Showing 21001 words to 24000 words out of 190707 words

Chapter 8 - KYALKYALIN KAUNA HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

11 Oct 2024

9311

nawa, wait dala miliyan nawa kakeso?” Cikeda isgalanci da tsantsan rashin kunya Maheer yace “nasan baka taba ganin sama da dubu dari biyu da hamsin ba arayuwanka, Commissioner Ibrahim Ibrahim name ur price banda lokaci meeting gareni in the next 45mins” wani kalan murmushi Baba yayi tareda girgiza kai yace “yaro kasami duniya saisa harkakeji ka isa kabani kudi daga kudaden dakake making a saida kwayoyin shaye shaye to bari kaji!” Baba yay maganan cikin kakkausan murya yace “ni Commissioner Ibrahim Ibrahim bana karban cin hanci da rashawa kuma bazan fara akanka ba koda ko zaka bani duka kudin duniyan nan ne, and listen to me your drivers might be hard but nan da few minutes or couple of hours zanyi cracking nasu, Pillow, Pablo ko wakake da suna, empire ka na saida kayan shaye shaye dakai kanka sun soma zuwa karshe I will makesure I bring you to justice koda shine the last thing I will do as a police offer, saina makesure na kawo karshenka ni Ibrahim Ibrahim nai maka alkawarin nan” dan murmushi kadan Maheer yasaki, yace “I wanted to be nice saisa personally nakiraka bansa an kiraka ba, zan maka alkawari kaman yanda kaima kamin alkawari, ni Pablo Escobar namaka alkawari koda ire irenka ku dubu kekaina bazan taba daina harkana ba! Idan kaga nadaina sana’an nan dan kaina ne badan sabida ku government pest da peasant ba, sai abu na karshe Comissioner Ibrahim Ibrahim” Maheer yakirashi cikin kakkausan murya yace “nabaka one hour kasaki kayayyaki na da direbobi na inba hakaba zan aika maka da yar karaman sako, your time start now! Don’t forget 1hour nabaka!” Dip Maheer yakai hannunshi yakatse wayan dake kan table ya zuki taba ya fuzar da hayakin yana huci yakalli Wike yace “what are his likes? And menene weak points nashi” wani kalan murmushi Wike yayi yace “Oga niko nasan likes nashi da weak points dinshi” yay maganan yana danna laptop nashi kafin yafito da hoton Baba dauke da Nanah a hannunshi yajuya laptop din yace “kadinga swiping zakaga sauran hotunan” hakan yasa yafara Wike dake kallonshi yace “Oga aduniyan nan babu abinda mutumin nan yakeso kaman yaran nan nashi mata guda 3, like he is obsess da yaran nan, and over protective of them, I think abinda kafiso aduniya shine weak point naka right Dan”? Gyadamai kai Dan yayi dake tsaye kaman soja yace “hakane Sir” sosai Maheer ke kallon hotunan, saida yakai wanda Baba ke rikeda hannun Yasmeen ya tsaya chak idanunshi kyam akan Yasmeen dabaisan mesa ba kawai face nata just grip his eyes, yakai kusan minti biyar yana kallon hoton, kafin ya janye idanunshi, yakalli Wike yace “nasan mutumin nan bazai taba sakin kayana ba just like that, dan haka inaso get your men ready” gyadamai kai Wike yayi, ijiye taban bakinshi yayi ahankali kan ashtray sannan yakalli Wike yace “duk inda this 3 gurls suke aduniya I want them found, but” dasauri Wike yakalleshi yace “don’t pick them up harsai 1hr dana bashi yacika, idan baisaki kayana ba Dan zai kiraku yabaka go ahead to abduct them and bring them here” dasauri Wike ya gyadamai kai yace “yes sir” yadauki laptop dinshi yajuya zai fita haryakai kofa Maheer yace “Wike” chak ya tsaya tareda juyowa yace “naam Oga” komawa yayi yashige cikin kujera tareda daura kafa daya kan daya yace “don’t hurt them!” Anatse Wike yace “yes sir” sannan yabude kofan yafice.

