Showing 126001 words to 129000 words out of 234058 words
jiransa" jikin Hajiya Mariya yyi sanyi sosai don har ga Allah bata ji dadin jin hakan ba duk da ita ma rashin aurensa na damunta amma aure without his knowledge kuma?? Sallama mumy tayi mata ta katse wayar.Tun da Khadijah ta fito rike da karamar jakarta daga cikin apartment dinta khaleel dake tsaye ya rungume hannunsa ke kallonta cikin bakin glass din idonsa kuma saboda ita ya sa glass din, abaya baki ne jikinta da mayafinsa, sosai kayan ya haska ta daga nisa kamar balarabiya, tana isowa gun da yake ya dauke kansa ya fara tafiya xuwa waje, taxi ya tsayar masu don motarsa na gun wani abokinsa, ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga, sai da suka dau hanya yace "Have you call home? I mean kin gaya masu kina tahowa?" Girgixa masa kai tayi, yace "Why?" Kamar xata yi kuka tace "Umma xata iya cewa kar in taho" khaleel ya hade rai yace "Toh tunda haka ne meye amfanin xuwan? Kawai ki fasa, da kin gaya min haka tun a gida ma ni baxan fito ba" Hararansa tayi daga sama har Kasa bata ce komai ba, ya xaro ido daga cikin glass dinsa, kamar me counting words din yace "Did... you... just... eye me?" ta sake juyawa ta maka masa wani hararan tace "You check for your self, kuma ni ban ce dole ka rakani airport ba, xaka iya komawa gida" lkci daya ya xare glass din idonsa suka hada ido, tayi saurin boye fuskarta a kafarta kamar xata yi kuka tace "Bana so" murmushi yyi bai ce komai ba ya mayar da glass din ya shiga danna wayarsa, har suka iso airport bbu wanda yace komai cikinsu sai dai lkci lkci yake satan kallonta, Khadijah ta bude cab din ta fita shima ya fita ta daya side din ya ba mai taxin kudinsa, kallon agogo yayi kafin su shiga airport din, khaleel ne yyi mata komai a airport din tana xaune ya dawo ya xauna gefenta ya mika mata ticket, xaro ido tayi tace "Noo, give me ur account details pls" wani kallo yyi mata yace "Toh Hajiya" daga haka ya dauke kansa, jikinta yyi sanyi bata iya tace komai ba, Wayarta ta ciro a jaka xata tura ma Vanessa text don bata ce mata xata yi tafiya ba, kamar ance ta kalli side dinta ta ga Aliyu xaune though nesa da su yana danna wayarsa, gabanta yyi mugun faduwa.... Lkci daya kuma babu abinda ya fado mata rai sai yan biyunta kamanninsu ya baci ne kawai, xuciyarta ya dinga bugawa ta dauke kai da sauri tana addu'ar Allah yasa ba jirgi daya xa su yi boarding ba, kallonta Khaleel yyi ganin yanda ta matso kusa da shi ba tare da tasan tayi hakan ba, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kai trying to control her self, da wani expression khaleel dake kallonta yace "What?" Ta girgixa masa kai da sauri kuma har lkcn ta ki dago kanta, bata kuma matsa daga kusa da shi ba, duk iya kallon khaleel a wajajen bai ga komai ba sai turawa da few bakaken fata dake wajen, a hankali yace "Khadijah" ta dago da sauri tana kallonsa, yace "What happened?" Girgixa masa kai tayi da sauri, a tsorace tace "I don't knw