Showing 174001 words to 177000 words out of 234058 words

Chapter 59 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17043

suka xauna su biyun, Maryam tace "Sun xo hutu ne nan da kanwarta shine na shigo da ita taga Cambridge" Deejah na kallon Maryam tace "Khadijah tana min kama da Safeenah, ko ke baki gani ba" Maryam ta kalli Khadijah da kyau, sai kuma tayi dariya tace "Suna dai yanayi ba kama ba, and the nose..." Deejah tace "Exactly, dama Ammi xata ganta cewa xata yi Safeenah ce" ita dai Khadijah bata ce komai ba banda murmushin da take yi, haka kawai taji tana son Deejah.... drinks da snack Maryam ta sa a kawo masu su uku, Maryam na shan drink din gabanta tace "Deejah wai me yasa jawahir ta ki biyo mu?" Khadijah ta daga kai tana kallonsu, Deejah ta tabe baki tace "Kilan kar su hadu da Dr Ayman" Maryam tace "Tab, Ayman sau biyu yake shigowa makarantar nan a sati, Mondays and Thursdays, I think ranakun yake nasa karatun" Maryam ta kalli Khadijah tace "Kingakiwa neighbor dinsa ce Khadijah fa" Deejah ta kalli Khadijah da sauri tace "Haba dai" Maryam tayi dariya tace "Wlh, ranan da naje gidanta tare da frnds dinmu na gan sa, yace min nan yake" Deejah tace "Wani anguwa kenan?" Maryam ta fada mata anguwar tana cin snack din hannunta, Deejah tace "Ayya, daxu dai naji da suka yi waya jawahir ta bashi address yace xai je anjima da yamma" Maryam tace "Gidan mu?" Deejah tace "Sure" Maryam tace "Ohk ai gwara dai ya je" Khadijah ta mike tana murmushi tace "Maryam xan shiga lectures yanxu" Maryam tace "Haba to baki dau snack din ba ai da drink" Khadija ta kirkiri murmushi ta dauka tace "Toh nagode" daga haka ta bar cafteria din bayan tayi ma Deejah ma sallama, Deejah ta bi ga da ido, kafin ta kalli Maryam tace "Maryam joke apart wllh kamar Safeenah, idan kin lura har da Maimoon ma suna yanayi, Maryam tace "A coincident" wani gun Khadija ta tafi ta xauna don sun cika mata kunne da surutu ne gaskiyar magana. Tana ta xaune nan har khaleel ya kirata bayan kusan awa daya, tana ta kallon Kiran kafin ta daga yace "Are you done with lectures Khadijah?" Girgixa kai tayi tace "No, idan na gama xan taho gida, kawai ka tafi" yace "Karfe nawa xa ku gama?" Turo baki tayi da kamar baxa tace komai ba sai kuma tace "Anjima" yace "Toh Ina jiran ki" daga haka ya katse wayar. Karfe hudu saura Khadijah ta isa gun da Khaleel ke jiran ta, fuskarta daure ta bude motar a hankali ta shiga, yana kallonta yace "Ya lectures?" Kamar ana tilastata tace "Fyn" sai bayan da suka bar cikin makarantar yace "Wa ya bata maki rai?" Shiru tayi bata ce komai ba, bai sake cewa komai ba har ya isa schl din Shureim ya fita ya daukosa ya dawo sannan suka dau hanyar gida, a waje yyi parking yana kallon Khadijah da ta bude motar ta fita, Shureim ma ya fito, yace "Am going somewhere now, sai na dawo" Khadija ta d'an buda ido tana kallonsa tace "Gun jawahir din ne somewhere??" Kallonta ya dinga yi da mamaki, ta tabe baki tace "Wai somewhere...." daga haka ta kama hannun Shureim suka wuce ciki, shafa kansa yayi ya tada motar yayi reverse ya bar wajen. Da daddare Khadijah na parlor aka danna bell, ta mike ta isa gun kofar tace "who is there" yace "Somebody" bude kofar tayi tana kallonsa ya mika