraim, yana gama parking a gida murya can kasa tana wasa da yatsunta a hankali tace "Thank you very much, Allah ya saka da alkhairi" kamo hannunta yayi yace "For?" Ta fixge hannunta hade da galla masa harara daga haka ta bude motar ta fita ta nufi flat dinta ya bi ta da kallo ta madubi. Tun da ta shiga bedroom dinta take bacci har azahar, biyu da rabi ta tashi ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana gabatar da sllhn zuhr ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, ko ba a fadi mata ba tasan ita kadai ce gidan coz everywhere was very silent, ta gama cin abinci ta dau materials din karatunta don rabonta da karatun tun xuwan kids din, gashi yau ma tana da lectures bata je ba, sai sha biyu saura na dare ta hakura da karatun ta kwanta don gobe da safe take da lecture. Washegari takwas saura ta fito xata wuce makaranta, dai dai fitowarsa shi ma, suna hada ido tayi saurin dauke kai ta kara pace dinta, kafin kuma ya fito da motarsa har ta hau taxi abun ta. Karfe uku da wani abu suka fito school tare da Vanessa da Angela, sauraren Vanessa dake mata korafi ta gama yi kafin tayi 'yar dariya da halshan turanci tace mata ba wai ta fasa xuwa bane xata dawo gidan nata amma sai during weekend, ko da wasa bata nuna mata su shuraim sun xo ba balle ta sake jin haushin rashin kawo su da tayi, juyawa Khadijah tayi tana kallon direction din da Angela da Vanessar ke kallo, sai a snn ta ga motar da ya tsaya gefensu dai dai lkcn da kuma ya sauke glass, hannu ya daga ma su Vanessa a hankali yace "Hi" suka mayar masa da "Hello" Ya kalleta yace "Are you heading home?" Tunani ta fara yi shi kuma wannan yaushe suka fara yin haka da shi, wani kallo tayi masa tace "Noo thank you" wani murmushi yyi yana shafa millionaires belt dinsa yace "Ohk a gaban kawayen naki xaki ce min A'a" Tace "Ka saba daukata ne?" Yace "Xan fara yanxu, shiga mu je" tabe baki tayi bayan few seconds ta kalli su Vanessa tace "Alryt, see you girls tomorrow" daga haka ta xaga ta bude front seat ta shiga ta kulle kofar, daga masu hannu yyi ya ja motar suka bar gun, basu yi tafiya me nisa ba yace "Twins sun isa lafiya?" Ta gyada kai tace "Sure" wayarsa dake ajiye kusa da ita yyi haske ta sauke kai tana kallon screen din, "Jawahir" sunan dake saman screen din kenan ta dauke kanta, bayan seconds kusan biyar ya dau kiran yace "Am driving baby, xan kira ki when am home" daga haka ya katse wayar ya mayar ya ajiye, suna isa gida yyi parking ta bude motar ta fita ta rufe ta nufi apartment dinta, xaro ido yyi ya bi ta da kallo.
Washegari Tuesday da yamma ta shirya bayan ta dawo makaranta don xuwa shopping mall ta yi shopping din turarurruka da man shafa, karamar jakarta ta sakale kafadarta ta fito ta rufe apartment dinta, ganin motarsa a parking space yasa ta gane yana nan don tun da ya ajiyeta jiya rabon da su hadu, babban shopping complex ne wajen ta gama daukan mayuka da turarukan da xata dauka, tayi deciding hadawa da disinfectant da antiseptics, Dettol babba ta dauka bata lura da mutumin dake bayanta ba kamar yanda shi ma din da alamar bai lura da ita ba don backing din juna suka yi, lkci daya suka juyo kusan a tare suka ci karo, pack din Sabulun dettol dake hannunsa ya fadi kasa, da sauri suka durkusa kusan a tare again ta rigasa daukan sabulun kafin ya kai hannunsa tace "Ohh sorry pls, I...i..." dai dai sanda suka mike tsaye ido cikin ido, shekaru kusan hudu kenan rabon da ta ji abinda taji a xuciyarta lkcn, a hankali ta saki dettol din hannunta tana kallonsa bbu kiftawa, wani kallo shi ma yake mata da wani expression, yana son magana amma da alama words din sun kasa fitowa, lkci daya words din yyi escaping lips dinsa cikin wani yanayi yace "IMANN...." Juya masa baya tayi tana ganin turawan da ke d'an nesa da ita doubled doubled, kawai ta nufi kofar fita complex din, tana jin yana kiranta da alamar bin ta yake ta kara saurinta, cikin sarkewar murya tace ma baturen gun ta mance ATM card dinta a gida yana bude mata kofa ta fice fittt without thinking twice ta nufi bayan mall din kamar xata tashi sama, ta xauna nan kasa jikin bango ta kai hannu dai dai kirjinta ta runtse ido, ta fi minti sha biyar wajen xaune, ji take kamar an mata alluran tsayar da Adrenaline ne don komai na jikinta gani take ya daina aiki kamar ba nata ba.
