Showing 63001 words to 66000 words out of 234058 words

Chapter 22 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17030

sun fi ni k'ima a idon ki, Anty fati dole ne sai na xama so dangi kamar ki? Me ya hada ni da 'ya yan wasu? Don Allah ki kyaleni in yi rayuwata yanda nake so, ke kije can kiyi ta kwashe kwashen mutane har sai kin kwaso warce xata fiddo ki a inuwar da kike ta tura ki rana, muna nan da ke kuma" Tashi Mumy tayi ta nufi kofa bata sake tanka ta ba, Anty Khadijah ta bi ta da harara tace "Ke so dangi... To mutanen nan su ne xasu raba ki da farin cikin ki idan ba ki yi hankali ba" Saleem dake ta xaune a dakin bai tofa nasa ba tun daxu ya girgixa kai bayan fitar Mumy, Anty Khadijah tace "Kai ka ji fa saleem, dole ne sai na ja mutane gantalallu da xa su daura min wahala a rayuwa a jiki? In ji da yarana da kai na mana, Ita taga xata iya ne halinmu ba daya ba kuma baxai taba xuwa daya ba in dai a kan wannan ne, gwara ta kyaleni, kuma duk shegen da bai gallaza ma 'ya yana ba bai haifu cikin uwarsa ba... Mutum ne idan ban son sa ban son sa har abada babu me canxa min ra'ayi" Saleem yace "Ni Anty ban san me yasa Mumy take haka ba wllh, yau wannan gobe wancan, dubi fa kwanaki da kyar ta mayar da fitsararriyar yarinyar nan kauyensu ga shi yanxu ta jajibo wata ita wannan har boko naga an sa ta saboda matsayi" Anty Khadijah ta juyo tana facing dinsa a hankali tace "Wani bokon?" Saleem yace "Essence wllh" kasa rufe baki Anty Khadijah tayi tana kallon Saleem xuciyarta na bugawa, can ta nufi kofa fuuu ta fita, k'asa ta sauka gun kyauta, Kyauta dake ta aiki a kitchen tana wake wake tayi shiru ganinta ta risina tace "Har kin samu fitowa Hajiya" Anty Khadijah bata saurareta ba da wani expression tace "Kyauta ina yar uwar ki mai aiki nan" kyauta tayi kasa da kai tace "Toh Hajiya, jiya madam ta sa a kai ta makarantar bokon su baby, yanxu haka ma tana can" Anty Khadijah ta saki salati bata sake saurarenta ba fuuu ta wuce sama ta bude dakin Mumy, daga bakin kofa tana huci tace "Anty ita mai aikin kika saka a makarantar su siyama?" Mumy ta daga mata hannu tace "Khadijah ki tafi ki ban waje kar ki sake bata min rai don Allah, da kudin ki na sa ta bokon ko da ajiyar da kika bani?" Wani murmushi Anty Khadijah tayi tace "Ko daya, amma wllh kinyi making babban mistake a rayuwar ki, ita mai aikin kika sa a boko koh? Tam Allah ya taimaka, aje xuwa" daga haka ta fice daga dakin, parlor ta koma ta xaune tana girgixa kafa xuciyarta na kuna, can ta dau wayarta ta shiga kiran Aliyu, Aliyu dake xaune office ya dinga kallon wayar ganin mai kiransa har ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne hade da sallama, ko amsa sallamar bata yi ba cikin daga murya tace "Yanxu Aliyu kana gidan nan ka bari Anty ta sa mai aikin nan a makarantar da ku kayi?" Tabe baki yyi bai ce komai ba har lkcn wayar na kare kunnensa, tace "Ko da yake its a mistake ma kiran ka da nayi don duk bakin ku daya da Anty, kai ne ma munafukin... amma ina son ka sani wllh ta dauko ma kanta dala ba gammo ne, sai tayi mugun da ta sanin sake ma 6are da take yi kwanan nan ba sai an dade ba, sai ta xo ta sameni har daki tace Ashe abinda kike yawan gaya min gaskiya ne Khadijah, ni kuma a lokacin xan mata dariya, kai kuma ka ci gaba da biye ma gurgayen shawarar da take yi da kai har kai sai ya shafa muna nan baxa a dade ba in sha Allah, ita yarinyar da ku ka sa a makarantar sai ta ma sharrin da har jikoki baxa ka mance ba, sai ta goga ka bak'i a idon duniya" daga haka ta katse wayarta, Aliyu ya tabe a baki a xuciyarsa yace Allah ya shirye ki, daga haka ya ajiye wayar ya ci gaba da abinda yake. Da yamma bayan su Khadijah sun dawo tana bathroom ta shiga wanka kyauta kuma na fiddo mata kayan da xata sa sai ga Anty Khadijah ta shigo dakin 