Showing 27001 words to 30000 words out of 234058 words
warce xata xauna ba cikin ku" Matarsa ta fari Hajiya Salaha tace "Toh ni dai yara sun yi yawa a gu na, ban san dai ko Maimuna ba" warce ta kira da Maimuna tace "Ni kuma sai nace maki yaran basu min yawa ba koh?" Kawu yace "A'a bbu xancen tada jijiyoyin wuya taje dakin ki Maimuna kayanta kuma a kai dakin salaha, shkkn" daga haka ya dinga fiddo da tsadaddun kayan Khadijah, daga shi har matansa bbu mai cewa komai sai kallon ikon Allah suke, Kusan set takwas ya cire ya ajiye gefe yace "Wannan siyar da su xa ayi in sha Allah, domin kuwa baxata xo nan ta dinga saye sayen kaya ba kamar wata er gote ta janyo ayi tunanin shi gareni..." Takalman ma duk ya ware kusan biyar, golds dinta na dankunni da awarwaro kuwa dama suna aljihunsa, Khadijah dake ta tsaye jikin kujera tana waiga ko ina na parlorn da idonta tana neman remote ta kunna TV amma bata gani ba, ganin kawu xai xuba duk kayan da ya ware a wani jaka ta karaso da sauri tace "Kawu ina son wannan takalmin, da shi nake xuwa makaranta" Dungurinta yyi da karfi ya kunduma mata ashar, ta koma baya a tsorace yace "Ki shiga hankalinki da ni fa xan xane ki wllh" xata mike ya fixgota ya cire dankunnin kunnenta, Hajiya Maimuna tace "Toh idan ba fitsara ba ita har xata gaya maka abinda xaka yi" mikewa yyi ya dau jakar yace "Ku shiga da sauran, ni na tafi kasuwa kan yamma yyi" daga haka ya nufi kofa" bayan fitarsa Hajiya salaha ta sake fiddo kayayyakin ta dau kusan kala biyu da panties da kayan bacci, Hajiya Maimuna ma ta jawo jakar ta dau huluna da kaya kala daya da dogon rigar kanti da safunayen hannu da kafa, Hajiya salaha xata sake jawo jakar Hajiya Maimuna ta rike tace "Tsiyace jakar xa ki yi" Hajiya salaha ta jefa mata wani tace "Ke ai arxiki kike karama jakar, abu baxa ayi sa da hankali ba, ita sai ta sa uwar me?" Hajiya Maimuna ta rufe jakar ta tura tana kallon Khadijah dake ta tsaye tana kallonsu tace "Dauka ki kai dakin can dake kusa da wancan kofar, kin wani tsaya ma mutane kememe" Khadijah ta karaso da sauri ta dau jakar ta bi hanyar da Hajiya Maimuna ta nuna mata, kafin ta fito sun dau takalma kala daddaya ta dau jakar takalmin ma ta kai dakin. Uban wanke wanken dake tule gun pampon da aka tanadar don yin wanke wanken Hajiya salaha ta nuna mata taje tayi, a hankali Khadijah tace "Ina jin yinwa" Hajiya salaha tace "Can baki ci abinci bane kafin ki taho, ki je bakin pampon akwai tukunyar taliyar da ta rage ki ci sannan kiyi wanke wanken" Fita khadijah tayi xuwa gun pampon, ta yi kusan minti daya tana kallon taliyar da kudaje ke bi, ta turo baki ta rungume hannayenta, Dawowa parlon tayi kamar xata yi kuka tace "They are flies perching all over the food, ni baxan iya ci ba" sakin baki suka yi gaba daya suna kallonta, can suka kwashe da dariya Hajiya Maimuna tace "Toh baturiyaa jikar mongo park...." Hajiya salaha tace "Kin wuce kin ba mutane waje ko sai na mike.. Ina ruwan ki da k'uda idan ba rainin wayo ba, ki bar abincin kar ki ci, kuma maxa ki tafi ki wanke kwanukan yanxun nan" juyawa khadijah tayi ta bar wajen, Hajiya Maimuna tace "Idan ba ma tsoron Allah ba har Alhaji xai yarda ya rike er Muhammad, uwar me ya tsinana sa yana raye" Khadijah dake ta turo baki ta dau omon da ta gani da sosan wanke, tsaye tayi ta rasa ta inda xata fara wanke wanken, can dai ta dauko babban bahon da ta gani ta tari ruwa ya kusa cika sannan ta xaxxage d'an omon, muryar wata mata da shigowarta gidan kenan taji tana cewa "Ke ya haka, da uban ruwan nan xaki kada kumfa?" Khadijah ta kalleta kamar xata yi kuka tace "Toh ban sani ba" matar ta karaso baki sake, nan ta rage ruwan ta kara mata omon sannan tace "Haka ya isa" parlor matar ta shiga wajen su Hajiya tana cewa "Ku kuma ina kuka samo wancan Ajebon" Karfe kusan hudu da rabi Hajiya Salaha ta fito bayan tafiyar bakuwarta, sakin baki tayi tana kallon Khadijah dake durkushe bakin pampo har lkcn, kwanuka ta ko ina, duk ta hade gumi ta jike kayanta jagab, kai kana ganinta kasan bata taba ba ne, Hajiya ta kwalo ma kishiyarta kira ta fito da sauri, ita ma ta xaro ido tace "Me xan gani ni Maimuna, wanke wanken awa biyu?' Khadijah dake kallonsu kamar xata yi kuka tace " plates din sun bushe, ya ki ya fita" Hajiya Maimuna ta rike ha6a tace "Ehh lallai muna da aiki, yanxu tsalelliyar budurwa kamar ki baki iya wanke wanke ba shekara sha uku sa'ar Murjata" Hajiya Salaha da ita ma ta bude baki ta kalli kishiyarta tace "kina da aiki dai, don ba ni aka kawo ma ita ba, mutum yaji da nasa 'ya yan mana, shima Alhaji wllh, da ba sai ya bar ta gun kishiyar marigayiyar uwarta ba" Juyawa Hajiya Maimuna tayi tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka ta shiga ciki, Hajiya salaha ta mata tsawa tace "Tashi mana kan kwanuka yar banxa kawai, ke ga yar masu kudi ko, to xa ki ci kwakwa a gidan nan don bbu shegen da xai dau iskancin ki, kawai kin bi kin ma mutane asarar omo, maxa kuma ki dau tsintsiya ki tattare gaba daya gidan nan idan shima kuma baki iya ba sai in ga" khadijah da ta bata fuska xata yi kuka ta karasa ta dau tsintsiyar da take nuna mata ta fara sharan, takaici ya rufe Hajiya ganin gwara ma ta shekara a tsugunne bakin pampon da wannan sharan da take na yan iska, juyawa tayi ta bar gun daga karshe tana cewa "Xaki san inda kika xo yarinya" da daddare Khadijah na rakube jikin kujera gaba daya hankalinta da soul dinta na kan kallon cartoon da kananun yaran kawu Jibril suka sa a TV, an kirata ya fi sau uku amma inaa, hauri Sajida er Kawu ta biyu ta kai mata tace "Yau naga mayyar kallo ana magana bata ma san ana yi ba" a firgice ta mike sai dai har lkcn idonta na kan TV, Hajiya Maimuna dake lekosu daga kitchen don ita ke kiran khadijar ta xo ta karbi abinci, ta karaso a fusace ta kai mata dundu, firgita ta juyo Hajiya Maimuna ta murda kunnenta tace "Gafara shegen kallon nan xai maki ne hala, ka ji min yar kaza kaza" sunkuyar da kai khadijah tayi kamar xata yi kuka, Hajiya Maimuna ta turata kitchen tace "Ga tuwon ki can a kitchen ki dauka, gayyar tsiya kawai" tafiya kitchen din tayi tana yi tana waiwayo TVn ta dauko tuwon a wata yar roba an ya6a masa miyar kuka koriya shar, sai kallon miyar take kamar idanuwanta xa su fito, ta dawo parlon