Showing 57001 words to 60000 words out of 234058 words

Chapter 20 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17049

aure zari'a" Mumy tace "Zaria? Sai ka dawo yaushe?" Yace "Anjima in sha Allah" tace "Toh shkkn" daga haka ya wuce sama, dole Sanusi ne ya tafi da su gaba daya makarantar khadijah dai na xaune daga jikin kofar motar su Siyama ko kallonta basu yi ba sai ma hade rai da suke ta yi, ko wace bata son jikinta ya taba nata don kuwa taxara sosai ne tsakaninsu a cikin motar, a ajin baby aka sa khadijah bayan anyi mata interview, nan Sanusi ya biya duk kudin ya karbar mata form ya koma gida don a cike mata, a ranan kuma mumy tasa ya je kasuwa ya yankar mata uniform da Hijab, kyauta sai murna take tayi mata bayan sun dawo da yamma, khadijah kuwa sai washe baki take tana bata labarin yanda islamiyyar yake, can kuma kyauta ta hade rai tace "Toh ni me yasa basu sani islamiyyar ba" khadijah ta xaro ido ta rike kugunta tace "Kaji Anty mai girki bayan kin girma?" Ranan lahadi bayan sun dawo islamiyya da yamma mumy ta sa Sanusi ya kai su saloon kasancewar duk lahadi suke gyaran gashi, tun da khadijah ta ji Mumy tace aje da ita hankalinta ya tashi, ta tafi ta kwanta kamar mai bacci a dakin kyauta, kyauta ce ta shiga ta korota waje ta rufe dakinta, haka dai suka tafi saloon khadijah kamar an aiko mata mutuwa duk ta daga hankali. Siyama aka fara gyara ma gashin sannan Aneesah sai baby, aka xo kan Khadijah tuni ta fara hawaye tace "Mai saloon ni gashina bai yi dirty ba ki duba ki gani" Mai saloon din ta saki baki tace "Toh bai yi datti ba me kika xo yi" cikin rawar murya tace "Anty ce tace sai na xo" Mai saloon na ganin xata tada mata hankali tace su wuce kawai bayan an bada kudin su siyama. Shiru Mumy tayi da mamaki tana kallon khadijah dake matsar kwalla bayan sun dawo, can tace "Sai kace yarinya khadijah, yanxu gyaran gashin ne kika ki tsayawa a maki?" Anty khadijah dake xaune tana ta girgixa kafa tana tabe baki cike da masifa tace "Ai maganinki kenan Anty Fati, gwara da ta kunyata ki ba ke sodangi ba" Mumy ta kalleta tace "Toh kika san ko tana da matsalar scalp ne?" Aliyu dake xaune dinning ya bar abincin da yake ci ya fito parlorn rike da makullin motarsa yana kallon khadijah yace "Mu je saloon din" xaro ido tayi ta nufi daki da gudu tace "Anty kice masa gashina bai yi ba datti wllh, mai saloon din ma ta duba tace mu tafi" ya hade rai yace "Xan xaneki idan kika shiga dakin nan...." Anty khadijah ta mike da mugun mamaki tace "Yau nake ganin ikon Allah... to ina ruwanka Aliyu? Meye damuwanka da gyaran gashinta da rashinsa har xaka zakalkale haka" Ko saurarenta bai yi ba ya sake ce ma khadijah ta fita kar ya xo ya sameta inda take, da gayya Kyauta ta kora masa ita waje tana satan kallon Anty khadijah, Ya bi bayan su bayan yasa baby ta biyosa, Kasa cewa komai Mumy tayi ta bi su da kallo, baby ce ta xauna gaba, Khadijah