Showing 123001 words to 126000 words out of 234058 words
ta rasa dalilin kukan nata, taji xuciyarta yyi mata rauni ga xugin da ya fara mata, mai adai daitan a tuaninsa rasuwa aka yi mata ya dinga bata hakuri bai ma karbi kudin ba ta shige gida, nan parlor ta xube ta kara rushewa da kuka kamar xata tsaga gidan, Nanny ta fito a rikice ta shiga tambayarta me ya faru ina su Shureim sai a sannan khadijah ta tuna da yaran nata, Nanny duk ta rikice ta mike ta fita ta sake dawowa a rude tace "Khadijah tambayar ki nake ina yaran me ya same su, ina suke" Khadijah ta hade kai da kujera cikin rawar murya tace "Ummata na gani Nanny" Nanny ta tsaya kallonta kamar idanuwanta xa su fito, can ta durkusa kusa da ita da sauri tace "Umma? Ummarki dai? A ina kika ganta" Khadijah ta kara fashewa da kuka tace "A gidan da muka je" Nanny tace "Toh sai ta ce maki me, ko bata gan ki ba?" Nanny bata rufe baki ba sai ga Shaheedah ta shigo parlorn a sanyaye, khadijah na ganinta ta kara hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Shaheedah ta isa kusa da ita ta durkusa a hankali tace "Dama ke ce khadijahr da mama ke shigowa Nigeria saboda tun shekaru uku da suka wuce, dama ke ce khadijahr da mama ke yawan maganar ta a can kasar mu?" Khadijah ta dago hawaye wasu na bin wasu tana kallon Shaheedah, girgixa kai Shaheedah tayi tace "Allah sarki khadijah na samu labarin ki a gun mama tun ban yi aure na dawo kasar nan ba, Khadijah Mama ta shiga wani yanayi bayan rabuwar ku, ta je garurruka da dama na Nigeria tana neman ki, ta dalilin ki mama bata da isashen lafiya har yanxu, Wllh wannan xuwan ma tana sauka Nigeria Kano ta fara xuwa wai ko Allah xai sa ta gan ki, daga kano ta tafi Katsina sannan ta taho Kaduna duk wai ko xa ku hadu kafin ta taho gidana nan Abuja kuma gobe ma take shirin komawa kasar mu" Shigowar Umma parlorn ya sa Shaheedah tayi shiru tana kallonta, kana ganinta kasan ita ma tayi kukan, Umma ta karaso parlorn a sanyaye ta xauna kan kujera kusa da khadijah wasu hawayen na sakkowa idonta, Khadijah ta kasa kallonta ita ma tana hawayen, Cikin sanyin murya Umma tace "Ko da baxa ki saurareni ba Khadijah ina neman gafarar ki, ki yafe min, na maki abinda uwar da ta haife ki baxa ta maki, Khadijah don nace ki tafi ba har xuciyata nake nufin haka ba amma kika yi wucewarki kika saka ni cikin kunci da damuwa, duniyar tayi min xafi barin idan na tuna baki da kowa, ban yi ma mahaifin ki hallaci ba, but what will someone expect from a frustrated Mother, God knows i was frustrated.... Shi yasa nace ki tafi, amma ban taba tunanin xa ki tafi ba" sakkowa Kasa Umma tayi ta durkusa kusa da khadijah tana kuka tace "Ki gafarceni Khadijah.... Forgive me plss" Khadijah ta daura kanta a kafarta tana kuka sosai cikin rawar murya tace "Umma baki min komai ba, nima ki yafe min, I know i failed you, amma ba laifina bane Umma, ni ban taba iskanci ba, I was raped...." Umma ta dagota ta rungumeta tana controlling nata kukan tace "I thought as much daughter, na yanke hukunci cikin fushi da tashin hankali ne, na yarda da tarbiyar da na baki, Allah ya saka maki koma waye yyi maki wannan aika aikan, shi ma xai ga sakamakonsa tun a nan duniya" Sosai Nanny da jikinta yayi sanyi tayi murnan haduwar Khadijah da ummarta, ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tana gode ma Allah da ya bayyana ma marainiyar ummarta, Shaheedah da duk jikinta yyi sanyi ita ma ta ji dadin reunion din Aminiyar mahaifiyarta da step daughtern ta after three good years. Shaheedah ce ta fita karbo su sudais gun Sadeeq dake mota bai shiga gidan ba, a hankali tace "Dear kaga for ur sake, mama will be happy once again, tayi reuniting da daughter dinta" murmushin karfin hali yyi yace "Sure, but am still confuse ban gane komai a nan ba fa, khadijah dai nasan gidan wan mahaifinta is few houses away from ours, so ban san kuma meye relationship dinta da mama ba" Shaheedah tayi murmushi tace "It's a long story, idan mun koma gida xan baka labarin dear" Sai kusan bayan Isha Sadeeq ya dawo daukan Shaheedah, Khadijah taki yarda Umma ta bi su don gani take kamar baxa ta sake kara ganinta ba. Da daddare suna xaune kan gado wajen karfe daya su Shureim na jikin Umma sun yi bacci, khadijah na bata labarin rayuwar da tayi bayan ta bar gida, tun farkon labarin har ta kawo karshe Umma kuka take, duk jikinta yyi sanyi don ta san