ta xauna cikin yara dake cin abinci su ma ta ci gaba da kallonta Hajiya Salaha ta shigo parlon tace "Wato kinsan idan mutum ba ayi masa tarbiya ba sai na kallo, kinga saura kadan ta xubar da tuwon tana kallo" da sauri khadijah ta kalli tuwonta taga ba daidai ta ajiye sa ba, Hajiya salaha ta fixgota a fusace ta juyar da ita tana kallon kofar kitchen tace "Duk kika sake juyowa sai na kashe ki" Khadijah dai bata ce komai ba ta kai hannu a hankali cikin tuwon ta mintsili kadan ta kai baki, yamutsa fuska tayi tana hadiyewa da kyar sai kuma ta kalli Er Kawu ta uku mai suna Rabi tace "Anty akwai indomie?" Yarinyar ta fashe da dariya sannan ta gaya ma Uwarta Hajiya Salaha, Hajiyar tace "Ehh akwai wanda ubanta ya kawo mana daga kabari" Khadijah dai bata ce komai ba, haka tayi ta kallon tuwon ta kasa ci, daga karshe haka ta mike ta kai kitchen ganin kowa na kai kwanonsa can, Hajiya Maimuna ta kwalo ma kishiyarta kira ta nuna mata tuwon da ta bari tace "kin dai ga koh? To wllh har in fita girki sai dai yunwa ya kashe yarinyar nan"
*Haske Writers Association*💡
07087865788 Contact me here.
✨ *Noor-Al-hayat*✨
_By Khaleesat Haiydar_
_Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan, yyi hakuri plss_
Washegari talata Khadijah na ta share tsakar gidan da aka sa ta tayi tun asuba har lkcn bata gama ba Kawu ya fito cikin shiga ta alfarma da daya daga kayan mahaifin Khadijah, matansa sun rakosa xuwa balcony ana yi masa Allah ya tsare hanya, ganin Khadijah da yayi ya juya yana kallon matan nasa yace "Gobe er can ta shirya da safe xa a kai ta makarantar boko" Hajiya Maimuna tace "Wanda su Sumayya ke xuwa?" Wani kallo yyi mata yace "Ke xa ki biya, ko ina naga kudin biyan wannan makarantar, makarantar da yaran Bala ke xuwa xa a kai ta, ina jin ko a Jss2 aka ce take ko one" Khadijah ta mike tace "Aa jss2 nake Abba" Wani shegen kallo yyi mata yace "Kun ga irin rashin tarbiyar ko, kun gani ko, to yanxu wa ya sako bakinta, dama na samu labarin an baki tuwo ki ci jiya da daddare kin ki ci tunda kin taho da abinci daga gidan marigayi Muhd, to wllh xa ku yi aiki hand in hand da yunwa in har baxa ki ci abinda ya sauwwaka ba, baxa ki taho gidana kina min sangarta ba" daga haka ya nufi daya daga motocin dake tsakar gidan, Khadijah ta ci gaba da sharanta na yan koyo da take yi. Throughout haka ta dinga aikin da ba ta iya ba bata taba yi ba a gidan, duk ta gaji amma ko kadan bata ce haka ba sai turo baki da take ta yi, Hajiya Salaha ta kai mata dundu yyi sau biyar daga karshe ta gaji da bin ta tana mata dundun ta kyaleta, Hajiya Maimuna kuwa ta surfa mata xagi ya fi a kirga, duk wnn abun sai dai ta turo baki ko ta bata fuska daga nan kuma shkkn, kunu da kosai a gantale aka bata a cup, ita ma ta ci a gantale ta bar masu abinsu don ba saba ci tayi ba, sai da suka yi baccin rana sannan ta samu tayi sallahn zuhr ta lallaba ta kunna TV ta rage volume ta xauna tana kallo happily, dauke wutan da aka yasa ta turo baki, a hankali ta kwanta nan kasan parlon nan da nan kuma bacci ya dauketa don tun tashin asuba. Ko abincin rana ba a bata ba wai sai yaran gidan sun