Showing 213001 words to 216000 words out of 234058 words
a baya, ki kwantar da hankalin ki da Yaya Aliyu you won't regret it am giving you my words...." khadijah ta dinga share hawayen dake sakko mata bata ce komai ba, tasan ita dai baxata taba kwantar da hankalin ta da wanda yyi disfiguring dinta heartlessly ba, cikin kwantar da murya Baby "Kiyi hakuri Iman, nima wllh ban san da yayanmu aka daura auren ba sai da muka tashi barin gida jiya da yamma kin dai ji na rantse maki" Har sannan khadijah bata iya ta ce komai ba sai goge idonta take, Baby tace "Ki sakko ki xo gu gaisa da su Barrister suna parlor" Kallonta khadijah tayi da sauri ta tsuke fuska tana girgixa kai tace "Am not going anywhere, they are nothing but group of deceivers..." duk yanda baby ta dinga lallabata Khadijah kin yarda ta fito tayi har da kukan ta, baby ta rasa yanda xata yi, mikewa tayi daga karshe ta dawo parlor, Aliyu na ganinta yasan kwanan xancen, Baby ta kirkiri murmushi tace "Tana fa bacci ne, Kuma bana son tada ta...." Murmushi Sudais yyi yana shafa beard dinsa a hankali yace "That's nyc, thanks for covering up for her, but we are not strangers, kuma baxa mu ji haushi ba idan kin ce tace baxata fito ba, wataran xata fito mu ganta ai" Dariya khaleel yyi yana kallon baby da ta rikice sai rawar baki take, Aliyu yyi murmushi bai dai ce komai ba, Sudais na kallonta duk da dariyar da ta basa shi ma yace "Sorry, just relax Mami ni ban yi haka don ki rikice ba" Baby bata san lkcn da ta balla masa harara ba ta juya da sauri xata wuce tana murmushi, Aliyu yace "Kawo masu drink" kitchen ta wuce ta dauko masu drink din ta ajiye, Aliyu yace "Abinci fa?" Sudais yace "Nop Alhmdllh" mikewa baby tayi ta dau abincin ta wuce sama, Dakin khadijah ta shiga tana harararta ta ajiye abincin hannunta tace "thanks for making me look stupid downstairs, Kuma abincin ma na daina kawowa sai dai ku fita eatry da mijin naki" daga haka ta wuce, tana shiga parlor tace "Yaya ni xan koma, Mumy tace kar in dade" Yace "Alryt then, da driver ku ka xo?" Ta girgixa kai yace "Toh je sama ki dau transport" Khaleel yace "Xa mu wuce yanxu sai Barrister yyi dropping dinta tunda hanyar daya" Har bakin mota Aliyu ya raka su bayan sun wuce ya dawo cikin gidan, sama ya wuce ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta. Har aka yi la'asar khadijah na daki, duk da ta ji gidan shiru ta kasa fitowa ta dau plate ta debi abinci, Tana tunanin yanda xata fita aka bude kofar dakin Aliyu ya shigo, sau daya ya kalleta ya mayar da dubansa kan abincin da Baby ta ajiye dakin, ya isa gun abincin yace "Ain't you eating the food?" Banxa tayi masa, ya duka ya bude warmer din yana kallon abincin, dauka yayi ya juya ya nufi kofa ta bi sa da wani kallo, ganin ya fita ta tashi da sauri ta bi bayansa har ya shiga dakinsa ta shiga ya juyo yana kallonta, tace "Nace maka na ci abincin ne ni?" Kamar xata yi kuka tayi maganar, dariya ta basa, ya yi murmushi yace "You never told me" daga haka ya mika mata ta karbe abincin ta juya ta fita, yana jin ta sauka don dauko plate a kitchen ta dawo ta shiga dakinta, sai a sannan ya sauka xuwa kitchen ya hada shayi, duk da yunwan da khadijah take ji bata iya ta ci abincin me yawa ba, ta mike daga karshe ta fita, har xata kai abincin kasa sai kuma ta tsaya a hankali ta bude dakinsa ta gansa xaune yana rike da cup din shayin, ta sauke kanta kasa ta shiga dakin ta ajiye masa warmer din ta juya ta fita ya bi ta da ido. Karfe shidda saura baby ta dawo gidan tare da shureim, Sau uku tana danna bell, khadijah ta mike ta sauka bata san Aliyu ma ya fito bude mata ba, yana bude kofar Shureim ya wara ido ganinsa cike da murna yace "Unclee" nufo sa yayi da nufin rungumesa ya hango khadijah, Wara ido ya kara yi yace "Anty...." Murmushi ta sakar masa ta buda masa hannu, Har ya dau hanyar inda take sai kuma ya tsaya ya juyo yana kallon Aliyu dake