Showing 111001 words to 114000 words out of 234058 words

Chapter 38 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17002

ya gama sa duk kayan su a booth din mota, komai da yasan xai lalace a gidan ya sa ta xubar, yana rike da little sudais ya rufe gidan ita kuma tana rike da Shureim ya nufi motarsa dake waje, ya bude back seat yana kallonta yace "Get in" shiga bayan motar tayi sannan ya mika mata little sudais da karamar jakar dake dauke da flask na ruwan xafi da table water sai gwangwanin madarar su na Nan, ya rufe motar, ya shiga maxaunin driver, sai da ya shiga filling station ya kara mai a motar sannan suka dau hanya, a hankali yace "We are going to Abuja Amira" kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan wani lkci tace "Me xa mu je mu yi a can?" Bai amsa ta ba yana ci gaba da driving dinsa, ba a dau lkci ba gaba daya yaran suka yi bacci tana rungume da su tana turo baki don duk sun mata nauyi a jiki, bayan few hours shureim ya tashi da kuka sannan little sudais ma ya tashi, sudais dake kallonsu ta madubi yace "Ki hada masu madaran a feeder" kamar xata yi kuka tace "Toh da wani hannun, bayan sun danne ni" murmushi yyi ya gangara gefen titi yyi parking ya fito ya bude back seat din ya shiga, shi yayi making din masu madaran a feeder guda biyu tana kallonsa, bayan ya tabbatar babu xafi ya mika mata daya sannan ya karbi little sudais ya fara bashi nasa ita kuma ta shiga ba Shureim, tsabar cin da yaran suke ko kwana biyu gwangwanin madaran baya masu, shi sa sudais ke siyowa da yawa, bacci little sudais ya koma a hannun Sudais ya mika mata shi ta turo baki tace "Wllh kafana ciwo yake min ni dai" yace "Toh ko in bari kiyi driving din?" Dariya ta yi tana wara ido tace "Ni kuma?" Ajiye mata yaron yyi a kafa kusa da twin dinsa da shima ya koma baccin sannan ya fita ya koma maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da tukin sa. Kafin su kai kaduna su shureim sun sha madaran su ba iyaka, kuma duk sai yyi parking ya taimaka mata, gashi ya hanata baccin da take ta ji saboda yaran hannunta da ta fara xai tada ta ta rike su da kyau, sai kusan karfe shidda Sudais ya isa Abuja ya nufi gidansa dake cikin garin, kai kana ganin gidan kasan an kashe kudi ba na wasa ba, ya bude motar ya fita don bude gate din gidan kafin ya shiga da motarsa, babu abinda babu cikin gidan don haka bedsheet yayi spreading a kan gado a daki ya kwantar da twins dake ta bacci, yana kallon khadijah da tayi laushi alamar duk ta gaji yace "Kiyi wanka kiyi sallah kafin in dawo yanxu" daga ya fita, da yake har sponge da sabulunsu ta dauko, bayin ta shiga bayan ta fiddo su a kayansu da sudais ya kawo dakin tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta canxa kaya ta sa Hijab ta kwanta dai dai lkcn da su Shureim suka tashi, Ji tayi kamar ta kwala ihu ta dinga hararansu kamar xata yi kuka, ganin xa su fara kuka ta mike ta fara hada masu abincinsu hawaye cike idonta, ita dai ta gaji da wahalan da yaran nan ke bata, tana cikin basu feedern ya shigo dakin, tausayi da dariya ta basa lkci daya ganin yanda take hawaye, ya amshi feeders din hannunta yace "Toh tashi ki dau abinci ki ci kiyi kwanciyar ki" kamar jira take ta mike da sauri, tana cin abinci ya karasa basu abincin su ya kalleta yace "Toh baxa su yi wanka ba" hade rai tayi tace "Nima ban sani ba" yace "Amma ke ai kin yi wanka" tace "Toh ai ni da su ba daya bane" mikewa yyi ya tafi bathroom ya hada masu ruwan xafi sannan ya fito yace "Kije kiyi masu" ta mike da sauri tace "Ni wllh baxan iya ba bacci nake don Allah kayi hakuri, dubi fa wahalar da suka dinga ban a mota" tsayawa kallonta yyi kamar yanda yaran nata ke kallonta su ma, ta je can karshen gado ta xauna fuskarta daure ta dauke kai, dukawa yyi kusa da shureim ya fara cire masa kayan jikinsa har ya gama ya wuce bathroom da shi, dariya ta fara yi kasa kasa ganin shi xai masu wankan, bayan wani