Showing 162001 words to 165000 words out of 234058 words
dakin da gawar sudais yake, ya karaso inda Aliyu yake fuska daure yana masa wani kallo yace "Gidan mahaifiyar sa xa a kai gawar yanxu...." kallonsa kawai Aliyu ke yi, Sudais yace "You will be the one to go break the news to her" Aliyu ya d'an bude ido yace "Why me?" Sudais bai sake saurarensa ba ya koma ya dauko gawar ya fita xuwa gun motarsa Aliyu ya bi sa da wani irin kallo. Kusan a tare duk su ukun suka isa gidan, khaleel ya fara fitowa sannan ya sakko da Shureim yana kallon Sudais da ya fito shi ma amma gawar na motarsa, dauke kai khaleel yyi ya shiga ciki yana rike da shureim, Aliyu ya fito daga tasa motar da Doctors biyu suka bi bayan Khaleel, Sudais ya kasa shiga ciki ya jingina da motarsa yana tunanin yanda Khadijah xata dau xan cen rasuwar d'an ta, lumshe ido yyi wasu hawayen na sakko masa, Nanny ce ta bude masu kofa khaleel yasa ta shimfida tabarma a nan balcony, duk gabansa faduwa yake damuwar sa daya khadijah, xuwa yanxu dai umma ta daina kuka bayan ta ce ma khadijah rasuwa aka mata, Khadijah sai kallonta take a sanyaye bayan ta gama kukan ita ma don bata san waye ya rasu ba kuma umma bata gaya mata ba, Umma ta sa Hijab ta fito a sanyaye ba tare da tace ma khadijah komai ba, khaleel ya dinga kallon umma da wasu hawayen ke xubo mata ganin su, Aliyu ya kasa kallonta a sanyaye yace "Allah ya yi masa rahama, ya sa mai ceto ne" Khadijah ta fito daga daki da sauri jin muryar Aliyu, kallonsu ta dinga yi daga inda take tsaye can ta karaso da sauri tana kallon khaleel gabanta na faduwa tace "Dr ina sudais din?" Khaleel ya kasa kallonta kuma ya rasa abinda xai ce, dai dai nan Barrister sudais ya shigo parlorn shi ma bayan ya ajiye gawar sudais kan tabarmar da ya gani balcony baya son ya shiga ciki da shi tukun, suna hada ido da khadijah yyi saurin sunkuyar da kansa, A hankali khadijah ta juya tana kallon umma dake share sabbin hawayen dake xubo mata, ta juya ya kalli Nanny da ta jingina da bango tana hawayen ita ma, a rikice ta nufi Aliyu ta durkusa gabansa cikin rudewa tace "Aliyu ka gaya min wani abu ya sami sudais dina ne, don girman Allah ka gaya min" kasa ce mata komai yayi ya kasa kallonta, lkci daya hawaye ya cika idonsa, mikewa khaleel yyi ya nufi kofa xai fita cos he can't stand it any more, ta mike kamar mahaukaciya ta bi bayansa da sauri, tsaye khaleel yyi balcony ganin gawar yaron a wajen don bai san Barrister ya shigo da shi ba, ya juya a hankali yana kallon khadijah dake kallon gawar kan tabarma an rufe, lkci daya jikinta ya dau rawa ta kamo hannun khaleel cikin rawar murya tace "Dr meye wannan, what is it...." Jawota khaleel yayi jikinsa ya rungume ta gam, cikin sanyin murya hawaye na taruwa idonsa yace "Don't forget Khadijah, Allahn da ya baki shi ya fi ki son sa.... Ba wayon ki ba ba dubarar ki ba ya sa ya baki, to yanxu ya amshe kayan sa, sudais addu'arki kawai yake bukata gare sa yanxu, pray to meet with ur son once again in
Jannah...." Jin Khadijah tayi shiru ya dago kanta a hankali yana kallonta, a hankali yaji tana neman sulalewa hannunsa yaki saketa, a haka ta suma yana rike da ita. A hankali khadijah ta bude idanuwanta bayan lokaci me tsawo, kwance take kan gado ta dinga bin mutanen dake xaune dakin da kallo, Wata kawar Umma ta taso ta dawo kusa da ita ganin tashi take son yi ta taimaka mata ta xauna, da kyar tace "Anty me ya ke faruwa?" Umma tayi karfin halin xuwa kusa da ita ta xauna tace "Ya jikin khadijah" shiru khadijah tayi tana ta kallon umma, lkci daya ta fasa ihu ta mike ta fice daga dakin da gudu suka bi ta, Aliyu ne ya fara mikewa a compound din ganin ta fito, ga maxa ko ina, Khaleel dake rungume da Shureim dake bacci jikinsa ya dinga kallonta amma ya kasa tashi, haka barrister sudais, tana ganin Aliyu ta taho gun sa ta rike hannunsa cikin matsanancin kuka sosai tace "Aliyu don Allah kar ka ce min sudais ya mutu, you assured me he will be fyn, kar ka ce min ya mutu don girman Allah" kasa cewa komai Aliyu yyi yana kallonta, ta rungume sa tana kuka kamar ranta xai fita tace "Ka ce min bai mutu ba Aliyu, wllh ina son sa, kar ya tafi ya bar ni" Aliyu ya ja ta suka bar wajen xuwa inda babu mutane ya xaunar xa ita ya durkusa yana kallonta, a hankali yace "Iman kin san Allah xai baki shi?" Ta girgixa masa kai hawaye na xuba idonta tace "A'a"