ta xauna a baya tana share hawayen da ya kawo idonta, kyauta ta rufe motar har da risinawarta tana daga ma Aliyu hannu tana masa Allah ya tsare hanya. Da kyar mai saloon ta gama gyaran gashin khadijah me tsayi bana wasa ba, sae sheki yake, ga gashin da uban laushi, khadijah tayi kuka har ta gode Allah, haka kowa ya saki baki yana kallonta a saloon din, babu sunan wanda bata kira ba bayan ummanta har da Anty mai girki da Mumy, shi dai Aliyu na tsaye yana kallonsu yana son yin dariya amma bai yi ba, baby ma na tsaye kusa da shi tana kallon khadijah, ba don shi ba da babu abinda xae sa khadijah ta tsayar da kanta har mai saloon ta samu daman gyarawa, dubu uku Aliyu ya ba mai saloon din tana ta godiya, yana ma khadijah wani kallo yace "Get up my friend" make kafada tayi wasu sabbin hawayen na xubo mata, kujera ya sa mu ya xauna yace "kiyi mata kitson kawai madam" da gudu khadijah ta fice a saloon din, baby ta kyalkyale da dariya mutanen dake cikin saloon din na taya ta, khadijah dake tsaye jikin mota ta dinga leka saloon din ko matar ta biyota, yana fitowa ya dagata yyi cikin saloon din ta rirrikesa tana ihu tana basa hakuri, mai saloon dake dariya tace "Ta tuba babban yaya ayi mata hakuri" baby ta rufe baki tana dariya har da kyakyatawa, bude bayan motar yyi ya saka ta ciki ya rufe ba shiri tayi tsit kirjinta na heaving, ya harareta ta madubi yace "Xan yi maganin ki ne" Bayan sun koma gida har daki Anty khadijah ta bi Aliyu, Ta rufe kofa tana masa wani kallo tace "Aliyu akan wani dalili ka tafi da yarinyar nan saloon daxu, ban gane me hakan ke nufi ba, ka taba sanin ta ne da can ko kuwa shisshigi ne da hali irin na uwarka ya motsa? Kai ma sodangin xaka koma" Aliyu dake ta kallonta yace "Meye a ciki don na kai ta saloon Anty, Kina fa ji Mumy ce tasa ta bi su Siyama kuma ta ki yarda ayi mata, to make my mum talk less shi yasa kawai ni na kai ta da kaina kuma ba gashi ta tsaya ba" Anty khadijah tace "Eh lallai ni kake gaya ma bakar magana ko Aliyu? Babu damuwa, xan yi maganinka" daga haka ta fita, Aliyu ya tabe baki ya mike ya rufe kofar sa don a bude ta bar masa. Yau khadijah ta cika sati biyu gidansu Aliyu, babu abinda Mumy ta rage ta da shi a gidan, duk yanda ta yi da su siyama haka take mata ita ma banbancin kawai shi ne har lkcn a dakin kyauta take, kusan dai kyauta ce kadai mai aikin gidan don ko kadan kyautan ma bata takura khadijah tayi aiki sai dai fa tana nuna mata abubuwa da yawa ko kadan ne tana barinta tayi har goge gogen, ranan da khadijah ke da sati daya a gidan Anty khadijah ta tafi Abuja ganin yaranta, hakan yasa hankalin khadijah kwance har na sati biyu yanxu, Tunda baby ta ci duka gun Aliyu ko kallon banxa bata sake ma khadijah ba, sai ma note da take bata wani lokacin ta kwafar mata na boko ita dai Mumy bata ce masu kala don kuwa rubutun khadijar ma ya fi na baby kyau, har assignment khadijah na kwatanta