kallonsu, dawowa yyi gun sa da gudu, Aliyu ya daga sa sama ya rungume sa yana murmushi yayi Pecking cheek dinsa, Lkci daya murmushin fuskar khadijah yayi fading, Baby bata san lkcn da ta fashe da dariya ba, Shureim ya xame daga jikin Aliyu ya nufi khadijah da gudu, wani kallo ta watsa masa tace "If I slap you" nan ya taka burki ya tsaya yana kallonta, Ta turo baki ta juya ta wuce sama, Murmushi kawai Aliyu yayi ya nufi yaron ya daga sa sama yace "How are you sweetheart" yace "Am fine" Baby ta ajiye abincin hannunta tace "Ina yini yayana" yace "Alhmdllh" tace "Driver na jira na waje, sai da safe" yace "Alright ki gaida mumy, tell her thank you" tayi murmushi tace "Toh yaya" daga haka ta juya ta wuce tana daga ma Shureim hannun, yana rike da Shureim suka haura sama ya shiga dakin khadijah ajiye mata shi yyi kusa da ita yace "Greet her now" a hankali Shureim yace "Anty good evening" dauke kai tayi ta hade rai tace "Evening" Daukansa Aliyu yayi suka fita dakin ta bi sa da wani kallo, har karfe kusan tara na dare khadijah bata ji motsin su ba, ta yi wanka ta shirya cikin night wear, jin shirun yyi yawa ta sa Hijab ta fita, ta fi minti biyu a tsaye, kafin ta tura kofar dakin a hankali, duhu ne dakin, ta laluba ta kunna switch, kwance taga Aliyu Shureim na kwance kusa da shi duk sun yi bacci, kashe Ac dake aiki tayi ta kashe switch din ta fita dakin ta koma nata ta kwanta. Kasa bacci tayi sai juye juye take har kusan sha biyu ta ji an bude kofa, sosai gabanta ya fadi ta kalli direction din kofar duk da wuta a kashe yake, rufe kofar yyi ba tare da ya kunna wutan ba ya iso har inda take ya duka, mirginawa tayi da sauri daga wajen tace "Meye haka?" Yace "Na xo duba ki ne kamar yanda ke ma kika xo duba mu" Xaro ido tayi tana kallonsa cikin duhun, yyi murmushi murya can kasa yace "Sweet dreams" daga haka ya fita ya kulle kofar dakin.
A hankali khadijah ta koma ta kwanta, bata kara minti biyar ba bacci ya dauketa. Da asuba tana jin fitansu tare da Shureim xa su masallaci, ita ma ta mike ta shiga bayi, tana xaune kan darduma tana azkar taji shigowarsu gidan, bude kofar dakinta Aliyu yyi suka shigo tare da Shureim, kallo daya tayi masu ta dauke kai, ya xauna gefen gado Shureim ya nufe ta ya durkusa gabanta yace "Anty ina kwana?" Tana kallonsa tace "How was ur nyt?" Ya wara ido yace "It was cool Anty" Bata ce komai ba ta saci kallon Aliyu suka hada ido, d'an murmushi yayi a hankali yace "Good morning Iman" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya mike ya nufi kofa Shureim ya bi bayansa da sauri ta bi su da ido har suka fita, ta fi minti ashirin xaune ganin gari ya fara washewa ta mike, tana sane jiya babu abinda tayi a gidan, yau kam ta sauka parlor ta share ko ina ta goge, ta shiga kitchen ma ta gyara ta goge, tana kokarin sa turaren wuta a burner aka danna bell, mikewa tayi tana kallon kofar, ta wuce sama da sauri don dauko hijab ta dawo ta bude, Baby ce tsaye da breakfast, Khadijah ta langwabar da kai tace "Don Allah daga yanxu kar ki sake kawo abinci xan yi girki muna ba Mumy wahala..." Baby ta wara ido sai kuma tayi dariya tace "Xa dai ki girka abinda xa ki ci, tunda nasan ba bama yayana xa ki yi ba, yaron ki kam nasan shi ma xa ki basa, Abbansa dai ne baxa a bai ma ba" tabe baki khadijah tayi ta bata hanya ta shigo ta ajiye abincin nan parlor tace "Da fatan kun tashi lafiya, yau naga har da su gyare gyaren gida meye sirrin Iman?" Tana murmushi da tsigar tsokana ta kare maganar, khadijah ta hade rai tace "Wani irin sirri?" yar dariya Baby tayi tace "Oho, ni dai xan wuce, a gaida min yayana" Daga haka ta nufi kofa khadijah ta bi ta da kallo har ta fita sannan ta tabe baki, ta koma ta ci gaba da abinda take, dinning ta kai breakfast din ta ajiye sannan ta wuce sama ta shiga daki, nan ma ta gyara gadonta tayi goge goge kafin ta shiga wanka, tana xaune gaban mirror bayan ta fito wanka tana shafe