Showing 66001 words to 69000 words out of 234058 words

Chapter 23 - Noor Al hayat Complete hausa novel

02 Nov 2024

17029

domin kuwa aurenta yyi uku ko ga maciji basa yi da shi idan ba yanxu da ta ja6e a gidansa ba take gaishesa don dole, idan ta ga yanda yake faram faram da khadijah sai taji abu ya makale mata a makogwaro, a haka daddy ya koma germany bayan sati daya shi kadai ba tare da saleem ba, Kusan kullum sai Iklima ta tsokani khadijah a gidan har da xagi tamkar dai uwarta ke sa ta, Amma ko sau daya khadijah bata taba kulata ba, tun da mumy tace kar ta sake ta kulata, hakan yasa fadanta yawanci da baby take yi, wani lkcn har da dambe, wanda ba haka Anty khadijah ta so ba, ta so ne ace da khadijah iklima ke wannan abun toh da bata samu fuskar su yi fadan gun khadijah ba yasa ta makale ma baby suke fadan, gashi baby ta nakada mata duka hakan bai sa kuma ta daddara, islamiyya mumy ta sa saleem ya kai Iklima, sanin ikliman ba gaida Aliyu take ba har sannan yasa Mumy bata ma sa shi ya kai ta ba, Ranan litinin da asuba mumy ta kira saleem ta basa cash na kudi tace "Gashi anjima idan yara xa su makaranta, ku tafi tare da Iklima kayi mata registration, ita ma tace jss3 take" Saleem yace "Toh Mumy, har da uniforms?" Tace "Eh Abbanku ne ma ya bada kudin" fita yyi dakin bayan ya amshi kudin ya kirga. Mumy ta bude kofar dakin Anty Khadijah don tare suke kwana da 'ya tata da take ji kamar ta mayar ciki, tun da ta ga Khadijah na kwana dakin baby ta hana iklima shiga dakin, Anty khadijah ta dauke kai ganin yayarta hade da daure fuska, Mumy ta tabe baki tace "Sai ki tashe ta daga baccin ta shirya xa su makaranta tare da su Siyama" daga haka Mumy ta rufe masu dakin. Aliyu na bedroom dinsa yana shiryawa da safen ranan baby ta shigo sanye da Uniform tana turo baki tace "Yayanmu kaga wannan ikliman mai shegen tsokanar mutane mumy tace xata fara school din mu yau kuma same class muke da ita da Iman koh, yaya a schl ma tsokanata xata dinga yi ni bana son ta xo schl dinmu Allah" yana karashe buttoning shirt dinsa yace "Toh ki je ki gaya ma Mumy mana" ta turo baki tace "I told ya Saleem yace xai mare ni, he is always supporting the dirty girl" Aliyu ya tabe baki bai ce komai ba, Baby ta karasa gun sa ta nuna masa takardan hannunta tace "Yaya.... Iman ce tayi solving din math din nan, I told her it's wrong ta ki ta yarda" karba yyi ya juyo yana kallon book din, ya langwabar da kai yace "Where is she?" Juyawa baby tayi sai ga ta sun dawo tare da Khadijah, khadijah ta tsayema bakin kofa ita ma tana sanye da uniform tace "Yayanmu ina kwana" yace "Lafiya lau, where u sleeping when solving dis?" Ta xaro ido tace "Aa idona biyu" ya mika mata yace "Toh it's wrong" karasowa tayi ta karba tana kallon baby, tace "but I told her to solve it let's see kuma taki yi fa, and tare muka yi wannan" Aliyu yace "Don't worry ku yi submitting haka, learn not to be afraid of failure..." Khadijah tayi murmushi tace "ohk thank you" daga haka ta fita baby ma tace masa thank sannan ta bi bayanta. Tun dawowarsu makaranta iklima ke ta ba uwarta labarin makarantar da ta fara ranan, Anty