Showing 159001 words to 162000 words out of 234058 words
going to India tomorrow" kallon khaleel yyi yana kwasan takardun da ya gama rubutu a kai yace "Don't tell her anything about it...." Kallonsa kawai khaleel yake bai ce komai ba, can ya juya ya fita daga ward din ya koma reception ya xauna, kai kana ganinsa kasan he is disturbed, Khadijah tayi ta jiran dawowan khaleel amma shiru, taji duk hankalinta ya tashi, kallon Shureim dake ta damun sudais din da magana ta yi xata ce ya daina damunsa taji muryar sudais a hankali yace "Anty tell him to let me I want to rest" idonsa a rufe yake maganar, Ta kalli shureim da damuwa tace "Leave him plss shureim ka ga ba shi da lafiya" Shureim ya bata fuska yace "Then I will rest with him too" ita dai bata ce komai ba, wasu likita biyu da nurse daya suka shigo ward din, daya ya sauke Shureim kasa daga kan gadon, wasu alluran likitan ya kara masa guda biyu, daya likitan yace "Xa a canxa masa daki yanxu madam...." Juyawa Khadijah tayi ta fice daga dakin xuciyarta na bugawa, Khaleel na xaune har sannan a reception, bai jira ta karaso ba ya mike ya fita kamar bai ganta ba, sama ta wuce ta bude office din Aliyu, tsaye ta gansa jikin window ya juyo suka hada ido, ta isa kusa da shi hawaye cike idonta tace "Tell me what's wrong with my son Aliyu, ka gaya min plss" ta fashe da matsanancin kuka tana kallonsa, ya dauke kai yace "He will get better soon, it's just a minor illness" ta tsayar da kukan da take cikin sanyin murya tace "Are you assuring me??" Yana kallon kwayar idonta yace "Sure, Allah xai basa lafiya" juyawa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Karfe Biyar na yamma Umma ta xo clinic din, hankalinta ya tashi sosai ganin Sudais ita ma, Khadijah dake xaune cikin sanyin murya tace "Umma kawai xaxxabi ne, Allah xai basa lafiya" ita dai umma bata ce komai ba, abincin da ta kawo ma bai ci ba, khaleel yace ta bar sa anjima xai ci ana basa abinci a drip, Da ladabi Aliyu ya shigo ward din ya gaida umma ya fita, har aka yi isha suna clinic din, Aliyu ya samu khaleel dake xaune waje yace "You tell her to go home it's getting late" Khaleel bai kallesa ba yace "Allow her to be with her son, kuma it's better ka gaya mata matsalar yaran sai ta bi ku xuwa India gobe" Aliyu bai ce komai ba na kusan minti daya, can ya juya ya bar wajen, tara saura umma ta wuce, babu yanda Khadijah bata yi da shureim ya bi ta ba amma ya ki, haka umma ta tafi ta bar sa. Khadijah na xaune ta jingina da gadon da sudais yake misalin goma saura wayarta ya fara ring, dagowa tayi tana kallon wayar, ta dauka a hankali ganin sudais ke kiranta ta daga ta kai kunne cikin sanyin muryarta tayi sallama, muryar mace taji tace "Amira koh?" Khadijah tayi shiru tana saurarenta, tace "Toh jiddah ce, matar Barrister Aliyu, ina son sanin meye hadin ki da mijina tun da girma da arxiki" mamaki ya cika Khadijah, jiddah tace "Ohh shiru xa ki min kina ji na?" Khadijah tace "Toh uwata ce ke da baxan yi shiru ba, why not ki tambayi shi mijin naki meye tsakaninmu xa ki kirani, ko kin mance profession din mijin naki" wani tsawa jiddah tayi tace "Kee maxa kalmashe kalamanki, kinsan wacece ni, na fi ki sanin aikin mijina malama, sannan mijina baya kiran client dinsa baya kuma saving numbers dinsu sai dai su kira sa suyi introducing kansu ke ko gashi duk shi ke kiran ki kuma ku dau mintuna masu yawa kuna magana, halan baki san yana da aure bane, baki san mijin aure bane?" Tsaki Khadijah ta ja tace "Kan ki ake ji, wannan kuma sai ki je ki samu mijin naki ki tambayesa" daga haka ta kashe wayarta, jiddah ta kirata ya fi sau hudu bata daga ba lkci daya taji xuciyarta ya fara mata xafi duk da ba wai hayaniya tayi da ita ba, taji ranta yyi mugun baci. Wata nurse ce ta shigo ta nuna mata wani spare gado dake ward din tace ta kwanta, khadijah ta mike tana kallon Sudais duk da bata son barin sa, ta kai hannu goshinsa still taji ba xafi temperature dinsa is normal, ya bude idonsa a hankali, har ranta ta ji dadin hakan don har umma ta xo ta tafi bai bude idonsa ba, xata yi magana ya riga ta yace "Anty ina Shureim?" Tace "Yana waje tare da uncle" ya bata fuska yace "Me yasa ya tafi?" Ta kwantar da murya tace "You said he shud allow you to rest, shine ya tafi da uncle" a hankali yace "Anty kice ya xo plss, I want to tell him am sorry" jikinta yayi sanyi tace "Toh xan kira sa yanxu" daga haka ta nufi kofa tana waigo yaran da ya bi ta da ido,