mata ledan hannunsa yace "Ki ba Shureim?" Bata karbi ledan ba tace "Yayi Bacci" yace "Toh ki ajiye masa" Bata yarda ta kallesa ba ta amshi ledan daga haka ta rufe kofarta. Washegari da sassafe Khadija ta fito apartment dinta tare da Shureim da tayi ma Shirin makaranta, ganin waje xa su fita Shureim yace "Anty baxa mu jira uncle ba yau" hararansa tayi bata ce komai ba har suka fita ta tsayar masu da cab, sai da ta fara dropping dinsa schl sannan ta wuce nata makarantar. Tare da su Vanessa suka fito daga lectures misalin karfe sha biyu, tun daga nesa ta hangosa da wani bature suna tahowa, har ya iso inda suke xaune bai gansu ba yana magana da baturen Khadijah ta dinga kallonsa har suka wuce, still ta bi sa da ido, muryar Vanessa ne ya dawo da ita tana cewa su je su ci abinci, mikewa tayi a hankali suka bar wajen xuwa cafterian da suka saba xuwa, xaune ta ga Aliyu da Baturen a ciki, suna shigowa kuma ya ganta, ta dauke idonta daga kallonsa bayan sun hada ido, waje daya suka xauna tare da su Vanessa, Vanessa tayi masu ordering abinda xa su ci, drink kawai Khadija ta sa aka kawo mata, duk suka gama cin abincin Vanessa ta biya bill sannan suka mike, Khadijah dai na xaune bata tashi ba, Vanessa tace "Ain't you attending the next lecture?" Khadijah tace "I will be going home soon" Tana kallon su Vanessa suka wuce, dai dai lkcn da Baturen dake tare da Aliyu ya mike shi ma ya fita, tasowa Aliyu yyi ya dawo inda take ya ja kujera ya xauna yana kallonta yace "Good afternoon" ba tare da ta kallesa ba tace "Same...." Ya shafa kansa yace "Ya Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Ohk kin gama lectures yau ne?" Girgixa kai tayi tace "Aa xan wuce gida ne" yace "Ohk, yanxu?" Sai a sannan ta kallesa tace "Soon" yace "Alryt if you are ready mu je sai in yi dropping din ki" tace "I prefer cab" yace "Ohk then," wayarsa ya mika mata yace "Sa min digit din ki anjima da yamma xan kawo maki sakon Shureim or I give Dr.. Ayman, Maryam tace min same house ku ke da shi, and I saw him a gidanmu jiya" Khadijah bata ce komai ba da farko, can dai tace "Sakon me?" Yace "Shine xan bada a kai maki ai" Ta Girgixa kai ta karbi wayarsa ta na sa number ta tace "You call me instead" daga haka ta mayar masa da wayarsa, ita ta fara mikewa kafin shi, ya bi bayanta suka
fita cafterian, sai da suka isa gun motarsa ya kalleta yace "Let me drop you Iman"

Bude mata motar Aliyu yayi yana kallonta, ta ki kallonsa tana dai tsaye kamar me contemplating ta shiga ko kar ya shiga, a hankali ta karasa gun motar daga karshe ta shiga ya rufe, sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar. Sai da suka hau saman titi yace "Wani anguwar kike?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Tun da Maryam ta gaya maka gidanmu daya da Dr Ayman nasan ai baxata rasa gaya maka address da house number ba" Murmushi kawai Aliyu yyi yana ci gaba da driving dinsa bai ce komai ba, sai da suka iso street din ya kalleta yace "I only know the street...." ta fada masa number din gidan, yana isa dai dai gidan yayi parking yana dubanta yace "Wani schl din Shureim ke xuwa Iman?" Sai a sannan ta kallesa tace "I don't think I have to tell you" Yana shafa kansa yace "It isn't an offense ai Iman" ta