'yar ta Iklima na biye da ita a baya, Ko rufe kofar bata yi ba tana ma kyauta matsiyacin kallo tace "Ina tsinanniyar take?" Kyauta ta rasa abun cewa ta fara kame kame sai ga Khadijah ta fito daure da towel, kin karasowa dakin ta yi ganin Anty Khadijah, kai kana ganinta kasan tayi mugun tsorata, Anty Khadijah ta karasa ta fixgota da karfi tace "Kina da gadon mutanen gidan nan ne da kika yarda suka sa ki a boko?" hawaye ya cika idon Khadijah cikin rawar murya tace "Ki yi hakuri Anty" kife ta tayi da tafin hannunta da karfi ta gwara kanta da bango tana hade hakoranta tace "Sai kin lalata tsafin da kika shigo mana gidan nan da har aka sa ki a boko don kaza kazan ki" Khadijah ta rike kanta tana kuka sosai tana kallon kyauta da ta tsaya a gefe idonta ya kada, dukanta Anty khadijah ta dinga ta ko ina tana cewa "Barin gidan nan ya kama Ki don kaza kazan ki" Muryar mumy suka ji tana cewa "Zo nan Khadijah" Anty Khadijah ta dago tana huci tuni Mumy ta juya ta bar wajen, Rankwashi ta kuma kai mata ta sake gwareta da bango tace "Da bakin ki xaki ce masu baki son makarantar idan ba haka ba in kashe ki, kuma ki kama hanyar kauyen ku" daga haka ta fita dakin fuskarta a murtuke, sama ta iske mumy a tsaye, mumy na kallonta rai a bace tace "Khadijah idan har baxa ki iya xama da ni da mutanen dake tare da ni ba ki tattara ki bar min gidana nan ba da dadewa ba, ai ban hanaki xaman gidan mijin ki ba, a kan wani dalili duk xaki bi ki takura ma bayin Allah a gida, ina fa sane da duk abinda kike ba wai ban sani ba, ina ruwanki da bokon da na sa ta? Kudin ki ne ko kudin wani naki, ki fita harkata a gidan nan wallahi, banda mugunta yayi maki katutu me yarinyar ta maki xaki je kina dukanta haka alhalin daxu kika gama nuna rashin jin dadin ki a kan yanda ake treating din naki yaran a gidan ubansu, wlh na fara gajiya dake da halinki, komai na harkan gidana ki cire idonki a kai ki jira idan kina naki gidan in kin so yan Adam ma su kwanta ki dinga tattakesu wannan matsalar ki amma baki isa ba a gidana tunda ba tsoronki nake ba, lastly bbu ruwanki da wannan yarinyar Khadijah, tsakanina da ke daban tsakanina da ita daban, ki yi ta kanki a gidan nan" daga haka mumy ta shige dakinta. Anty Khadijah tayi kuka har ta gode Allah, har ta hada kayanta da na 'yar xa ta bar gidan wata xuciyar tace mata wato ma kenan yarinyar har ta isa da xaki bar mata gidan, ki tafi saboda ita, Inaa ai sai dai Ita ta bar maki, kyale Anty fati kawai kina xaune xata xo ta sameki, tunanin hakan yasa ta hakura da tafiyar duk da ba wai tasan inda xata bane, a ranta kuwa jin tsanar Khadijah take fiye da komai a duniya har kishiyarta ta kuma dau kudirin sai ta 6ata ta gun Mumy da kowa na gidan kafin a koreta. Tun da Aliyu ya dawo misalin karfe biyar yake xaune dinning, bai damu da rashin amsa gaisuwarsa da Anty Khadijah da ke xaune parlorn tayi ba, ya gama cin abinci ya hau danna laptop, iklima sai kai koma take a parlorn sun hada ido ya fi a kirga bata gaishesa ba shi ma bai ce mata komai ba, dinning taje ta dau ruwa suka sake hada ido ya hade rai yace "Sai na fasa idanuwan nan da kike kallona da shi a wajen, a gidan ku ba a koya maki gaisuwa ba ai sai kallon mutane kamar bakauyiya" turo baki tayi ta dauke kai ta bar wajen, Anty Khadijah da taji komai ta mike kamar jira take tace "Ae da ka fasa idon, tunda kai ka hallitar mata su, kuma bakauyiyar ce uban waye ba daga can ya fito ba? Idan ba munafurci da borin kunya ba ka nuna ka san ta ne balle ta gaisheka, ina ce kai ne ya kamata kace A'a iklima ce... ashe kun xo, yaushe ku ka xo ya hanya, amma kayi gum da baki tunda ba tarkacen da uwarka ta saba kwasowa bane, to wllh iklima ita ce dolen ka ba su ba, kuma baxa ta yi gaisuwar ba, ni din ma ba a walakance ka gaisheni ba kake jiran 'ya ta ta gaisheka