Showing 219001 words to 222000 words out of 234058 words

Chapter 74 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17042

Khadijah tace "Toh iklima fah?" Yace "We will get her something idan mun fito" Bata ce komai ba ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da driving. karfe sha daya saura suka isa asbitin da Anty khadijah take a Zaria, Aliyu na gama parking gaban khadijah ya dinga faduwa, ga mugun fargabar da ya ziyarce ta, Aliyu na lura da ita bayan sun fito ya dawo gefenta a hankali yace "You need not to be afraid of anything Iman, relax ur mind, or you stay behind, baxa mu dade ba xamu fito" Ta girgixa kai tace "A'a xan shiga" daga haka ta bude bayan motar ta fiddo fruits din shi kuma yana rike da hannun Shureim suka shiga babban asibitin, har ward din da Anty khadijah take suka tafi, Aliyu ya bude kofar a hankali hade da sallama, shi ya fara shiga tare da Shureim sanann khadijah dake makale a bayansa, ta dade bata yi fargaba irin na lokacin ba, Baby ce xaune ward din tana xuba mata abinci, daga one side kuma Barrister Sudais ne yana xaune saman kujera rike da makullin mota, da alamar dai lokacin suka xo su ma, Aliyu ya dinga kallon Anty khadijah dake kan gado....

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

Mikewa Sudais yyi yana murmushi ganin su, Aliyu ya karasa gun sa shi ma murmushin dauke fuskarsa ya basa hannu suka gaisa, Sudais ya duka yana kallon Shureim yace "How are you son?" Shureim ya washe masa hakora yace "Fine Uncle" Khadijah dai har sannan bata dago kanta ba gabanta sai faduwa yake, Sudais ya dago yana kallonta yace "Good morning Amira" sai a sannan ta kallesa tayi murmushi a sanyaye tace "Ina kwana Barrister" yace "Lafiya lau, ya gida" a hankali tace "Alhmdllh" a karo na farko ta kalli direction din da Anty khadijah ke kwance, ita ma kallonsu kawai take, duk tayi baki ga ciki 6aro 6aro ya fito, khadijah bata ganeta da farko ba ta dinga kallonta babu kiftawa, gaba daya Anty khadijah ta canxa kamar ba Anty khadijahr da ta sani yar gayu fara ba, Aliyu ya karasa har kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Sannu Anty, ya jikin?" Maimakon ta basa amsa sai ta fashe da matsanancin kuka ta dafe kanta, ya duka kusa da ita cikin sanyin murya yace "Haba Anty, kuka kuma? There is no need for that, in sha Allah xa ki samu lafiya soon, kiyi hakuri...." Shi dai Sudais kallonta kawai yake daga inda yake a tsaye, a xuciyarsa kuwa tunani yake anya ma da gaske kanwar mahaifiyar Aliyu ce ba kawai kara ake yi ba, shi bai ma wani ga resemblance ba, Khadijah ta sunkuyar da kanta hawayen da ya taru idonta ganin condition din Anty khadijah suka xubo mata, Anty khadijah na girgixa kai cikin kuka tace "Kaico na... kaico... don Allah ku rufa min asiri ku yafe min Aliyu, ku yafe min ko xan samu saukin abinda nake ji kullum, ku yafe min kar in....." Katse ta yayi da sauri yace "Anty ni baki min komai ba na sha gaya maki, idan ma kinyi wllh na yafe maki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki daya, don Allah ki daina cewa haka, Allah xai baki lafiya albarkacin annabi Muhammad S.A.W" kuka take yi sosai tace "Aliyu nasan idan ka san gafarar da nake nema gun ka baxa ka yafe min ba, ba lallai ka yafe min ba coz i don't deserve it, ni din muguwa ce, na cuce ku, na ci amanar yayata, wllh sharrin