Showing 6001 words to 9000 words out of 234058 words

Chapter 3 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

16976

Khadijah ta mata wani kallo a takaice tace "I don't knw" Matar tace "Really? And I have being Calling but I can't reach him" Khadijah da har ta bude kofar ta tace "Hard luck" daga haka ta shiga ciki sai kuma ta juyo suka hada ido da cute babyn hannun matar, kasa rufe kofar tayi a hankali tace "Or you go come back, may be later" matar tace "Am from a far place, and he knws I will be here" Khadijah ta rasa abinda xata ce, can dai ta dauke kai ta juya ba don ranta ya so ba kuma don tausayin babyn hannun matar tace "If it's ohk... u can come in and wait him" daga haka ta shiga parlor matar tace "Alryt Thank you" ta shigo parlorn ta xauna, Khadijah ta bude fridge ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye mata, matar ta d'an yi murmushi tace "I am fatima Ayman" kallonta Khadijah tayi na yan sakwanni kafin tace "Am Khadijah Muhd" Matar da ta kira kanta da fatima tace "Ohh that's nyc, from which country?" Khadijah tace "Nigeria" d'an buda ido fatima tayi tace "Tribe" Khadijah tace "Hausa Fulani" Fatima tace "Waow ashe Hausa ce ke sister" Khadijah ta kalleta tayi murmushi tace "Ehh" Fatima tace "Allah sarki, amma naji dadin haduwa da 'yar uwata daga Nigeria, na xo nan last 3 weeks but kamar baki nan" Khadijah tace "Eh naje gida ne" Fatima tace "Maa sha Allah, tare da mai gidana muke ya xo wani aiki a nan shine nace ya ajiye ni kawai mu gaisa da yayana tunda yau xa mu koma, kuma fa na sanar da shi yayan nawa xan xo amma dubi yanda ya shanya ni a waje" murmushi kawai Khadijah tayi ta amshi babyn hannun ta tana kallonta tace "Ya sunanta?" Fatima tace "Iman...." Lkci daya murmushin dake fuskar Khadijah yyi fading jikinta yayi sanyi......

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨






_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






5.....

