Showing 186001 words to 189000 words out of 234058 words

Chapter 63 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17047

Deejah ke fadi? Tabe baki tayi ta wuce bedroom dinta, wanka tayi ta sauya kaya tayi sllhn azahar sannan ta linke Hijab dinta ta yafa mayafi ta fito, a hankali ta danna bell din apartment din khaleel, bayan wani lkci wata ta bude kofar, Khadijah tace "Ina yini" yarinyar dake ta kallonta ta bata hanya tace "Lafiya lau" shigowa parlorn Khadijah tayi gabanta na faduwa, few mutane ne parlorn kuma yawanci duk manya ne, ta durkusa jikin kujera a hankali tace "Ina yinin ku" amsa mata suka yi da fara'a, wata a cikinsu tace "Ikon Allah, ji mai kama da su Maimoon" Yarinyar da ta bude kofar tace "Wllh Anty na xata Safeenah ce ta da farko, haka na tsaya da mamaki Ina kallonta don nasan Safeenah na daki ai" Ita dai Khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Wata mata dake kusa da ita tace "Dama haka Allah ke ikon sa ai, tashi ki shiga ciki yan mata suna can gaba daya" warce ta bude mata kofar ne ta kai ta har dakin da jawahir da yan uwanta suke, Khadijah dai gabanta sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, da sallama ta shiga dakin bayan yarinyar ta bude mata kofa, suka hada ido da Jawahir dake xaune gefen gado tana danna wayarta, sosai tayi kyau sai wani glowing chocolate skin din ta yake, hannayenta sun sha lalle, kai kana ganinta ka ga amarya, Khadijah ta sunkuyar da kanta, Maryam ce ta fara mikewa ganinta tace "Lah Khadijah ashe kin dawo" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Ehh ban dade da dawowa ba" Maryam tace "Ayya, Sannu da dawowa, ga waje ki xauna" Bata kai ga xama ba Deejah ta fito daga bayi tana ganinta ta rungume ta da murna tace "Khadijah har na gaji da jiran ganin yaushe xa ki dawo, gashi babu mai number ki, Sannu da xuwa" Khadijah tace "Ayya ni ban san jiya xa ku taho ba ina gidan frnd dita ce" A hankali Khadijah ta xauna Deejah ta xauna kusa da ita tana kallonta da fara'a tace "Mun taho rakiyar amarya" Khadijah ta kalli jawahir a hankali tace "Sannu Amarya, Allah ya bada xaman lafiya" sai a sannan jawahir ta kara kallonta babu yabo babu fallasa tace "Ameen" Deejah sai kallon jawahir take alamar bata ji dadin yanda ta amsa mata ba, ita kanta Maryam dauke kanta kawai tayi, Safeenah ta shigo dakin tace "Lahh ashe har kin shigo" Khadijah tayi murmushi tace "Eh na shigo" ta karaso ta xauna ita ma tace "Su Anty Deejah na ta labarin ki a Nigeria sai gashi yau na gan ki, kin lura da kamar da muke yi kuwa?" Dariya ta ba Khadijah, Maryam da Deejah ma suka yi dariya ban da Jawahir da ta tsuke fuska, A hankali Khadijah tace "Ikon Allah kenan" Safeenah tace "Gaskiya ne, Ammin mu na gaishe ki" Khadijah tayi murmushi tace "Na amsa sosai" hira suka dinga yi dakin banda Khadijah da sai dai tayi murmushi idan sun kallota, duk a takure take ta kagu ta tashi ta wuce amma ta kasa tashi, agogo ta kalla ganin uku ya wuce tayi karfin halin mikewa tace "Xan dan shiga ciki ina aiki ne" Safeenah tace "Amma xa ki dawo ai?" Murmushi Khadijah tayi tace "Ehh xan dawo anjima" Rakota suka yi parlor, Khadijah tayi ma wa enda ke xaune parlor sallama ta bude kofa xata fita suka kusa cin karo da khaleel, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yanda