yi ma baby, su siyama dama ba wani interacting suke da ita ba, don haka babu ruwansu da ita, A yau da ta cika sati biyu ne mumy na bedroom dinta da yamma Aliyu ya shigo, Gaisheta yyi tace "Halan ka fita nyt duty ne?" Yace "Tun three days back yanxu morning xuwa yamma nake yi" tace "Ohk, kun yi waya da Abbanku" Aliyu ya shafa kansa yace "Ehh ai gobe xai taho in sha Allah" tace "Nima haka yace min daxu" yana fiddo wayarsa a aljihu yace "Wai yaushe Anty xata dawo mumy?" Mumy tace "Toh nima dai ban sani ba wllh, amma jiya da ta kirani kamar akwai damuwa kilan su Iklima na cikin wani hali...." Yace "Toh Mumy wai me yasa iklimar baxata dawo nan gidan ba, su Ahmad maxa ne bbu damuwa sosai amma ita macen da ta dawo nan" Mumy tace "Ai ubansu baxai yarda ba ne matsalan sai dai ta taho da ita ba tare da ya sani ba" Aliyu ya girgixa kai yace "Allah ya kiyaye" mumy tace "Ameen dai" Shiru yyi bai sake cewa komai ba, Mumy tace "Ya aka yi kamar kana son yin magana koh?" Murmushi yyi don sure yasan mum dinsa ta gama karantarsa gaba daya, yana facing dinta yace "Mumy dama ba komai bane a kan Mai sunan Anty ne" tunda khadijah ta shigo gidan bai taba kiran sunanta ba saboda Anty khadijah, Mumy ta kallesa da sauri tace "What about her?" Yace "Noo, kawai mum naga da ki taimaka a sa ta a boko..." Katse sa tayi tana kallonsa da kyau tace "Ko saboda me?" Ya d'an bude ido yace "Noo Mumy naga kawai she isn't an illiterate, its just anyi depriving dinta right dinta ne, from all indications she was born with a silver spoon, you knw... it's just condition mum, ina tausayinta ne wllh, kin dai ga har coaching Baby tana kokarin yi, she is very intelligent, Allah will reward you idan kika taimaka mata mumy" murmushi mumy tayi tace "Kasan me Ali?" Ya girgixa kai da sauri yana kallonta, strictly tace "Abuturrab ko da wasa, I mean ko ba a cikin hankalinka ba, kayi making mistake din ce min kana son yarinyar nan wataran I will show u my other side, because it will and will neva be possible, that is just it" da mugun mamaki yake kallonta, a hankali yace "Sonta kuma mum?" Ta gyada kai tace "Yes" yyi shiru na few seconds kafin yace "Mai ya kawo wannan xancen mumy?" Ta hade rai tace "Kai ka kawo sa, for I see no reason har xaka damu In sa ta makaranta kai ka kawo min ita gidan?" Ya girgixa kai kawai, tace "To be careful, yes xan sa ta makarantar boko amma wllh wllh ko a mafarki ka cire ran akwai aure tsakanin ka da yarinyar nan, period" Ya kalli Mumy a hankali yace "But.. Ko saboda me" strictly Mumy tace "Hakan nake so ya kasance, or are you querying me" yace "Amma mumy ni ai ba ce maki nayi ina son ta ba, boko kadai nace ki sa ta for the sake of Allah, meye ma xai sa kiyi tunanin nan mumy, ni kuma in rasa warce xan ce ina so sai karamar yarinyar nan? Wallahil azim ban taba kawo hakan a raina ba, gaskiya I am nt happy mum" daga haka ya mike ya fita a dakin.