shaidan ne ba yin kai na bane, ga sakayya tun a duniya Allah ya maku, ashe dama mugunta na komawa mai shi....." mikewa Aliyu yyi bai sake ce mata komai ba don ji yayi har xuciyarsa ya karaya, Ashe tana sane mugunta take yi dama, cikin magiya da kuka tace "Aliyu don girman Allah, don xumuncin dake tsakanina da mahaifiyar ka ka yafe min abinda nayi maku da khadijah...." Aliyu na kallonta ya dake duk da yasan sauran xancen yace "Me kika yi mana ni da ita Anty?" Tana shessheka, fuskarta caba caba da hawaye tace "Wllh ni ce nayi asiri na xuba lipton din da baiwar Allahn nan ta kai maka ranan ka sha, Kuma na kwashi yaran duk muka bar gidan, na bar ku daga kai sai ita, ni ce silar abinda ya faru tsakanin ku, ni ce sillar lalata ta da kayi" shi dai Aliyu bai ce komai ba, sai dai har wani tafarfasa xuciyarsa yake duk da ya riga ya gama jin ranan da take waya, khadijah da Sudais dai ta bari cikin shock din xancenta, Baby ta mike ta kama hannun Shureim dake ta kallon Anty khadijah ta fice daga ward din, Anty khadijah ta kara rushewa da kuka tace "Wllh sharrin shaidan ne la'ananne, shi ya sa min tsanar ta khadijah, shi ya asasa min k'in ta a xuciya, don duk xamanta gidan bata taba min komai da ya wuce biyayya da girmamawa, abinda yasa na aikata abinda nayi ina tsoron kar wataran ka ce kana sonta da aure don naga yanda kake tausayinta kuma kake damuwa kan lamarinta, gashi naga yanda Mumy ma ke sonta, shi yasa nayi duk haka... ban mance ranan da suka dawo bayan ta bar gidan da wancan bawan Allahn ba wai tana dauke da cikin ka na ki saurarensu nace su tafi kuma suka tafi, toh yanxu wa gari ya waya, ka lalata mata rayuwa ta tafi ta fuskaci kalubale iri iri wanda da alama hakan alkhairi ya xame mata, sai gashi dai bayan shekaru da dama kai din dai ka aureta, Ni kuma ga yanda nawa rayuwar ta kasance, ga 'ya ta can rai a hannun Allah, yanxu ina ji ina gani nima xan girbe abinda na shuka" ko kadan Sudais bai ji tausayinta ba sai ma kawai ji da yayi ya tsaneta, dama akwai mutane irin haka a rayuwa, the wickedness is just too harsh, khadijah dai na tsaye tamkar wanda aka dasa a gun, gaba daya jin xancen Anty khadijah ta dinga yi kamar a mafarki, lkci daya ranan da ta je kai ma Aliyu Lipton a daki ya fado mata, irin yanda ya dinga cewa ta tafi da yanayinsa a lokacin ya dawo mata fresh a memory dinta, bata manta ba har saloon yace ta tafi sanusi ya kai ta amma saboda tausayin halin da ta gansa ta ki tafiya, ashe duk asiri ne dama, sai a sannan ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga ward din, Anty khadijah ta dinga kuka tace "Aliyu nasan ita ba lallai ta yafe min ba idan kai ka yafe min... Nasan da wuya don na xalunce ta da yawa" Aliyu bai iya yace komai ba, Sudais ya fita ward din, bin bayan khadijah yayi ya sameta can waje tana aikin rusa kuka, Baby ma na nesa da ita amma bata samu courage din xuwa inda take ba, Sudais na kallonta a hankali yace "Amira" juyowa tayi tana kallonsa hawaye wasu na bin wasu, yace "Kiyi hakuri, duk abubuwan da take fada anyi su an wuce ya kuma xama passed tense, this is ur new life... Don't allow ur past to spoil ur happiness, kin dai ji da kunnen ki kuma kin tabbatar ba yin kan Aliyu bane, ba laifinsa bane, ba halinsa bane, babu wanda ya tambayeta kuma babu wanda ya matsi bakinta amma sanin cewar hakkin ku ke bibiyar