dawo, basa kuma dawowa sai karfe biyar, suna dawowa kuwa da yamma aka xuba ma kowa shinkafa da wake da mai da yaji da Hajiya Maimuna ta girka, Hajiya Salaha ta sa Sumayya ta xuba ma Khadijah don ita Hajiya Maimuna rantsuwa tayi baxata bata ba, khadijah ta tsura ma shinkafa da waken ido da aka barbada ma yaji, a hankali ta kai hannu ta dinga tsince waken tana ajiyewa a kasa gefenta, Hajiya Maimuna dake ta kallonta ta mike ta karbe kwanon abincin ta kai kitchen ta rufe, abincin da ba ta ci ba kenan har aka yi magrib sannan isha, tana ganin aka ba kowa shinkafa da miyar da Hajiya maimunar tayi amma ban da ita, bayan ta idar da sllh ta samu Sajida dake waya ta duka gefenta a hankali tace "Anty ni ba a ban shinkafar ba" ta mata wani kallo tace "Toh ni na dafa ki samu su Hajiya mana" mikewa tayi ta wuce dakin Hajiya salaha, ta samesu xaune da yaranta ana assignment, kallonta tayi tace "Lafiya??" ta girgixa kai tace "Ni ba a bani abincin ba ina jin yunwa" tsawa tayi mata tace "Fita ki ban waje, ba dai shayi da soyayyen kwai kike jira ba yunwa xai kashe ki gidan nan" a hankali Khadijah ta juya ta fita, ta tafi gun kwanciyarta ta rakube hade da rufe ido tana tuno Ummarta. Washegari kamar jiya da asuba aka tasheta, har gari ya waye tana shara, sai da duk yaran suka wuce makaranta sannan Hajiya maimuna tace idan ta ga dama ta wuce tayi wanka ta shirya, tsaye khadijah tayi a bathroom dake tsakankanin dakunan su Hajiya, soson wankan ta da Abbanta ya siyo mata daga Kasar waje ya xama na kowa da kowa hadda sabulunta mai tsada, ta turo baki ta dau sabulun kadai ta yi wanka da shi ta fito cike da kyankyanin bayin, tun da ta fito parlor Hajiya Salaha ke kallon kayan jikinta, khadijah ta durkusa gefenta a hankali tace "Na gama" tabe baki Hajiya salaha tayi ta nuna mata cup din kunu tace "Gashi can ki dauka, kosan ya kare" Khadijah ta leka cup din da sauri a xaton ta shayi ne, a hankali ta mike ganin ba shi bane ta isa gun cup din kunun ta dauka, Hajiya salaha tace "Ko yau ma baxa ki sha ba" bata ce komai ba ta dinga shan kunun da yyi mata tsami a baki tana d'an yamutsa fuska, sai hararanta Hajiya salaha take tana kwafa, daga karshe kadan ta sha ta ajiye ta mike tace "Na koshi" duk da uban yunwan da take ji cikinta na kugi, Hajiya Salaha tace "Toh ki hutar da kanki tafi ki juye a flask ki hada duk kwanukan ki wanke, kuma ki min irin na ranan in fasa maki jiki da wayar wuta" ita dai khadijah bata ce komai ba ta mike taje yin yanda tace nata. Wani almajirin Kawu ne ya taho kai ta makarantar, shegen nisa ce da makarantar kuma almajirin me suna musa yace da kafa xata dinga xuwa kullum don haka gwara ta dinga kallon hanyar da kyau, tunda suka shiga makarantar Khadijah ke kalle kallen ko ina, don ita dai bai yi mata kama da schl ba, gashi ko plaster ba ayi ba, yaran ma basu da yawa, Musa ya shiga gun wani wanda da alama shugaban wajen ne, ita tana tsaye waje, tana jin mutumin na ce ma musa ai lesson ne wa yaran da basa gane karatu, kuma na shekara daya ne kafin yaro ya shiga boko, musa ya tambayesa nawa ne yace dubu uku da dari biyar, nan take musa ya basa