✨KYALKYALIN KAUNA✨


✍🏻M SHAKUR



EPISODE 1️⃣1️⃣

Kina neman kayan GHT irin nasu kara girman nono, katon bombom, rage kiba da sauransu ga way nakawo muku, join this group dan ganin abubuwansu.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KO6bdcXjxmh2l6pM6T0meI

Yau Juma’a kasancewan yanda Ammi ta tashi da damuwa yasa har Nanah datace sai rannan Monday zata koma school tasa Farida dasu Hassana suka wuce da ita dan yaran gidan kap dsame school suke zuwa banda Sa’a da Wanta dakuma Yasmeen dasuka gama suka shiga uni, sosai Ammi ke cikin damuwa Baba ko kiranta baiyiba tun bayan jiyan nan daya koma office da yamma wanda abu mai wuya ne zaisa Baba bazai kirata ba.

Wajejen 10 Yasmeen da ita kadaine tarage agidan dan har Sa’a itama ta tafi school tun 8:30 dan tanada lectures 9, tana sanye da doguwan riga na atampa straight gown red da black daya mata kyau sosai ga gogaggen red hijabinta a hannu da jakanta da wayanta, murmushi Ammi tayi ganinta tace “zo ijiye kayan nan kije dakina ki dauko kwalli nasamiki haba idanu sunyi fari tas kaman na wacce batada lafiya ke bakisan kwalli adon mace bane kuma sunna ne ba” ijiye kayan dake hannunta tayi kusada Ammi tace “Ammi ni zafi yakemini a idanu” hararanta Ammi tayi tace “ya bazai miki zafi ba ke bakiga idanun naki daban yake da idanun yan gidan nan ba” kaman jira take dasauri tadawo gaban Ammi ta tsugunna tace “Ammi a school sai ayita kallon idanuna wlh ni kunya nakeji saisa kullum kaina na kallon kasa bana iya kula kowa cus my eyes looks different da na mutane” murmushi sosai Ammi tayi takai hannunta tashafa soft kumatunta da another pimples guda biyu sababbi sun fito tace “that’s is why u are my special child Maman Babanta, ke kinsan kyan wacce kika gada kuwa Maman Baban ku? Bakiga yanda Babanku keda kyauba, Allah jikan Hajiya haka itama keda kyau ga idanu harta tsufa idanunta manya farare, da gray kwaiduwan idanun nan gareta kaman naki, it’s beauty kinji” murmushi Yasmeen tayi tace “to Ammi” pimples dinta Ammi tashafa tace “kai banson pimples din nan su bata miki fresh smooth fuskanki” dariya Yasmeen tayi tana mikewa tsaye tace “Ya Sa’a cewa tayi wai sun karama fuskana kyau” tabe baki Ammi tayi tace “shirmammun yara kawai, abin arziki daman baitaba yima Sa’a kyau ba” tabi Yasmeen din da kallo data wuce uwardakan, fitowa tayi dauke da kwallin Ammi ta karba tace “to tsugunna kiga nasamiki kitafi school kada kiyi latti” ahankali ta tsugunnawa Ammi ta zizara mata kwallin abin kaman wani tsafi saita kara wani kallan kyau idanun nata saisuka rikida suka kara wani irin kyau sosai fatan fuskanta nawani glowing, ta mike tsaye tana kyafkyafta idanun dake mata kaikayi sosai Ammi dake kallonta tace “kada ki sosa kwallin ya lalace kuma dau hijabi kisa, kinsaka pad ajaka ko incase”? Gyadama Ammi kai tayi sannan tabude idanun tass tadauki hijabi tasaka daya mata wani kalan kyau tadau jakanta tarike da wayanta tace “Ammi Baba zai dawo yau ko”?Tabe baki Ammi tayi tace “ki kirashi ki tambayeshi mana mayun babansu kun hanani sukuni da tambayan shi yanachan yana aiki ko takaina baibi ba” sosai yanda Ammi ke korafi yabama Yasmeen dariya dudda taso ta rike dariyan sai kawai ta tuntsire da dariya dayasa Ammi tamata wani mugun kallo, hadiye dariyan tayi tace “Ammi kinason Baba sosai wlh” daure fuska Ammi tayi tamau duk kunya yakamata, takowa Yasmeen tayi kusada ita tazauna dab da ita innocently tace “Ammi call him tunda shi bai kiraki ba” wani kallan kallo datama Yasmeen yasa da sauri Yasmeen ta mike taje wajen kofa ta tsaya, cikeda tsokana tace “Ammi kinaso kinajan aji nidai bazan jama mijina aji ba idan nayi aure wlh” baki Ammi tabude tana kallon Yasmeen dake dariya kasa kasa tana kallonta tace “laaaa hailaha illallahu Yasmeen!” Hannunta Yasmeen tadaura akan fuskanta akunyace tace “to Ammi ai kina missing Baba ne sabida kawai bai kwana gida jiya ba” raruman throw pillow dake kan kujeran Ammi tayi tadauka tareda jefa mata ihu Yasmeen ta kurma tafita aguje tana dariya Ammi ta jinjina kai kana ganin Yasmeen ahaka kaman bata magana but surutu da gulma dake bakin yarinyar nan yafi karfinta iyye.
Dakin Yaya tayi tadaga labule Yaya na zaune tana shan shayi tace “Yaya natafi” murmushi Yaya tayi tace “Allah bada sa’a diyar kirki, ke kadai kemini salllama idan zaki school sauran gantalallun yaran gidan nan ba ruwansu da neman albarkan iyaye idan zasu school, zo ga hamsin ma kinji” Murmushi tayi tashiga dakin ta amsa tace “nagode Yaya” fitowa tayi tawuce dakin Hajjo tamata sallama sannan tawuce tafita daga gidansu, ahankali take tafiya alayinsu tadanyi nisa kawai jitayi kaman ana binta hakan yasa ta tsaya chak tajuyo ganin babu mai binta yan layinsu ne ke activities nasu yasa tacigaba da tafiya tana kaiwa bakin titi ta tare keke tashiga tawuce school.


