Showing 180001 words to 183000 words out of 234058 words

Chapter 61 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17019

tace "Toh ya xan ce masa?" Ya d'an yi murmushin karfin hali yace "You where direct, which is not suppose to be so" turo baki tayi ta rungume hannunta tace "Ae shikenan" Aliyu ya shafa kai murya can kasa yace "You want me to talk to him?" Ta buda ido sosai tana kallonsa da sauri tace "Kace masa me?" Ba tare da ya kalleta ba yace "I will only explain to him what you meant by wat u said to him, kila..." ta hade rai ta katse sa tace "Noo, you don't need to, ba ruwana da shi, and am wishing him d best also" Aliyu na kallonta da kyau yace "Then forget him, kuma kar ki sake xubda hawayen ki" Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace "But I can't forget him just like that, yayi min hallacci a rayuwa" ba tare da Aliyu ya kalleta ba yace "Me ya maki?" Hararansa tayi da kamar baxata ce komai ba, sai kuma a takaice tace "He nursed my Heartache, he always made sure I was fine" Kallonta kawai Aliyu yake, "Wani irin heartache?" Tambayar da ya mata kenan har sannan yana kallonta sauke idonta tayi daga karshe tace "Ciwon xuciyata" da wani expression yake kallonta kafin yace "Kina nufin kina da ciwon xuciya?" Shiru tayi bata ce komai ba, jin hawayen talaici na xubo mata ta shiga gogewa, lkci daya jikinsa yayi sanyi, cike da karfin hali yace "I... i am the cause ko Iman?" Taki cewa komai, jin taki magana yace "Iman" sai a sannan ta juya tana kallonsa, sai ya rasa ma mai xai ce mata duk jikinsa ya mutu, tada motar sa yyi cike da karfin hali yace "Let me get you something to eat" Bata ce komai ba ya nufi wani gidan cin abinci da ita, suna isa bayan yayi parking ya juya yana kallonta a hankali yace "Mu je" daga haka ya bude motar ya fita ita ma ta fito, one side of the eatry khaleel ne xaune da cup din coffee gabansa ya jinginar da kansa da kujera har coffeen ya gama hucewa bai fara sha ba, kallonsu ya dinga yi ko kiftawa babu, ganin kujerar dake kallon nasa xa su zauna ya juya masu baya, Aliyu ya mika mata order list din da aka basa, kamar baxa ta karba ba da farko sai kuma ta amsa, ya dinga kallonta tunani iri iri a xuciyarsa, bata yi second talatin tana kallo ba ta mayar masa a sanyaye tace "Just anything" ya karba yana gyada mata kai, abinci iri daya ya sa aka kawo masu, duk da gaba daya ya ji ba ya da appetite hakan bai hanasa dinga cin abincin a hankali ba, ita ma haka, gaba daya suka fada duniyar tunani kowa da wanda yake, ita tana ganin yan biyunta tare da shi barin late Sudais, kuma ta dalilin haka har ranta tasan she is now comfortable with him even if it's not 100% unlike before, shi kuma yana tunanin in har bai auri Khadijah ba till the end of him baxai taba samun rest of mind ba, a hankali ya dago daga karshe yana kallon yanda take cin abincin kamar ana tilastata sai turo baki take, suka hada ido ta yi saurin sauke idonta, ya d'an yi murmushi yace "Naga bakya ci" a hankali tace "Ina ci mana" shi ya fara matsar da abincin gabansa jin ya ishesa gaba daya duk da ba da yawa ya ci ba, ta kalli abincin nasa tace "Ka koshi?" Ya gyada mata kai, yanda yayi da bakinsa kamar Shureim idon