bude motar ta fita tace "Thanks for the ride" murmushi kawai yayi ta wuce ciki ya bi ta da kallo, tabe baki Khadijah tayi ganin babu motar khaleel a garage ta fiddo makullinta cikin jaka ta bude kofar ta shiga ciki, wanka tayi sannan tayi sllh ta canxa kaya ta fito parlor, xaunawa tayi tana tunanin abinda xata girka, can ya mike ta wuce kitchen din, shinkafa da miya tayi deciding tayi sanin Shureim na son sa sosai, tana parboiling shinkafa taji shigowar motar khaleel gidan, da gudu ta fita parlor ta isa gun kofa ta sa makulli sanann ta koma kitchen ta ci gaba da abinda take, bell taji an danna, ta hade rai ta tura kofar kitchen din, ba a sake dannawa ba sai ringing din wayarta dake parlor ta ji, ta bude kofar ta fita ta dau wayar tana kallon screen din, ganin khaleel ke kiranta da har xata ajiye sai kuma ta daga ta kai kunne ta ki cewa komai, yace "Bacci kike ne?" Tace "What about that?" Yace "Ohk, naga takalman ki kin bari a waje, and ki fito ku gaisa da jawahir" Wani kallo tayi kamar yana gabanta tace "For what?" A hankali yace "Am waiting Khadijah...." daga haka ya katse wayar, mamaki ne ya cikata, a kan wani dalili xa ta gaisa da jawahir, tsaki tayi xata ajiye wayar text ya shigo nasa, ya budewa tayi tana kallon content din, "Plsss" abinda ya turo mata kenan, ta turo baki sai kuma ta harari kofar, a hankali ta isa gun kofar ta bude, tsaye ta gansa shi da jawahir din, suna hada ido jawahir tace "Sannu Khadijah ya gida?" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Lafiya lau, fatan kin xo lafiya" Jawahir tace "Alhmdllh, ya hakuri?" A hankali Khadijah tace "Alhmdllh nagode" kallonta kawai khaleel yake, Jawahir tace "Dama Dr yace in taho in maki gaisuwa ne" Khadijah tace "Ayya nagode, baxa ki shigo ba" khaleel na kallon jawahir yace "Shiga sai kiyi sllh" jawahir tace "Toh bari in yi" daga haka ta shiga parlorn Khadijah, ba tare da Khadijah ta kallesa ba ta rufe kofarta fuska daure, murmushi kawai khaleel yyi yana kallon kofar. Jawahir na kan darduma xaune parlorn Khadijah ta kawo mata abinci a plate, jawahir tace "Ayya na ci abinci Khadijah, am not hungry" Khadija tace "Haba ki ci ko kadan ne" Jawahir tace "Da gaske bana jin yunwa ki bar sa kawai" juyawa kawai Khadijah tayi rike da abincin ta koma kitchen, tana fitowa jawahir ta mike tace "Toh nagode bari in je" Khadijah tace "Welcm" daga haka ta fita, tana ji ta bude apartment din khaleel ta shiga, tabe baki Khadijah tayi, ta ja tsaki ta wuce daki, mayafinta ta dauko ganin Shureim ya kusa tashi a schl, tana fita apartment dinta ta sa makulli ta nufi waje, cab ta samu ya kai ta har makarantar, Rungume ta Shureim yayi bayan ya fito daga cikin makarantar yana kallonta yace "Anty me yasa uncle bai xo ba" Khadijah ta hade rai tace "Don't ask me that again" daga haka ta kama hannunsa suka shiga cab din, suna isa gida ta biya mai cab din ta wuce ciki tana rike da hannunsa, sai kallon kofar khaleel take ta tabe baki ta bude kofarta ta shiga parlor da Shureim, makulli ta sa ma kofar, ta Shiga bedroom da shi ta cire masa uniform, tayi masa wanka ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi sanan ta sa yayi sllh, suka fito, a plate daya ta xuba masu abincin, tana ci a hankali tana