duk ita ja ma khadijah duk abinda ya sameta, shiru ta yi tana tunanin me xata ma sudais kuma a ina xa ta gansa, khadijah da ke share hawayen ta cikin raunin murya tace "Umma har yau bai kara dawowa ba, i will never forget him in my life..." Umma ta jawota jiki tace "In sha Allah xai dawo wataran, he will come back to you daughter" Kai kawai khadijah ke gyada mata a xuciyarta tana addu'ar Allah ya gwada mata wannan rana, Umma ta katse silence da ya biyo baya tace "A ranan da kika tafi Khadijah babu inda ban fita nemanki ba tun ina yi da kafa har na koma abun hawa, sai bayan isha na dawo gida a lkcn ina addu'ar Allah yasa kin dawo sai na ga akasin haka, na shiga tashin hankalin da bana fatan in kara shigarsa har karshen rayuwata don nasan baki da kowa Khadijah, Wa ennan makiran dake gidan dama tuni sun sanar ma Alhaji kafin ma in dawo, ina shigowa kuma ya bani takardata kamar jira yake, hakan yasa naji bakin ciki kamar ya kashe ni domin, ce maki nayi ki tafi kar ki kashe min aure duk da bai kai xuciya ba sai gashi sakin ma na walakanci yyi min don ce min yi 1st thing da safe in tattara ina wa ina wa in bar masa gidansa, hakan kuwa aka yi don ban jira gari ya waye ba na fita neman wanda xai siya kayan daki na, ina siyarwa kuma kafin sha biyu na bar masa gidansa, da kudin kayan ba tafi Ethiopia... Bana son in dinga tuna yanayin da na shiga rashin ki Khadijah, ni dai kawai ki gafarce ni domin ni na ja maki komai da ban kai ki gun yakumbo ba da duk hakan bai same ki ba, ita kuma Yakumbo bani da abinda xance a kan ta yanxu domin kuwa ta riga mu gidan gaskiya" Khadijah ta dago da sauri tana kallon Umma tace "Umma yakumbo ta rasu?" Umma tace "Ta rasu kusan shekaru biyu kenan, electric ring ne ya ja ta har lahira, wai ta sa ruwan xafi a daki" jikin khadijah yyi sanyi ta ma rasa abinda xata ce, bayan wani lkci tace "Allah ya ji kanta" Umma tace "Ameen" a hankali khadijah tace "Umma na ki yafe min" sai kusan karfe uku suka kwanta, washegari da safe Umma tayi ma su Sudais da Shureim wanka suka fito parlor, Nanny da ta gama breakfast a kitchen ta fito ta gaida Umma, Umma ta amsa mata da murmushi nan tayi mata godiya kan tsayawa ma khadijah da yan biyun ta da tayi all this while, satin Umma daya a gidan tace ma khadijah xata koma kasar su amma xata dawo, kuka khadijah ta fara yi tace "Umma kina son ki tafi ki kara bari na ne" Umma tace "Noo khadijah xan dawo, ki bari in je in yi sallama da dangina sai in dawo mu xauna, amma fa baxan xauna wannan gidan ba sai dai in kama mana haya a Kaduna, wannan kuma ki rufe masu kawai" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma?" Umma tace "Ehh" sauke idonta Kasa tayi bata ce komai ba, Umma tace "Forget ur past Khadijah, life moves on, don wani baxa ki ki xama a garin ba Beside gari me girma ma a ina xaki gansa?" Kai kawai khadijah ta gyada mata, wannan kuma shine mafarin komawarsu Kaduna, suka bar gidan da Sudais ya mallaka ma twins dinta a Abuja, life in Kaduna was smooth for them, sai dai khadijah ta kasa kwantar da hankalinta ta xauna lafiya a garin, ko yaya sai taji abinda ya faru shekaru uku na dawo mata duk da a kinkinau gidan da Umma ta kama masu haya yake, Tunanin da ta kasa cirewa a ranta yasa ciwonta ke yawan tashi wani lkcn har da kwanciya asibiti, hakan ya dinga daga ma umma hankali ta shiga tunanin to wani garin kuma xa su koma, don gaskiya bata son kano, a hankali dai khadijah ta hakura bayan watannin su shidda Kaduna. Kasuwanci sosai Umma ke yi don har Dubai tana fita Allah ya dubeta lkci kankani dukiyarta ya bunkasa, yanda take ji da jikokin nata ko Khadijah bata samu wannan gatan ba, tamkar ta mayar da su ciki take ji, su ma kuma haka suke sonta don ko da yaushe suna manne da ita, duk anguwan babu wanda yasan yaran Khadijah ne yan biyun masu shiga rai duk tunaninsu umma ce ta haifesu Nanny ma na tare da su har lkcn, kuma kusan tare da ita Umma ke fita waje ta xama kamar yar uwarsu, yanxu kam su sudais da baki ya bude basa gudun uwar ta su da suka dauka yayarsu ce Umma kuma Mumynsu, a haka Umma ta yi iya kokarin ganin khadijah ta samu admission a University of Cambridge dake UK, Khadijah bata ji dadi da farko ba ganin pharmacy suka bata don ba shine burin sudais a kan ta ba, amma umma tayi convincing dinta to go for it, shine ta tafi a haka, farkon xuwanta kasar tare da Umma Nanny da yan biyun ta suka taho suka mata sati sannan suka koma nan kuma ta mayar da hankali tana karatu ba ji ba gani domin xama qualified pharmacy, and then..... 1st khaleel ya sa ta gaba a kasar, that not being enough sai gashi ta hadu da wanda bata burin sake gani har karshen rayuwarta, why????