ta daburce shi ma haka, yyi saurin bata hanya, ganin Deejah da Safeenah na bayanta tayi karfin halin ce masa "Ina yini" yace "Lafiya lau, ya gida" fita tayi daga parlorn bata ce komai ba ta bude apartment dinta ta shiga ta rufe, ganin la'asar yayi ta daura alwala a bayi tayi sallah sannan ta kwanta, bude data tayi da sauri tunawa da tayi daxu Barrister yace xai turo mata sako ta duba, ko ya bar Dubai din ma oho, ai ko tana budewa taga messages da ya turo mata da yawa, ta shiga tana kallon message din, kusan gaba daya hotuna ne, downloading din su ta fara yi, murmushi tayi ganin set na akwatuna ne yace ta xabi wanda take so, a hankali ta dinga scrolling tana duba boxes din, bbu na banxa gaba dayansu, murmushi tayi masa as reply, sannan ta tura masa message tace duk sun yi kyau sosai, daga haka ta kashe datan ta, bayan kusan minti goma sai ga kiransa, kuri ta kura ma wayar ido, can ta daga a hankali ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren yace "Amira" tace "Na'am good day" yace "Thanks, I saw ur reply, kuma ni ba tambayar ki nayi ko sun yi kyau ba" Yar dariya tayi tace "Barrister amma ai kai ma kasan sun yi kyau" yace "My question is wanne kika fi so" tayi murmushi tace "Uhm ni ban san wanne xan ce ba barrister" yace "Ask ur frnds then" tace "Toh xan tambaya" yace "Ina fa jiran ki kafin gobe, don goben xan bar Dubai" a hankali tace "Toh barrister" daga haka yayi mata sallama ya katse wayar ta koma ta kwanta a sanyaye, juye juye ta dinga yi tana kokarin bata ba damuwar dake neman dirar mata a xuciya space ba, can ta mike jin ta fara jin yunwa, kitchen ta tafi ta daura ruwan xafi don tafasa na shayi, kamar ance ta leka window taga khaleel xaune waje doing nothing, hada ido suka yi tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take, tasowa yayi a hankali ya iso kusa da windown ya tsaya yana kallonta, trying her best not to look toward his direction tace "Wishing a happy married life, Allah bada xaman lafiya" kallonta kawai yake, can a hankali yace "Khadijah" kashe gas dinta tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta nufi kofar fita kitchen din ya bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar. Shayin da bata sha ba kenan tana ta xaune parlor wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tayi shiru, "Ki fito muna waje" abinda Aliyu yace mata kenan, ta mike a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta ta sa ta fita, Tana isa kusa da motar ta bude ganin bashi da alamar fitowa ta fiddo Shureim tana kallonsa, xata wuce yace "Jira ki karbi sakon Mumy" Bata ce komai ba ta tsaya ya fito ya bude bayan mota ya ciro wani leda ya bata, amsa tayi tace "Mun gode Allah saka da alkhairi" Har ta juya xata tafi sai kuma ta tsaya tana kallonsa ta basa wayarta tace "Ka sa min number ta sai in kirata in mata godiya" karbar wayar yayi ya sa mata digit din Mumy ya mika mata, ta amsa tace "Thanks" yace "Don't forget ki tambayeta jikin Anty Khadijah idan Kin kirata" tace "Har yanxu bata samu sauki ba?" Yace "She is still at the hospital" Shiru Khadijah tayi, lkci daya jikinta yayi sanyi, can tace "Toh Allah ya bata lafiya" Yace "Ameen" Cike da karfin hali tace "Ya jikin iklima fa?" Ya shafa kansa yace "Tana can family din babanta, ban samu xuwa dubata ba coz I spent only three days kuma throughout Zaria nake ta tafiya gun Anty Khadijah" Khadijah tace "Toh Allah ya sauwake, idan muka yi hutu soon xan je gida sae in je in duba Anty Khadijah da Umma" Yace "Alryt" shiru ta kara yi, sai kuma ta kallesa tace "Ina son tambayar ka pls" yana kallonta ya rungume hannunsa yace "Ina jin ki"