lkci sai gashi ya fito ya kwantar da yaron da ya wanke ya rufesa da bedsheet sannan ya dau dan uwansa ya cire masa kayan shi ma ya wuce bathroom da shi yayi masa wankan ya fito da shi ya kwantar kan gado, jaka ya bude ya fiddo masu over all gaba daya da powdernsu da man shafawa, khadijah sai boye fuskarta take kar tayi dariya ganin yanda ya sa masu pampers din, shi dai ko kallonta bai yi ba ya hade rai, yana gama shirya yan biyun ya daukesu ya fita dakin ya kai su nasa dakin ya kwantar da su, Khadijah ta turo baki a xuciyarta tace huta roro, ta mike ta rufe kofar da ya bari a bude ta nufi kan gado ta gyara bedsheet din ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. A haka khadijah da sudais suka fara rayuwa a garin Abuja da yan biyunta, sai dai sudais wasn't comfortable staying under the same roof with khadijah ya rasa dalili, gaba daya a takure yake barin yanda ya ga ta saki jiki totally da shi don ma akwai little sudais da shureim, karfe goma na safiya yake barin gidan baxai kuma dawo ba sai yamma, duk khadijah ta rame saboda rainon yaran don ma ba ta shayar da su, wahalansu yyi yawa, da daya ya fara kuka dayan xai cafke duk su rikitata, satinsu uku a Abuja sudais ya sa aka samar masa Nanny don tausayi take basa barin yanda ya ga ta rame, kamar kar Nanny ta xo lkci daya khadijah ta watsar da lamarin yaran gaba daya ya koma nanny ce ke masu komai ita sai dai tayi girki tayi bacci, abinda sudais ya guda kenan tun farko but saboda tausayinta da yake kawai ya kyaleta, nanny na xuwa gidan da kwana biyar sudais ya tafi damaturu don duba su Mami don Allah ma yasan yana kewar mahaifiyar tasa, kwana biyu yyi a can ya dawo Abuja bayan ya sanar ma Mami yawancin aikinsa yanxu a Abuja yake yi, ta yi masa addu'a da fatan alkhairi. karfe uku saura na yamma sudais ya shigo gidansa na Abuja, sai dai a waje yyi parking don ya gaji da yawa, babu kowa parlorn sai Ac dake ta aiki da kamshin dake tashi, ya haura sama ya bude kofar Nanny da yan biyu a hankali, suna xaune cikin keken koyan xamansu sai wasa take masu da abun jikin keken suna ta dariya gaba daya, sosai matar ke son su don yaran akwai shiga rai, Nannyn baxata wuce shekara talatin da biyar ba, tana ganin Sudais ta mike tace "Sannu da dawowa yallabai" yace "Sannu" ya karasa cikin dakin yana kallon cute yaran dake ta kallonsa, kyawawan karshe ne yan biyun ga manyan idanuwa ga su farare kal kamar larabawa, da wuya mutum ya kallesu bai kara kallonsu ba, ya rasa ne yasa khadijah ta ki sonsu har ynxu, daukansu yayi one by one yayi kissing dinsu suna masa dariya ya ajiye su ya fita dakin, bude kofar dakin da Khadijah take yyi, ya ganta kwance daga ita sai yar doguwar riga tana bacci, ya kusa minti biyu tsaye yana kallonta kafin ya rufe mata kofar ya wuce nasa dakin, wanka yyi ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya gabatar da sallahn azahar sannan ya kwanta, Nanny ce ta shiga dakin Khadijah ganin har kusan la'asar ba ta fito ba alamar bata san Sudais ya dawo ba, ita duk tunaninta sudais mijinta ne, cike da natsuwa ta tasheta tace "Yi hakuri na tashe ki madam, yallabai ya dawo" da sauri khadijah ta mike xaune tace "Yaushe?" Nanny tace "Tun daxu" Khadijah tace "Toh" Nanny ta juya ta wuce sannan khadijah ta mike ta tafi bayi ta wanke fuskarta ta fito ta dau Hijab har kasa ta sa ta fita, a hankali ta tura kofar dakin sa ta gansa yyi rub da ciki yana bacci, a hankali ta isa kusa da shi ta durkusa tana kallon kyakkyawan fuskarsa, bude manyan idonsa yyi a hankali, ta koma baya da sauri ta fara kame kame, ya mayar da idonsa ya rufe na kusan minti daya kafin ya bude ya mike xaune, murmushi tayi murya can kasa tace "Sannu da dawowa, baka ce yau xaka dawo ba da ka kira da safe" yace "I was thinking sai gobe xan taho" tace "Ya hanya? Ya su mama" Yace "Alhmdllh, ya twins? duk da nasan kilan duk yau baki gansu ba" sauke idonta tayi daga kallonsa jin yyi