shafe aka bude kofar bedroom din, xaro ido tayi tana gyara towel din jikinta, ganin Shureim ne ya shigo ta sauke ajiyar xuciya, ya iso kusa da ita yace "Anty am hungry" tace "Me ya hana uncle din baka breakfast" Ya buda hannu yace "He told me I shud come to you ki bani" Tana shafa mai a kafarta tace "Shi me yake yi?" Shureim ya matso cream din xai shafa mata ta 6alla masa harara tace "Ina wasa da kai koh?" Ya mike yace "Anty taya ki xan yi" toes dinta ta mika masa tace "Toh shafa a nan" ya durkusa yana shafa mata tace "Tambayar ka nayi me uncle din yake?" Ya kalleta yace "He is lying down" shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Anty yace min he is not feeling fine" Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "What's wrong with him" Yace "I don't know" Tace "Je parlor ka jira ni in sa kaya sai in xo in baka breakfast" yace "Toh" sanann ya fita dakin, mikewa tayi ta dau atamfar da xata sa na riga da skirt, sosai dinkin yayi mata kyau tayi simple dauri na dankwali ta sa eye pencil a idonta sai chapette ah two colored lips dinta, sosai tayi kyau, ta fesa turare daga karshe ta fita dakin, har xata sauka stairs sai kuma ta tsaya, ta fi minti biyu tsaye kafin ta karasa kofar dakinsa a hankali ta bude, kwance ta gansa ya rufa da duvet har kansa, ta sauke idonta kasa ta karasa dakin kamar mai counting steps dinta, tana ta tsaye kusa da gadon tana kallonsa, a hankali ta durkusa dab da shi ta cire duvet din fuskarsa, idanuwansa a lumshe suke, ta kai hannu forehead dinsa, lkci daya ya bude idonsa tayi saurin dauke hannunta ta koma baya, kasa tashi tayi kuma bata yarda sun kara hada ido ba ta fara kame kame, kallonta kawai yake, ta dago daga karshe tana kallonsa a hankali tace "Are you sick?" Ya mike xaune yace "No.... am alright" shiru tayi tana kallonsa, ya sauka daga kan gadon ya nufi bayi ta bi sa da kallo don kana ganinsa kasan karfin hali yake yi, Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita dakin, kwance ta ga Shureim ya kunna cartoon yana kallo parlorn yana ganin ta yyi saurin kashe tvn da remote din hannunsa, ta tsaya tana kallonsa tace "Who asked you to switch on the tv?" Shiru yyi yana kallonta, ta wuce dining ta hada masa shayi a cup ta debar masa dankali da kwai da plantain, sannan ta yankar masa bread karami ta daura gefen plate din Irish din, tace "Zo ka xauna nan Shureim" ya taso ta ja masa kujerar dinning din ya xauna ta ajiye masa abincin a gabansa sannan ta koma kitchen ta dauko wani cup din ta dawo ta hada wani shayin, ta debi Irish da kwai a plate, ta dauko wani bowl ta xuba pepper soup na kayan ciki, gaba daya ta daura su kan tray ta dauka ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakin nasa, xaune ta gansa gefen gado ya rike kansa, jin an bude kofa ya dago yana kallonta, kanta a kasa ta iso har kusa da shi ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta fita dakin. Dining ta koma gun Shureim ta xauna kujerar kusa da na shi ita ma ta hada shayin, a hankali take sha har ta gama, tuni Shureim ma ya gama ya mike pleadingly yace "Anty plss in kunna tv?" Kai ta gyada masa ya juya ya wuce parlor, ta kwashe duk abinda suka bata ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, sama ta wuce ta bude bedroom din Aliyu, kwance ta gansa ya kara rufa da duvet, ta karasa tana kallon breakfast da ta ajiye masa, Bata san lkcn da ta xauna gefen gadon ta yaye duvet din tana kallonsa da damuwa tace "Baka yi breakfast din ba? What's wrong with you?" Ganin bai bude ido ba kuma bai ce komai ba ta kamo hannun sa da damuwa tace "Talk to me plss" bude ido yyi ya mike xaune, ta dauko cup din shayin da ta rufe ta bude tana mika masa tace "Gashi ka sha sai ka sha magani" karba yyi xata dauko plate na irish ya dakatar da ita "Noo I will take this first" da kyar yyi maganar, ta dago tana kallonsa ya kai shayin baki kamar wanda xai sha magani, kadan