*Sorry if I disappoint anybody*
Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Toh kar ki masa butulci Iman, baki san xai baki shi ba ya baki, prayer is all what ur little boy wants from you, kiyi masa addu'a ba kuka ba Iman, if you continue like this what will be the fate of his twin, kin ga shi ma xai shiga damuwa sosai na rashin halve dinsa and this might affect him badly.... Or did you want anything bad to happen to him also, For his sake plss ki kwantar da hankalin ki so you won't loose him too, am telling you damuwar da shi xai shiga sai ma ya fi naki" khadijah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Na shiga uku don girman Allah kar ya bar ni shi ma" yace "Then ki kwantar da hankalin ki and accept this fate" hawaye na xuba idonta tace "Toh" yace "Promise me baxa ki sake kuka ba Iman" k'in cewa komai tayi, ya kira sunanta a hankali ta daga kai tana kallonsa, sosai gabanta ya fadi, ta kuma rushewa da kuka tace "Yanxu Sudais ya tafi ya bar ni.... Shi fa yace min in je in kira masa Shureim he wants to tell him he is sorry, dama mutuwa xai yi baya son ya mutu a kusa da ni" Ta hade kai da gwiwa tana kuka kamar ranta xai fita maganar Sudais na karshe na dawo mata "Anty ki ce Shureim ya xo, I want to tell him am sorry" kuka ta ke kamar ana dada tunxurata, Aliyu ya kasa ce mata komai duk jikinsa yyi sanyi, Ta rikosa tana girgixa kai cikin tashin hankali tace "Yanxu shkkn baxan sake ganin sa ba, me yasa ya tafi ya bar ni da Shureim" Aliyu ya kasa cewa komai wani mugun tausayinta na shigarsa, cikin sanyayyen muryarsa yace "Pls ki daina kukan nan Iman, da duk biyun Allah ya raba ki da ya xa ki yi kenan, you neva knew why he took him so soon, be a good Muslimat plss" shiru khadijah tayi jin yace Dukka biyun, ta goge idonta gabanta na mugun faduwa cos she can't just imagine that, Murya can kasa yace "You make the promise now, that baxa ki sake masa kuka ba sai dai addu'a...." Ta gyada kai da kyar trying not to cry tace "I promise" yace "Add in sha Allah to the promise" a hankali tace "In sha Allah" Ya d'an yi murmushi yace "Good" mikewa yyi ya dago ta ta mike ita ma tana goge idonta yace "Ki wuce ciki and remember the promise you make" tace "Toh" daga haka ta fara tafiya ya bi ta da kallo, da sauri ta juyo sai kuma ta dawo tace "Ina shureim plss" da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace "Yana nan tare da mu" ta hadiye abu da kyar tace "Ka dauko min shi plss" yace "They are people everywhere, later xa a kai maki shi" shiru tayi sai kuma ta juya a sanyaye ta fara tafiya, Juyowa tayi ta kara dawowa idonta har ya fara kawo kwalla tace "Toh me yake yi?" Yace "Kukan xa ki fara kuma" da sauri ta girgixa kai tana goge idonta, yace "He is just sitting down" bata ce komai ba ta fara tafiya kamar iska xai kadeta ta fadi har ta bar wajen, Aliyu ya koma a sanyaye ya xauna ya jinginar da kansa jikin bango yana jin mutuwar yaron har cikin ransa, Tun da khadijah ta dawo compound din khaleel ke bin ta da kallo har ta shiga parlor, sai a sannan barrister Sudais ma ya dauke idanuwansa daga kallonta, Bedroom ta wuce duk mutanen parlon suka bi ta da kallo cike da tausayinta, Umma na xaune har lkcn duk jikinta yyi la"asar, da ido ta bi khadijah har ta dauko Hijab dinta ta sa ta xauna kan darduman dake shimfide ta jingina da bango, hawaye ya cika Idon Umma don bata yi xaton hakan ba, tashin hankalinta ta Inda xata fara lallashin Khadijah sai ga shi taga ta ma daina kukan, Wata frnd din umma ta dawo kusa da ita a sanyaye tace "Kiyi hakuri kinji Khadijah, Allah