Fatima da bata lura da yanayin da Khadijah ta shiga ba tace "But ina jin kilan ya shiga schl ne, kinsan PhD din nan sai hankali, yanxu ma idan Abban Iman ya kira dole sai dai mu wuce kawai tunda ban san lkcn da xai dawo ba" Khadijah dai bata ce komai ba ta mike a hankali ta kwantar da babyn da uwarta ta kira da Iman, ta kirki murmushi tace "Bari in shiga kitchen" daga haka ta kunna masu kayan kallo ta wuce cikin kitchen, kauda damuwar da ya so dirar mata a rai tayi, ta jingina da kitchen cabinet tana tunanin light abinda xata girka masu da baxae dau lkci ba, can dai ta fiddo Irish ta shiga ferewa, cikin minti ashirin ta gama hadadden porridge din Irish da yaji kayan hadi da hanta da nama, tuni kamshin dahuwar abincin ya kauraye ko ina na gidan, fitowa parlor ta yi fatima dake xaune tana danna wayar hannunta tace "Sannu da aiki" Murmushi Khadijah tayi tace "Thank you, hope ba ku yi fushi ba na bar ku ku kadai" Fatima tace "Ayya ba komai ke da kike aiki" Khadija ta koma kitchen tayi serving abinci a plate tasa fork ta daura kan tray da glass cup na ruwa a gefe ta fito parlorn tun kan ta ajiye fatima tace "Toh fah, ni fa a koshe nake khadijah, wlh am nt hungry bamu dade da cin abinci ba" Khadijah ta d'an canxa fuska tace "Saboda ke fa nayi girkin" fatima tace "Ayya, to ban san xai ko anjima ba amma yanxu gaskiya a koshe nake kiyi hakuri" dai dai nan aka bude kofar parlorn duk suka kalli direction din, tsaye yyi bakin kofar kamar me examining din wani abu, Khadijah da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta tayi saurin kauda kanta gabanta na faduwa, mikewa fatima tayi da fara'a da farko sai kuma ta hade rai tace "Yaya ai da sai ka ce min kar in xo baka nan, ka wani shanya ni a waje ina ta jiran ka," karsowa yyi cikin parlorn da takalmansa ba tare da ya kalleta ba bare ya tanka ta, fatima ta xaro ido tace "Ana fa sallah yaya.... Ka cire takalmin" Bai ce komai ba ya duka yana kallon Iman dake kwance saman kujera, sai a snn yyi murmushin da ya bayyana light dimples dinsa yace "She's.... growing" daga haka ya dau babyn ya manna mata kiss a cheeks dinta ya juya ya nufi kofa yana cewa "Wayata na silent I don't knw u were calling," Fatima tace "Uhn ai shikenan, ya karatun" bai tanka ta ba har ya fita, kallon Khadijah tayi tace "Nagode sosai Khadijah Allah ya saka da alkhairi" Khadijah ta kirkiri murmushin karfin hali tace "Welcm" fatima ta dau jakarta da abun daukan babynta tace "Bari in je mu gaisa" daga haka ta juya ta nufi kofa Khadijah tace "Toh abincin fa?" Fatima ta yi yar dariya tace "Toh shkkn bari dai in je da shi" dawowa tayi ta duka xata dauka ganin kayan hannunta khadijah tace "Let me help" fatima tace "Toh nagode" khadijah ta duka ta dau abincin, sai kuma tayi still tunawa da tayi hakan na nufin parlornsa xata shiga kenan?? Tuni fatima ta isa kofa, a hankali ta bi bayanta a sanyaye ba don ta so ba, fatima ta bude kofar yayan nata ta shiga da sallama, b'akin cover shoe dinsa na ajiye bakin kofa wato ita ya raina xai shigo mata parlor da takalmi, xaune suka gansa kan daya daga kujerun parlon yana rike da Iman dake 6a66aka masa dariya, kallo daya Khadijah tayi ma hadadden parlon nasa tayi saurin sunkuyar da kai gabanta na faduwa, fatima da har ta xauna tace "Ina yini yayana" yace "Ya kike" tace "Alhmdllh ya karatun" karasowa Khadijah tayi ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta dago kai ba, ya kafeta da ido, kamar ta sani kuwa ta ki kallon inda yake, fatima tace "Yaya neighbor dinka tana da kirki sosai, ka taya ni yi mata godiya" yace "Koh?" Kallonsa fatima