*Haske Writers Association*💡
✨ *Noor-Al-Hayat*✨
_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻
10....
Hadarin da ta gani garin ya kara mata kwarin gwiwa ta tashi da kyar tana layi kmr warce ta tashi ciwo ta samu taxi bayan ta fita haraban mall din, sai da suka dau hanya kafin ta iya bude baki ta gaya masa inda xa ta, kanta ta daura a kafarta har suka isa, tana jin yana ce mata sun kawo amma ta kasa dagowa, har sai da ya fito da sauri ya bude bayan motar yana cewa "Madam, are you okay" mugun karfin hali tayi ta dago tana dubansa da idanuwanta da suka yi jajur, yace "You look sick..." Da taimakonsa ta fito taxin, bai karbi kudi ba ya ce taje ta sha drugs ta gyada masa kai ta shiga gida tana hade hanya, Ikon Allah ya kai ta bakin kofar flat dinta ta fadi dai dai kofar Khaleel tana dafe da xuciyarta da take jin kamar an caka mata mashi, bugu daya ta ma kofar ta hade kanta da kasa, bude kofar aka yi, Khaleel ya d'an ja baya yana kallonta da mamaki, saurin durkusawa yyi yace "Subhanallah, Are you okay...." Ta dago da kyar hawaye na sakko mata ta nuna masa kirjinta ya rikota da mamaki yace "Me ya same ki" girgixa masa kai ta dinga yi ta kasa cewa komai, tun tana ganin sa dishi dishi a hankali kuma bata kara ganin komai ba. A hankali ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana bin dakin da take da kallo, dai dai nan aka bude kofa wani matashi ya shigo Khaleel na biye da shi a baya, mutumin ya karaso inda take ya duka ya d'an yi murmushi yace "Hello...." Kallonsa kawai take, yace "How are you feeling now?" Tayi shiru, yace "Sannu, Allah ya sauwake, babu inda ke maki ciwo yanxu koh?" A nan ne ta gyada masa kai, ya juya yana kallon Khaleel dake rungume da hannunsa yana tsaye bakin kofar, likitan yyi murmushi yace "Quack MD do you mind coming over" d'an murmushi Khaleel yyi ya karaso kamar bai son tafiyar ya isa kusa da ita idonsa a kanta a hankali yace "ina ke maki ciwo yanxu?" Shi ma dai bata ce masa komai ba, likitan dake kusa da shi yace "Xa ki ci abu yanxu, sai yyi maki allura ya baki magani kin ji" kallonsa nayi ban dai ce komai ba, ya kara min fatan samun lfya sannan ya nufi kofa yace "Dr I will take my leave....." bin bayansa Khaleel yyi suka fita waje, da damuwa Dr Ahmad yace "But... Tayi k'ank'anta da wannan matsalar, naga kamar she is in her early 20's...." Khaleel ya sauke ajiyar xuciya yace "Probably it's an inheritance...." Ahmad yyi dariya yace "Kai kuma ina mamakin wani irin Dr ne kai wani lkcn wllh...." Dakatar da shi Khaleel yyi yace "No you ought to have known me for long, I don't treat people that are close to me, ban iya bane..." Dr Ahmad yace "Close to you? Yanxu kana nufin yarinyar nan is close to you? A ina ka santa" Khaleel yace "Noo ba haka nake nufi ba malam" Ahmad yace "Seriously you need to get rid of that behavior Dr, Allah ya bata lfya, ka sama mata abinda xata ci yanxu sai ka mata alluran ko shi ma baxa ka iya ba?" Khaleel ya hararesa yace "Wa ya sani...." dariya Ahmad yyi yace "Toh shknn ni dai bari inje in d'an yi karatu kai kam nasan tun ba yau ba ka gama, abun ka da manya" Khaleel ya shafa