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

Khadijah tace "Ya dangartakar ku da su Deejah?" Ya d'an yi shiru yana tunani kafin yace "Wacece Deejah kuma?" Ta kallesa tace "Deejah ce baka sani ba?" Buda ido yyi yace "Ohh wai warce kika tarar gida ranan da na kai ki kike nufi, kawar Maryam" Khadijah tace "Ehh" yace "I think, noo they are just family frnds kawai, Dad din Maryam da dad dinsu are just good frnds, childhood frnds if I am not mistaken, that's just it" Khadijah tace "Toh Maryam fa?" Ya shafa kansa yace "Her mum kanwar Abbana ce, dad dinta kuma was once under my dad, so Maryam is my cousin" Khadijah tace "Ohk" yana kallonta yace "But why did you ask?" Wani kallo tayi masa tace "Is there anything wrong with me asking?" Murmushi yayi yace "Not at all, yaushe xa ku fara exams?" Tace "Nan da 3wks" yace "Ohk Allah ya kai mu" tace "Ameen" daga haka ta kama hannun Shureim dake tsinkar flowers ta nufi cikin gida, Aliyu ya bi su da kallo Shureim na daga masa hannu har suka shiga cikin gidan. Da daddare Khadijah na bedroom tana karatu bayan Shureim yayi bacci taji an danna bell, sosai gabanta ya fadi ta kalli agogo, a lokacin ma takwas yayi, ta mike a hankali ta isa gun kofar ta tsaya tace "Waye?" Jin muryar mace ta bude kofar, Safeenah ce tsaye bakin kofar tace "Khadijah I want to spend the nigh here if it's ok by you" Khadijah tace "Oh you are welcm" daga haka ta bata hanya ta shigo parlorn tana cewa "Su Anty Deejah na takura ni shi sa na yo nan, da dare bai yi ba gidansu Maryam dama xan tafi" Khadijah tayi murmushi tace "To mu shiga ciki" bin bayanta Safeenah tayi har suka isa bedroom dinta, Safeenah na kallon Shureim dake bacci tace Woaw brothern ki ne wannan" Murmushi Khadijah tayi bata ce komai ba, can kuma tace "Ki hau saman gadon" Safeenah ta hau kan gadon xuwa daya side din tace "Hope baxan takura ku ba" Khadijah ta xauna gefen gadon tace "Haba dai ba wani takura" Safeenah tace "Kin san har na fara ba Abban mu labarin ki" Khadijah tayi dariya tace "Haba dai" Safeenah tace "Ehh mana, Ko mijin Jawahir Dr Ayman ya din ga kallona jiya da muka xo, da yake bai san ni ba dama tunda ba gida daya muke da jawahir ba, she is my cousin, My father and her mother are having same parent" Khadijah tace "Ayya that's nyc" Safeenah tace "Ke karatu kawai ya kawo ki kasar nan kenan" Khadijah ta gyada kai tace "Na ma kusa gama wa" Safeenah tace "Ayya, a Nigeria wani state ku ke da parent din ki?" Khadijah tace "Kaduna" Safeenah ta gyada kai tace "Su jawahir ne ke kaduna mu a Abuja muke" Wayar Safeenah ya fara ring ta duba, mike tayi ta koma can karshen gado tace "Let me answer my call Khadijah" daga haka tayi picking call din, murmushi Khadijah tayi ta mike don dauko masu rigar sanyi, har ranta taji tana son Safeenah, she's just free minded, daya side din gadon ta tafi ta kwanta bayan ta ajiye ma Safeenah rigar sanyin, ta lumshe