kawai don kun ga mutum na xaune gidan ubanku, bari ka ji.... yau sai uwarka ta rabu da ku amma ni muna makale ko min wuya don nice dolenta ba ku da ta samu a gidan nan ba, uwan mu daya ubanmu daya da ita, tun kan ku xo duniya muke tare, munafuki kawai" daga haka ta ja hannun iklima dake tsaye kusa da ita ta wuce sama tana cewa "I can't wait ranan da tarkacen da ku ke debowa da har suke neman haddasa mana matsala xa su kunyata ku a gidan nan, wllh sai na xuba ruwa a kasa na sha don farin ciki, ke kuma iklima ko da wasa kar ki gaishesa ya fasa idon mu gani tun ance masa kwai ne" Aliyu ya tabe baki ya mayar da dubansa kan laptop din gabansa, baby ta karaso dining tana kallon Aliyu tace "Anty Khadijah can just shout for African ehennn, I don't even like that her daughter that is eying me since, it seems she even used my sponge to bath this morning coz it wasn't d way I left it" shi dai bai ce komai ba, ta bude masa textbook din math dinta tace "Yaya koya min assignment don Allah" ya kalli book din sannan yace "Ki je ku yi da Classmate din ki mana" Baby tace "Iman?" Yace "Yes" ta ce "She told me she is not feeling fine, kayi mana sai in kai mata ta yi copying nawa, she is even lying down now" yace "Me ya sameta?" Baby ta bude hannu tace "I don't knw, or may be it's because Anty Khadijah ta doke ta daxu, kasan duka tayi mata daxu fa" yace "Duka? Why? A ina ta doke ta?" Baby tace "Dakin can ta shiga ta mata dukan shine ni kuma naje na gaya ma Mumy a sama ta sakko downstairs tayi ma Anty Khadijah fada sosai, har sai da Anty Khadijah tayi kuka, I even saw her packing her load but I don't knw what made her Change her mind kuma" yace "Kira min ita" ta ce "Iman?" Yace "Ehh" tace "Noo daxu da naje tana bacci na tasheta, shine kyauta tace kar in kara tashinta tace mata kanta yana ciwo sosai, kuma kamar Anty Khadijah ce tayi causing din ciwon kan coz she hit her head on the wall many times" Tashi Aliyu yyi yace "Mu je wajen ta" baby ta mike ta bi sa suka tafi dakin kyauta, kwance take kan gado kyauta ta rufe ta da bargo bayan uban rub da ta shafa mata a jiki, ya isa kusa da gadon Baby na biye da shi, sosai lebbenta yyi ja kana ganinta kasan ta ci kuka ba na wasa ba, ya kai hannu forehead dinta ya ji har ya dau xafi, baby ma ta taba tace "Kaji jikinta da xafi koh, Anty Khadijah ce tayi causing din komai" juyawa yyi ya fita ya wuce dakin Mumy, yana tsaye har mumy tayi hanging kiran da take tana kallonsa tace "Ya aka yi Abuturrab?" Yace "For God sake abinda Anty Khadijah ke yi a gidan nan is getting out of hands, why will she just best someone's child the way she did" Mumy tace "Na fa yi mata magana nasan baby ce da gulma xata gaya maka, wllh ni kaina nayi mamakin abinda nayi mata daxu cos gaskiya I am nt happy" yace "Toh yanxu da ta sa ma yarinyar xaxxabi fa?" Mumy tace "Toh sae in ce Allah ya saka mata, don yarinyar dai bata mata komai ba" juyawa yyi ya fice daga dakin ya harari saleem da fitowarsa daga dakin Anty Khadijahr kenan ya sauka downstairs ya koma dinning ya xauna, mumy ce ta sakko ta shiga dakin kyauta, jin xafin jikin khadijah ta tada ta ta wuce sama da ita xuwa dakin baby, baby da ta biyo su ta xauna kusa da khadijah da mumy ta kwantar saman gadonta tace "Mumy let her be staying in my room sae mu dinga assignment tare ba sai ina xuwa dakin kyauta ba" Mumy tace "Tafi ki kira min yayanku" juyawa baby tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tace yana xuwa, mumy na ta jiransa har ya shigo da sallama tana kallonsa tace "Ko xaka samo mata magani don Allah Aliyu" ya karaso gadon yana kallon khadijah, mumy ta mike tace "Ae ita ma ga nata can ana gallaza masu kuma bata yarda don tana ma 'ya yan wasu bne" daga haka ta fita Aliyu ya bi bayanta, baby kuma ta xauna tana ta kallon khadijah.