Ranan Monday da asuba Mumy ta shiga kitchen gun kyauta dake ta kokarin hada ma yan makaranta breakfast, cike da ladabi ta gaida Mumy, mumy ta amsa tana mata sannu da aiki sannan tace "Khadijah bata tashi ba?" Kyauta tace "Ina jin tana can tana sallah ne" kyauta ta dai fada haka ne amma in dai khadijah tasan tana can tana bacci, Mumy tace "Wai boko nake son ta fara xuwa yau..." Kyauta ta xaro ido tace "Boko Hajiya, Allah ya saka maki da alkhairi, ya kara daukaka, Allah ya biya maki bukatun ki masu kyau Hajiya, yanda kike taimako kema Allah ya ji k'an ki a nan duniya da ma lahira" Mumy da ke ta kallon kyauta tayi murmushi tace "Toh Ameen" daga haka ta juya ta wuce, kyauta ta rike ha6a baki bude murya can kasa tace "Ko ya baxawara xata dau xancen nan idan ta dawo, Ashe ko akwai karamin yaki a gidan nan" a stairs mumy ta hadu da Aliyu ya shirya xai fita aiki, tace "Da asuban xaka fita aiki?" Yyi kasa da kai ya gaisheta ta amsa tare sa cewa "How was ur nyt?" Yace "Alhmdllh" tace "Breakfast din fa?" Yace "Xan yi a office" tace "Bawan Allah ai bbu xancen yin sammakon fita aiki xaka kai khadijah makaranta anjima" Juyowa yyi ya kalleta da sauri yace "A'a ni Mumy baxan iya xuwa ba, Ba ga sanusi ba da mai aikin can su kai ta mana" kallonsa mumy ta tsaya yi, can tace "Directly ma kake ce min baxa ka iya xuwa ba koh?" Yace "Toh Mumy ni da xan fita aiki kuma wani makaranta xan kai ta, komai fa sanusi xai iya yi kin sani" Mumy bata kuma saurarensa ba tayi wucewarta sama, fuskarsa daure ya juya ya koma sama shi ma. Tun da kyauta ta tada Khadijah tayi mata albishir din xancen da Mumy tayi mata khadijah ke ta murna har da rawanta, can kyauta dake taya ta murnar ita ma ta hade rai tace "Wato ni ce dai hajiya bata so a gidan nan ba arabi ba boko, sai dai in sauke in daura in yi shara inyi wanke wanke, akwai Allah" khadijah da har xata shiga bathroom ta dawo da sauri ta yo waje da ido tace "Anty mai girki? Katuwa da ke baki gama school ba dama, me kika tsaya yi toh?" Kyauta ta dunguri hancinta tace "Ai ban kai baxawara ba da take kamar buhu" Khadijah ta wara ido tace "Ni kinsan yaushe rabon da in je school, to in gaya maki tun ina gidanmu tare da Ummata, Allah ya sa ban girma ba da shikenan yanxu ni ma baxan je ba" bata sake sauraren kyauta ba ta shiga bathroom da sauri ta rufe. Kafin karfe bakwai duk yaran gidan sun shirya kyauta ta tabbatar khadijah ma ta shirya cikin daya daga kayan da ta siyo mata a kasuwa shekaranjiya ta lafta mata uban kwalli a ido, ta shafa mata jan powderta a fuska, Da kyar khadijah ta yarda xata yi breakfast saboda excitement, duk ta kagu su wuce makarantar, shi dai Aliyu na xaune parlor hannunsa rike da mug din coffee, su siyama kuma na dinning suna breakfast, Khadijah kuma na kitchen kyauta ta shimfida mata wani xaninta a kasan tiles din kitchen din don kar kayan jikinta yayi stain, jin Driver na horn a waje Kyauta ta daga khadijah da sauri ta kwace bread din hannunta ta turata waje tana cewa "Shegiya sai ta sa sun canxa ra'ayinsu maxa tafi xa su wuce" Aliyu ya fita ya samu Driver yace "Sanusi ni xan kai su, don't worry" Har su Siyama sun fita Sanusi ya gaya masu abinda Aliyu yace, Siyama ta tabe baki hade da jingina da motar tace "Shine yana ganin mun fito baxai gaya mana ba, I don't just like this Ya Aliyu sometimes" Aneesah tace "Ni kuma ina son sa haka, ya ma fi min ya Saleem" Siyama tace "Shi yasa nake ta addu'ar ya saleem su dawo tare da Abba anjima" Motar Aliyu suka nufa, baby