ya kurba ya cire a bakinsa, tace "Da zafi ne?" yana girgixa kai ya mika mata, ta hade rai tace "Me xan yi da shi?" Xai ajiye kasa tayi saurin cewa "Kar ka ajiye shi, u better force ur self to drink it..." Bai saurareta ba ya ajiye ya mike ya nufi bayi da sauri, a sanyaye ta mike bi sa da kallo, tana ta tsaye ita dai bata ji yana amai ba kamar ynda tayi tunani, can dai ta bi bayansa, jingina tayi da kofa tana kallonsa ganin aman yyi har ya wanke wajen, ya juyo xai fita bayin ta rikesa a hankali tace "Let me make you water sai kayi wanka" yana gyada kai yace "Finish first" daga haka ya fita, ta hada masa ruwan ta fito, kwance ta samesa ya kara rufe kansa, ta cire duvet din da damuwa tace "Kayi wankan sae mu je asibiti" da kyar ta samu ya mike xaune, tana ta kallonsa ganin har rama yyi, sauka yyi daga kan gadon ya cire jallabiyar jikinsa ta amsa ta ajiye sannan ya wuce bathroom, sai a sannan ta fita dakin a sanyaye. zaunawa tayi gefen gadonta tayi tagumi bayan kusan minti talatin ta tashi ta koma dakinsa, dai dai lkcn ya fito wanka daure da towel, tayi saurin juyawa kamar mai neman abu sai kuma ta fita dakin, turo baki tayi ta sauka downstairs ta tadda Shureim yana ta kallo ta xauna kusa da shi. Jin alamar Aliyu na sakkowa stairs ta kalli direction din, kananun kaya ne jikinsa yana rike da makullin mota ya iso parlorn, ta mike tana kallonsa tace "Where are you going to?" Bai ce komai ba, ya nufi kofa, ta isa gabansa ta hade rai tace "Nace ina xa ka?" Ya ki kallonta yace "To get drugs" kwace makullin hannunsa tayi tace "Let me do the driving" Daga haka ta nufi stairs ya bi ta da kallon gefen ido, mayafi karami ta dauko a daki ta rataya a wuya ya dinga kallonta, ganin ta nufi kofa yace "Iman!!!" juyowa tayi tana kallonsa, yana nuna mayafin kanta yace "Haka xa ki fita?" Kallon kanta tayi daga sama har kasa tana masa wani kallo tace "So?" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta hade rai ta dawo ta damka masa makullinsa tace "Sai ka ja motar, ka tafi inda xaka" Komawa tayi ta xauna ya bi ta da kallo kafin ya fita parlorn, turo baki tayi jin yana warming mota ta mike ta wuce sama ta dauko Hijab dinta ta sa ta sakko parlor, kashe tv tayi tana hararan Shureim da duk hankalinsa gaba daya na kan kallo as if his life depend on it, ya mike da sauri yana kallonta yace "Anty ina xa ki je" Bata tanka sa ba ta nufi kofa ya bi bayanta, Tun daga nesa Aliyu ke kallonsu daga cikin motarsa ko kiftawa babu har suka iso ya dauke kansa, Ta hade rai tace "Ka koma daya side din" D'an murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba ya fito ya koma daya bangaren Shureim na biye da shi a baya, yaron ya bude back seat ya shiga, shi kuma ya xauna front seat, ta shiga maxaunin driver, sabon mai gadi dake bakin gate ya bude gate din ta fita da motar, a hankali take driving din har suka hau saman titi, kamar ana tilastata tace "Wani pharmacy?" Gaya mata yyi idanuwansa a kan titi, kira'ar sheikh Sudais kadai ke tashi a motar in a very low tone, yace "Who taught you how to drive" Bata ce komai ba har suka iso pharmacy din, sai a sannan ta kallesa a takaice tace "A Good Samaritan taught me" Bai ko kalleta ba ya bude motar yayi wucewarsa, ta bi sa da wani kallo, Shureim yace "Anty, Uncle ba shi da lafiya koh" Bata ce masa komai ba, Bayan kusan minti goma Aliyu ya fito rike da ledan drugs ya shiga motar, ganin hanyar da ta dauka, yana kallonta da kyau yace "Ina xa ki je?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Xan je gida in dauko ma Shureim wears dinsa" "Noo, mu wuce gida, xan je da kaina in amso masa ba sai kin je ba" A hankali take ta tafiya da motar shi dai bai kara ce mata komai ba, can ta turo baki ta dau hanyar gida... Tana gama parking ya bude motar ya fita ya bude back seat ya fiddo Shureim suka wuce ciki ta bi su da kallo, Babu kowa parlorn da ta shigo, ta ajiye makullin hannunta ta