Silence din kusan 3 minutes ne ya biyo baya a parlorn, a hankali Khaleel ya dago kansa yana kallon khadijah da ta hade kanta da gwiwa, har ransa yake jin shesshekar kukanta, gashi ya kasa cewa komai, he is just lost of words, jinginar da kan sa yyi da kujera na kusan minti biyu kafin ya tashi a hankali ya isa gabanta ya duka ya dago kanta yana kallon idanuwanta da suka yi jajir, ta yi saurin sauke idonta daga kallon nasa kwayar idon da su ma suka sauya kamanninsu xuwa ja wasu sabbin hawayen na sakko mata, har lkcn Khaleel ya kasa cewa komai sai kallonta yake, bayan wasu dakiku abinda ya fito bakinsa cikin xaxxakan muryarsa shine "Forget about sudais, he did what he did for the sake of Allah, eraze him of ur mind"
Da sauri khadijah ta dago tana kallonsa, ya mike ya koma kujerar da yake xaune yace "Yeah, ki mance da kin ma taba sanin sa a rayuwar ki, I mean that sudais..." Khadijah dake ta kallonsa ko kiftawa babu tayi karfin halin cewa "Ko saboda me?" A takaice yace "Ohk, it seems biyansa abinda ya maki kike son yi kenan?? If that's ur wish kema xaki iya taimakon marayu ai, I see no reason for good six years xa ki dinga tunani daya ba, beside he needs nothing from you, domin Allah yayi kuma Allah ne xai biyasa" Khadijah ta hade rai ta mike tana masa wani kallo tace "I regret telling you who i am, of all my story... part din sudais kadai ka ji da kyau halan? Shi kadai ka iya recalling? I just wasted the time I was suppose to use for sleeping" Daga haka ta nufi daki ta bar masa parlorn tana share hawayen idonta, Khaleel ya bi ta da ido ko kiftawa babu, jinginar da kansa yyi da kujera ya lumshe ido a hankali, wani mugun tausayinta ne ke shigarta, Sudais? Abinda ya fadi kenan a xuciyarsa ya bude ido da sauri, can ya tabe baki ya mike, ya fi minti biyu a tsaye yana kallon agogon dake nuna karfe uku saura kafin ya nufi bedroom dinta, xaune ya ganta kasa ta hade kai da gwiwa, Aliyu ne kawai ya fado xuciyarsa... ya hade hakoransa yana imagination kala kala a xuciyarsa, can yyi wani murmushi ya karasa cikin dakin yana kallonta ya durkusa gabanta, da farko rasa abinda xai ce mata yyi, can a hankali yace "Am sorry Khadijah, you misinterpret what I meant, ur story.... It is just heartbreaking, it's sad... you've past through a lot in life at a very tender age, but am happy you proved to be a strong lady, strong lady indeed...." Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa babu har lkcn ta ki dago kanta, a hankali ya kai hannunsa ya dago ta suna hada ido ta rufe idon, murmushin sa mai kyau yyi yana kallonta, murya can kasa yace "Those cute boys...." Sai kuma yyi shiru, bayan wani lkci yace "You are going no where from UK, Aliyu ne xai bar maki UK ba ke xaki bar masa ba am giving you my words, kina nan har ki gama karatun ki" ta bude idonta a hankali tace "Ae ya riga yasan makarantar, he will surely keep on looking for me" hawaye ne ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Ni ban san me xan masa ba yake nema na" murmushi Khaleel yyi yace "Xai daina neman ki soon" Tana son kallonsa amma idanuwansa are not encouraging, ya lura da haka sai ta basa dariya ya mike yace "Alright then, life moves on, ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya hana ki walwala a kasar nan am assuring you, ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh if you wish and then go to bed, the night is far gone" Khadijah dake wasa da fingers dinta tace "But ina son xan je in ga su Umma..." Yace "When?" A hankali tace "Ko gobe" shiru ya d'an yi kafin yace "Alryt then Allah ya kai mu" Ya fi minti uku a tsaye har sai da ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake tayi saurin dauke kanta, yayi murmushi murya can kasa yace "Good nyt" kai ta gyada masa daga haka ya juya ya fita duk jikinsa a sanyaye, she is really a strong lady, yana fita ya kulle mata kofar, haka kawai khadijah taji ta samu relieve sosai don kusan ji tayi babu abinda ke damunta a ranta kuma, tashi tayi a hankali tayi yanda Khaleel ya ce mata, sai kusan karfe uku da rabi bacci me nauyi ya dauketa.