khadijah dake saurarenta fuskar nan a yamutse tace "Yanxu ajin ku daya da annobar can kenan?" Iklima ta tabe baki tace "Ehh mana, class din mu daya, kuma ko wani tambaya aka yi a class din ita ke bada amsa, Iman ma ake kiranta a class, she is always bragging she knws everything, in the afternoon ya Aliyu ya xo school din ma...." Katse ta Anty khadijah tayi da sauri tace "Wajen wa?" Iklima ta kara tabe baki tace "Water colour naga ya kawo mata da Math set, may be she told him since yesterday, lokacin muna break ma ya xo" Anty khadijah da ta wangale baki tace "Haba...." Iklima tace "Wllh, kuma yyi kamar bai gan ni ba har bin wajen motarsa nayi" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Anty khadijah da idonta ya kankance tace "Ita kadai ya kawo wa ko har da baby??" Iklima tace "It seems baby tana da shi, ita kadai naga ya kawo ma" shiru Anty khadijah tayi tana naxari iri iri a ranta, can tayi kwafa hade da murmushi. Baby ce tsaye a class tana kyakyata dariya har da rike ciki, Khadijah dai murmushi kawai take tana kallon sheet dinta na quiz da suka yi ranan over 20 both math and English gaba daya kuma ta cinye, Wata yarinya ta karbe script din baby dake ta kyalkyale dariya taga 15 gare ta, Baby ta sake satan kallon iklima dake can gefe tsaye tayi keeping strong face ta linke script dinta ta boye, baby ta kara rushewa da dariya har da kwanciya, har sanusi ya xo daukansu ranan baby da ta saci kallon iklima sai ta kwashe da dariya, Siyama da ke kusa da iklima ta kalli baby tace "Dariyar me kike ke kuma" Baby tayi keeping innocent face tace "Nothing" a nan ne ta fiddo script dinta a jaka tana murmushi ta mika ma Siyama tace "Quiz da muka yi daxu a class, I got 15 over 20, Iman kuma scored 20/20" Aneesah tace "Iklima fa?" Baby ta danne dariyarta tace "I don't really knw" Siyama ta kalli Iklima tace "Ke meye score din ki" Iklima ta tsuke fuska tace "16" wani kara baby tayi tana xaro ido tace "Wllh karya take she scored 3 over 20 I saw it with my two naked eyes" Iklima ta cakumota ta kunduma mata xagi tana huci tace "Ke kika ban 3 din, munafuka shegiya" kokuwa suka fara yi cikin motar har sai da Sanusi yyi parking, Siyama ta fito da baby daga cikin motar, sai da Sanusi ya sa baby ta dawo gaba sannan fadan ya lafa, amma sai xage xagen juna suke baby na kiranta olodo har suka isa gida, Iklima ta fice daga cikin mota ta shige gida da gudu ta rushe da kuka tana kwala kiran Uwarta, Da gudu Anty khadijah ta fito tana tambayarta menene da yake Mumy na gun aiki bata dawo ba, cikin kuka Iklima tace "Su baby ne ke ta tsokanata suna kirana olodo tun a school mumy bana son same class with dem, gwara a mayar da ni jss2..." Baby ta shigo parlorn tana turo baki Anty Khadijah tace "Baby me ya hada ki da 'yar uwarki, uban waye ya shiga tsakanin ku har yake neman raba min kan ku?" Baby tace "Anty ita ce take dambe da ni a mota, just because she scored 3 over 20, ni bani nayi marking din ba da take fada da ni" Anty khadijah bata ce komai ba ta ja Iklima xuwa daki ta kulle kofar tace "3 over 20 iklima garin yaya" iklima ta turo baki tace "Toh the questions