Showing 183001 words to 186000 words out of 234058 words
gama ta dauko masa lunch box dinsa ta mika masa, ya nufi kofa yana daga mata hannu har ya fita khaleel ya kama hannunsa xuwa gun motarsa, ta tsaya bakin kofa tana kallonsu har suka fita gidan. Washegari Thursday da yamma Khadijah na parlor tana goge ma Shureim kayansa da uniforms, shi kuma yana bedroom yana waya da su Umma, mikewa tayi bayan ta kashe iron din jin an danna bell, ta isa kofar ta bude, khaleel ta gani tsaye, ya shafa kansa ba tare da ya kalleta ba yace "I will be traveling to Nigeria today Khadijah" shiru tayi tana kallonsa, yace "You take care of the little boy" tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare" yace "Ameen" xai shiga apartment dinsa ta fito a hankali tace "Dr..." Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta, Kasa magana tayi, murya can kasa yace "Am all ears Khadijah" Jin hawaye na neman taruwa idonta ta juya ta koma ciki kawai, da ya tashi tafiya kuma bai ma ce mata ya tafi ba yayi wucewar sa. Tun da Khadijah ta tashi sllhn asuba duk ta rasa me ke damunta, gaba daya ta ji bata jin dadi, komawa tayi ta kwanta kasancewar friday ne, tana ta kwance har kusan karfe takwas, can dai ta tashi tunawa da tayi anytime soon flight din su Barrister xai sauka kasar, Ruwan wanka ta hada ta fara tashin Shureim ta wanke masa baki tayi masa wanka ta sa yayi alwala sannan suka fito bayin, shirya sa tayi ta shimfida masa darduma yayi sllh sannan ta wuce bathroom don yin wanka, tana tsaye kitchen misalin karfe goma tana tunanin abinda xata girka ma Barrister, Shureim ya kawo mata wayarta dake ring, karba tayi ta kai kunne hade da sallama, yace "Kun tashi lafiya Amira?" Tace "Alhmdllh, har kun sauka kenan?" yace "Sure, tun karfe tara" Tace "Toh ina ka sauka?" Murmushi yayi yace "Baki san ina da apartment nan ba koh?" Ta langwabar da kai tace "I never knew" yace "You now know" murmushi kawai tayi, yace "Ina Shureim" kallon bakin kofar tayi taga ya wuce tace "Yana parlor, barrister sorry I asked... plss mai xan girka maka I don't know what u like most" Yace "Noo you don't worry dear, Ni nayi breakfast ma" shiru tayi jin abinda yace, Can tace "Toh lunch fah?" Yace "Just tea may be with cake" xaro ido tayi tace "Tea da cake kuma?" Yace "Uhm sure" tayi murmushi tace "Toh shikenan yaushe xaka taho?" Yace "After I am done with what I am doing, may be in the afternoon" tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, bye dear" daga haka ya katse wayar, fita tayi daga kitchen din don dama sun yi breakfast da Shureim. Karfe Sha daya ta shirya tare da Shureim suka fita don yin shopping, sun fito daga shopping mall wayarta dake jakarta ya fara ring, ta ajiye kayan hannunta ta bude jakar ta ciro wayar, number Aliyu ta gani, ta d'an yi jim kafin ta daga, shi yayi mata sallama ta amsa tayi shiru, yace "Ya kike Iman" tace "Lafiya lau" yace "Ya Shureim?" Tace "He is fine" yace "Maa Sha Allah" shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Xan tafi Nigeria later, you need anything?" Tace "As in?" Yace "I mean ko kina bukatar wani abu daga Nigeria?" Tace "Nothing" a hankali yace "Ohk can I go with Shureim plss" wani kallo ta shiga yi kamar yana gabanta tace "Beg your pardon?" D'an murmushi yayi kafin yace "Ranan litinin xa mu dawo Iman, daurin auren Neighbor din ki xan je, it's tomorrow, so we will be back Monday morning" Shiru Khadijah tayi tana son apprehending abinda Aliyu ya ce mata, a hankali yace "Hello, are you there Iman?" Ta dake tace "Waye Neighbor dina?" Da kamar baxai ce mata komai ba sai kuma yace "Dr Ayman"
Khadijah na rike da hannun Shureim suka fito waje, tun daga nesa Aliyu dake cikin motar ke kallonta, har suka iso kusa da motar ya fito, ko ba a fadi masa ba yasan tayi kuka, kuma gaba daya a sanyaye take, ya duka yana kallon Shureim a hankali yace "How are you" Shureim yyi masa murmushi yace "Fine, good afternoon uncle" shafa kansa yyi ya mike ya kalli Khadijah yace "Thank you Iman" jakar Shureim ta mika masa ya karba ya sa bayan mota sannan yana rike da hannunsa ya xaga ya sa shi gaban motar ya dawo, ya bude maxaunin driver ya shiga, sae a sannan Khadijah ta juya ta koma ciki ko sallama bata yi da yaron nata ba, har cikin ranta take jin tsanar khaleel ynxu kam, ta ji ko ganinsa ma bata son kara yi a rayuwarta, bedroom ta wuce ta kwanta, lkci daya ta mike da sauri tunawa da tayi Sudais yace