Showing 60001 words to 63000 words out of 234058 words
ba ta shiga share kwallin, jawota yyi ya fixge handkerchief din a hannunta ya fara goge mata idon, sai bata fuska take xata yi kuka, ya hade rai yace "What?" A hankali tace "It's painful" yace "Good... Next time idan xata sa maki baxa ki yarda ba" ajiye handkerchief din yyi bayan ya tabbatar bbu sauran kwallin a idonta ya fita, ita ma ta fito ya wuce direct office din principal din kasancewar shi ma makarantar da yyi kenan, kuma har lkcn ba a canxa principal ba, da ladabi ya gaisa da principal din da shi ma yyi murnar ganinsa sosai, nan Aliyu ya sanar masa ya xo enrolling khadijah ne, principal din ya tambayi khadijah class din da take xata ce jss2 Aliyu yyi saurin cewa Jss3, xaro ido tayi ta kallesa ya mata wani kallo ya ci gaba da yi ma principal din bayani, farkon abinda principal din ya bukata shine transfer letter daga previous schl dinta, Aliyu ya d'an yi jim, can yace masa xai karbo ya kawo, da yake principal din ya san shi yasan family dinsu bai masa gardama ba, nan kuma yasa aka yi interviewing dinta, babu bata lkci kuma aka yarda a sa jss3 din coz she is capable, a take Aliyu yyi transfer din school fees da other fees da ake biya na makarantar har takardu da uniforms guda uku, Principal na kallonta xai cike mata receipt yace "What's ur name" kafin Khadijah tace komai Aliyu yace "Khadijatul Iman" Khadijah ta xaro ido tana kallonsa, principal din yace "Surname" sai a sannan Aliyu ya kalleta, ta langwabar da kai a hankali tace "Muhammad" principal din ya so aliyu ya maida ta gida gobe tayi resuming yace A'a ta fara yau din shi aiki xai wuce ba gida ba, a tare suka fito da Khadijah office din principal din bayan yace Aliyu ya nuna mata ajinta, Tana biye da shi a baya ya juya yana kallonta yace "Wani makarantar kika yi primary da jss1?" Tace "Yan dutse" yace "Kano?" Ta gyada masa kai, bai sake cewa komai ba har ya isa class dinsu Baby ya nuna mata ta shiga tana daga masu hannu, ya juya ya tafi gun da ya bar motarsa. Karfe hudu saura driver ya ajiye su a gida, sai da su siyama dake ta kumburi cikin motar suka fita sannan khadijah ta fito rike da ledan uniforms dinta da takardu, Baby ma ta fito rike da sauran takardun khadijah, Duk sai da kyauta ta bi ta yi ma uniforms din tsirara daga ledansu tana washe baki tace "Yarinya ta xama yar boko, toh me suka koya maku yau a makarantar" Khadijah tayi dariya tana cire kayan jikinta tace "anty mai girki yanxu xan yi wanka ne, idan na fito xan koya maki" daga haka ta shiga bathroom da sauri, har daki kyauta ta kawo mata abinci bayan ta xuba ma su siyama nasu a dinning, khadijah dake ta kallon pepper soups kala kusan uku da ta xubo mata tace "anty mai girki, kinyi girki da yawa kenan yau?" Kyauta tace "Ke Alhaji da kanin Aliyu xa su dawo anjima, yanxu haka suna can cikin jirgi a sararin samaniya, ai girkin da nayi ya fi kala shidda yau tun safe nake kitchen, na kuma ji Hajiya nacewa kila baxawara ma ta dawo yau" Khadijah ta tallabi cin dinta tace "Waye Alhaji anty mai girki?" Kyauta ta hade rai tace "Babansu Aliyu mana" Khadijah ta xaro ido da mamaki tace "Dama yana da baba, ai na xata shine baban gidan" Kyauta tayi tsaki tace "Dadina dake shegen shirme, toh an ce maki shi ya haifi kansa, ubansa nace maki xai dawo anjima tare da kanin sa saleem" Khadijah ta turo baki tana d'and'ana naman ragon gabanta tace "Toh naji" Baby ce ta shigo dakin bayan Khadijah ta gama cin abinci kyauta ta fita da plates din, baby tace "Mumyna tace in kira ki" Mikewa Khadijah tayi ta bi bayanta suka wuce sama, tun bayan da Anty khadijah ta koreta sai ranan ta sake hawa saman gidan, baby ta bude kofar dakin mumy ta shiga, khadijah ta tsaya daga bakin kofa tana lekan dakin, Mumy da ta hangota tace "Shigo khadijah" khadijah ta shiga ta xauna kasa tace "Ina yini Anty" mumy tace "Lafiya lau, ya school din" Khadijah tayi murmushi tace "I like it Anty" Mumy tace "Sun baki uniform?" Khadijah ta gyada mata kai, Baby tace "Mumy same class fa muke da ita" Mumy tace "That's good, ina books din da suka baki" mikewa Khadijah tayi da sauri ta ce "Xan dauko" daga haka ta koma kasa ta dauko books din ta ajiye ma Mumy, Mumy na kallon book din ganin Iman a jiki tace "Iman? Is that ur name?" Khadijah tayi murmushi ta gyada mata kai a hankali, mumy tace "Maa sha Allah" wani sabon jaka da bakin cover shoe da socks uku mumy ta dauko ta mika ma khadijah tace "Gashi sai ki xuba books din ciki" khadijah ta wara ido tace "Anty nagode, thank you" Mumy tace "Welcm, tashi ki tafi" mikewa khadijah tayi cike da murna ta fita, baby dake kallon mumynta tace "Mumy ni yaushe xa ki siya min sabon jaka?" Mumy tace "Soon" har kitchen Khadijah ta kai ma kyauta abinda mumy ta bata, kyauta ta amshe tana washe hakora tace "Allahu Akbar barin baxawara gidan nan ya maki rana dije, Allah ya makaleta a duk inda take har Hajiya ta gama dake ta dawo kai na nima" Shigowar Aneesah kitchen din yasa Kyauta tayi shiru sum sum ta fita don kai kayan daki Khadijah na biye da ita a baya. Suna shiga dakin ko minti biyar ba ayi ba aka kwankwasa kofa kyauta ta tashi da sauri ta bude, Aliyu ne tsaye rike da wani jakar mai kyau ya mika ma kyauta yace "Gashi ki bata" kyauta ta risina ta karba tace "Toh ta gode, Allah saka da alkhairi" bai ce komai ba ya juya ya bar wajen, kyauta ta bude jakar jin da nauyi ta ga takalma har biyu da safa uku a ciki sai water bottle irin nasu baby, kyauta ta rike haba tace "Ni dai ce ba a so a gidan nan wllh" Khadijah dake jera books dinta a jakar da mumy ta bata ta taso da sauri tace "Anty mai girki menene" Kyauta ta dungura mata tace "Duk kin fi ni goshi wllh" Khadijah ta kyalkyale da dariya ta karbi jakar da a gabansa aka rubuta *Iman* ta wara ido tace "Waowww"
Shirin tafiya islamiyya suka yi bayan sun ci abinci, tun da Khadijah ta fito sanye da uniform din islamiyya Siyama ke ta harararta, kyauta da ta lura da hakan ta ja Khadijah kitchen tace "Kafin su gama iskancinsu da harare harare tafi gun Sanusi ki jira a gun motar" Khadijah ta fita ta tafi gun da motar yake ta tsaya, Aliyu ne ya fito baby na biye da shi a baya ita ma ta shirya, Baby tace "Yayanmu kenan baxan je mu taho da Daddy ba?" Yana bude motarsa yace "Ai islamiyya xa ki baby" ta bata fuska tace "Yaya yau kadai xan yi fashi fa" yace "Bulalan da xa a maki fa?" Tace "Ae cewa xanyi bani da lafiya sai ka rubuta min medical report in kai" yace "C'mon wuce ki shiga mota ku tafi makaranta my frnd... Bakin ki kamar medical report" Juyawa tayi kamar xata yi kuka ta tafi gun Khadijah dake kallonsu, ya shiga motarsa ya bar gidan. Karfe shidda da 'yan mintuna suka shigo gidan daga islamiyya, wani saurayi ne xaune parlorn shi kadai yana danna laptop, ba can suke kama da Aliyu ba amma kana ganinsu kasan yan uwan juna ne, su siyama suka yi kansa cike da murnar ganinsa, siyama ta rungumesa tace "Wllh nayi kewarka ya salim, wai don Allah yaushe Yaya Aliyu xai tafi duk ya takura mu gidan nan, the house is just boring with him, idan Abba xai koma ya tafi da shi ya bar mana kai plss, Allah ya Aliyu is a problem in this house ko irin d'an birthday din frnds da party ya hana mu xuwa daga boko sai islamiyya" kamar xata yi kuka ta kare maganar, shi dai saleem sai uhn, uhm yake ta cewa yana sunkuyar da kai, sum sum Aneesah ta wuce sama, hakan yasa siyama ta bi parlon da kallo ta ga ya Aliyun xaune dinning yana kallonta, dauke kai tayi da sauri ta toshe baki tana xaro ido tace "Na shiga uku" Saleem ya dinga dariya kasa kasa har da kyakyatawa ba tare da ya kalli direction din Aliyu ba, Khadijah dake tsaye ita ma ta rufe fuskarta da Hijab ta wuce dakin kyauta tana murmushi, bin ta da wani kallo saleem yyi da wani expression yace "Who's this?" Siyama ta yamutse fuska tace "The new housemaid after kyauta...." ya buda ido yace "What" tabe baki tayi ta mike tana satan kallon Aliyu tace "Sannu da gida yayanmu" kallon fork din gabansa yyi ya dauka tana ganin haka da gudu ta wuce sama tana turo baki, Saleem yyi murmushi ya mike ya isa dinning din yace "Big bro duk ka takura masu koh" Aliyu bai tanka sa ba ya dau Apple din gabansa ya fara ci. Bayan isha duk yan gidan suka hallara a dinning kasancewar in dai Daddy na garin duk a tare suke yin dinner a dinning area, Last cooler din kenan na soyayyen kaji kyauta ta dauka xata kai masu dinning din kasancewar ta mance Daddy ya hango Khadijah da ita ma ta fito daga kitchen xata shiga dakin kyauta rike da plate din abincinta, yana kallon Mumy yace "Kun yi baki ne?" Mumy ta kalli direction din Khadijah kafin ta shiga dakin ta kira ta, Juyowa Khadijah ta yi ta dawo, Sau daya Aliyu ya kalleta ya ci gaba da cin abincinsa kansa a sunkuye, Mumy tace "Yarinya ce aka kawo min riko daddy, kayi hakuri ban sanar maka ba yau satinta kusan uku, dama ina jiran sai ka dawo ne" yace "Riko kuma, daga ina" mumy ta yi yar dariya tace "Marainiyar Allah ce nan da ka gani" Saleem ya juya yana kallo Khadijah dake tahowa, Siyama ta tabe baki tare da tura abincin gabanta, Khadijah na isa wajen tana kallon Daddy a hankali tace "Good evening sir" da fara'arsa yace "Evening how are you" Khadijah tace "Alhmdllh, hw was the trip?" Ya kalli Mumy yana murmushi yace "It's great" Shiru Khadijah tayi daddy ya nuna mata kujeran dake kusa da Saleem yace "Have ur sit ke ma" Ta gefen ido Saleem ke kallonta, Khadijah ta buda ido tace "Noo uncle I will love eating alone" daddy