where very hard" Anty khadijah ta bude baki tace "Toh ita babyn me ta ci?" Iklima ta tabe baki tace "Wai 15" Anty khadijah tace "kina me iklima, to ita shegiyar yarinyar can fa" Iklima ta kara turo baki gaba tace "She scored everything, mumy kuma na ji suna cewa xa su nuna ma ya Aliyu xai siya masu wani abu" hawaye cike idonta ta kare maganar, Anty khadijah tace "Ba kwa xuwa makarantar ne a can gida!" Iklima tace "Ina xuwa" Anty khadijah ta dungureta tace "Amma kin kunyata ni Wllh, yanxu da wani ido xan dubi yan gidan nan, yar iskar can xata iya cinye duka quiz din ke me kike da baxa ki iya ba" Iklima sai matsar kwalla take, Anty khadijah tayi shiru tana cixan yatsa, can tace "Tafi kije dakinsu ki dauko min script din shegiyar da sauri" da gudu iklima ta fita dakin, ta je dakin baby tayi sa'an ba kowa ta bude jakar Khadijah ta dau takardan quiz dinta ta fita ta kai ma Anty khadijah, yayyage papern Anty khadijah tayi ta bude window ta watsar tace "Tafi kiyi wanka ki je ki karbi abincin ki" cike da murna Iklima ta wuce bayi. Da daddare babu irin neman da Khadijah bata yi ma takardanta ba baby na taya ta xa su kai wa Ya Aliyu, Baby tace "Ni nasan Iklima ce ta sace maki script, she openly showed she is jealous tun a schl," daga haka ta fice ta tafi ta gaya ma ya Aliyu dake dakinsa, shiru yyi yana kallonta.

Throughout schl days ko assignment aka ba su Iklima ko average bata ci, daga 2 sai 3, baby ta samu abun dariya kullum cikin mata dariya take, ita dai Khadijah ba ruwanta nata ido, yau Friday tun da suka dawo schl khadijah ke kitchen gun kyauta tana bata labarin makaranta, kyauta tace "Toh ni abinda nake son sani a nan shine, ita ikliman bata gane karatu ne da bata amsa tambaya a aji?" Khadijah ta hade rai tace "Ni Anty mai girki am not gisting you about her ba ruwana kawai ina baki labarin masu kokari ne a aji" Kyauta tace "Ke dai kin fiye tsoro tsiya shi yasa baby ke burgeni, shegen duka take ma mummunar yarinyar" Khadijah tayi yar dariya tace "Ni dai ba ruwana Anty mai girki" Kyauta ta kyabe baki tace "Yo ai ba karya nayi ba, mummunar karshe ce yarinyar da nanikakken hanci kamar an taka amala a kan hanya, ido mitsi mitsi kamar na tana, baki kamar gidan tsutsa, ga gashinta kamar na hammata na" Khadijah ta fashe da dariya har da kyakyatawa, kyauta ta washe baki tace "Atoh, duk uwarta ce ta ja mata ai, da bata gallaza ma 'ya yan wasu da Allah bai hada yar ta da kwakwalwar tantabara ba, da yanxu bata nuna maki tsana kiri kiri ba ai ke xa ki dinga assisting dinta kina koya mata kamar yanda ku ke yi da baby, amma uwar taki xaman lafiya da kowa, meye amfanin haka a rayuwa.... Da ta kwantar da hankalinta ma wataran duk baxa ta gan mu a nan ba sai dai idan Allah yyi xa a sake saduwa" ita dai Khadijah bata ce komai ba, kawai ji suka yi ana cillo da jakunkuna waje, duk suka kalli juna sannan suka fita da sauri, Anty Khadijah ce tsaye parlorn duk ta fiddo Ghana must go da jakar kyauta da komai nata dake cikin daki waje, Tana wani murmushi tace "Dama rana irin ta yau nake jira, har ni kyauta xaki tsaya kitchen kina yi da ni kina yi da 'ya ta, to xaman ki