tayi ta kasa cewa komai jin kalan tambayar da ya jefo mata, sannan tafi kowa sanin halin wan nata, hakan yasa kawai ta bude jakarta tana murmushi tace "Guess what yaya...." Ya kalli jakar bai ce komai ba dai, Envelope ta dauka ta mika masa tana yar dariya tace "3 days ago su Ummu suka ba Abban Iman ya taho da shi" Karba yyi yace "Meye a ciki?" Ta buda ido tace "Invitation card din ku mana...." Mayar mata yyi yace "So?" Tace "Aa cewa aka yi in kawo maka" yace "To mayar" Fatima tayi murmushi tace "Ko dai Jawahir din ta tura maka ne" Ya hade rai yana kallonta sai kuma ya juya yare xuwa larabci, tuni khadijah ta nufi kofa dai dai lkcn da aka bude kofar, wata black American mai kyau ta shigo parlorn tana sanye da wasu damammun kaya, ta daga masu hannu gaba daya da murmushinta tace "Hi" daga haka ta nufi bedroom, lkci daya mood din fatima ya canxa ta bi yarinyar da kallo, shi kam ya dauke kai, Khadijah ta saci kallonsa suka hada ido, tabe baki tayi ta dauke kai ta juya ta bude kofar ta fice abin ta a ranta tace Allah wadaran naka ya lalace, ko kunya bai ji ba, Tana komawa apartment dinta ta shiga gyare gyaren ko ina na gidan, duk wani abu da tasan xai iya samun matsala a fridge duk ta tattara su gu daya don tafiya da su gidan Vanessa, kafin la'asar ta gama komai tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta shirya cikin kananun kaya ta daura kimono a kai ta yafa gyale a kanta xata fito parlor aka danna bell, karasawa tayi ta tsaya bakin kofar tace "Who's there?" Muryar fatima taji tace "Ni ce Khadijah, dama nace in maki sallama xan wuce" Khadijah ta bude kofar tace "Ayya, har xa ku tafi" fatima ta kirkiri murmushi duk da Change din mood dinta tace "Wllh kuwa, Abban iman na jiran mu" Khadijah tace "Toh shkkn, Allah ya tsare hanya, ya kai ku gida lafiya" Fatima tace "Ameen ngd, tnx once more for the hospitality" murmushi kawai Khadijah tayi, aka bude kofa sai gashi ya fito rike da Iman, Fatima ta kallesa da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ya Khaleel da gaske baxa ka kai mu ba mu hau taxin kawai" a takaice yace "Ehh" ta langwabar da kai tace "Toh shkkn" majestically yyi wucewarsa waje, Khadijah ta bi sa da ido, fatima da ta bi sa da kallon ita ma tayi murmushi tace "Kinga da gaske taxi xai tsayar mana maimako ya ajiye mu da motarsa daga na gaya masa gaskiya...." Khadijah tayi murmushi bata dai ce komai ba, Fatima tace "Toh muje wayana na gun sa sai ki sa min digit din ki mu dinga xumunci" Khadijah ta bi bayan ta ba don ta so ba, ko da suka isa har ya tsayar da mai cab yana jiran kanwar tasa, fatima tace "Yaya idan ma fushi kake da ni kayi hakuri pls" ya kalleta bbu yabo bbu fallasa yace "Not at all, shiga ki tafi inda xa ki" tace "To bani wayar Khadijah ta sa min digit dinta" yayi kamar bai ji ba ya bude back seat yace "Shiga malama" fatima ta shiga ya mika mata yarinyarta sannan ya bata wayarta, tace "Bata sa number ba ai yaya" ya hade rai yace "Xan tura maki ta WhatsApp" rasa abinda xata ce masa tayi, ganin yanda ya hade rai tace "Toh baxa ka ba mai cab din kudi ba" yace "Bani da" yar dariya tayi tace "Kai ya khaleel ba ma haka da kai fa, kayi hakuri kar in tafi kana fushi da ni" Khadijah da ko kallonsa bata yi ba ta daga ma fatima hannu tace "Toh Allah ya tsare hanya Maman baby" daga haka ta juya da sauri ta koma ciki don bata son ta ci gaba da jin kayan takaici, tana shiga bedroom ta wuce direct ta dinga fiddo kayan da ta harhada, taje dauko na karshen taji an bude kofar parlor, still tayi na yan sakwanni sai kuma ta juya da sauri ta fito xuciyarta na bugawa.