ta shi yasa ta fallasa kanta, don haka just forgive her and life moves on, gashi ita ma ai tana reaping shukar da tayi, yanda kika haifi yara out of wedlock ita ma gashi haka xata haifa, gwara ke naki yaran masu gata ne, ita fa, kilan ba lallai tasan uban cikin ba, sannan ga karaya har kafa biyu, da wuya kuma kafufuwanta su dawo dai dai ba fatan hakan na mata ba, shi yasa idan mutum xai gina ramin mugunta yasan size din da xai gina, let bygone be bygone Amira, ki koma yanxu kice ke kin yafe mata, sai ki ga ta dalilin hakan kila ta samu wani saukin... " Kai kawai khadijah ke gyada masa hawaye na sakko mata duk jikinta yyi sanyi, yace "Mu je" ba musu ta bi bayansa har suka koma ward din, amma ta kasa karasawa gadon tana daga inda take a tsaye cikin rawar murya tace "Anty ni na yafe maki,
Allah ya baki lafiya ya kuma yafe mana gaba daya" kallonta kawai Anty khadijah take hawaye na sakko mata, sai a sannan wani tausayinta ya rufe khadijah, ita ma hawayen ya dinga sakko mata, ta isa har bakin gadon ta kamo hannunta cikin rawar murya tace "Na yafe maki, kema ki yafe min for making you go the wrong way, don nasan da ban je gidan ba baxa ki jefa kanki a halaka ba, Allah ya baki lafiya ya tashi kafadun ki Anty" cikin rawar murya Anty khadijah tace "Amin Nagode, Allah ya baku xaman lafiya da xuri'a dayyaba, ya kauda duk wata fitina tsakaninku, I wish Allah xai bar min rai na inyi witnessing din haka, amma ina jin kamar mutuwa xan yi, Alhmdllh naji dadi da na sauke wannan nauyin a kai na don kullum da shi nake kwana nake tashi, ban san ta ina xan fara ba, Allah ya yafe mana baki daya kuma ya shiryi masu xuciya irin tawa" Khadijah ta kasa amsa mata sai kuka kawai take, Aliyu yace "Ameen, baxa ki mutu ba sai lokacin ki yayi Anty" Ita dai bata ce komai ba sai kukan takaici da danasani da take yi, ganin kukan da khadijah take, Anty khadijah tace "Ku tafi Aliyu kar in bata maku mood, Allah maku albarka, ya kuma kaddara saduwar mu" Yace "Ameen mun gode, xan dawo nan da kwana biyu" tace "Allah ya kai mu nagode" Gun Barrister ya nufa yana kallonsa yace "xa mu koma Barrister, Allah ya bada lada" Barrister yyi murmushi yace "Ameen, Allah kai ku gida lafiya" Dawowa yyi ya kama hannun khadijah da kamar daman jiran hanyar kuka take suka fita dakin bayan ta daga ma Barrister dake murmushi hannu. Baby bata iya tace masu komai ba duk jikinta yyi sanyi, Aliyu ya kama hannun Shureim dake ta kallon uwarsa da damuwa ganin kuka take yi, ya bude back seat ya sa shi a ciki, ya bude mata front seat, shiga tayi tana goge hawayen dake xubo mata, ya rufe motar yana kallon baby, a sanyaye tace "Allah ya tsare hanya yayanmu" yace "Ameen, tare ku ka xo da Barrister?" D'an murmushi tayi bata ce komai ba, yayi dariya yace "Nasan rakiya kawai yayi koh?" Dariya tayi bata ce komai ba, yana murmushi ya xaga ya shiga driver seat ya ja motar suka fita asibitin, Shureim na kallonsa kamar xai yi kuka yace "Uncle why is Anty crying?" Aliyu ya kalleta yayi murmushi yace "Allura aka mata" Shureim ya fashe da kuka yace "Me yasa uncle" parking Aliyu yyi ganin kukan da yaron yake, yana kallon khadijah yace "Kinga dama idan ba neman hanyar kuka kike ba toh ya ishe ki haka Iman" ta balla masa wani Harara tace "Toh ina ruwanka, hanyan nake nema dama" murmushi yayi, ya kwantar da murya yace....