da fitowarta kenan ta bi bayansu, Aliyu ya wuce upstairs dakin mumy ya sameta har ta shirya xata kai khadijah makarantar da kanta, ya d'an bude ido yace "Mumy kin fa san I didn't mean it, ko baki fada ba ai xan kai ta..." Ta katse sa tace "Toh tunda Allah ya ban lafiyata ba gwara in fita in biya ma kai na bukatar dake gabana ba, Saleem will Neva look into my face yace min baxa shi ba ai, so this is just ur differences" Aliyu yayi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri Mumy, ban san ran ki xai baci ba, I am very sorry" tace "Noo ni rai na bai baci ba, kai dai da na bata ma rai xaka iya tafiya aikin ka kayi hakuri, ni da ya xame min dole xan kai ta da kai na" murmushi yayi yace "Don Allah mumy kiyi hakuri ni xan kai ta ba sai kin je ba" da kyar Aliyu ya samu ya lallaba Mumy ta hakura ta bar shi ya kai khadijah makaranta tare da Kanninsa, babu yanda bata yi ya amshi wayarta ya masu transfer din duk fees din a can makarantar ba ya ki yace xai yi da nasa kudin, da haka dai ta hakura ta kyalesa ya sakko parlor rike da makullin motarsa, makale ya tadda Khadijah jikin kofar parlor da alama su siyama dai sun korota ne, Kyauta ma na bakin kofar bayan sanusi yace mata Aliyu ne xai kai su, sai leken su siyama take tana Allah wadaran da halin baxawara da suka yi, tana ganin Aliyu tayi tsit, tayi kasa da kai tace "Sannu da fitowa yallabai" yace "Yauwa" sannan ya fita, tura khadijah tayi ta rufe kofar parlorn. Khadijah ta dinga bin Aliyu har suka isa gun motarsa, su siyama suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce na kallonsa, Yace "Wacece ta korata a cikin ku?" Da sauri baby tace "Allah ya so bani bace ba wllh yayanmu" yana kallonta yace "Toh waye?" Nuna masa su Aneesah tayi, yace "Why did u both send her away?" Aneesah tace "Toh yaya kawai ta xo gun mota ta tsaya mu da makaranta xa mu" yace "Ita ma makarantar ae xata" Da sauri siyama tace "What??? Wani makarantar?" Baby tace "Na mu mana, ai Mumy ta gaya min da na yi wanka a dakinta daxu" Siyama da ta rikice tace "Yaya kamar ya makarantar mu, ni yaya ko xa a sa ta makaranta let it not be ours, they are a lot of schools out there don Allah a kai ta" Har da guntun hawayenta, Aneesah ma duk hankalinta ya tashi, ita dai khadijah na daga gefe tana kallonsu, yace "Alryt idan na kai ta makarantar taku kada ku bari ayi admitting dinta" daga haka yace baby ta shiga mota, baby ta shiga gaba ya bude back seat yana kallon khadijah yace "Get in" da sauri ta shiga motar ya rufe ya bude driver seat ya shiga yana kallonsu siyama yace "Ku je sanusi ya kai ku coz xan iya maku abinda ke raina idan ku ka shiga motar nan, mind u kada warce ko da wasa ta sake shiga cikin gidan can, it's either ku je sanusi ya kai ku makaranta or you remain here till 4" daga haka yayi warming motarsa mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, siyama ta fashe da kukan takaici Aneesah na taya ta. Essence int'l school, abinda khadijah ke ta nanatawa kenan a xuciyarta tun shigiwarsu cikin babban makarantar, baby ta bude kofa ta fita, ya juya yana kallon khadijah, xaro ido yyi yana kallon nata idon yace "Meye wnn din a idon ki?" Ta buda hannu tace "Anty mai girki ce ta sa min kwalli" tsaki yyi ya Ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace "Common goge wannan bakin abin da ta goga maki a ido kamar herbalist" khadijah ta kyalkyale da dariya ta karba tace "Herbalist kuma" bai tanka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login