yyi murmushi yace "Alright then, do what pleases you" a hankali tace "Thank you" daga haka ta juya ta wuce, Daddy ya dau cokalinsa yace "She is sharp, haka nake son baby ta xama but baby is too meek" baby ta turo baki, Mumy tayi dariya tana kallon Baby da ta bata rai, kyauta ta bar wajen tana washe hakora a ranta tace "Har da mai gidan ma turanci take tsabar iya turancinta" sai da Daddy ya bar dinning area din sannan Saleem yyi facing Mumy yace "Wai mumy wacece yarinyar?" Aliyu ya ajiye cup din hannunsa yace "Did you have any business with her" Siyama ta hararesa ta gefen ido tace "Ya saleem na gaya maka house maid ce ko baka yarda bane, xan ma karya ne?" Mumy ta kalleta tace "She is a house maid or other wise thats nt ur problem, kuma kada ki sake kiranta da haka, yar rainin wayo kawai" jefar da cokalin hannunta tayi ta bar dinning din da sauri Aliyu ya bi ta da wani irin kallo, mikewa saleem yyi yace "Akan wata banxa can xaki bata mata rai mumy, for what...." Daga haka ya bar dining din shi ma, Aneesah ma ta tabe baki ta mike ta bi bayansu, Mumy ta bi su da kallo kafin tace "Allah ya kyauta" shi dai Aliyu bai ce komai ba, can mumy ma ta mike ta bar dining din, Baby ta bi abincin da suka bari ta kwashe naman kai ta sa a nata, Aliyu dake ta bin ta da kallo yyi murmushi yace "Glutton of the house" washe baki tayi tace "I don't want it to waste yayanmu" yace "Then go and share it with Iman" mikewa tayi rike da plate din ta wuce dakin kyauta, ba a dau lkci ba ta fito ta ajiye plate din kan dinning tace "Na bata yayanmu, xan je wajen mumyna" daga haka ta wuce sama, yana ta xaune dinning din Khadijah ta fito rike da plate xata kai kitchen, tsayawa tayi ganinsa sai kuma ta nufesa tana murmushi ta buda dara daran idonta tace "Yayanmu thanks for the school bag I love it" kallonta yake yace "Wa yace maki sunana yayanmu" tayi dariya tace "Na ji baby tana kiranka haka, Anty kuma tana ce maka Aliyu, su Anty siyama kuma yaya Aliyu" bai ce komai ba ta juya xata wuce sai kuma ta dawo tace "But did you buy the bag with d name iman or you where d one dat place it there?" Yace "I don't knw" wara ido tayi tace "Okay" sannan ta wuce kitchen, ganin kyauta ta fito gyaran dinning din ya mike ya wuce sama. Kafin Khadijah tayi bacci baby ta shigo mata da tsaraban da Daddy ya kawo tun daga kan chocolates, teddy bears, novels, takalma, rigan sanyi da ribbons na gashi sai kaya kala daya, kai kana ganin tsabar kasan na baby ne Mumy ta raba ta bata ta kai ma Khadijah, kyauta ma baby ta kawo mata nata tsaraban tana ta godiya baki har kunne. Kyauta na kitchen bayan su Khadijah duk sun wuce makaranta taji muryar saleem yana cewa "The great Aunt, ko minti goma ban yi da cewa xan kira ki inji yaushe xaki dawo, don duk gidan ba dadi ashe dai kina hanya" Anty Khadijah dake shigo da jakunkuna tace "Wllh kuwa, don ma d'an iska tsinannen mai mota muka samu, shi yasa na so Anty fati ta bani motar ta da xan tafi ta ki, banda haka wani banxan ne ya isa ya bata min rai a titi" Saleem dake taimaka mata shigo da kayan yace "Ae sai a hankali bin motar haya Anty da baki fara ba" Kyauta ta kwalalo