ido nan da nan bacci ya dauke ta. Da asuba bayan sun idar da sllh Safeenah ta koma ta kwanta, Khadijah ta fita xuwa kitchen tana tunanin abinda xata yi na breakfast ta kai ma su Deejah, Irish tayi deciding ta soya da kwai ta dafa masu ruwan shayi don ita iyakar abinda take ci kenan gidan sai indomie ko shinkafa... Gaba daya cimar kasar bai dameta ba shi yasa ko siya bata yi, ta fi ga abincin Nigeria, har ta gama abinda take a kitchen Safeenah bacci take, daukan Shureim tayi ta fita daga dakin xuwa wani dakin tayi masa wanka ta dauko Uniform dinsa ta shiryasa ta sa masa kayan sanyin sa sannan ta basa Breakfast, wankan tayi ita ma kafin ya gama ta shirya cikin abaya ta yafa mayafinsa ganin da sauran lokaci yasa bata kai masu breakfast din ba ta tafi kai Shureim makaranta, tana dawowa ta tarar da Safeenah a parlor, Tace "Har kin tashi?" Safeenah tace "Wllh Dr Ayman ne ya tashe ni yanxu shi ya xo neman ki" Khadijah tace "Nema na kuma?" Safeenah tace "Noo xai fita ne yace xai yi dropping brother dinki a schl sai nace kilan kin je kai sa" Khadijah tace "Ayya ai daga can nake ma, akwai ruwan xafi bathroom idan xaki yi wanka" Safeenah ta mike tace "A'a bari in je can inyi tunda kayana na can din, dama jira nake ki dawo" daga haka ta nufi kofa Khadijah tace "Toh shkkn, Amma xa ki dawo?" Safeenah tayi dariya tace "Eh xan dawo" Khadijah tace "in bar maki breakfast din ki a nan kenan" Safeenah tace "Da safen nan fa xa mu wuce Khadijah" Khadijah tace "Da gaske" Safeenah tace "Ehh amma can gidansu Maryam xa mu je, Mum dinmu na can anjima da yamma sai mu dau hanyar Naija" Khadijah tace "Ayya to shikenan, idan na fito lectures da yamma kila in taho gidansu Maryam sai muyi sallama" Safeenah tace "Ba wani kila, kawai ki taho ku gaisa da Ammin mu tana can gidan ai, plss ki xo wllh ni dai ina son ki fa Khadijah I want us to be frnds" dariya Khadijah tayi tace "Toh in sha Allah xan xo" daga haka Safeenah ta wuce, Khadijah ta dau breakfast da ta masu a kitchen ta kai masu, a hankali ta bude kofar dake bude ta shiga parlorn, babu kowa parlorn sai ac dake kunne duk da sanyin garin, a hankali ta durkusa nan tsakiyar parlorn ta ajiye abubuwan hannunta, tana tunanin shiga daki wata xuciyar na ce mata kawai ta yi wucewarta idan sun fito xa su gani, har xata mike sai ga Khaleel ya fito, ya shigo parlorn yana kallonta, dai dai nan Safeenah ta fito daga daki ita ma ganin Khadijah tace "Yauwa Khadijah na bar wayata bedroom din ki" Khadijah ta mike da sauri tace "Lah to bari in dauko maki, dama xan taho da flask yanxu" Daga haka ta fita Khaleel ya dinga kallon safeenah da bata yarda ta kallesa ba tace "Ina kwana Doctor" yace "Lafiya lau" juyawa yayi ya wuce bedroom dinsa ya xauna kujera yana kallon jawahir da shigowar ta dakin kenan ita ma, atamfa ne jikinta ta yafe jikinta da mayafi tayi kyau sosai, a hankali tace "Ina kwana" yace "Lafiya qlau dear, I want to ask you something, shud i?" tana kallonsa tace "Ina jin ka" yace "Safeenah naji kamar ake kiran ta koh?" Jawahir na kallonsa tace "Ehh, what about her?" yace "Ya ku ke da ita pls?" Jawahir tace "She is my cousin sis, My mum and her father are having same parent, me ya faru?" Kallonta ya dinga yi kafin yace "Where do they stay?" Tace "Abuja" yace "Ohk