xai xo da rana, ta fita xuwa kitchen don daura masa ruwan Lipton, ta xuba kayan kamshi sosai a ciki, sake gyara gidan tayi tana juye ruwan Lipton a flask ta ji wayarta na ring ta fito parlor ta dau wayar, dagawa tayi ta kai kunne tace "Ina yini barrister?" Yace "Alhmdllh, ki turo min address Amira" tace "Toh" katse wayar tayi ta tura masa street da house number ta text message, ta ajiye wayar taje ta ci gaba da abinda take, few minutes later Sudais ya kirata yace yana waje, ta sa hijab ta fito, Tsaye ta gansa jikin mota cikin shigar da ta lura ya fi so, wato na suit, har ta iso kusa da shi idonta na kan sa, kamar yanda shi ma yake kallonta, yayi murmushin sa mai kyau yace "Kyau kike karawa idan kika xo Uk kenan" Tayi murmushi ta sunkuyar da kanta, a hankali tace "Sannu da xuwa" yace "Yauwa sannu, ke daya ce cikin katon gidan nan?" Ta girgixa kai tana murmushi tace "A'a bani kadai bace, mu shiga ciki Barrister" Yace "Do I have to Amira?" Tace "Why not?" Daga haka ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, yana shiga cikin gidan ganin fararen kujeru da table a bangaren flat dinta karkashin wani shade yace "That's all, I will prefer staying outside" daga haka ya nufi wajen ya xauna ta tsaya tana kallonsa, bata fuska tayi tace "Barrister mu shiga ciki mana kaga fa akwai sanyi wajen..." Yace "Ke dai kike jin sanyin, just get me my tea sai ki yi wucewar ki ciki tunda kina jin sanyi" murmushi tayi ta wuce ciki sai ga ta ta fito da tray mai dauke da karamin flask da plate din cake" ajiye masa tayi ta ja kujera ta xauna tana dubansa tace "But me yasa baka son shiga ciki Barrister?" Ya bude plate din ya dau cake daya yace "What did you mean?" Ta xaro ido tace "But is there anything wrong with going inside?" Shiru yyi yana kallonta, can ta wara ido da sauri tace "Ohh yes you are right Barrister" sai kuma tayi murmushi, murmushin yayi shima ya kai cake din baki, a hankali tace "But.... Seven years back...." Sai kuma tayi shiru, kallonta ya dinga yi kafin yace "Don't forget you where sick and pregnant then, I have no choice...." shiru tayi a sanyaye tana kallonsa, ya buda ido sosai yace "Wait... Ina Shureim din?" Ta sauke idonta daga kallonsa, cikin sanyin murya tace "Sun tafi Nigeria da Aliyu" da mamaki yace "Wani Aliyun?" Bata ce komai ba na few seconds kafin daga karshe tace "Aliyu dai" Sudais ya ajiye sauran cake din hannunsa yace "is he also in Uk?" Kai ta gyada masa, Bai iya ya sake cewa komai ba, bayan wani lkci a hankali yace "Kuna haduwa da shi kenan?" Ta sauke idonta daga kallonsa tace "Sometimes in school" Sudais bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, tana ta kallonsa har ya gama wayar sanann ta sunkuyar da kanta, ya ajiye wayarsa in a very low tone yace "Amira?" A hankali ita ma tace "Na'am" yace "I don't want to deprive you of anything you wish for ur self, be frank plss Amira ki fada min gaskiya, did you want to go back to the father of ur kid?" Kallonsa ta dinga yi da wani expression, cike da karfin hali tace "Ban gane ba Barrister" Dago kai yyi yana kallon eye balls dinta yace "I mean, kina da ra'ayin komawa gun Aliyu ku yi aure ne?" Ta fashe masa da kuka tace "Anybody can say this but not you barrister, kai me tuna min irin wahalar rayuwar da na sha ta dalilin Aliyu ne, you witnessed everything, ko kuma ince tare muka sha wahalar barrister coz all those time you where by my side, Aliyu raped me without mercy har yau memory din na kai na very fresh, scene din na ido na, bayan faruwar hakan ya canxa min a gidan ya daina ma amsa gaisuwata ya daina xama duk inda nake, daga karshe he sent me away without thinking twice, with huge sum of money bayan yasan bani da kowa, Bai yi tunanin ko xan gane gida ko baxan gane ba" kuka take sosai, Sudais ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido ya kasa cewa komai, Tana ci gaba da kuka tace "Har yau ni ban ga wani prove that will convince me that ba da gangan Aliyu yayi min abinda ya min ba, ban ga prove da xan yarda cewar ba da gangan yayi raping dina ba, fine... Mahaifiyarsa cewa tayi it's a set up, did she have any choice? Dole ta kare d'an ta, an taba set up da rape dama?? Wllh dalilin marigayin yaro na nake raga ma Aliyu har nake kulasa naji kuma xan iya xumunci da shi albarkacin yaran dake tsakaninmu, of recent I dreamt of my little boy telling me to forgive his dad, so why will I not forgive him, nasan ya