bai son cin abinci, tayi shiru tana kallonsa, yayi murmushi yana shafa kansa ya matsar mata da sauran abincin nasa yace "Ko xaki kara?" Wani Harara ta maka masa ta tura masa nata tace "Sai dai ma ka kara da nawa" sunkuyar da kansa yayi yana dariya, tayi murmushi a sanyaye tana kallonsa komai yayi wani lkcn sai ta ga exactly her kids, it's just too obvious, ya dau tissue yana goge bakinsa a hankali yace "Ranan Aunt dita ke tambayar ki, coz I told her a nan kike karatu...." Khadijah ta sauke idonta kasa tace "Ina gaisheta" lumshe ido yyi ya bude yace "Or xa ki je ku gaisa yanxu, tana son ki sosai, anjima sae in mayar da ke gida then u face Ur Dr Ayman.... Sai ki masa bayanin abinda kike nufi ya daina fushi da ke" ta hade rai tace "Ni ba ruwana da shi, bana son sa kuma" tana fadin haka ta kife kanta da table ta fara rera kuka, Aliyu ya dinga kallonta ko kiftawa babu, can yyi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri kar ki sake kuka, am sure shi ma ba har ransa ya gaya maki haka ba fa" Bata sake cewa komai ba ya biya bill din yana kallonta yace "Tashi mu je" mikewa tayi ya mike shi ma, tana gaba yana biye da ita Dr Ayman ya bi su da kallo har suka fita, har suka iso gun motarsa bbu wanda yace komai, ya bude mata motar yana kallonta, a hankali ta karaso ta shiga, ya rufe sannan ya xaga ya shiga ya tada motar ya fita eatry din, sae da suka hau saman titi a hankali yace "Mu je ku gaisa da ita Iman?" Shiru tayi da farko kafin murya can kasa tace "Toh" yayi murmushi yace "Thanks Ummu Shureim" har suka iso gidan babu wanda yace komai cikin su, yanxu kam ta daina jin xugin da take ji a xuciyarta, yayi parking yana kallonta yace "Toh fito" ba musu ta fita shima ya fita, Yana gaba tana biye da shi har suka shiga parlorn gidan. Maryam kadai ce parlor tana rubutu a takarda, ganinsu ta mike da mamaki tace "Lahh Khadijah ce gidanmu yau, sannu da xuwa" Khadijah ta xauna tana kirkiran murmushi da kyar tace "Yauwa nagode" Aliyu ya wuce sama, Maryam ta bi sa da kallo, kamar yanda Khadijah ke kallonta, tashi tayi daga karshe ta dauko mata ruwa da drink ta ajiye gabanta tana tambayarta Shureim, a hankali Khadijah tace "Yana schl" Maryam ta xauna tace "Ayya, kin shiga schl kuwa yau?" Khadijah ta gyada kai tace "Daga can nake" Maryam tace "Nima kin ga yanxu na dawo, nama yi ta jiran ya Aliyun don ya ce min xae shigo shi ma amma ban gansa ba...." Fitowar Hajiya Mariya ya sa Maryam ta mike tace "Anty yau ga mum Shureim gidan mu" Da murna Hajiya Mariya ta karaso cikin parlorn tace "Wlh kuwa, maa Sha Allah, sannu da xuwa Khadijah" Khadijah ta sunkuyar da kanta da ladabi tace "Nagode mumy, Ina yini?" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau Khadijah ya gidan?" Tace "Alhmdllh" Hajiya Mariya tace "Ya karatun fa?" Khadijah tana wasa da xobenta tace "Alhmdllh Mumy" Hajiya Mariya tace "Maa Sha Allah, Allahu ya baku sa'a, Ina Shureim din?" Aliyu da ya shigo parlorn yace "Yana schl Anty" tace "Allah sarki, ashe ya fara schl din a nan, Allah yayi masa albarka ya raya sa" Mikewa tayi daga haka tace "Mu je sama kiyi sallah ki ci abinci koh" kasa cewa komai Khadijah tayi ganin ta fara tafiya ta mike ta bi bayanta a sanyaye suka haura sama, Maryam na kallon Aliyu tace "Yaya shine ka shanya ni schl koh?" Ya shafa beard dinsa bai ce komai ba, Khadijah na haurawa sama tare da Mumy ta juya tana kallonsu, suna hada ido da Aliyu tayi saurin dauke kanta ta shiga dakin da Mumy ta shiga. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh Maryam ta shigo dakin rike da tray na abinci ta ajiye mata tace "Ga abinci Khadijah" Khadijah ta xaro ido tace "Wallahi na ci abinci kafin mu xo nan am not hungry" Maryam tace "Toh ko kadan ne dai ki ci" Khadijah xata yi magana aka bude kofar, jawahir ce ta fara shigowa, suna hada ido Khadijah ta sunkuyar da kai, Jawahir dake ta kallonta ta ajiye jakar hannunta ta fice daga dakin, sosai jikin Maryam yayi, ita dai Khadijah bata sake dago kanta ba, sai ga deejah ma ta shigo dakin, ta wara ido ganin Khadijah tace "Wow Khadijah ke ce gidan yau?" Murmushi Khadijah tayi tace "Ina yini" Deejah tace "Lafiya lau, ya lectures? Tare da Maryam ku ka xo?" Maryam na yar dariya tace "Ehh mana" Deejah tace "Ayya ya little shureim" Khadijah tace "Yana schl" Deejah tace "Toh maa Sha Allah" daga haka ta fita, Khadijah ta kalli agogon dakin don gaba daya hankalin ta yyi kan yaronta sanin ya kusa tashi a schl, ganin Maryam na sllh ta jira har ta idar kafin tace mata tayi ma Mumy magana xata wuce, Deejah ce ta dawo dakin tana video call ta iso kusa da Khadijah ta durkusa tana murmushi ta haska ta tace "Ammi ki duba fa plss basa kama??" Khadijah ta ki kallon screen din tana murmushi, Deejah tace "Khadijah ki tsaya ku gaisa da Ummar mu pls" sai a sannan Khadijah ta kalli screen din wayar, wata matashiyar mata ta gani gaban wayar, a hankali tana kallonta tace "ina yini?" Matar na kallon ta da fara'a tace "Lafiya lau yan mata, ya kike ya karatu?" Khadijah tayi murmushi tace "Alhmdllh" matar tace "Maa Sha Allah, Allah yayi maku Albarka ya bada abinda aka je nema, sai ayi ta kula kin ji?" Khadijah ta ji dadin addu'ar cikin sanyin murya tace "Ameen mama nagode" matar tayi mata sallama, Deejah ta mike rike da wayar tace "Ammi idan Safeenah ta dawo plss ku kira ni in nuna mata duplicate din ta" murmushi kawai Khadijah tayi, Deejah ta fice daga dakin tana ci gaba da waya da mum dinta. Khadijah ta kalli Maryam dake kallonta tace "Kice ma Mumy xan wuce" mikewa Maryam tayi tace "Toh" daga haka ta fita, tare suka dawo dakin da Mumy tace "Har xa ki koma daughter?" Khadijah tayi murmushi tace "Eh mum, Shureim sun tashi a schl" Hajiya Mariya tace "To maa Sha Allah, mun gode da ziyara Khadijah, Allah yi albarka" a tare suka sakko kasa har da Maryam, Mumy ta ba Khadijah sako a leda ta kai ma Shureim, a kunyace ta amsa tace "Allah saka da alkhairi mum" Deejah vata ji dadi ba ganin wucewa Khadijah xata yi, tace "Ae ko xan xo gidan ki ko gobe" Yar dariya Khadijah tayi tace "Allah ya kai mu" tare da Maryam suka rakota har bakin motar Aliyu don yana cikin motar yana jiranta, daga masu hannu tayi bayan ta shiga tace "Toh nagode, sae anjiman mu" Aliyu ya ja motar ya fita cikin gidan, sae da suka dau hanya tace "Xan dau Shureim a schl" yace "I thought as much, naga it's time" Mamaki Khadijah tayi ganin ya dau hanyar makarantar, ta kasa daurewa tace "How