kallonsa, muryarsa taji yace "Anty yaushe Sudais xai dawo? Umma tace min after one month, kuma ai one month yayi ai koh?" Khadijah ta sauke idonta daga kallonsa tana ci gaba da cin abincinta tace "Nima ban sani ba, sai dai anjima idan Umma ta kira ka tambayeta" ya langwabar da kai yace "Ohk" kallon wayarta dake ring tayi taga sabon number ke kiranta, ta dauka ya kai kunne, muryar Aliyu taji yace "Iman" a hankali tace "Na'am" yace "Fito ki amshi sakon Shureim din" kallon Shureim tayi tace "Ohk" daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon Shureim tace "Mu je ka rakani Shureim" ya tashi ta dauko plate ta rufe abincin, ta dau tissue ta goge masa bakinsa sannan ta dauko masa takalmansa ya sa suka fita, ba dai dai kofar gidan yayi parking ba, Khadijah na rike da hannun Shureim ta tsallaka xuwa side din da yake, daga cikin motar Aliyu ke kallonsu ko kiftawa babu har suka iso dai dai inda yayi parking, a hankali ya bude motarsa, Shureim na ganinsa ya nufe sa da gudu cike da murnar ganinsa Aliyu ya daga sa ya rungume sa ya lumshe ido, cike jin dadi shureim yace "Uncle ka kai ni wajen mama plss" Aliyu ya dago kansa yana kallonsa yayi pecking goshinsa yace "Mama tana Nigeria ai, idan kun yi hutu sai in kai ka" Shureim yace "Uncle plss ka tafi da ni" Aliyu ya kalli Khadijah dake wasa da ring din hannunta, a hankali yace "Thanks for coming out Khadijah" Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, jin bata ce komai ba ya bude bayan motar ya fiddo babban leda, Shureim yace "Uncle Anty ta bani irin wannan chocolate da kake bani da Sudais..." Aliyu ya wara ido yace "Da gaske?" Yace "Yes uncle" ya kalli Khadijah ya langwabar da kai yace "Toh Anty ki bari muje in siyo masa irin chocolates din, sai mu dawo yanxu" Khadijah bata ce komai ba, Aliyu yayi kasa da murya yace "Ko xa ki raka mu?" Girgixa kai tayi tace "No way" daga haka ta tsallaka ta wuce ciki abun ta, Aliyu ya bi ta da kallo kafin yayi murmushi ya xaga ya bude front seat ya xaunar da Shureim, ya dawo ya shiga driver seat ya tada motar ya bar street din. Khadijah na dai dai apartment dinta khaleel ya bude motar ya fito rike da makulin motarsa, ganinta yace "Let me go pick Shureim, na sha'afa wllh" a takaice tace "You don't worry na dauko sa, Ni ban sha'afa ba" daga haka ta Shiga ta rufe kofarta, ya fi minti daya a tsaye kafin ya koma nasa apartment din. Shopping mall din da Aliyu ya kai Shureim kusa da gidan kanwar Abbansa yake, don haka yana gama masa shopping ya shiga gidan tare da Shureim, Tasowa Maryam dake xaune parlor da Deejah tayi ganinsa ta tafi da sauri dau yaron ta rungumesa tace "Waow yau ga Shureim a gidanmu, Yaya Aliyu a ina ka samo mana shi? Jiya kuwa muka hadu da mum dinsa a cafteria a schl" Maryam ta kalli Deejah dake parlorn tana kallon Shureim da expression na Waow a fuskarta tace "Kin tuna warce muka gani a cafteria jiya?" Deejah ta xaro ido tace "Wai Khadijahr nan da nace maki suna kama da Safeenah??" Maryam tace "Yauwa ita" da mamaki Deejah tace "Kar ki ce min ita ta haifi yaron nan?" Maryam tayi dariya tace "Yaronta ne mana, yan biyu ne ma, daya ya rasu" lkci daya jikin Deejah yayi sanyi ta mike tace "Allah sarki" Aliyu dai bai tanka su ba ya wuce sama bayan