cuce ni ya bata min rayuwa but he gave me happiness at the same time... My boys" hade kanta tayi da table tana kuka sosai, Sudais ya bude idanuwansa yana kallonta cike da tausayin ta, cikin sanyin murya yace "Am sorry Amira, you misunderstood me, I know ur pain but..." Ta dago hawaye na sakko mata tace "But what?" Yyi kasa da murya pleadingly yace "I am sorry plss" kin cewa komai tayi, yace "Kin hakura?" A hankali ta gyada masa kai, ya lumshe ido ya bude yace "Nagode dear, do you have any plans for our wedding?" Ring dinta ta dinga jujjuyawa bata ce komai ba sai dai gaba daya tunaninta a lkcn ya tafi kan khaleel, a hankali yace "Kin yi shiru" wani mugun haushin kanta taji ganin Wanda ya fado mata a rai, d'an tsaki tayi ba tare da ta san tayi hakan ba, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Ke da wa kuma??" Da sauri ta kallesa ta xaro ido tace "Don Allah kayi hakuri barrister wllh ba da kai nake ba, ban san...." Katse ta yayi yace "Nasan ba da ni kike ba Amira, I can see you are lost in ur thought, tel me what u are thinking of" ta girgixa kai tana kirkiran murmushi tace "Uhn ba komai fa" murmushi yayi yana shafa kansa yace "Toh shkkn" flask din ya bude ta mike da sauri tace "Bari in xuba maka" daga haka ta karasa budewa ta xuba masa a cikin mug dake kife, kallonsa tayi taga kallonta kawai yake shi ma, ta sauke kanta kasa a hankali tace "In sa maka Madara?" Ya girgixa kai yace "Noo, I prefer it black" Komawa tayi ta xauna tana murmushi tace "Toh, what will you take for dinner?" Ya d'an bude ido bayan ya dau Lipton din yace "Da daddare sometimes ina shan tea with irish and egg" ta langwabar da kai tace "Toh da safe fa?" Yayi murmushi yace "Tea and bread" da mamaki ta kallesa tace "Toh barrister baka cin tuwo ko shinkafa ko dai any other food?" Yace "Ina ci idan na samu" shiru tayi bata sake cewa komai ba, lkci daya taji tausayinsa don ko bai fito fili ya gaya mata ba ta gane Matarasa ce bata girki kenan, d'an murmushi tayi tace "Toh xan maka tuwo anjima ka dawo ka karba" ya xaro ido yace "A'a ku mata da bakwa son girki mai wahala don't stress ur self dear I will take tea na riga na saba" tace "No, ba ko wace mace ce ke jin kiwiyar girki ba, I am also exceptional, ko mai kake so xan girka maka anjima" murmushi yayi sosai yace "Toh nagode Amira" Sai biyar saura ya bar gidan, shi ma saboda ya damu bai yi la'asar bane..." Ta rakasa har bakin motarsa sai da ya wuce sannan ta koma ciki. Kamar yanda ta fada masa kafin magrib har ta gama yi masa tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup, ta xuba masa a warmer, ganin bai kirata ba har bakwai ita ta kirasa, bayan ya dauka a hankali tace "Barrister baka dawo ka karba ba kuma" yayi kasa da murya yace "I really don't want to stress you dear, I learn girka tuwo akwai wahala..." Katse sa tayi tace " Ni dai ka xo ka amsa na gama, akwai wahala gun ragwayen mata dai" dariya yayi yace "Ohh really?" Tace "Yea, tun daxu na gama, ka taho ka amsa plss" a hankali yace "Toh gani xuwa Amira, I am proud of you" murmushi kawai tayi ta katse wayarta, cikin minti goma ya taho amsan abincin ya dinga sa mata albarka har ya tafi. Washegari Saturday da yamma Sudais ya xo ya fita da ita su xaga gari, duk da sanyin garin, the moment was just waow, ita dai ta san Sudais na sonta fiye da xaton ta but bata san me yasa ta kasa kwantar da hankalinta ba, he really made her day on Saturday, don babu wani damuwa tare da ita ya maido ta gida, kewan Shureim ma da take ji gaba daya taji babu shi yanxu. Ranan lahadi da safe tun da ta tashi ta shiga kitchen don girka masa shinkafa da miya, karfe goma ta kirasa, bayan ya dau wayar jin muryarsa a hankali tace "Bacci kake barrister?" Yace "Uhn am now awake" tace "Kayi hakuri ban san baka tashi ba, ka gaya min address din ka sai in kawo maka breakfast" ya mike xaune daga kwancen da yake kan gado yace "Noo ba sai kin ba kan ki wahala ba xan shirya yanxu in fito" tace "Toh, kayi hakuri" ya wara idanuwansa yace "Hakuri kuma dear" murmushi tayi ta katse wayar, bedroom ta wuce ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin kananun kaya, tana xaune gaban mirror tana gyaran gashinta kawai ta tabe baki ita kadai, yanxu su Maryam gaba daya sun tafi Nigeria biki kenan, d'an tsaki tayi a ranta tace do I have to care, turo baki tayi ta mike ta daure gashinta ta dau rigar sanyi ta sa da head warmer ta dawo parlor ta xauna.
✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Ranan lahadi da safe Khadijah ta raka Sudais Airport, har ranta ta dinga jin kewarsa bayan ya tafi duk jikinta yayi sanyi, tana tsaye inda xata hau cab a wajen airport din kamar ance ta kalli gefenta taga khaleel tsaye alamar fitowarsa kenan shi ma daga cikin airport, farar shadda ce jikinsa sai walkiya take, Khadijah ta dauke kai da sauri tun kan ya kallo inda take ta karasa gun cab da ta gani ta shiga ta fada ma driver din inda xata. Suna isa gida ta fito ta basa kudin sa sannan ta shiga ciki da sauri ta bude jakarta tana kokarin ciro makulli, dai dai nan khaleel ya shigo gidan, bata yarda ta juya ba ta bude kofarta ta shige. Daki ta wuce ta tattara reading materials dinta, ta dau kayanta kala biyu da nyt wear ta fito rike da jakarta, kulle apartment dinta tayi ta wuce kamar warce ake jira a waje tsabar haste din, tana fita ta samu Cab ta hau xuwa gidan Vanessa. Gaba daya ranan a gidan ta yini, sai dai she was just uncomfortable saboda mazan turawan dake xuwa suke fita gidan, gashi ba isasshen hankali gare su ba duk ta takura, ta so komawa gida da daddare amma saboda sanyi ta hakura ta kwana gidan, washegari daga gidan ta shirya xuwa sch tare da Vanessa bayan sun yi breakfast, suna gama lectures Vanessa ta sake jan Khadijah suka koma gidanta, tana xaune parlorn Vanessa bayan tayi magrib idonta a kan takardun hannunta ta jawo wayarta dake ring, number Aliyu ta gani sai a sannan ta tuna da yaronta ta yi picking kiran, daga daya bangaren yace "How are you Iman" tace "Fyn, how about my son" yace "Naga kin ma mance da shi gaba daya" ta hade rai tace "Taya xan mance shi?" Murmushi yayi yace "Toh gobe da safe xan kawo shi don ya samu yaje schl" tace "Kun dawo ne?" Yace "Yea daxu da yamma" shiru ta d'an yi kafin tace "Bring him in the afternoon" yace "Alryt then" daga haka ta katse wayar ta. Ranan talata bayan sun gana lectures misalin karfe biyu Khadijah ta koma gida, bude kofar apartment dinta tayi a hankali ta shiga sannan ta rufe, gyaran gidan ta shiga yi, bayan ta tsaftace ko ina, ta bude kofar kitchen xata xubda shara suka yi ido hudu da wata yarinya da ta xo xubda sharan ita ma, yarinyar ce ta fara cewa "Sannu" Khadijah tace "Ina yini?" Yarinyar tace " Lafiya lau, jiya da muka xo mun duba baki nan ashe kin dawo" Khadijah ta d'an yi murmushi tace "Ehh yanxu na dawo" yarinyar tace "Ayya, to Sannu da xuwa" Khadijah tace "Idan na gama xan shigo yanxu" yarinyar tace "Toh sai kin shigo" daga haka Khadijah ta wuce ciki, Allah ma ya san ba don ranta ya so ta fada haka ba, kawai dai yarinyar ta mata kwarjini ne, and kuma sai taga kamar suna kama, toh ko dai ita ce warce su