did you knw d schl?" D'an murmushi yayi murya can kasa yace "Kin raina irin bond dake tsakanin a son and his father?" Shiru Khadijah tayi tana kallonsa, lkci daya ta hade rai ta turo baki tace "Don't call him ur son, stop calling him that" kallonta yyi, A hankali yace "Ko saboda me?" A takaice tace "His father is a barrister" Murmushi yayi bai ce komai ba, he really really don't want to hurt her da babu abinda xai hanasa tambayar ta ko barrister ne yayi mata cikinsu, suna isa schl din bayan yyi parking ta bude motar ta fita don dauko d'an ta ya bi ta da kallo, ba a dau lkci ba ta dawo a sanyaye, yace "Where is he?" Ta bude motar ta shiga a hankali tace "Dr ya tafi da shi wai"

Aliyu bai ce komai ba ya tada motar a hankali ya bar premises din school din, har suka isa babu wanda yace komai, yana gama parking ya juya yana kallonta, ta bude motar ta fita tace "Nagode" yace "ki gaida min Shureim" ba tare da ta juyo ba tace "Ohkk" Da ido ya bi ta har ta shiga cikin gida, yayi wani murmushi ya ja motarsa ya bar wajen, tun da Khadijah ta shiga compound take ta kallon motar khaleel, lkci daya mood dinta ya canxa ta isa apartment dinta ta bude jaka ta fiddo makulli ta bude kofar ta shiga. Wanka tayi ta kwanta parlor ta fada duniyar tunani, murda kofar parlorn taji anyi ta mike xaune da sauri, Shureim ya shigo ya taho wajenta da gudu ya hau kanta yace "Anty we came back before you" ta rungumesa tace "How are you?" Yace "Am fyn" tace "Have you eaten?" Ya gyada mata kai yace "Uncle ya bani" tace "Toh mu je ka cire uniform" tashi tayi ta daga sa suka wuce bedroom, wanka tayi masa ta sa masa kaya da sweater ta bar sa dakin yayi assignment ta fito don daura girki. Tana kitchen tana fere Irish taji kamar mutum waje, a hankali ta leka window ta gansa xaune waya kare kunnensa, hada ido suka yi, ta dauke kai da sauri, ta ci gaba da abinda take cikin sanyi. Shidda da yan mintuna ta fito kitchen din bayan ta tsaftace ko ina, daki ta wuce taga Shureim kwance kan carpet yayi bacci, ta daukesa ta daura sa saman gado ta kwashe books dinsa ganin ya gama assignment din ta sa a jaka ta rufe, har xata fita wayarta dake kan gado yayi haske, ta karasa gadon ta dau wayar tana kallon screen din, alert ta gani na dubu dari da hamsin, a hankali ta ajiye wayar ta shiga bathroom, Karfe takwas saura Khadijah ta fito parlor da hijab har kasa, duk gaba daya ta rasa sukuni, a sanyaye ta wuce kitchen ta xuba abinci ta fito ta xauna, kasa cin abincin tayi ta tura plate din daga gabanta tana hadiye na bakinta da kyar, tashi tayi ta kara shiga kitchen ta dau warmer ta wanke ta xuba abinci a ciki ta rufe sannan ta fito, ta fi minti uku tsaye parlon kafin ta nufi kofa ta fita gabanta na faduwa, a hankali ta danna bell din khaleel, tana ta tsaye gun ga wani sanyi dake ta shigarta, ganin bai bude ba ta kara dannawa, lkci daya ya bude kofar tayi saurin sunkuyar da kanta kar su hada ido, barin bakin kofar yayi ya koma ciki ta bi bayansa kamar mai tausayin kasa ta rufe kofar sannan ta isa tsakiyar parlorn ta durkusa ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta yarda sun hada ido ba tace "Good evening" Xaunawa yyi kan kujera yace "Evening ya kike?" A