sorry I'm asking this dear, bayan Dad din Safeenah, da Umman ku, da Uncle din ki na Lagos, akwai wasu kawun nan ki da ban sani ba ko aunt din ki? ta bangaren mumy fa nake tambayar ki" jawahir ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Dama su biyar ne kawai gun maternal grand parent dina, kawun mu na Lagos ne babba, sai Abbansu Safeenah, sannan kawu Abdul, sai Ummata da kuma autarsu, but she is late, ta rasu" Khaleel dake ta kallonta yace "Since when?" Ta girgixa kai tace "I really don't know don Umma tace min muna yara lokacin, she is always talking about her younger sis til date, seems tana sonta sosai" Khaleel na kallonta har lkcn yace "Kuma tayi aure kafin ta rasu?" Jawahir tace "Gaskiya ban sani ba" Khaleel ya dawo kusa da ita yace "Plss do me a favor of asking Umma to tell you more about her" da mamaki Jawahir ke kallonsa tace "But why?" Ya shafa kansa yace "Ke dai ki tambayar min ita plss wife" d'an murmushi tayi tace "Toh xan tambayar maka in sha Allah" yace "Yauwa nagode sosai" Khadijah na komawa apartment dinta ta dauko wayar Safeenah da flask na Lipton da ta dafa ta dawo apartment din Dr Ayman, har lkcn Safeenah na parlor tana jiranta, bayan ta karbi wayar tace "Thanks much Khadijah, baxa ki shigo ku gaisa da su Deejah da jawahir ba?" Khadijah tayi murmushi tace "Toh ina xuwa, xan dawo yanxu" daga haka ta fita, tana shiga apartment dinta jakar makarantar ta kawai ta dauka ta bar gidan don bata son sake jamming da khaleel, she just can't withstand the sight of him. Kamar yanda tace ma Safeenah suna gama lectures karfe uku da yan mintuna ta tafi gidansu Maryam tunda ta mata alkawari, Hajiya Mariya taji dadin ganinta haka mahaifiyarsu Safeenah, Khadijah na ganinta ta ganeta don ita ce suka yi vid call kwanaki, Safeenah tace "Ammi kin ganta koh" Ammi tayi murmushi tace "Ae kam na ganta, ya iyayen naki Khadijah" Khadijah tace "suna lafiya..." Ammi tace "A kaduna ku ke da xama?" Khadijah ta gyada kai tace "Ehh" Hajiya Mariya tace "Ina Shureim din Khadijah?" Khadijah tace "Yana schl Mumy" shirye shiryen wucewa Airport suke, Khadijah dai na ta xaune parlor tare da Hajiya Mariya da Ammin su Safeenah, gaba daya hankalinta yayi kan Shureim sanin sun tashi amma ta rasa me yasa ta kasa masu sallama ta wuce, wayar ta ne yyi ring ta kalli Deejah dake kusa da ita tayi excusing kanta ta fita, kasa daukar wayar tayi duk jikinta yayi sanyi, gaba daya ta mance ita yake jira, ganin xai tsinke ta dauka daga karshe ta kai kunne a hankali tayi masa sallama, amsawa yayi yace "Uhnn it seems.... Amira ni kadai nake hauka na koh?" Da damuwa tace "Am very sorry barrister, I wanted calling you na mance, but kasan me duk wanda kaga ya maka kyau Wallahi ina so, I want ur choice" jin yayi shiru a hankali tace "Ka yi shiru barrister" yace "Ohk then..." Marairaicewa tayi tace "You are still angry koh?" Yace "Sure" tace "But nace fa kayi hakuri" yace "Amira if I am important to you baxa ki ce kin manta ba, am still in dubai because of you but kuma kice min kin mance" jikinta yayi sanyi tace "Don Allah kayi hakuri..." Yace "Nayi" daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, tana ta tsaye duk bata ji dadi ba don tasan bata kyauta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login