shiru ta daga kai suka hada ido, wara mata ido yyi, ta yi murmushi tace "Me xaka ci?" Yace "Komai ma" mikewa tayi tace "Toh bari in yi maka" daga haka ta fita ya koma ya kwanta. A hankali watanni suka dinga ja kamar wasa sai ga shi su shureim sun yi wata bakwai, babu inda basa xuwa da rarrafe, wani shakuwa ne ba na wasa ba tsakaninsu da Sudais, ji yake da su kamar ya hadiye su don so, in har suna wasa a Parlor to suna ganin khadijah suke barin wajen da gudu su tafi gun Nannynsu, sai dai ta tabe baki ko tayi tsaki, har lkcn kamanninsu sak na Aliyu barin hancinsu da idanuwa shi sa take kara jin bata son su, ko ina na gidan kayan wasan su ne, don komai sudais ya gani na yara ko da ya fi karfinsu sai ya siyo masu, dakinsu ya koma kamar na siyar da kayan wasa, yau lahadi sudais na xaune garden shi kadai files a gabansa kana ganinsa kasan aiki yake, lkci daya ya rufe files din gabansa ya lumshe ido, for how long xai ci gaba da ajiye khadijah da yaranta a gidansa, har ransa yake jin baxai iya rabuwa da su ba, but duk ranan da Mami ta gano abinda yake aikatawa yasan that day won't be funny, then meye xai yi da xai kasance da Khadijah da yaranta na har abada With his parent consent, bude ido yyi a hankali ya furta abinda ke ransa a ciki "I shud marry her" girgixa kai yyi ya na murmushi lkci daya abinda Yusuf ya gaya masa one year ago a mota ya fado masa. Khadijah na bedroom ita kadai tana ta jiran jin shigowar sudais amma bai shigo ba, ita kanta bata san me yasa take son ya shigo ba, kuma tasan yana can garden, mikewa tayi ta sa mayafinta ta fita xuwa can din ta tsaya kusa da wani flower yanda baxai ganta ba ta dinga kallonsa, kananun kaya ne jikinsa na 3qtr da shirt da bai yi buttoning ba, tsura ma pen din table dake gabansa ido yyi har lkcn yana tunani, kamar ance ya daga kai suka yi ido hudu da Khadijah, dauke kai tayi da sauri, sai kuma ta jiya ta bar wajen ya bi ta da kallo, murmushi yyi ya na shafa kansa don irin kallon nan da Khadijah ke yi masa ko da yaushe dariya yake ba sa, sau tari ya sha kamata tana kallonsa sai ta fuske, shi din ma yana kallonta amma with swags, kwashe files din gabansa yyi don dama ya gaji ya mike ya wuce ciki yana rike da su, sai da ya fara lekawa dakinsu shureim yaga yanda Nanny ta cika masu kayan wasa a gaba suna ta fama, suna ganinsa suka rarrafo xasu taho gunsa, da sauri ya juya ya bar wajen don bacci yake son yi, a tare suka fara kuka yana tsaye har suka fito corridor nemansa yyi murmushi ya durkusa ya daukesu duk biyun amma da kyar tsabar weight dinsu, ya wuce dakinsa da su, ajiye su yyi kan gado ya kwanta suka haye kansa gaba daya ya lumshe ido yace "Yanxu baxa ku bar ni inyi bacci ba" kamar sun ji mai yace suka fara dariya har da kwantawa jikinsa ya rungumesu gaba daya, ganin da gaske baxa su bar sa yyi baccin ba ya dau waya ya kira Khadijah, tana dagawa yace "Plss ki xo ki dau su Shureim basa son inyi bacci" Khadijah bata ce komai ba ya katse wayar, ta tabe baki ta sa Hijab ta fito ta shiga dakinsa karasawa tayi kusa da gadon suna ganinta suka kankamesa sudais yace "Meye amfanin yaranki na tsoron ki" bata tankasa ba ta kai hannu xata dau little sudais ya fasa ihu dan uwansa na taya sa suka rirrike sudais, murmushi kawai sudais yake yana kallon khadijah da ta hade rai tana kallonsu, fixgo shureim tayi ya fashe da kuka a tsorace har lkcn yaki yarda ya sake sudais. Sudais ya fixgota ita ma har ta fada kansa ya daure fuska yace "Ciwo xa ki ji masa" xata tashi ya ki saketa yana kallonta kamar yanda yaran ta ma ke kallonta, murmushi tayi ta xame kanta ta xauna kasa, murya can kasa sudais yace "Tafi basa son daukan naki" kamar sun ji abinda yace suka kara yin lamo a jikinsa, Khadijah ta mike ta nufi kofa sudais ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya lumshe ido a hankali. A ranan da su Shureim suka cika wata goma Sudais ya sa Nanny ta shirya su kamar dai