Wike dake cikin wata black van dawani yaronshi ke tukawa ne sunabin Keken da Yasmeen keciki wayanshi tahau ruri dasauri yace “it must be Oga” ciro wayan yayi daga wandonshi yakalli screen din ganin number dayay saving da Dan yasa ya amsa da sauri yakai kunne yace “Dan” anatse Dan yace “Oga yace execute operation” cikin murna Wike yace “angama” katse wayan yayi yashiga dialing number yaranshi dake school nasu Farida yace “CP idanma bakasan Pablo Escobar ba, yau zaka sanshi zamuga wazaici wannan yakin and wazai lose” daidai yaron shi yadauka, anatse yace “execute the plan Usman” dasauri yace “daman nagama shiryawa tsaf Oga bari naje” katse wayan yayi, sauka yayi daga motar yabar wani saurayi shima sanye da kayan police station aciki, sannan yawuce cikin school din yana sanye da kayan police harda nametag da aka rubuta Aliyu SS ajiki, private school ne normal one ba irin masu tsadan nan ba, direct office na principal yawuce yana shiga matar tace “welcome” murmushi yamata yana kallon agogon hannunshi yace “barka da safiya Hajiya, Ogana ya aikoni Commissioner of police Ibrahim Ibrahim na dauko yaranshi za’amusu interview ne a office nashi kinsan jiya aka maidashi commissioner” cikeda farin ciki matan tace “ai nakalla a AIT wlh, bari nasa akirasu, Farida da Nanah ko” tashi tayi ta leka waje tasa wata Malama taje ta kirasu sannan tadawo tazauna tace “ai daya kirani da kaina da ko direbanane sainasa yakaisu” murmushi Usman yayi yace “yana meeting ne wlh” daidai nan Farida da Nana suka shigo office din dukansu police din suka kalla murmushi yamusu, Principal tace “Baban ku ya aiko akaiku wajen aikinshi za’amuku wani interview” dasauri Farida dake kallon mutumin tace “dama kaine Aliyun da Baba yake yawan magana”? Gyadamusu kai yayi tareda mikama Nanah hannu yace “muje” makemai kafada tayi takama hannun Farida tarike tace “hannu Baba kawai nake rikewa Baba yace babu kyau rike hannun wasu maza” mugun kallo Farida tamata alamun tadaina rashin kunya hakan yasa tai shiru yana gaba suka binshi abaya har zuwa wajen motan baya yabude musu duk suka shiga suka zauna suna gaida dayan police dasuka gani agaba sannan yazagaya yashiga mazaunin direba yatada motan suka shiga hanya daga Nana har Farida sukai shiru Farida sai kallon cikin motan take dataji yana wari wari kaman na wiwi, sundanyi nisa atafiyan sannan Usman yama dayan sign hakan yasa yabude wata leda ya zazzaga hoda a hannun yajuyo da kanshi yace “girls” duk sun dago kai sun kalleshi kawai ya hura musu hoda, ihu Farida tayi tana kakkabe hodan tace “mehak……..” bata karashe maganan ba luuuu kawai ta zube itama Nanah haka dasauri yakira Wike yace “Oga operation successful gamu nan mun dauki hanyar palace” dasauri yace “muma yanzun nan zamuyi grabbing babban.”
Wannan kenan.