Tun da ya fito daki Kanwar Abbansa Hajiya Mariya ke bin sa da kallo, kitchen ya shiga ya fito ya sake shiga ya fito kamar xai koma daki sai kuma ya sake shiga kitchen din sai gashi ya kara fitowa Hajiya Mariya tace "Aliyu" juyawa yyi da sauri yana kallon direction din da take don bai ma san tana wajen ba, har ya iso inda take kallonsa take, ya xauna gefen kujera yace "Na'am mum" da damuwa tace "Aliyu what's wrong with you pls, meye matsalar ka dubi yanda ka lalace, abun har ya kai ya kawo ka fara behaving kamar mara hankali, yanxu meye ma'anar shiga da ficen da kake a kitchen kamar wanda ya xauce" k'asa kallonta yyi ya sunkuyar da kansa, wanda hakan yasa jikinta yyi mugun sanyi, tasowa tayi ta dawo kusa da shi tace "Gaya min abinda ke damun ka Aliyu, you Neva knw if I can be of help, ko baka dauke ni kamar Anty fatima bane" Hawayen da ta gani idonsa ya kara daga mata hankali duk ta rikice tace "Subhanallahi, Aliyu, why the tears, don girman Allah ka gaya min meye ya faru, or have you gone wrong somewhere? Tel me son.." damuwa ce karara dauke fuskarta, ya girgixa kai yace "Just keep on praying for me mum, and... I will be going to Nigeria tomorrow, amma baxan jima ba xan dawo" daga haka ya mike ya bar ta gun xaune ta bi sa da kallo baki bude, tashi tayi ta wuce dakinta ta dau waya ta shiga kiran Mumy, ba a dau lkci ba ta daga bayan sun gaisa da damuwa tace "Anty fatima ni dai ko xa ki kira Aliyu ki ji me ke faruwa wllh gaba daya na rasa gane kansa yana cikin damuwa sosai, yanxu ma da na sa shi gaba sai ya fada min damuwarsa hawaye fa ya fara min kuma ya ki fada, I really don't knw his problem, wllh ko abincin kirki bai ci sai kinga yanda ya rame..." Mumy ta tabe baki tace "Ina ga ke ce baki taba lura ba sai wannan xuwan da yyi maki, amma Aliyu ai ko da yaushe cikin damuwa xa ki gansa, ni na saba ma ganinsa a hakan, ni dai bani da xurfin ciki haka ma mahaifinsa so I don't knw... Shi ya sani, na sha ce masa idan ma wani laifin ya aikata ma Allah yayi ta istigifari, or may be ya ji labarin auren da Abbansa ke shirin masa ne shi yasa hankalinsa ya kara tashi" da mamaki Hajiya Mariya tace "Aure kuma?? Yaushe?" Mumy tace "Yanxu ma shirye shiryen da ake ta yi kenan, idan ya dawo sai ya dau matar su yi ta yawon da yake yi tare, amma kar ki gaya ma sa, shi yasa ma yayan ki bai gaya maki ba, just let him... Kila idan aka yi auren xai dawo hankalinsa" Hajiya Mariya tace "Toh ai ya ma ce min gobe xai tafi Nigeria" Mumy tace "Toh dai dai kenan goben juma'ah dama xa a daura auren ke dai kar ki ma ce masa komai, sai ya xo muna