why I am afraid" ya d'an bude ido yace "Afraid? Of what" ta buda masa hannu kamar xata yi kuka, shiru yyi na few seconds, a hankali taji yace "Ohk shud I accompany you?" Ta dago tana kallonsa, dogon hancinsa da bakinsa kadai take gani banda idanuwansa, samun kanta tayi da gyada masa kai, yace "Ohk then" mikewa yyi ta bi sa da kallo tana boye fuskarta da mayafin jikinta ta saci kallon direction din Aliyu, yanxu ba danna waya yake ba ya dai jinginar da kansa da kujera yana kallon yaran turawa dake tare da uwarsu suna tafiya, da sauri ta dauke kanta. Har suka shiga jirgi Khadijah bata daina shisshge ma Khaleel ba, tayi sa'a kuma seat dinsa kusa da ita, suna keta haxo ta dinga bin jirgin da kallo cikin dubara amma ba ta ga alamar Aliyu ba, bacci ne ya dauketa daga karshe sai dai ta rufe rabin fuskarta da veil dinta, khaleel ya dinga kallonta, ya rasa gane irin tausayin da yake ma khadijah, ya san har ransa kuma he don't knw why, a hankali ta jinginar da kanta a shoulder dinsa, jawota yyi jikinsa ya lumshe idanuwansa, bayan awanni da dama Khadijah ta bude idonta a hankali, kallonsa tayi ta janye jikinta da sauri daga nasa, ya buda manyan idanuwansa yace "Are you hungry?" Ta girgixa masa kai, kamar ance ta kalli gefensu taga Aliyu xaune ya makala earpiece a kunnensa idonsa a lumshe, boye fuskarta tayi jikin khaleel jikinta na bari, khaleel ya riketa da mamaki yace "Are you okay?" Girgixa masa kai tayi a tsorace, bin jirgin ya dinga yi da kallo shi ma, lkci daya idonsa ya sauka kan Aliyu, haka kawai yaji gabansa ya fadi... Ya dinga kallonsa ko kiftawa babu don ko ba a fada ba kawai ya ga shureim da sudais a tattare da shi, lkci daya ya dauke kai, Khadijah da ta rufe fuska ta ki yarda ta kallesa, sauran journey din gaba daya daga ita har khaleel they where uncomfortable, khaleel ya kalli direction din Aliyu ya fi a kirga, gwara Khadijah tayi kokarin ganin bata sake kallon direction din ba, few hours kafin jirginsu ya sauka Abuja Khadijah ta d'an saci kallon gefensu dai dai lkcn da Aliyu ya juyo, hada ido suka yi sai dai fuskarta dama a rufe yake, ji tayi kamar an soka mata mashi a xuciya tayi saurin kauda kanta, shi ko yana ta kallonta bayan wani lkci ya dauke kansa. Har suka yi set down Khadijah ko da wasa ba ta juya kanta ba. Khaleel ya jira mutane suka fara sauka kafin ya mike, ita ma ta tashi da sauri, kamar xata shige jikinsa haka ta dinga bin sa har suka sauka matakalan jirgin, tsaye ta hango Aliyu nesa da jirgin yana kallonsu bayan shi ya sauka, taji kafafuwarta sun kasa daukar ta don tasan kila ya ganeta ne, har suka sauka Khaleel bai gansa ba don wani abokin sa bature ya dauke hankalinsa suna gaisawa, Aliyu dake ta kallon idanuwan khadijah da su kadai yake iya gani ya nufo ta, dai dai gabanta ya tsaya lkci daya ya fixge veil din fuskarta yana kallonta, rikicewa tayi, khaleel ya juya da sauri, ganin abinda Aliyu yyi ya cakumosa cikin tsawa yana masa wani mugun kallo yace "How dare you?"