*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

6......

*Nigeria*

Ajiye fork da knife din hannunsa yyi ya tura abincin gabansa lkci daya ya fuzar da iska ya dau tissue yana goge bakinsa ya mike ya bar dinning din, mum dinsa dake xaune parlor ta bi sa da wani kallo tace "Barin abincin kayi sbda xancen da nake maka Aliyu?" Kallonta yyi da sauri yace "Noo, not at all Mum, xan je sallama da Granny ne coz am leaving as early as possible tomorrow" daga haka ya dau makullin motarsa da ya ajiye kan Center table ya nufi kofa yace "Sae na dawo mum" tagumi mahaifiyar tasa tayi ta bi sa da kallo cike da damuwa har ya fita, ya fuzar da iska bayan ya shiga motarsa ya jinginar da kai jikin kujera hade da lumshe ido yace "Ba ta taba barin in ci abinci in koshi Mum, always with a particular complain" ya bude ido a hankali snn ya tada motar yyi horn mai gadi ya bude gate ya fita rai ba dadi, bai yi minti goma yana tafiya a Independent way ba wata 206 dake gabansa ya taka wani burki da har sai da ya kusa bugesa ba dan shi ma yyi saurin preventing hakan ba, wanda hakan kuma ya janyo motar dake bayan tasa motar ta buge sa, Kilan rudewa ya sa me 206 din ya juye kan steering wanda hakan yasa ya buge motar gefensa shi ma da karfi, everything just happened all of a sudden, lumshe ido Aliyu yyi ya bude yana kiran Allah a xuciyarsa bayan komai yyi still kamar ba ayi ba, sai a sannan ya lura da wani bike ne ya shigo ma mai 206 din yyi kkrin avoiding da ya janyo faruwan slight accident din, Aliyu ne ya fara fitowa daga motarsa daga nn kuma kowa ma ya fara fitowa, ya nufi 206 din da har driver din ya fito da sauri ya bude back seat, kukan yara ke tashi a motar, jin hakan Aliyu ya karasa da sauri gun motar, identical twins ne bayan motar da baxa su wuce shekaru biyar ba, Aliyu ya fiddo su duk biyun daga motar yana kallon yaran dake sanye da uniform din makaranta ya durkusa a hankali yace "Hey boys are you okay??" Dayan kadai ne ya gyada masa kai a tsorace, dayan kuwa banda kuka babu abinda yake yana kiran Anty, kallon yaran kawai Aliyu yake ko kiftawa bbu, muryar mutanen da ke tsaye gun kowa na fadin albarkacin bakinsa yasa shi mikewa a hankali yana shafa kansu yace "Sorry Boys, Allah ya tsare gaba" Wani mutumi ne ya dinga tambayarsu inda ke masu ciwo duk suka girgixa kai, Aliyu ya daga kai jin abinda mutumin da ke gefensa ke ce masa yana kallonsa, "Allah dai ya kiyaye gaba ka tafi da yaranka gida kawai, Allah kyauta na gaba" cewar mutumin kenan, wani mutumi ma ya sake fadin makamancin hkn, murmushi yyi yace "No, ni ban san su ba" mutumin karshe da yyi magana ya kalli yaran sannan Aliyu, kada kai yyi yace "Ikon Allah...." bude bayan motar Aliyu yyi ya shigar da yaran yana kallon Drivern yace "Ka ajiye su gida, Allah ya kiyaye gaba" godiya Drivern yyi ma mutanen wajen ya shiga motar ya tada ya hau kan titi ya bar wajen. Aliyu ya koma gun motarsa ya shiga har lkcn cute twins din na ransa, bai kuma damu da kallon da wasu suka bi sa da shi ba. A waje yyi parking ya shiga gidan grandmum dinsa da sallama bayan sun gaisa da masu gadi, wata budurwa ce da baxata wuce shekaru ashirin da daya ba kwance kan kujera dake parlon tana danna waya, sau daya ya kalleta bai sake kallon inda take ba ya wuce dakin grannynsu da suke kira da yaya, sllh ya sameta tana yi ya kalli agogo sanin Magrib bai yi ba, ya tabe baki ya dawo parlon ya xauna ko sallan me take, ba a dau lkci ba ta biyosa tace "Mijin