ya xo karshe gidan nan yanxun nan kuma ba sai anjima ba, in dai ba gidan ubanki bane, ba kuma na uwarki bane nan din tattara ina ki ina ki ga su nan ki kama gabanki" kyauta tayi shiru tana kallonta, kofa Anty khadijah ta nufa kamar xata tashi sama ta fita compound cikin tsawa ta dinga kwala ma Usman kira ya biyota da gudu yana amsawa ta shigo parlor tana nuna masa kayan tana huci tace "Maxa kwashe tsummokaran nan ka fita da su can wajen gate" Khadijah ta fashe da kuka tace "Anty don Allah kiyi hakuri kar ki koreta..." Fixgota Anty khadijah tayi ta kai mata wani mugun dundu har sau uku a baya ta gware kanta tace "Tsinanniya ae nan ba da dadewa ba xa ki bi ta kema, mu dai je xuwa" Khadijah bata daddara ba ta durkusa tana kuka sosai tana kallon kyauta dake ta kallon Anty khadijah tace "Anty mai girki kice tayi hakuri don Allah" cikin tsawa Anty khadijah tace ma kyauta "Ki fita nace kar in fitar da ke da kai na munafuka annamimiya" Kyauta tayi murmushi tace "Xan tafi, ke kuma Allah ya hada ki da dai dai ke a rayuwa" Khadijah ta fashe da matsanancin kuka ta rike kyauta cikin rawar murya tace "Don Allah Anty mai girki kar ki tafi ki bata hakuri, kar ki tafi ki bar ni" haurinta Anty khadijah ta yi kamar ta samu ball tana huci tace "Tashi ki kwaso naki kayan ki bi ta kema.... Ba sai kin ce kar ta tafi ba" Tashi da sauri khadijah tayi tana kuka xata je dauko kayan nata Kyauta ta rikota tace "Kar ki damu Khadijah in sha Allah xa mu hadu wataran, ke dai ki kula da kanki ki rike maraicin ki Allah na tare da ke" daga haka kyauta ta saketa ta dau jakarta daya da ya rage parlorn ta nufi kofa ba tare da ta bi ta kan kudin aikinta ba, Baby dake tsaye parlorn ta fashe da kuka tace "Anty me yasa xa ki koreta, she is very kind, and she can cook" Anty khadijah ta ja kunnenta da karfi tace "Nan din gidan ubanta ne da baxan koreta ba, masu halin tsiya... Ga ku so dangi" daga haka ta bi bayan kyauta da sauri domin ta tabbatar ta tafi, bata dawo ciki ba sai da ta tabbatar kyauta ta bar layin gaba daya, mai gadi duk jikinsa yyi sanyi amma bai ce komai ba, ta dawo ciki tana yatsine fuska tace "Gayyar tsiya, ita kuma Anty fatima idan ta dawo nima sai ta koreni in ga" jan iklima dake ta murmushi a parlor tayi xuwa sama, don ita ce ma taje ta kira ta a daki wai kyauta na xaginta. Har mumy ta dawo khadijah na xaune can inda kyauta ta saba ce mata ta xauna farkon xuwanta gidan, tayi kuka har ta gode Allah, kasa cewa komai Mumy tayi bayan baby ta gaya mata abinda Anty Khadijah tayi ma kyauta, jikinta yyi mugun sanyi ta wuce daki da kyar ta kira Aliyu, ce masa tayi ya dawo gida yanxu, jin yanayin muryar mahaifiyar tasa yasa ko minti biyar bai kara ba a clinic ya taho gida, har ta gama bayyana masa abinda ya daga mata hankali bai iya yace komai ba yana tsaye dakin shi ma jikinsa yyi sanyi, can ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "kiyi hakuri mumy, yanxu kinsan inda xa a samo kyautar?" Cike da damuwa Mumy tace "A ina xan sani Aliyu, matar da ba waya gare ta ba, gashi ko kudin aikinta ba a bata ba, yanxu Khadijah ciwon xuciya take son sa min ne a gidana shine