kai yace "Xan dai yi, tnx for ur care frnd" daga haka suka yi sallama Khaleel ya koma ciki, a hankali ya tura kofar bedroom din nasa, har lkcn tana xaune ta dago kai tana kallonsa, yace "What will you eat Khadija?" Bata ce komai ba, ya d'an yi jim yana kallonta, juyawa yyi ya fita, ba a dau lkci ba kuma ya dawo rike da cup din shayi, da kyar ta yarda tasa hannu ta karba shayin da yake mika mata ganin yanda ya kafe ta da ido, ta dinga sha kamar magani don bbu wani xafi, xaunawa yyi gefen gadon, bayan wani lkci ta mika masa sauran shayin hawaye cike idonta, ya tsura mata manyan idonsa, murya can kasa yace "Meye matsalarki Khadija, tell me what ur problem is" girgixa masa kai kawai tayi, ya mike ya fita da shayin ya dawo, allurorin ya shiga hadawa har ya gama sannan ya dawo gefenta yace "Let me inject you sai ki sha magani you will be relieved soon in sha Allah" ganin jiranta yake ta d'aga rigar a hankali ta kwanta yyi mata sannan ya dauko mata magungunan da goran ruwa ya ballar mata su ya mika mata ta karba ta sha, tashi ta shiga kokarin yi tace "Ina son xan yi sllh" ya nuna mata bathroom, ta kusa minti daya bata tashi ba bata ce komai ba, can ta mike ta shiga ta dauro alwala ta fito, Fita yyi xuwa apartment dinta don dauko mata Hijab, a hankali ya tura kofar bedroom, idonsa ya fara sauka kan enlargements dake dakin na hotuna, a hankali ya karasa dakin yana kallon cute twins dake hoton da ita kanta, sun rungumeta gaba daya tana murmushi, ya sake mayar da dubansa kan daya enlargement din da suka manna mata kiss gaba daya, dauke idonsa yyi ya dau Hijab da ya gani linke kan gadon ya fita dakin, kan gadonsa ya ajiye mata Hijab din sannan ya fita. Ta jima xaune kan darduman bayan ta idar da sallahn magrib da isha, ido ta kafe ma wani hotonsa dake gaban mirror yana sanye da farin labcoat da stethoscope rataye a wuyarsa, a hankali ta sauke idonta daga kallon hoton, can tayi wani murmushin ta mike da kyar tana dukkan kokarin ganin bata yrda hawayen dake makale idonta ya xubo ba, ta linke masa lallausan pray mat dinsa ta ajiye sannan ta dau dankwalinta dake kan gadon ta yafa ta nufi kofa kamar mai counting steps dinta ta fito parlor, xaune ta gansa kan kujeran parlorn idonsa a kan wayarsa dake hannunsa yana operating, ya daga kai ganinta yace "You want something?" Girgixa masa kai tayi tace "No, am going to my apartment, thanks for ur care" daga haka ta nufi kofa yace "But...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Are you sure you will be okay all alone" tace "Yea sure" karasawa yyi kusa da ita ya mika mata makullin hannunsa ta karba ta bude kofa ta fita ta rufe masa. Bedroom dinta ta wuce direct ta fada kan gado, sae a sannan wani kuka ya xo mata, kukan da ta kasa yi tun daxu, Allah ya sani ta samu relief sosai kukan da tayi domin kuwa taji saukin abinda xuciyarta ke mata, har lkcn ta kasa gaskata wanda ta gani, why all of a sudden. Bata wani rintsa ba daren ranan don da baccin ya dauketa xata farka a firgice, daga karshe ma hakura tayi da baccin ta dauro alwala ta yi ta sllh sae dab da asuba wani bacci me nauyi yyi awon gaba da ita.