Pharmacy Aliyu ya tafi ya siyo mata drugs ya dawo gidan, bedroom din mumy ya shiga ya bata ledan maganin tace "Toh ni nasan prescription dinsu Aliyu, ka tasheta ka bata mana" yace "Ohk" sannan ya fita xuwa dakin baby, baby na xaune kan study table din ta tana solving mathematics din, Ya karasa kusa da gadon yana kallon khadijah, kallon baby yayi yace "Je ki tambayi mai aiki a downstairs ko ta ci abinci" Baby ta fita ba a dau lkci ba ta dawo rike da plate din abincin ta ajiye a kasa tace "Tace bata ci ba" Yace "Tell her to make a cup of tea" baby ta juya ta fita, da cup din shayin ta dawo ya karba ya ajiye sannan ya tada khadijah, mikewa xaune tayi tana murxa ido ya dau shayin ya mika mata, ta girgixa masa kai tace "Am not hungry" yace "I know you are not Hungry, kafin in dawo kin shanye shayin nan" daga haka ya fita, Baby ta taho da sauri tace "Kawo in taya ki sha kafin ya dawo" khadijah ta mika mata, baby ta fara shan shayin don ba xafi sai da ta yi rabi ta mika ma khadijah, ta bata fuska tace "It's till plenty" baby ta sake kafa kai bata sauke ba sai da ya rage mitsitsi, ta mika ma khadijah ta karba, ta bar gun da sauri tana goge baki ta ci gaba da abinda take yi a study desk dint, khadijah ta shanye sauran ta ajiye cup din, xata kwanta sai ga shi ya shigo yana kallon cup din dake ajiye, hade rai yyi baby sai satan kallonsa take ya juya direction dinta tayi saurin dauke kai, kallon khadijah yyi yace "Shayin kika bata ta shanye kenan" ko rufe baki bai yi ba baby ta fice daga dakin da gudu, ya bi ta da ido, daukan cup din yyi ya mika ma khadijah yace "Tafi ki kai a sake hada maki wani da kanki" kamar xata yi kuka tace "Ni ba yunwa nake ji ba" ya wani hade rai yace "Tashi ki fita" ta mike da kyar ta dau cup din xata fita yace "Ina jiran ki fa" Rabin cup ta sa kyauta ta hada mata shayin ta dawo dakin yana tsaye ta shanye sannan ya bata magungunan da bottle water, da kyar ta shanye su har da kukanta, ya wani hade rai, xata kwanta ya hanata ya dauko textbook din da baby take assignment yace "Solve it now ba sai kin kwanta ba" karba tayi a hankali yana kallonta ta fara solving maths din, yace "Idan kin gama ki kawo min downstairs" tace "Toh" sannan ya juya ya fita, dinning ya koma ya xauna, saleem dake xaune parlor bai ce masa ba shi ma bai ce masa ba, bayan kusan minti sha biyar khadijah ta sakko rike da textbook da note book din baby, gun Aliyu ta nufa ta ajiye tace "Na gama yayanmu" ya dau book din yana kallon abinda tayi, after sometime yace "Good, shine kike son a sa ki jss2" ta d'an yi murmushi ce "A jss2 nake ai, it's just that lesson teacher dina back then at home yana koya min karatun jss3" Aliyu bai ce komai ba ya rufe books din, ganin tana ta tsaye ya daga kai yana kallon idonta da suka rine yace "Toh tafi" juyawa tayi xata tafi dakin kyauta ya kirata, ta dawo yace "Tafi dakin baby kiyi kwanciyar ki" Sama ta kalla tayi shiru, yace "Tafi na ce" juyawa tayi ta nufi stairs din, saleem ya bi ta da kallon gefen ido, tana kwanciya dakin baby bacci ya dauketa. Tun daga wannan lokacin khadijah ta koma dakin baby da kwana ba don kyauta ta so ba, baby da kanta tace ma Mumy ta gaya ma kyauta ta dauko kayan khadijah a kawo ta saka a cikin press dinta akwai space, duk wannan abun Anty khadijah na nan ta sa masu ido abun na cin ranta wai khadijah ce har sama dakin baby... tabdii, sai dai bata ce wa kowa komai ba da yake har lkcn bata magana da Aliyu, Mumy ma ko shiga dakinta ta daina yi, yanxu saleem ne nata da siyama da Aneesah a gidan, sai dai fa ita kadai tasan kudurin dake ranta, kusan a dakin Anty Khadijah Saleem ke yini, da yake ba wani shiri suke yi da Abbansu Aliyu ba bata fara ce masa komai kan khadijah ba, tun da ta ki xaman aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login