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

Ya kwantar da murya a hankali yace "Haba my Ummu Shureim..." turo baki tayi ta dauke kai tana goge idonta, ya juya yana kallon shureim, murmushi yayi yace "Toh kaga tayi shiru kai ma kayi shiru" Kai ya gyada masa yana kallon mum dinsa, ya dawo kusa da ita a hankali yace "Anty kiyi hakuri" kallonsa tayi, tayi d'an murmushi tace "Toh na yi" komawa yayi ya xauna, Aliyu ya tada motar ya ci gaba da driving, murya can kasa yace "Mu bari next time sai mu je duba iklima, coz i really don't have the energy to start consoling you again" tace "Ni ka kai ni yanxu, ba wani next time, I will be going back to schl soon" murmushi yayi yace "Ohk then" hanyar family house din su iklima Aliyu ya dauka, bayan minti kusan sha biyar suka isa babban gidan, yayi parking a waje suka shiga, yan gidan basu wani tarbe su ba, hakan bai wani dame Aliyu ba, ita dai khadijah jikinta yayi sanyi, autar su mahaifin Iklima ta nuna masu wani kofa tace "Tana can" Aliyu ya mike yana kallon khadijah ita ma ta mike, Shureim xai tashi ya duka ya dafa shoulder dinsa a hankali yace "You wait for us here sweetheart ka ji?" Kai Shureim ya gyada masa ya koma ya xauna, Aliyu ya nufi kofar dakin khadijah ta bi bayansa gabanta na faduwa, ita kadai ce kwance dakin mai dauke da yar katifa ko leda babu, katifar ma babu xanin gado, da ganin dakin babu me shiga ciki, Ga cup da plate da spoon dinta nan gefen gadon, da kadan iklima ta fi skeleton kwance a kan gadon, khadijah ta kasa karasawa cikin dakin tana iya kokarin ganin bata fashe da kuka ba ta toshe bakinta, Aliyu ya karasa ciki yana kallonta shi ma a sanyaye, Durkusawa yayi kusa da ita a hankali yace "Sannu iklima" maimakon ta amsa masa sai hawaye, duk jikinsa yayi sanyi ya kasa cewa komai lkci daya shi ma idonsa ya kada, khadijah ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga dakin, Da kyar Iklima ta iya bude baki tace "Kace ta yafe min don Allah" Ya sauke idanuwansa kasa a hankali yace "Kina shan magani iklima?" Girgixa masa kai tayi hawaye na xuba idonta, ya fi minti biyu durkushe gabanta bai iya yace komai ba, can ya dago da kyar yace "Wa ke kula da ke?" Nan ma ta girgixa masa kai, cikin sanyi yace "Yaushe rabon ku je asibiti?" Kallonsa kawai take alamar maganar ma baxata iya ba, mikewa yayi a hankali ya fita dakin, ya kalli khadijah da ta hade kai da kujera tana kuka Shureim na kusa da ita shi ma yana kukan yana kallonta, Babu wanda yace masu komai, kowa na harkan gabansa a babban gidan, gun yayar mahaifin iklima da ya sani ya nufa a waje, tana xaune su kusan uku suna hira, ya d'an duka ya gaishe ta, ta amsa tana tambayarsa yaushe ya xo, yace "Ba mu jima ba, mama nace iklima na xuwa asibiti kuwa?" Matar tace "An kwan biyu ba aje ba tunda uban nata bai turo kudi ba kilan ya gaji shi ma, mu kuma ya bar mu da wahala" Shiru Aliyu yayi yana kallonta, can ya mike yace "Toh bari mu je yanxu" tace "Kar ma ka bata lokacin ka ko tashi bata iya yi, idan ba likitan xaka je ka gayyato a asibiti