sanyaye tace "Lafiya lau" Yace "Ya lectures?" Shiru tayi bata ce komai ba, tana dai duke inda take yace "Baxa ki xauna ba" a hankali ta mike tace "Sai da safe" yace "Alryt, Allah tashe mu lafiya, todays cold isn't gonna be funny ki sa ma Shureim sweater and lock all the windows" tace "Toh" daga haka ta nufi kofa xata fita yace "And...." Tsayawa tayi bakin kofar don jin abinda xai ce, yace "Thanks for the food" bata ce komai ba ta fita ta rufe masa kofar. Abincin da ta xuba ta kai kitchen ta fito ta kashe wutan parlorn ta wuce bedroom, warm water ta xuba a kettle ta daura alwala ta fito ta kashe wutan dakin ta hau gado ta kwanta kusa da Shureim ta rufa masu Duvet, har ta fara bacci vibration wayarta ya tasheta, ta bude ido a hankali ta jawo wayar, tasan Barrister ne xai kirata wannan lkcn, tayi picking call din ta kai kunne tayi sallama cikin sanyin murya, daga daya bangaren yace "Amira..." Tace "Uhm Ina yini?" Yace "Lafiya lau, Ya Boy dina?" Tace "Yayi bacci" yace "Maa Sha Allah, kema tashin ki nayi koh?" Tace "Uhn, na dai kwanta ne, ina little Amira fah?" Yace "Tana gun Mum dinta" Khadijah tace "Am sorry ban kira ka ba Barrister, daxun na ga sako thanks very much we are grateful" yace "Is there any need for that Amira?" Murmushi tayi bata ce komai ba, yace "I think nan da 3 days xan taho ba sai next week ba" Khadijah tace "Ayya Allah ya kawo ka lafiya" yace "Ameen, daxu ma naje gun Umma" Khadijah ta bude ido tace "Haba dai?" Yace "Sure, kafin in taho Uk xan je can katsina" shiru Khadijah tayi bata ce komai ba, yace "Are you there?" Tace "Uhm ina jin ka" yace "Me yasa kika yi shiru" a hankali tace "Isn't it Early barrister" yace "It's not Amira, I want everything to be done in not less than 2 months plss, ba ki jin tausayina koh" jikinta yayi sanyi tace "Amma barrister ni tsoron Ummu Amira nake, plss ka sanar da ita don ya xamo da amincewarta kake yin komai, Ni tsoro nake ji" D'an murmushi yayi yace "Ba ruwan ki da Jiddah, beside ta san komai, ke din dai ce bata sani ba, sannan ba gida daya xa ku xauna ba" Ita dai har sannan bata ji hankalin ta ya kwanta ba, banda faduwa babu abinda gabanta ke yi, cikin sanyin murya tace "Toh shikenan, Allah yayi jagora" yace "Ameen Amira, let me allow you sleep" tace "Toh nagode" a hankali yace "Do have a nyc nyt rest" Ta d'an yi murmushi tace "Thanks" daga haka ya katse wayar, komawa tayi ta kwanta ta rufe har kanta da duvet. Washegari bata da lectures da safe amma saboda Shureim dole ta tashi cikin sanyi don shirya sa, tausayin little boy din nata take don sanyin isn't funny at all, haka dai ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi babba da head warm, tea ta hada masa ta soya masa kwai sanin baya cin bread, tana xaune parlor tana jiran ya gama aka danna bell, kallon agogo tayi kafin ta mike ta isa kofar ta bude, khaleel ne tsaye ya shirya xai fita, shi ma kayan sanyin ne jikinsa yana kallonta a hankali yace "Good morning" ta kasa kallonsa ganin yanda ya tsare ta da ido, ji tayi yace "let me drop Shureim in school tunda baki da lectures yau" tace "Toh" daga haka ta dawo parlorn, yana ta tsaye har Shureim ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login