Wani kalan shan gaban Keken Van din yayi saida keken yaci bala’in burki dudda haka saida suka daki van din. “Subhanallahi” Yasmeen dake cikin keken tai ihu daidai Wike yabude gaban motan yafito yace “kasha wiwi ne baka ganin gabanka” shima azuciye Mai keken yafito yace “kaine kasha wiwi dan kaine baka ganin gabanka” Yasmeen zaro idanu kawai take ita kadai acikin keke tana kallonsu, dayan mutumin dake tareda Wike ne yasauko daga motan yana kallon mai Keken da Wike yace “dan Allah kuyakuri bari na duba passenger ko taji ciwo” yabar mai keke da Wike na chachan baki, baya yaje inda Yasmeen ke zaune kallo daya tamai tasauke kanta kasa tana kara kankame jakan school nata ahankali yace “sannu baiwan Allah kinji ciwo ne” girgizamai kai Yasmeen tayi batare data kalleshi ba, dan jujjuyawa yayi ganin babu mutane wajen yasa yakai hannu aljihun shi yazaro wani handky yace “to ga handky kishare fuskanki kinata zufa” yay kaman zai bata hanky hakan yasa Yasmeen tadago kanta danna mata hanky yayi ahanci tana mitsi mitsi yana kokarin magana da ihu hango haka yasa Wike yawani fizgo mai keken ya matseshi jikin mota yaciro bindiga yadannamai aciki yace “kawai ka tsaya ahaka kona harbeka wacce ka dauko nake bukata bakaiba” zaro idanu mai keken yayi fitsari na gangaromai jin bindiga acikinshi, Wike yajuyo yana kallon keken daidai Yasmeen takarasa passing out, chak Guy din yadauketa yafito da ita Mai keken na kallonsu van din yabude yasata aciki sanna yarufe yazaga da gudu yadhiga gaba yace “come on Wike” wani kalan wurga mai keken Wike yayi bayan ya fizge key keken sannan yashiga mota sukaja motan da mugun gudu sukabar wajen.

✨KYALKYALIN KAUNA✨



✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣2️⃣

Maryam Eygpt abaya gidane na abayoyi daban daban na Egypt da sauransu, tana bada sari tana saida daidai abayanta are damn affordable, click on this link and join her group.
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj





Yana zaune kishingide acikin office dinshi ya lumshe idanu kaman wanda ke bacci akai knocking, batare daya bude idanunshi ba hannunshi ya mika ya danna wata botur hakan yasa aka bude kofan office din aka shigo, anatse Dan ya maida kofan yarufe yajuyo yataho zuwa gaban table din, cikeda girmamawa yace “Sir Wike yakawo girls din” shiru yayi still idanunshi a lumshe batare dayay motsi ba, kusan 2min yayi ahaka sannan yabude idanunshi ahankali sundanyi ja kadan ya zubasu akan Dan, sauke kanshi Dan yayi kasa, ahankali yace “kayi abinda nace kama dakin?” Gyadamai kai Dan yayi yace “yes sir” tashi yayi ahankali dagakan kujeran yadauki kwalin tabanshi dake kan table yazaro daya yasa abaki yadauki lighter ya kunna sannan yafara tafiya kadan kadan yana busan taban yatafi zuwa wajen babban window dake dakin dakenan da wasu hadaddun plain design milk curtains, wani dan remote dake gefen labulen dake makale a bango yakai hannu yataba hakan yasa window yabude, garden ne lafiyayye abayan window da flowers but daga window kana iya hango wani separate building again wanda yakenan ta bayan gidan, ga yaran Wike tsaye gaban flat din rike da bindigogi suna gadi, taban yakai bakinshi ya zuka ya busar idanunshi kyar akan building din kaman mai tunanin wani abu, hannunshi daya yakai yatura a aljihun wando dayan hannun kuma rikeda karan taba yana zuka yana kallon building din chan yace “take that phone kamini snapping nasu all 3 together” dasauri Dan yace “sir the girls are unconscious” batare daya juyoba yace “that’s how I want the pics” dasauri Dan yace “yes sir” yawuce gaban table din wannan special phone din daya kira Baba dashi yadauka yawuce yafita daga office din, Maheer na tsaye yana shan taban yana kallon Dan yawuce yaje building din yashiga ciki ko 1min baiyiba acikin dakin ba yafito duk Maheer na kallonshi ta window yadawo, kai tsaye wannan karan yashigo office din har inda Maheer yake tsaye gaban window yazo yamikamai wayan yace “gashinan nayi hotunan” ko juyowa baiyiba balle yayi alamun karban wayan saida yakarashe shanye taban tass sannan yamikamai hannu batare daya juyoba, samai wayan yayi a hannu hakan yasa yadawo da wayan gabanshi ya danna screen din tai haske saiga Yasmeen, Farida dakuma Nanah, dukansu zazzaune akan wasu kujeru irin na kulle mutanen nan, kujerun nada belt tawajen hannu da wajen kafafu duk an kulle hannuwansu da kafaffuwansu da belt, dukansu idanunsu lumshe suna bacci kansu ya lankwashe babu wacce tamasan inda kanta yake, kusan 1min yabata yana kallon hoton sannan yasa fingers dinshi yashiga scrolling yana kallon 5 different pics da Dan ya dauka nasu checking and rechecking dan tabbatar babu wani abu dazai incriminating ko sanar da komi game da inda suke, sannan yajuya ahankali yakoma kan kujeranshi hoto daya ya zaba cikin hotunan yay sending nashi as MMS ma CP tareda kashe wayan dip sannan ya ijiye agogon hannunshi ya kalla yace “today is Friday yeah”? Dasauri Dan yace “yes Sir” tashi yayi yadauki wayanshi kadai dagakan table din yawuce batare daya jira Dan yabudemai kofa ba yabude da kanshi yafice yawuce sama dakinshi yashiga lafiyayyen wanka yayi yafito ya goge jikinshi yawuce closet yana tsane kanshi wani Riga da wando yadauko na jean dark blue da farin riga yadawo ya shirya tsaf bayan yagama wankan turare, dadduma yadauka ya shimfida sai alokacin yay sallan asubahi sannan yatashi yafito Dan na falo ganinshi yasa yay wajen kofa budemai yayi yana zuwa yafice yace “take me to mosque”.



Wuraren 12:30 Baba na cikin wani kurkuku da ake dukan criminals idan anaso su bada information yana kallon yanda akecin uban direban kan sunada information akan Pablo Escobar amman sai cewa suke su basu sanshi ba basuma taba ganinshi ba iya kansu dauko kaya daga lagos zuwa nan shikenan, address na border ma sunki badawa har lokacin dan kowannensu naji no matter what zasu fito, Baba dake tsaye daga ta waje yana kallon abinda ke faruwa aciki wayanshi ne na office yay karan shigowan sako, dasauri yakai hannunshi aljihun wandonshi yaciro wayan, messege yagani from no number, kawai just sako, hakanan yaji kirjinshi kawai ya buga shi kanshi baisan dalili ba, ahankali yabude message din idanunshi suka sauka kan Yasmeen, Farida da Nanah dukansu basa hayyacinsu an daddaure musu hannu da kafafu, wani kalan wawan bugawa zuciyanshi yayi baisan lokacin da wayan tafadi daga hannunshi zuwa kasa ba, hakan yasa dasauri yakira sunan Allah. “La’ilaha illallah” still kirjin nashi na dukan uku uku amman yadaure yaduka ahankali yadauki wayan yakara kallo gashi nan yaranshi ne tabbas dudda duk suna bacci basa hayyacinsu, ga Nanah da Uniform, Farida ma sanye da uniform na school nasu, dasauri yajuya yafita daga dakin yaciro dayan wayanshi yashiga dialing number Ammi yana tafiya da sauri da sauri kaman mahaukaci, ringing daya biyu Ammi ta daga kafin tama gamamai sallama yace “Nanah taje school yau ne”? Ammi fushi takedashi sosai but jin yanayin muryanshi yasa tace “eh taje meya faru”? Shiru yayi yakasa magana saikuma ya katse wayan da sauri tunawa da yanada number principal din school nasu dasauri yanemo number ta yayi dialing,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login