Khaleel na xaune waje idonsa a kan wayar hannunsa Khadijah ta nufosa, ya daga kai yana kallonta har ta iso inda yake, yace "Is he awake?" Tace "Yace yana son ya ga shureim wai" Khaleel yace "Yana sama" ta d'an bude ido tace "Wajen wa?" Bai ce komai ba, hakan yasa ta hade rai tace "But me yasa ka bar sa ya je can? Why did u allow him go to him?" Khaleel ya ci gaba da danna wayarsa yace "He followed him, sae in hanasa..." Juyawa tayi a fusace ta wuce office din Aliyu, Khaleel ya d'an yi murmushi ya tashi ya shiga clinic din shi ma, Aliyu na tare da Dr Mukhtar Khadijah ta shigo office din, duk suka juya suna kallonta, ta dinga kallon office din tana neman shureim can ta hango sa kwance kan gadon masu ciki a office din yana bacci, karasawa tayi xata tashe sa, taji Aliyu yace "Don't wake him" ko kallonsa bata yi ba xata daga yaron taji jikinsa yyi xafi sosai, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, a firgice ya farka ta rikesa sosai tana kallonsa da damuwa tace "Shureim me ya faru, ur temperature is high" rungumeta yayi yyi lamo jikinta, ta sauke sa kan gadon ta nufi kofa, Aliyu ya bi ta da kallo, ba su kai ga kai wa kofar ba yaron ya shiga kwarara amai, ta dukar da shi da sauri ita ma ta duka hankalinta tashe tace "What's wrong shureim, me ka ci?" Dr Mukhtar ya taho gun su ya dagosa yana masa sannu, dai dai nan wata nurse ta shigo tana kallon Aliyu tace "Dr, ur attention" daga haka ta fita, Khadijah ta bi nurse din da kallo, Aliyu ya fita office din Dr Mukhtar ya cire ma Shureim rigar jikinsa yana rike da hannunsa ya isa table din Aliyu, duba sa yyi, bayan wani lkci ya ajiye stethoscope din hannunsa ya nuna ma Khadijah bathroom yace "Ki gyara masa jiki sai ki kwantar da shi kan gado, let me get him drug? Ya ci abinci?" Ta girgixa masa kai yace "Ohk" daga haka ya fita xuwa gun nurses, Ganin duk basa wajen yayi tunanin ko an kawo emergency ne, ya kalli direction din Emergency ward, yaga Aliyu tsaye ya jingina da bango, Karasawa Mukhtar yyi gun sa, ganin yanayinsa yace "Me ya faru Dr?" Kallonsa kawai Aliyu yake ya kasa cewa komai, Dr Mukhtar ya shiga cikin emergency ward din, khaleel ne kusa da gadon da sudais yake ya hade kansa da karfen gadon, Dr Mukhtar ya dinga bin Doctors din da kallo, ganin yanda suke tsaye hopelessly, can ya kalli Sudais lkci daya jikinsa yyi mugun sanyi, gaba daya he became lost of words ya kasa karasawa cikin ward din, juyawa yyi da kyar ya fita office din yana kallon Aliyu dake jingine da bango har lkcn, ya dafa shoulder dinsa cikin sanyin murya yace "Hardluck Doctor, Allah ya masa rahama" Aliyu bai iya yace komai tunaninsa daya a lkcn Khadijah, Khaleel ma ya fito ward din yana kallon Aliyu amma ya rasa abinda xai ce, Aliyu yyi karfin halin ce masa "Plss take her home" Khaleel ya bar wajen a sanyaye ya fiddo wayarsa yyi dialing number sudais, yana dagawa a hankali yace "Barrister the boy is late" daga haka ya katse wayar, kujera Aliyu ya nema ya xauna jin ya kasa ci gaba da tsayuwa, sai a sannan ya ji hawaye na sakko masa ya rike kan sa, how will Iman take this?? Who is to break the news to her, Khaleel ma na tsaye ya jingina da bango yana tunanin yanda xai yaudareta ya mayar da ita gida, can ya nufi sama xuwa office din Aliyu ya ganta ta fito office din rike da shureim, khaleel na ganinta sai da gabansa yyi mugun faduwa ya nufeta da sauri sai dai bai bari taga idonsa ba trying hard to be