A hankali Aliyu ya bude idanuwansa jin kwankwasa kofa da ake ta yi, ya tashi xaune yana kallon kofar yace "Who's there?" Muryar small mum dinsa yaji tana cewa "Are you okay Aliyu? Baka fito sllh yau ba" a hankali yace "Nayi a nan Anty... Was having a slight headache ne" tace "Toh Allah ya sauwake, ka fito kayi break sae ka sha magani" daga haka tayi wucewar ta, mikewa yyi yana dafe kansa da yayi masa nauyi ya nufi window ya tsaya, lkci daya ya dawo ya xauna gefen gadon ya rike kan yace "Noo, nasan ba ita bace, ba Iman bace, it's her look alike.... But...." mikewa yyi da sauri cike da damuwa da confusion yace "Why did she run then, me yasa ta gudu?? Does it mean ita ce? Ya Allah...." Jingina yyi da bango ya runtse ido, ya kusa minti ashirin a haka aka sake bubbuga kofa, ya bude ido a hankali cikin sanyin murya yace "Who's there?" Muryar Maryam cousin sis dinsa yaji tace "Yaya ni ce" yace "Ya aka yi" bata ce komai ba, hakan yasa ya karasa ya bude kofar tace "How was ur nyt?" Ya dauke kai yace "T'was good" Tace "Mumy wai ka fito ka yi breakfast" yace "Ohk" daga haka ya rufe kofar ya koma gefen gado ya xauna, kallon agogo yayi ganin takwas ya tashi ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito, ya fi minti sha biyar kwance jin kamar xaxxabi xai rufesa, can yyi ta maxa ya mike ya shirya ya dau makullin motarsa ya fice gidan ba tare da ya bari Small mum dinsa taga fitarsa ba. Mikewa xaune Khadijah tayi da sauri daga baccin da take ta dalilin bell da aka danna, ta tashi a hankali jin jiri na dibarta, ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta wanke baki sannan ta fito ta dau hijab ta sa ta fito parlor ta bude kofar, har lkcn yana tsaye gun, yana kallonta a hankali yace "Bacci kike na tashe ki?" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Na tashi" yace "How are you feeling now?" Tace "Alhmdllh, ina kwana" yace "Lafiya lau" jin yyi shiru ta dago kai suka hada ido, saurin sauke idonta tayi, yace "You cried!" Ta girgixa masa kai kawai, yace "Noo you cried malama" lkci daya hawaye ya kawo idonta ta kasa ce masa komai, shiru yyi bai sake cewa komai ba, bayan wani lkci yace "Shiga ciki" ba musu ta juya ta koma ciki ya rufe kofar, daki ta koma ta kife kai da pillow wasu hawayen na xubo mata, duk taji ta tsani xaman UK din, ta tsani karatun, dago kanta tayi da sauri ta dalilin *SUDAIS* da ya fado mata, bata san lkcn da tayi murmushi ba kawai taji kamar an yaye mata bakin cikinta, tayi tagumi a sanyaye.... Ta fi minti sha biyar a haka, ji tayi duk duniya bbu wanda ta tsana... tsanar da bata da iyaka irin wanda tayi tozali da jiya a mall, taji an bude kofa ta dago da sauri, jin shiru ta mike ta fito parlor tana goge idonta, xaune ta gansa kan kujera yana hada allura, ya dago ya kalleta, lkci daya ya hade rai , bata yrda sun sake hada ido ba, ya ajiye alluran hannunsa ya mike yace "Are you alright? under this condition stil xaki dinga xama daki kina kuka haka, dama kuka na magani? idan ma damuwa gare ki baxa ki sa Allah ran ki ba" bata iya tace komai ba bata kuma yrda ta dago ba, ya koma ya xauna, bayan kusan minti uku ya nuna mata cup din shayi da bread dake ajiye kan table yace "There" ta karaso ta dau shayin yace "With d bread" girgixa masa kai tayi ta fara shan shayin, murya can kasa yace "Look..." ta dago idanuwanta ta kallesa ya nuna mata kujera, a hankali ta karasa ta xauna, ajiye cup din tayi bayan ta sha shayin, yace "ur injection" tashi tayi ta wuce daki ta daura xani cikin Hijab din jikinta ta fito, nan parlorn yayi mata alluran ya bata maganinta, yace "You go get some rest now, ki yi bacci da yawa kin ji" yyi kasa da murya yace "And please kar sake kuka ur condition isn't encouraging, always remember Allah xaki samu natsuwa sosai..." Bata ce komai ba ta mike ta wuce daki ya bi ta da ido, tashi yyi ya dau cup din ya fita. Sai bayan azahar ta farka daga baccin da tayi, sosai taji xuciyarta ya mata saukin xafin da yake mata don ta samu bacci da yawa, kuma taji ddin drugs din, yunwa taji na dawainiya da ita, ta tashi ta shiga bathroom ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, shafe shafe tayi ta dau