yanda ya saba duk lahadi xa su fita, yanxu kam babu inda shureim bai xuwa da kafafuwansa banda little Sudais da tashi ma wahala yake masa, kaya iri daya nanny ta sa masu as usual, kwankwasa kofar dakin Khadijah sudais yayi, tana xaune gaban madubi tana rubuta a farar takarda jin an kwankwasa kofa ta dauke takardar da sauri xata boye, dai dai nan ya bude kofar, cukuikuye papernta tayi, ya dinga kallonta yace "What's that" girgixa masa kai tayi ba tare da ta bari ta kallesa ba da sauri tace "Bakomai" yace "Uhn, sure?" Kin cewa komai tayi, yace "Toh ki shirya xan fita da twins sai ki raka mu" ta girgixa kai tace "Baxan je ba" yace "Why?" Sai a sannan ta kallesa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ya d'an yi murmushi ya juya ya fita, bude takardar tayi tana duba abinda ta rubuta, a hankali ta linke ta boye sa sannan ta sa Hijab dinta ta fita, har ya sauka parlor da su little sudais, ya juya ya kalleta yace "Ko d'an kwalliyan ma baxa ki yi ba" tace "Ehh" ya tabe baki ya fita tare da yaran ta bi bayan su, driving yake Khadijah na back seat da twins din shi kuma yana kallonsu ta madubi, horn ya ji an yi ya juya, da mamaki yake kallon matar da ta fito daga wani gida a motar ta kafin ya tsayar da tasa motar ya bude ya fito, ita ma ta sauka tace "Aliyu dama kana Abuja?" Ya kirkiri murmushi yace "Wallahi kuwa Mama, ina yini?" Tace "Lafiya lau Aliyu" lekan bayan motarsa ta dinga yi kafin tace "Kar dai kayi aure Hajiya Khadijah bata gaya min ba naga mace da yara a mota" sosai gabansa ya fadi yace "A'a mama, matar abokina ne da yaranta" Tace "Ayyo wajen ka suka xo?" Yace "A'a ajiye su xan je in yi" shi kansa ya san he just sound stupid, yayi saurin cewa "Amma mama kun dawo ne?" Tace "Noo, na xo yin abu ne yau sati na daya, amma ina jin jibi xan koma" yace "Holland din?" Tace "In sha Allah" yace "Toh Allah kai mu mama" tace "Ameen Aliyu, Allah yayi maku albarka" yana murmushi yace "Ameen" daga haka ya koma motarsa har lkcn gabansa na faduwa, Hajiya Rukayya aminiyar Mami ce don childhood frnds ne ma, ita ce ta sa Mami tayi ma Abba magana ya siya masa gida a layin lkcn anguwar na sabo, ita ma kuma a anguwar take amma sai su yi wata da watanni basa Nigeria da yaranta, har sudais ya kai bakin titi Hajiya Rukayya bata dauke idonta a kan motarsa ba, mace da yara a motarsa kuma yace matar abokinsa, kallon gidan Sudais din tayi kafin ta karasa can da kafa, kwankwasa gate ta dinga yi ko mai gadi xai bude amma shiru, can sai ga Nanny ta fito ta bude gate din, gaisheta Nanny tayi, Hajiya Rukayya tace "Ya kike" Nanny tace "Lafiya lau sai dai Masu gidan basa nan" shiru Hajiya Rukayya tayi kafin tace "Shi da matar suka fita kenan?" Nanny tace "Ehh har da yan biyun" Hajiya Rukayya tace "Toh shkkn" daga haka ta bar wajen da sauri ta wuce gidanta tana tunanin to ko dai karya sudais yyi mata yace bai yi aure ba, tana shiga motarta ta dau waya ta shiga kiran Mami.

Gaisawa Hajiya Rukayya suka yi da Mami, Mami tace "Ki ce kun dawo Nigeria kenan Hajiya" Hajiya Rukayya tace "Ina fa, just came a week ago to put things in other, ina ga xuwa jibi ma xan koma" Mami tace "Ayya, ashe baxa mu hadu ba kenan, ya yarana fa?" Hajiya Rukayya tace "Suna can, Jaheed ne dai ke Lagos" Mami tace "Toh maa sha Allah, naji dadin da kika kira wllh, kina Abuja koh?" Hajiya Rukayya tayi dariya tace "Toh ai baki sani ba, Aliyu na gani ma ya sa na kira ki yanxu" Mami tace "Haba dai..." Hajiya Rukayya tace "Wallahi kuwa ashe ya dawo gidansa, na fito gida xan je mall yanxu na gansa a mota shi ma" Mami tace "Toh, ni ban san me yasa ya koma Abuja da xama ba yanxu, sai mu yi wata ma ba mu gansa ba, idan nayi magana yace aiki" Hajiya Rukayya ta d'an yi shiru kafin tace "Amma yyi aure ne Hajiya Khadijah?" Mami tace "Ina fa, ba na gaya maki abinda yayi ma yarinyar nan da yake nema jiddah ba, da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login