okay yace "Where did u see him?" Da damuwa tace "Amai yake ta yi Dr, kuma jikinsa da xafi" Khaleel ya duka yana kallonsa yace "What happen shureim" yace "I want go to Sudais" Khaleel ya hadiye abu da kyar yace "Okay xan kai ka my boy" daga haka ya mike yace "Bani wayar pls ina son inyi call mine is out of airtime" mika masa wayar hannunta khadijah tayi ya kama hannun Shureim yace "Mu koma ciki in duba sa" tace "Ai wani Dr ya duba sa yanxu" yace "Ehh let me check him again sai a basa magani" tace "Toh ku tafi, let me go to sudais..." da sauri ya juyo yace "Noo ki xo mu je sai ku tafi tare da shureim he won't be happy idan bai ga shureim ba" a hankali ta bi bayan Khaleel dake rike da shureim, office din Dr Aliyu ya shiga, ya xaunar da Shureim kan gadon office din, ya kalli khadijah yace "You stay with him ina xuwa" daga haka ya juya ya fita, Number Umma ya shiga dubawa a call logs dinta, Ummata... yaga tayi saving number da, nan ya gane number umma ce, yayi saurin kwashe number a tasa wayar, ya sauka kasa bayan yyi dialing, ba a dau lkci ba Umma ta dauka, ya gaisheta cikin sanyin murya yace "Umma khaleel ne, I called to inform you that Sudais is late umma, yanxu ya rasu" mikewa umma dake xaune tayi cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilai raji'un ya rasu?" Jikin Khaleel yyi sanyi jin yanayin da umma ta shiga, a hankali yace "Ku yi hakuri Umma, but har yanxu Khadijah bata sani ba kuma ba a son ta sani a nan so plss, ban san ya xa ayi ko xaki kirata ki dai fada mata wani abu da xai sa ta wuce gida yanxu, cos we can never convince her taje gida ynxu" Kuka kawai Umma take ta kasa cewa komai ta katse wayar ta dinga salati wanda hakan ya ja hankalin Nanny ta shigo, cikin tashin hankali tace "Umma me ya faru?" Da kyar Umma ta iya ce mata "Sudais" tun umma bata fada ba Nanny ta san kwanan xancen ta fashe da kuka ta xube wajen tana salati ita ma, tausayin khadijah ya sa Umma ta kasa controlling kanta, kuka take kamar ranta xai fita, babu mai lallashin wani ita da Nanny, Khaleel ya kasa komawa sama gun khadijah duk iya kokarin sa na ganin ya dake ya ji ya kasa kuma, kujera ya nema shi ma ya xauna yana ganin abun kamar a mafarki yanxu shikenan yaron nan ya tafi, Nurses din ma gaba daya duk jikinsu a sanyaye yake, Aliyu yyi karfin halin fiddo wayarsa ya shiga kiran Mumy, bayan ta daga cikin sanyin murya yace "Mumy ya rasu yanxu" Yanda mumy ta rikice a lokacin sai ayi tunanin sun yi shekara shidda tare da yaron ne, ta dinga kuka kawai ya katse wayar sa,Sudais ne ya shigo reception din duk hankalinsa a tashe ya nufi khaleel cike da karfin hali yace "Dr plss kar ku ce min yaron nan ya rasu, tell me he is still alive" Khaleel ya kasa ce masa komai, Sudais ya tafi gun wata nurse yace "Take me to him plss" nurse din ta nuna masa emergency, da sauri ya shiga wajen, kallon gawar yaron ya dinga yi ganin kamar mai bacci da murmushin sa a fuska, sudais ya karasa gadon ya hade kai da karfe hawaye na sakko masa ya dinga nanata "Innalillahi wa inna ilai hi raji'un" Bai taba ba yaron mutuwa yanxu ba, ranan da aka haifesa tare da d'an uwansa ya tuno, da irin wahalar da khadijah ta sha kamar baxa ta yi ba, ya ji ya kasa controlling hawayen sa, memory din ya dinga dawo masa freah, tun daga san da yaran suka fara wayo, suka yi mugun sabawa da ahi har xuwa ranan da ya barsu suna kukan xa su bi sa amma har ya fita bai waiwayo su ba, cikin raunin murya sudais yace "Allahummaghfir li-fulanin Aliyu warfa' darajatahu fil-mahdiyyina, wakhlufhu fi'aqibihi fil-ghaabirina, waghfir-lanaa wa lahu yaa Rabbal-'aalamina, wafsah lahu fee qabrihi wa nawwir lahu feehi" daga haka ya karasa rufe masa idanuwansa amma ya kasa barin dakin hawaye na xuba idonsa, ya jima bai ji mutuwar da ta taba sa haka ba tun bayan rasuwar maminsa 3 years back, hakan yasa ya kasa daina hawaye, ya ki fita ward din don gani yake kamar yaron xai tashi. Da kyar Umma ta iya