Daga sama har kasa Aliyu ke kallon Khaleel da ya ki sake sa, Aliyu ya dake yace "Who are you?" khadijah na ganin haka a rikice ta ajiye jakar hannunta tace "Noo plss Dr ka kyale shi..." Khaleel na kallon kwayar idon Aliyu strictly yace "Stay away from her or else you regret it...." Yana fadin haka ya sakesa, Aliyu yyi wani murmushi yace "And who are you to tell me that? Her boyfriend? Husband or??" Juyowa khaleel yyi a mugun fusace ya sake cakumosa Aliyu ma ya cakumesa yana mayar masa da irin kallon da yake masa, khaleel yace "Both! Husband and boyfriend" dariya Aliyu yyi yace "You are very very stupid, idan ma mijinta ne kai ka shirya rabuwa da ita domin kuwa she is not meant for you" Khadijah na ganin abun ya kai haka ta shiga tsakaninsu da sauri cikin kuka tace "Wayyo na shiga uku, don Allah don annabi ku rufa min asiri ku yi hakuri" tayi facing din khaleel dake hade fist dinsa yana ma Aliyu wani irin kallo ta rikesa hawaye na sakko mata tace "Plss am begging you ka kyale sa don Allah Dr" lkci daya khaleel ya sake Aliyu ya kama hannunta ya dau jakarta, Aliyu ya fiddo complimentary card dinsa a aljihu ya saka a na Khaleel yana kallon kwayar idonsa yace "I will be waiting for ur call young man" still khaleel yyi kamar xai cire ya jefar sai kuma ya bari ya juya kamar xai tashi sama ya bar wajen Khadijah ta dinga bin sa xuciyarta na bugawa, Aliyu ya bi su da kallo yana murmushi a hankali yace "I will surely get you soon Iman, not when I have set my eyes on you" ta waigo ta kallesa tayi saurin dauke kai, har suka shiga cab Khadijah waigawa take taga ko ya biyo su, sai dai ta kasa ganewa don mutane ne da yawa ko ganinsa bata sake yi ba, duk ta kasa samun nutsuwa, tana kallon Khaleel da har sannan fuskarsa ke a daure kamar xata yi kuka tace "Plss Dr kar ka sake kulasa" Kallonta khaleel yyi a fusace xuciyarsa na heaving yace "That's idan bai shiga rayuwar ki ba, Billah xan iya yi masa komai, I don't care... Ina da wanda ya tsaya min a kasar nan, look... my father...." Sai kuma yyi shiru, lkci daya idanuwansa suka canxa kamanni, Khadijah jikinta yyi sanyi sosai, muryar khaleel ne ya dawo da ita tunanin da ta tafi, cikin sanyayyan muryarsa yace "Don't forget this is Abuja, ina xa mu? Thinking Kaduna kika ce min Umma take" A hankali tace "Dole sai mun bi train xuwa Kaduna" yace "Why not flight" ta hararesa tace "Bayan mun baro airport din, kawai kaje xaka tara mana crowd a airport ko meye na kulasa" bai ce komai ba sai kallon tagar taxin yake, khadijah ta sanar ma mai taxin train station xai kai su, Tsaki taji khaleel ya ja yace "Seriously It's being long aka ba ta min rai haka... Da ba don airport bane we ought have teach each other a lesson da guy din nan, I don't even care about d securities there..." Khadijah dai sai kallonsa take ganin how serious he was, Juyowa yyi ya kalleta tayi saurin dauke kanta, murya can kasa yace "It's because of you khadijah, don ke na kyalesa da mun yi karamin exercise a wajen nan" ta tabe baki tace "Ni dai babu ruwana" yayi murmushi da ya bayyana dimples dinsa yace "Billah ke kuwa ke da ruwa baby" kallonsa tayi da sauri, ya tsuke fuska kamar ba shi ya fada ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, tayi murmushi tana ci gaba da kallon waje, suna isa station suka samu jirgin kasa mai xuwa Kaduna, Khaleel ya yankar masu ticket, sai da jirgin ya tashi khadijah ta kallesa tace "Are you a Nigerian" kallonta yyi, ta sauke idonta, yyi murmushi yace "Sure, A Nigerian... From Kaduna also, why do you ask, ko ban yi kama da ku ba ne" bata ce komai ba, shima bai ce komai ba, bayan few hours suka isa station din train dake kaduna, Napep suka dauka da xai kai su har gida, Yace "Do I have to accompany you har kofar gida" Khadijah ta kallesa sannan ta sa mai Napep ya tsaya tace "Sauka toh ka hau wani adai daitan ka tafi gidan ku" wara ido yyi yace "Like serious??" Ta langwabar da kai tace "Sure" murmushi yyi ya sauka yace "Ohk then" tace "Yeah, thanks" daga haka ta sa mai Napep din ya wuce khaleel ya bi su da kallo. Khadijah na isa gida ta sauka ta bude Jakarta, tunawa tayi ba kudi wajenta ta basa hakuri tace bari ta amso a ciki sannan ta shiga gida, sudais da shureim ne parlor suna kallon cartoon, suna ganinta suka mike a guje suka yi kanta suna mata oyoyo ta rungumesu gaba daya cike da murnan ganin yan biyunta, Umma dake kitchen ta fito da mamaki tana kallonta, da kyar ta yakice yaran a jikinta ta nufi Umma ta rungumeta tace "Ummata na dawo" Umma na kallonta tace "What happened Khadijah??" Ta marairaice tace "Umma ina missing din ku ne na taho fa" Umma ta hade rai tace "Kina da hankali kuwa, kamar warce xata taho daga kano, yaushe kika koma da har xaki taho yanxu" shiru ta yi bata ce komai ba, Umma ta saki baki tana kallonta a mamaki, juyawa khadijah tayi ta nufi jakar Umma dake ajiye parlorn ta bude ta fiddo kudi tace "Umma bari in kai ma mai adai daita" daga haka ta fita ta kai ma sa kudin sa twins dinta na rike da ita, suna dawowa parlor duk suka haye kanta Shureim yace "Anty ina wannan uncle din nan dake UK, did he tell you to greet us?" Khadijah tayi murmushi tace "Sure sweetheart" Sudais yace "Anty is he also from Nigeria, I like him" Umma dake kallonsu tace "Wani uncle suke fadi?" Khadijah ta saci kallonta tace "Neighbor dina ne fa Umma" Umma tace "Ba mace bace kwanaki da muka je?" Khadijah tace "Ayya, Nancy ai ta tashi" Shiru Umma tayi kafin tace "Toh dai a kula, Allah ya ci gaba da tsare ku" A hankali khadijah tace "Ameen" Umma tace "Toh don me wai baxa ku xauna tare da Vanessa ba?" Khadijah tace "Umma am nt comfortable a gidanta ne" Umma tace "You have no choice, bana son xaman ki gida daya da namiji" da sauri khadijah ta kalleta, murmushi tayi tace "Umma he is a Nigerian, kuma I think bahaushe" Umma tace "So?" Shiru Khadijah tayi, Dai dai nan wayar dake jakarta ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo tunawa da tayi wayar khaleel ne, shiru ta yi tana kallon number kafin ta daga, muryarsa taji yace "Are you home?" Ta saci kallon Umma Kafin ta mike tace "Uhn" daga haka ta wuce daki yaranta suka bi bayanta Umma ta bi su da kallo.