ba" Bai ce komai ba ya koma parlorn sannan ya shiga dakin da iklima take, Kallonta kawai yake yana kokarin gano stage din da cutar nata yake, bayan wani lokaci ya juya ya fita, gun khadijah ya nufa yace "Tashi mu je" Ta mike da kyar har lokacin kuka kawai take, Aliyu ya dau shureim ya rungumesa suka fita, bank ya fara tsayawa, ya kalli khadijah kafin ya bude motar ya fita xuwa gun automated teller machine, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar, wani babban pharmacy dake area din ya tafi, yana kallon khadijah da taki daina kuka yayi kasa da murya yace "Am begging you ki daina kukan nan Iman, baki kyauta ma yaron nan, even for his sake kiyi hakuri ki daina kukan" Juyawa tayi tana kallon Shureim da ke kuka bakin rai shi ma, hadiye kukanta tayi xuciyarta na mata xafi, Aliyu ya bude motar ya fita, bayan kusan minti goma ya dawo rike da ledan magani masu yawa da tsada, murmushi yayi ganin yanda Shureim yayi shiru yana kallon khadijah dake ta kukan xuci, Bata taba tunanin ganin Iklima a yanda ta ganta ba, ta ji duniyar ba bakin komai yake ba, wani store Aliyu yayi parking ya fita ya siya cartons of malts da Madara masu yawa, sai locozade boost, a booth aka xuba abubuwan da ya siya, ya shiga motar ya kalli khadijah da ta jinginar da kanta jikin kujera ta fada duniyar tunani, kamo hannunta yayi ta juya a hankali tana kallonsa, murmushi ya sakar mata yace "Kowa da irin kaddararsa, su irin tasu kenan, so you just have to pray for them, Allah ya sa mu cika da imani" wasu sabbin hawayen suka sakko idonta, ya tada motar suka bar wajen, shi kadai ya shiga dakin iklima ya ajiye magungunan gefenta yaran gidan suka dinga shigowa da abubuwan da ya siyo, Yana kallon iklima ya fiddo magungunan gaba daya ya shiga nuna mata yanda xata sha, kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan ya nuna mata yace "Idan kin ji kina jin yunwa sai ki daure ki tashi ki sha malt ko madara, idan lokacin shan maganin ki yayi ba a baki abinci ba sai ki sha malt ki sha drugs din kin ji?" a hankali ta gyada masa kai, ya fiddo dubu talatin a aljihunsa ya daga gefen katifar ya ajiye mata yace "Ki dinga aika yaran gidan su siyo maki fruits sai ki basu ko dari biyu don su dinga xuwa kin ji?" Nan ma ta gyada masa kai, ya d'an yi murmushi yace "Allah ya sauwake lil sis, idan kina son ki samu lafiya sai kin yi ta shan drugs din ki" Nan ma dai ta gyada masa kai, yace "Xan dinga xuwa duba ki always, idan kika fara samun sauki xan kai ki gun Mumy dama Abbanki ne yace a kawo ki nan" kallonsa kawai take, jikinsa yayi sanyi ganin hawayen dake sauka idonta, da kyar yace "I will be back soon" daga haka ya mike ya fita dakin ta bi sa da ido, Har suka shigo kaduna, Daga khadijah har Aliyu duk jikinsu a sanyaye yake, tuni Shureim yayi bacci bayan motar, Aliyu na gama parking ya juya yana kallon khadijah da ta bude motar ta fita, fitowa yayi shi ma ya bude back seat ya fiddo Shureim, ya rufe motar ya bi bayanta, bedroom dinsa ya shigar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login