ya amshi Shureim hannun Maryam don kai ma Antyn sa shi, Deejah ta bi su da kallo murya can kasa tace "but naga yaron na kama da cousin din naki ai, I mean sosai fa" Murmushi kawai Maryam tayi sai dai bata ce komai ba, bude kofa aka yi sai ga jawahir ta shigo, wurgar da takalman kafar tayi, ta jefar da jakar hannunta kan kujera ta xauna, Deejah dake ta kallonta tace "Ke kuma meye haka? me ya faru?" A fusace ta fara magana tace "Wllh Anty deejah na gaji da Ayman, abinda yake min ya fara isata, am just tired" Maryam ta xauna kusa da ita tace "Toh fah, me kuma ya hada ku?" Mikewa Jawahir tayi rai bace tace "Don rainin hankali sai yayi ta wani hada ni da yarinya da ban san meye tsakaninsu ba, I really want to know wacece yarinyar nan, sanann ta wani dinga daga min hanci tana amsa min da kyar kamar dole.... Da yaje Nigeria gaba daya lkcn sa ita yayi dedicating ma, ashe ma gidansu daya a nan ban sani ba sai daxu da ya fita yake gaya min, Ni kuma abinda yasa ma na sake ma yarinyar fuska tun farkon da muka hadu a Nigeria naga tana min yanayi da Safeenah ne, ban da haka tayi kadan in ganta da saurayina in raga mata, sannan ni a tunani na matar aure ce don ina ganin yaran nan nasan nata ne but now I am totally confuse...."
Deejah ta kamo hannunta a hankali tace "Kilan it's not what u are thinking lil sis, may be they are just frnds and neighbors, Kar ki bari shaidan ya ci galaba a kan ki, na kuma san ki da hakuri sosai jawahir so meye nasa wannan a ran ki?" Kamar xata yi kuka tace "Anty da kyar fa take amsa min magana idan na mata, kamar ma haushi na take ji shi kuma sai yayi ta sa ni in mata magana, to idan ba budurwarsa bace ita me yasa xata dinga haka" Deejah ta sauke ajiyar xuciya tace "But ni dai she was very free with me da muka hadu a cafteria jiya" Jawahir ta jinginar da kanta jikin kujera cike da damuwa bata ce komai ba, tausayinta Deejah ta dinga ji, Maryam dai na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, mikewa Jawahir tayi ta dau jakarta ta wuce sama, Xaunawa Maryam tayi, Deejah na kallonta tace "Maryam ko dai budurwar Ayman ce Khadijah kar ki boye min?" Maryam ta bude ido tace "A'a gaskiya ban sani ba, ni ban ma taba ganinsu tare ba ko a schl" Tare Aliyu ya sakko da Hajiya Mariya dake rike da Shureim, shi kuma yana rike da ledan na lotion da turaren yara da small mum din tasa ta ba Shureim, Maryam na kallonsu tace "Ya Aliyu dama ba kwana xai yi ba" Aliyu ya kalleta yace "Aa" Hajiya Mariya ta xauna kan kujera tana kallon Shureim dake gabanta tace "Ka gaida mumy ka ji boy?" Ya wara idanuwansa irin na Aliyu yace "Mumy ai tana can Nigeria, Anty xan gaida maki" Murmushi Hajiya Mariya tayi tana shafa kansa tace "Toh ka gayar min da Anty son" Aliyu ta kalla tace "Toh yaushe Antyn xata xo ta gaisheni" Aliyu yyi yar dariya yace "Ai Antyn nan sai a hankali ba xuwa xata yi ba" a hankali Hajiya Mariya tace "Kar ka damu, Allah xai dai dai ta ku ko don albarkacin yaron nan" murmushi kawai Aliyu yyi bai ce komai ba ya kama hannun Shureim xa su fita yace "Toh bari in mayar da shi mum, it's getting late" Shureim ya daga ma Hajiya Mariya da ta bi sa da kallo ganin sak mahaifinsa yana daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login