kudin, ita kuma aka kira wata daliba ta kai ta ajin karshe musa ya wuce, su kusan goma ne a ajin, ita dai tunda ta shiga ajin take kallon malamin dake ta koya sentence making, "The boy was tall..." Shine abinda malamin ke ta nanatawa yaran na fadi su ma, khadijah dake ta kallon sa tace "Excuse me, but you said present tense sir?" Malamin yace "Yes" tagumi tayi tace "Sorry but that's past tense class master" kallon board din yyi da sauri sannan ya kalleta, bai kulata ba ya ci gaba, nan ma kuma sai da ta sake masa gyara, hade rai yyi yana kallonta, can ya basu classwork ya koma ya xauna, sai bayan kusan minti sha biyar ya karba sannan ya fara koyar da Multiplication a board, sai da ya gama tas, sannan ta kai masa gyaransa a littafi tana nuna masa, fita malamin yyi xuwa gun shugabansu, ba a dau lkci ba ya kirata, tana tsaye yace "Ke tunda baki da kunya kar ki sake xuwa makarantar nan daga yau, tunda kin iya abinda ake koyarwa ki xauna a gidan ku ko kuma a kai ki school ga kudin ku" karba tayi tace "Ohk, in tafi yanxu" yace "Tafi" juyawa tayi ta fice daga uncomplete building din, gano gida bai mata wahala ba saboda sharpness dinta, su Hajiya salaha dake xaune parlor suna hira suka saki baki suka ce me kika dawo yi, tace "Ba abinda suka iya fa a wajen, they are just teaching rubbish, ni bana son wajen school nake so, am in jss2" Hajiya maimuna tace "Shine kika dawo" gyada mata kai tayi ta mika mata kudin hannunta, ta tafi jikin kujera ta rakube ta xauna, duk suka bi ta da kallo baki sake. Yunwa sosai take ji amma bata ce komai ba, Kawu ne ya fito a shirye xae fita wajen karfe goma da rabi, ganinta yace "Wannan yarinyar musa bai kai ta makarantar bane" Hajiya salaha tace "Uhn gata nan ya kai ta ta dawo wai bbu abinda suka iya kilan mai tsada take so" ya juya da sauri yana kallonta yace "Me ya dawo da ke?" Tace "Abba they are teaching rubbish there, kuma ina ta correcting dinsa, ban san whether he reported me bane, sai aka kira ni wai in tafi kar in sake dawowa, har da kudin ma an bani na dawo da shi" Kawu ya gyara tsayuwa yana gyada kai yace "Ohhhw haka aka yi kenan, toh kin ma kanki, Alhmdllh Muhd baxae gan ni da ko wani laifi ba don na kai ki makarantar kika gudo, don haka sai kiyi ta xama gidan" daga haka yyi ficewarsa, ita dai bata ce komai ba, Hajiya Maimuna tace "Wato ke isassa kin raina makarantar shine kika je kina ma malaman fitsara ko, uban wa ke da kudin asaran da xai kai ki irin makarantar da ubanki ya sa ki tun farko?" Khadijah dai sai kallonta take, Hajiya Salaha tace "Ni da nace xan fara awaran siyarwa xan dauko mai aiki wllh da Alhaji xai yarda da sai ta dinga kai min can bakin kasuwa, kinga ai ba talla bane wnn, xama waje daya xata yi" Hajiya Maimuna tace "Ae ko da xai yarda nima sai in hada mata da Omon siyarwa na" Hajiya salaha tace "Toh bari ya dawo dai mu ji" suka gama dai hirarsu duk suka shiga dakunansu domin kwanciya suka bar ta ita kadai a parlorn ga yunwa dake dawainiya da ita, da rana yau kam taliya da wake suka girka, gashi ita bata cin wake tun tana karama, Hajiya salaha ta dan yarfa mata a kwano ta bata, kamar