yayi masa rahama..." A hankali khadijah tace "Ameen" Umma taji hankalinta ya kwanta sosai, tashi tayi ta fita da kanta taje kitchen ta hado mata shayi ta dawo, kasa sha Khadijah tayi har lkcn ta kasa yarda Her lovely Sudais is gone forever, tana son kuka amma sai ta tuna promise din da tayi, hakan yasa xuciyarta ya dinga mata xafi sosai, kowa ya ganta sai yaji tausayinta, Umma har lkcn mamakin karfin halin nata ta dinga yi, a haka har aka yi la'asar, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh umma ta xubo mata abinci ta xauna kusa da ita cike da lallami tace "Don Allah ko kadan ne ki ci Khadijah, tun jiya fa baki ci komai ba" Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, can ta dago da kyar tana kallon Umma tace "Umma yanxu shikenan Sudais ya tafi" Rungume ta umma tayi tana kokarin ganin bata xubda hawayen dake baraxanar xubo mata ba, cikin sanyin murya tace "Pray for him daughter, Allah yasa can ya fi masa nan, Allah ya sa mai ceton mu ne" cikin rawar murya Khadijah tace "Ameen" umma tace "Toh ki ci abincin kadan don Allah" ta girgixa kai tace "Umma baxan iya ci ba" Umma tace "Ko cokali biyu ne ki yi" Nanny ce ta shigo dakin da kumburarrun idonta ta duka kusa da su tace "Umma akwai baki parlor sun xo mata gaisuwa ta daure ta fito" Umma tace "Kice su shigo nan" mikewa Nanny tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tare da su Mumy, Baby da su seeyama da wata daban, Mikewa Umma ta yi ganin su ta shimfida masu babban darduma tana masu sannu da xuwa, Khadijah ta dinga kallon Mumy har ta xauna, A hankali tace "Sannu da xuwa Mumy" mumy da kana ganin idanuwanta kasan ta yi kuka sosai tace "Sannu Khadijah, ya hakuri" Khadijah ta kasa amsawa ta dakar da kanta, Su siyama ma suka mata gaisuwar a sanyaye, sai a sannan khadijah ta kara dago kanta tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta suka xubo ba, Kallon warce ke xaune kusa da baby ta dinga yi, ita ma yarinyar kallonta take da mamaki, Khadijah tayi karfin halin cewa "Maryam sannu da xuwa" Maryam tace "Ashe yaron ki ne ya rasu Khadijah, Allah ya ji kansa" Khadijah tayi karfin halin cewa "Ameen" sai dai xuciyarta cike yake da mamaki, Maryam dama yar uwar su Aliyu ce kenan, makarantar su daya a UK amma Hi kadai ne mutuncin da ke tsakaninsu kawai ta rasa me yasa bata son yarinyar, kawarsu Vanessa ce dai. Mumy sun kusa minti sha biyar a dakin, duk tausayin khadijah ya cika don tasan rashin yaro da ciwo sosai ga uwarsa barin yaro mai shiga rai irin sudais, bata ma samu courage din tambayar ina Shureim ba, Karfe biyar da yan mintuna tace ma umma xa su tafi, Umma tace "Toh mun gode kwarai Hajiya, Allah ya bar xumunci" Mumy tace "Ameen, kuyi hakuri bamu xo tun safe ba kanwata ce ba lafiya tana asibiti sun yi hatsari tun shekaranjiya" Umma tace "Subhanallah, toh Allah ya bata lafiya, ya yaye mata" Mumy tace "Ameen mun gode" hakuri ta kara ba khadijah Umma ta rakasu suka fita parlor, Sai a sannan Mumy tace "Kanin Aliyun yana waje ya xo mata gaisuwa amma ko xuwa anjima sai ya dawo" Umma tace "A'a bari ta fito" mumy tayi convincing dinta kan ta bari sai anjima ya dawo daga haka suka wuce Umma ta koma ciki. A hankali khadijah ta tako har cikin parlor tana sanye da Hijab dinta har kasa ta xauna kujera a sanyaye tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yyi, ta sunkuyar da kai a raunane tunawa da lkcn da suka dinga dragging sunan da ta xabar ma sudais dinta da shi, A hankali yace "Amira..." Ta daga kai tana kallonsa lkci daya idanuwanta suka kada, cikin sanyi yace "Keep on praying for him, Allah ya sa mai ceton mu ne, life moves on plss, ai da baki san Allah xai baki shi ba, so kiyi hakuri ki cire sa ranki, tsakanin ki da shi yanxu addu'a, baxai ji dadi kiyi ta masa kuka ba" Tana gyada masa kai da kyar tace "Ai na daina, Allah ya ji kansa, ya hada ni da shi a aljanna" Barrister sudais yace "Ameen, Allah ya kara maki hakuri" Murya can kasa tace "Ameen" yace "Toh yi ma Umma magana xan mata gaisuwa" Ta mike tace "Toh" daga haka ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Umma ta fito, da ta amshi gaisuwar sudais tana sa masa albarka, Bai dade parlorn ba yace mata xai koma gida, tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita parlorn, ita dai har ranta taji Sudais ya kwanta mata, ta kuma san har abada baxa ta mance hallacin da yayi mata ba, don ko ita yayi ma, bata kuma san da me xata saka masa ba. Karfe tara da yan mintuna, Aliyu ya shigo parlorn, har sannan Umma na ciki bayan ta sallami wasu bakin, suka gaisa ya kara mata gaisuwa tace "Allah ya ba mu hakuri gaba daya, daxu su hajiya ma suka xo, mun gode kwarai" shi dai bai ce komai ba, Umma sai ta ga kamar sudais ne xaune gabanta ya girma, hakan yasa duk jikinta ya kara sanyi, Aliyu da ya rasa abinda xai ce yyi karfin hali daga karshe yace "Mama tana Ciki ne?" Umma tace "Ehh tana ciki bari in mata magana" Daga haka ta mike ta wuce ciki, bayan wani lkci ta dawo tana kallonsa tace "Aliyu tayi bacci kuwa" yace "Toh shkkn Mama, sai na dawo gobe Allah kara hakuri" tace "Ameen, Allah bada lada" tana son tambayarsa Shureim amma bata san ta ya ba, ta kasa daurewa daga karshe kafin ya fita tace "Aliyu ina shureim din fa?" Juyowa yyi yace "An tafi da shi mama" tace "Can gidan ku?" Ya girgixa mata kai, Umma tace "Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya" daga haka ya fita, umma ta san khaleel ne ya tafi da shi can gidan nasu. Ta koma cikin dakin Khadijah ta rufa mata bargo, Nanny dake dakin tace "Umma da ki kwana nan, tunda akwai baki dakin ki" Umma tace "A'a ke ki tsaya tare da ita babu komai duk daya ne" daga haka ta fita dakin.
Karfe goma na safiyar washegari Khadijah na kwance daki ta rufe ido kamar mai bacci don gaisuwar da ake mata na shureim na kara daga mata hankali, hakan yasa duk wanda ma ya xo umma da Nanny yake ma gaisuwar, Umma ce ta shigo dakin ta taba ta duk da tasan ba bacci take ba, Khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana kallon umman nata, cikin kwantar da murya umma tace "Taso mu je an xo maki gaisuwa" ta d'an hade rai tace "Umma ba ga ku ba bacci fa nake" Umma tace "Mahaifiyar khaleel ce shi yasa ma na tashe ki" shiru khadijah tayi tana kallon umma, can Khadijah ta mike xaune a hankali, umma ta kama hannunta ta tashi daga kan gadon, hijab ne har kasa jikinta, hakan yasa ta bi bayan umma dake rike da hannunta suka fita parlor, balarabiyar matar na xaune parlor da jikokinta su uku sai shureim dake jikinta shi ma, Suna hada ido Khadijah ta sauke kanta a sanyaye ta karasa cikin parlorn ta xauna, da gudu shureim ya taho ya rungume ta yana kallonta yace "Anty are you sick?" Kallonsa Kawai khadijah take taji kamar ta fashe da kuka, Ummu dake ta kallonta da tausayi tace "Sannu Khadijah, ya karin hakuri?" kasa cewa komai tayi da farko, can dai tayi karfin halin bude baki da kyar tace "Alhmdlh Mumy, nagode" Ummu tace "Allah yayi masa rahama, ke kuma Allah baki dangana, ya sa mai ceto ne" Umma tace "Ameen thumma Ameen" don khadijah kasa amsawa tayi, Shureim na kallonta da damuwa yace "Anty uncle yace min sudais travelled, why will he travel alone, why didn't we go together plss, and now I am missing him, plss I want to go to him, I promise I will never fight him again...." umma ta jawosa jikinta tana kokarin boye hawayen idonta tace "He will be back soon sweetheart, and I am sure he is missing you too" Shureim yace "Toh Umma I want to talk to him on phone, am missing him" Ummu dake ta kallon shureim tace "Shureim har ka gaji da wasa dasu fadeel, ain't they ur frnds anymore" ya juya ya kalleta yace "Noo Ummu I like them, but sudais is my brother, they will like him also" Ummu tace "Toh taho mu wuce tunda ka gaida Anty" kallon khadijah da kanta ke kasa shureim yyi ya dawo kusa da ita a hankali yace "Anty, is sudais coming back soon? I want the both of us to be frnds with fadeel and Adeel" Ummu ta mike