dialing number Khadijah, khaleel dake xaune ya jingina da kujera jin wayar na vibrate ya kalla da sauri ganin Umma ke kiranta ya mike ya ba wata nurse yace "Plss ma ki dan taimaka ki kai ma warce ke office din Dr Aliyu wayar nan" ta amsa ta wuce ta kai ma khadijah, a stairs suka kusa cin karo xata sakko, nurse din ta mika mata khadijah ta karba ganin umma ke kiranta ta daga wayar, Umma tayi gathering courage bayan ta saita muryarta tace "Khadijah ki dawo gida yanxu ina son ganin ki" hankalin khadijah ya tashi sosai jin yanayin muryar umma a tsorace tace "Umma baki da lafiya ne?" Hawaye na sakko ma Umma cikin sanyin tace "Ehh bana jin dadi ki dawo yanxu kin ji daughter" tashin hankali ne sosai tare da Khadijah ta dinga kallon wayar sannan ta sauka kasa da sauri, khaleel na ganinta ya mike da sauri, ta nufe sa da damuwa tace "Dr Umma ce ta kira wai bata da lafiya yanxu" ya dake yace "Subhanallah, bata da lafiya kuma?" Ta gyada masa kai hawaye cike idonta, yace "Toh bari inyi dropping din ki gidan yanxu..." Tace "Toh, Shureim din yana ta aman har yanxu amma wani Dr na gun sa" Khaleel yace "Toh shkkn mu je" juyawa tayi ta nufi ward da little sudais yake kafin a kai sa emergency tace "Let me check sudais kafin in tafi pls" Khaleel bai san lkcn da ya fixgota ba ta kusa fadawa kansa da mamaki take kallonsa, ya wara ido yace "Mu je, idan mun dawo sai ki duba sa, bacci yake daga can na fito yanxu" kasa cewa komai tayi Khaleel na rike da hannunta ya nufi kofar fita ta dinga bin sa, Aliyu dake xaune one side of the clinic duk yana kallonsu ya lumshe ido to prevent more tears, he still can't believe that cute boy, his blood is gone forever, kiran Abbansa ne ya shigo wayarsa, ya san mumy ta kira sa ta fada masa kenan, don tun bayan da Mumy ta gaya masa abinda ya shiga tsakaninsa da khadijah da batun yan biyun ya dauke masa wuta duk da a ranan ma ya bar kasar, a hankali ya mike ya daga kiran Abban nasa. Har suka isa gida khaleel bai ce ma khadijah komai ba, sai dai ya lura duk a sanyaye take, yaji wani mugun tausayinta na dawainiya da shi, jiki ba kwari ta fita daga motar bayan yyi parking ta wuce ciki tana tsoron yanda xata je ta samu Umma, Xaune umma take har lokacin a daki tayi kukan har taji ba dadi, nanny ma duk ta fita hayyacinta da ta tuna sudais ya mutu sai ya rushe da kuka don tun suna jarirai take tare da su. suna ganin khadijah duk suka shanye kukan Khadijah ta karasa da sauri ta xube gaban umma gabanta na mugun faduwa tace "Ummata mai ya faru, why are you crying plss" rungume ta umma tayi ta sake fashewa da wani kukan, Khadijah duk ta rikice ita ma ta fashe da kuka tace "Umma don Allah ki gaya min me ya faru, waye ya mutu?" Nanny ta mike ta bar dakin wani sabon kukan ya xo mata. A sanyaye khaleel yyi reverse ya koma clinic din, dai dai lkcn da Sudais ya fito daga emergency ward, Dr Mukhtar kuma ya sakko kasa rike da shureim, shureim na ganin Khaleel ya nufe sa da sauri, Aliyu ya bi yaron da kallo a sanyaye, khaleel ya duka yana kallonsa murmushin karfin hali dauke fuskarsa yace "How are you feeling now?" A hankali yaron yace "Uncle I want to see my brother plss" Khaleel ya dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ya kirkiri wani murmushin yace "He is sleeping now" ya fashe da kuka yace "Nooo, I want to sleep with him too" daga haka ya juya xai tafi inda dan uwansa yake, khaleel ya jawo sa da sauri yace "He is sick, baka son ya samu lafiya, idan kana damunsa baxai samu lafiya ba ai" cikin rawar murya yaron yace "Toh uncle kar ya tafi ya bar ni" Khaleel dake kallonsa ko kiftawa babu a hankali yace "Ina xai je?" Shureim yace "Gida" tashi Khaleel yyi ya kama hannunsa ya fita duk jikinsa a sanyaye. Aliyu dake xaune ya dinga kallon colleagues dinsa dake tambayarsa inda xa a kai gawar sudais ko a nan xai kwana, mikewa yyi da kyar yace "Xan tafi da gawar gida yanxu" a kunnen Barrister sudais da sai lkcn ya fito daga