ido ta jingina da kofa tace "Asshaa... Baxawara an dawo" Muryar Anty Khadijah taji tana cewa "Toh baxa ki shigo bane iklima ko kin kasa cire takalmin ne" kyauta ta leka a hankali suka yi ido hudu da Anty Khadijah, fitowa kitchen din tayi baki har kunne tace "Lale marhaba, Hajiya ashe ku ne, sannun ku da isowa" babu yabo babu fallasa Anty Khadijah tace "Ki hado ma iklima breakfast bata karya ba muka taho" sai a sannan yarinyar ta shigo parlorn, baxa ta wuce su baby ba a shekaru amma kana ganinta kasan cikin wahala take, ga tabo duk jikinta, kyauta ta karasa kusa da ita da gudu ta rungumeta tace "Yau ga iklima na gani ashe kece, yar kyakkyawa maa sha Allah, sannu da xuwa iklimatu" Anty Khadijah tace "Dalla ki cikata ki tafi ki nema mata abun k'ari, dangi uwa ko na uba" da sauri kyauta ta juya ta nufi kitchen, iklima ta bi ta da harara tace "Ashe ma house maid ce, kawai xata shafa min datti a jiki" Saleem yace "Iyye kaji Iklima manya, wato datti xata shafa maki koh, to ina su Yusuf?" Ta turo baki tace "Ai basu san mun taho ba" Anty Khadijah da ta yi hanyar stairs da jaka tace "Kafin ta gama maki breakfast din taho in sa maki ruwan xafi kiyi wanka, Saleem ku kuma saukan yaushe" Saleem yace "Jiya muka dawo Anty" tace "Daddy na part dinsu kenan" Saleem yace "Ina ji" bin bayanta yyi da sauran kayan, sai da suka isa dakinta tace "Aliyu fa?" Ya ajiye jakar hannunsa yace "Ya fita aiki." Mumy ce ta fito jin muryar yar uwarta ta shiga dakin ita ma.
Har bakin daki kyauta ta kawo ma su Anty Khadijah breakfast din, Mumy ta taso ta karba ta dawo ta ajiye ta xauna tana sauraren 'yar uwar ta, Anty Khadijah tace "Toh fa kin ji Anty fati, kuma in sha Allahu da daddaya xan dauke yarana gaba daya a gidan, a kan wani dalili ina raye, dubi yanda iklima ta koma, mata muguwa axxaluma kawai duk ta gama da ubansu, tana neman kashe min 'ya ya ni wllh da ba dan bana ra'ayin Salisu ba da bbu abinda xai hana ni fitar da matar nan in koma gidan" Mumy dake ta kallonta tace "Ta ya?" Anty Khadijah tayi kwafa tace "Lallai kina wasa da ni Anty" Mumy bata sake cewa komai ba sai bin iklima take da ta fito wanka da kallo, Anty Khadijah ta sauka ta shiga hada mata shayi tace "Yi maxa ki shafa mai ki taho kiyi breakfast Pretty" Mumy tace "Toh Allah ya kyauta, Allah kuma ya shiryi masu irin halin ta, Allah ya raya mu tare da yaranmu" Anty Khadijah tace "Ameen fa" Mumy tace "shi yasa na ke nuna maki masu aikin nan ki rabu da su lafiya, tsakaninki da su gaisuwar mutunci wani hantara da nuna isa duk ba shi bane" dakatar da ita Anty Khadijah tayi da hannu ta daure fuska tace "A'a kar ki fara Anty kar ki bata min, dangin uwa ko na uba da xan dinga gaisuwar mutunci da su su rainani, ni ba gashi yarana basu ji ba basu gani ba ana walakantasu suna wahala, don haka ki kyaleni nayi ma kowa ma haka" Mumy ta tabe baki tace "Ka ji xancen banxan, to ai wannan a rubuce yake duk abinda kayi ma 'ya yan wasu sai an ma naka abinda nake ta nuna maki kenan kin ki gane wa" rai bace Anty Khadijah ta mike tana kallon Mumy tace "Ni dama tun da dadewa nasan ba so nake kike ba kawai kina xaune ne da ni dole don 6are ma