Flight Aliyu ya bi ya taho kaduna, Ji yayi gaba daya ba wani sauran damuwa a tare da shi, lkci lkci sai yyi murmushi, har ya isa gida a taxi tunanin Khadijah yake, he is just happy seeing her today, bayan ya sauka taxi mamakin me ake yi a gidan ya dinga yi ganin mutane da manyan motoci har su Usman da Sanusi shadda ce sabuwa jikinsu, suna ganinsa suka washe baki suna masa sannu da dawowa, ya amsa gaisuwarsu ya entrance din gidan, ganin takalma da yawa alamar mutane ne sosai parlorn ya xaga ta baya, iklima ce bakin tap a durkushe tana kwarara amai, ya karasa yana kallonta ganin uban kunshin da aka mata ga kitso an yaryara mata a kai, yace "Baki da lafiya ne?" Jin muryarsa ta dago da sauri, lkci daya ta mayar da kanta ta sunkuyar, tana maida numfashi da kyar tace "Sannu da dawowa yaya Aliyu" bai damu da ya amsa ba yace "Me ake yi a gidan nan?" Shiru tayi da farko kafin tace "Aurenmu" Few seconds yyi amfani da wajen apprehending abinda ta fada, cike da confusion yace "Aurenmu? Aurenmu da wa?" Still bata kallesa ba tace "Ni da kai" bude baki yyi yana kallonta dai dai fitowar Anty khadijah tayi wani shegen haske ta xama katuwar gaske, tana ganinsa ta saki guda tace "Saukar yaushe ango?" Aliyu na xaro ido yace "Anty ban gane ba, ango kuma?" Anty khadijah na taunar cingam da ya cika waje da kara tace "Tafi Anty fati na daki xata maka bayani yanda xaka gane my son" daga haka ta nufi 'yar ta tace "Ki taso mu je, mai make up din ta gaji da jira" janta tayi suka Wuce ciki suka bar Aliyu tsaye baki bude, har lkcn shi dai bai fahimci komai ba. Wucewa ciki yyi direct ya tafi sama Dakin Mumy ba tare da ya kula da mutanen dake parlor ba, ita da frnds dinta sai mahaifiyar Abbansa da suke kira da yaya ne xaune dakin, yyi hankalin gaishesu kafin yace "Mumy I don't get what's happening in this house" Yaya tace "Bikin ku ake yi da 'yar uwar ka" Aliyu ya yo waje da ido yace "Wace yar uwar tawa?" Yaya tace "Iklima, Allah bai yi da Hanan ba" Wani kallo Aliyu ya dinga yi mata kafin yace "Allah ya kiyaye, wace iklimar? Iklima da ta gagari kowa gidan nan xa a makala min, No Mumy I have never failed you but... No mum me yasa xaki min xabin da xai cutar da ni, mumy kema kinsan iklima ta fi karfina, Mumy ki rufa min asiri..." Tsawa Mumy tayi masa ta mike tana masa wani mugun kallo tace "Get out Abuturrab, idan an kai ma iklima gidan ka kayi gunduwa gunduwa da namanta ko kuma ka koro mana ita, fita nace" Juyawa Aliyu yyi ya fice daga dakin, Yaya tace "Fatima, da gaske yarinyar ta gagari kowa? Ni dai an san ba saninta nayi ba, kar ku cutar min jika" Mumy ta hade rai tace "Yaya yar yar uwata ce uwa daya uba daya fa" tana fadin haka ta fita dakin, kawayenta suka bi ta da kallo.
Washegari da yamma khadijah na xaune parlor tare Umma da Nanny dake yankan alaiyahu, reading material dinta ne hannunta tana dubawa, Umma tace "Wai da wa su sudais ke waya haka ne tun daxu Khadijah?" Khadijah ta dago kanta tana kallonta a hankli tace "Umma wani ne" Umma tace "A ina kika san sa? Ko in ce a ina suka san sa" Murmushi kawai khadijah tayi bata dai ce komai ba, jin little sudais na kiranta ta juya tana kallon direction din dakin sai ga shi tare da d'an uwansa, wayar hannunsa ya mika mata yace "Uncle yace we shud hand over the phone to you" Khadijah ta amshi wayar tana satan kallon Umma dake kallonsu ta mike ta wuce daki, rufe kofar dakin tayi ta xauna gefen gado ta kai wayar kunne tace "Yes? Ina ji" Yace "Yea I knw kina ji, can I come over to see d boys now?" Shiru Khadijah tayi tana kallon agogo kafin tace "Xan gaya ma Umma tukun" yace "Alryt then, I will be waiting for ur call" a hankali tace "Tohm" daga haka ya katse wayar, tunanin me xata ce ma Umma ta dinga yi kafin ta mike ta fita, xauna gefen kujera tayi murya can kasa tace "Umma someone is coming over now" Umma ta daga kai ta kalleta tace