abinda ban sani ba har yanxu, don me yasa bata son in xauna lafiya yanda nake so a gidana, me yasa khadijah take min haka, don nace ta xo mu xauna tare laifi nayi Aliyu da xata dinga cuta ta haka, don wannan wallahi cuta ce" Yyi kasa da murya yace "Don Allah kiyi hakuri mumy, Allah ya ganar da ita.... Xan ma mai gadi magana yanxu idan Allah yasa kyautar ta dawo ya bar ta ta shigo kawai" daga haka ya fita, labe ya ga Anty Khadijah jikin kofa tana eavesdropping duk abinda suke cewa, tana ganinsa tayi masa wani shegen kallo hade da tsaki ta shige dakinta, bai ce komai ba sai tabe baki da yayi ya sauka downstairs. Bayan ya sanar ma mai gadin ya bar kyauta ta shigo ko da xata dawo.... ya koma cikin gida, har lkcn baby na ta kumbure kumburen an kora kyauta a dinning, su siyama kam ko a jikin su, a ransa yace "xa su ci gidansu da aikin gidan nan kuma Yanxu" ya karasa dining yana kallon baby yace "Ina Iman?" Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, kitchen ya shiga ya fita waje, xaune ya ganta har lkcn a gun idonta ya kumbura don kuka, ya tsaya yana kallonta can ya karasa wajen ta, tana ganinsa ta kuma rushewa da kuka ta kife kanta da gwiwa, ya durkusa gabanta yace "Kukan me kike?" Ta dago da sauri cikin rawar murya tace "Yayanmu Anty ta kori Anty mai girki" shiru ya d'an yi kafin yace "Ko xa ki bi ta ne?" Ta gyada masa kai da sauri, yyi murmushi yace "Toh kiyi hakuri, xata dawo in sha Allah" a hankali tace "Yaushe?" Yace "Mumy xata nemo ta" shiru khadijah tayi ya mike yace "Tashi ki je ki wanke fuskar ki" Tashi tayi ta tafi gun tap ta wanke fuskarta sannan ta dawo tana kallonsa yace "Kar ki sake kuka fa" tace "Toh" juyawa yyi ya shiga gidan ta bi bayansa, tsaye suka ga Anty Khadijah a kitchen ta hada kwanukan wanke wanke xata yi, Aliyu ya danne dariyarsa bai sake kallon direction dinta ba har ya fita kitchen din, Khadijah xata wuce tace "Zo nan..." Dawowa Khadijah tayi ta nuna mata tsintsiya tace "Maxa ki tafi ki share gaba daya gidan ai aikin ki ne kema, kuma babu uban da xai maki" daukan broom din Khadijah tayi ta fita, dai dai sakkowar mumy tana ganinta tace ta ajiye tsintsiyar su je daki su yi assignment da baby, ajiyewa tayi ta wuce sama dakin baby. Washegari da Asuba Anty khadijah ta shiga kitchen, Aliyu dake xaune parlor tun bayan da ya dawo masallaci sai murmushi yake jin yanda take ta dambe da utensils a kitchen, idan ta dauke wancan sai wannan ya fadi, tayi tsaki ya fi a kirga, karfe bakwai saura ya wuce sama don yin wanka ya tafi aiki, yana gama shiryawa ya fito ya shiga dakin baby kamar yanda ke yi duk safiya don ganin ko sun shirya, tsaye ya ga baby tana duba ma khadijah idonta da yyi ja, ya karasa dakin yace "What happen" baby tace "Yayanmu we where just on our own muna shiryawa fa, kawai sai ga ikliman nan ta shigo wai mun sace mata pen, can you imagine fa, alhalin karya ne she lost her pens gaba daya da mumy ta ba mu, shine ta dauke na Iman wai nata ne ta sace har da buga mata pen din a fuska shine ya taba idonta gashi yana mata ciwo yanxu, Yayanmu a daina siya mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login