ka xo kenan" ya gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa ya hanya, yace "Alhmdllh" ta kalli budurwar dake kan kujera tace "Ke koh Salmah kun gaisa da yayan naki" yarinyar ta gyada mata kai idonta a kan waya, ya kalleta fuskarsa daure yace "Uban wa kika gaida?" Ba ta ko kallesa ba tace "Yaya ni ki ce ya daina xagi na plss" Mikewa grandmum din tasu tayi tace "A'a ni dai gaskiya ba a gidana ba yau, ku je can gidan iyayen ku ba ruwana, kai kuma naga ai ba dole bane sai an gaisheka, ke kuma sa'an ki ne shi din da baxa ki gaishesa ba" mikewa yyi ya nufi kofa, kakar ta bi bayan sa da sauri tana cewa "Ina kuma xaka Aliyu" bai juyo ba yace "Sallama dama na xo maki gobe xan wuce Uk...." da sauri take bin sa ganin yaki tsayawa tace "Toh baxa ka tsaya ba ina ma magana" yace "Mu yi waya" bata fasa bin sa ba tana cewa "Da kai fa nake Aliyu..." juyowa yyi yace "Don Allah yayah ki rabu da ni dama sallama na xo maki kuma gashi na maki dai ko" rike ha6a tayi tace "Yo ni me ya sha min kai da sallamar ka da rashin sa, magana ce dai baxan fasa maka ba tunda ba tsoronka nake ba, baka kuma isa inji tsoron ka ba, kum maganar dai da baka so ce xan maka wato maganar aure, Aliyu sa'annin ka daga me d'an shekara biyar sai mai d'an shekara shidda kai har bakwai akwai, yanxu kai baxa kayi ma kanka fada ba kasan inda ke maka ciwo d'an nan, ga mahaifin ka ya xuba ma na mujiya ya kyaleka ya fita lamarin ka, me kake son mayar da rayuwar ka ne, idan ma lafiya ce baka da ba sai ka mana bayani ba ko ni in kai ka asibiti amma ka mayar da mu shashashai...." tsaye yake yana saurarenta sai dai bai juyo ba har ta kai karshe sannan ya juyo yana kallonta yace "Allah kawo lkci yayah" daga haka yyi ficewarsa daga gidan, ya jima xaune mota ya kasa barin anguwar, ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido a hankali ya bude cikin sanyin murya yace "Can I ever get her? Then Where?" Lkci daya idonsa ya kada ya hade kansa da steering, ya fi minti goma a haka kafin yyi karfin halin dagowa ya tada motar ya bar gun jikinsa a sanyaye, yana hawa independent way yaran daxu suka fado masa, ya d'an yi murmushi loving to see them once more and their parents. Bai yarda ya wuce gida ba a lkcn kawai ya wuce gidan abokinsa kuma amininsa Farouq, ganin Magrib tayi sai da ya fara shiga masallacin dake anguwar don gabatar da magrib bayan yayi alwala, ana idarwa kuma suka fito tare da Farouq, gaisawa suka yi Farouq yace "D'an rashin kirki kace min xaka dawo ranan kasa Madam tayi serving har da kai amma kaki dawowa, ina ta xuba ido, I called kuma you refused picking saboda kasan baka da gaskiya koh" Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace "Na ma mance me ya hanani dawowa wllh" har suka shiga gida mitan xancen Farouq yake, suka karasa har parlor, Boys din Farouq suka taho da gudu don gaida abokin dad din nasu, Aliyu ya rungumesu yana tambayar su ya school suka ce masa "Alhmdllh" Wara ido yayi yace "Toh ban ga "Baby Fiddausi ba" Ahmad yace "She's upstairs with mum" yace "Alryt maxa ku je ku ce masu Ina gaishesu" Ahmad me shekara shidda da kaninsa takwaran Aliyu suka wuce daki da sauri. Farouq dake ta kallon Aliyu yyi kasa da murya yace "Doctor...." Kallonsa Aliyu yyi da sauri, Farouq yace "I don't knw, may be am nt worth ur best..." Aliyu ya d'an bude ido yace "Ban gane ba Umar" Farouq ya girgixa kai yace "Kullum tambayata why

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login