Showing 66001 words to 69000 words out of 190707 words

Chapter 23 - KYALKYALIN KAUNA HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

11 Oct 2024

9335

to pharmacy kaman daga sama yaji Maheer yace “I want to get married!” Durun dum! Maganan yasauka akan Hamad dasauri yadago kanshi ya kalli Maheer din da kaman bashine yayi magana ba, karasa tura sakon Hamad yayi sannan yataso yazauna kan table yana facing Maheer tareda rungume hannunshi a kirji yace “wazaka aura? Hope ba wanchan matar data haifeka kake shirin aure ba sabida dan ciwon datayi kanka” shiru Maheer yayi sai danna waya yake kaman bazaiyi magana ba saikuma ahankali yace “not she” dasauri Hamad yace “to wakake so ka aura Maheer”? Wannan karan yakai kusan 3min baice komiba kafin ahankali yace “that girl” “which girl”? Hamad ya tambayeshi da sauri dudda already shi yasan wace girl Maheer yake nufi, sake shiru Maheer yayi kafin chan yace “Fateema” “you mean Yasmeen? Yarinyar dakai kidnapping nazo namata treatment”? Murya chan kasa Maheer yace “eh, yarinyar comissioner of police” dasauri Hamad yace “yarinyar da Babanta ya kwace kayanku ai tafadamin ranan” shiru Maheer yayi bai kara cewa komiba sai danna waya dayake wanda Hamad yasan bawai wani abun kirki yake dannawa ba, yadade yana kallon Maheer saikawai yasauko daga table din yakaraso gabanshi hannu yasa ya karbi wayan hakan yasa Maheer yadago kanshi dasauri, sa wayan Hamad yayi a aljihunshi tareda folding hannunshi a kirji cikeda seriousness yace “Maheer kasan what u are telling me kuwa? Yarinyar comissioner of police dayake nemanka ruwa a jallo yay arresting kakeson ka aura? How? Tayaya? Did you even know abinda kakeyi? Maheer kanaso kaje prison ne? Eh”? Hamad yay maganan cikeda damuwa, dan shiru Maheer yayi yana kallonshi idanunshi sunyi ja anatse yace “I don’t care about anything I just wants to marry her” dasauri Hamad yace “is she the reason dayasa ka nemi lecturing a school dinsu”? Gyadama Hamad kai Maheer yayi ahankali, sake yin shiru Hamad yayi yana kallon Maheer din kaman yanda yake kallonshi kafin anatse yace “Maheer son yarinyar kake ne?” Shiru yayi yakasa magana Hamad yace “talk to me, are you in love with her”? Lumshe idanu Maheer yayi kafin yabude murya chan kasa yace “I don’t know, I don’t understand myself, I don’t even know the meaning of all this things danakeyi, I don’t know anything again, all I know, all I see is just her” dudda Hamad so yake yayi murmushi daurewa yayi yace “to tayaya zaka dumfari wannan dan sandan kace zaka auri yarshi kaima kasan bazai taba bakaba wannan ma super story ne, sokake asirinka ya tonu yarinyar ai she will tell Baban ta wayekai” girgixamai kai yayi cikeda damuwa anatse yace “he will never know nine, I will handle the girl” dasauri Hamad yace “tayaya? Wai Maheer kasan me aure kuwa? Aure is not one of your tricks fa? You can’t handle aure kaman yanda kake handling harkan cocaine, Maheer wai kakosan wat you are getting kanka into kuwa?” Lumshe idanu Maheer yayi saikawai yasauko daga bakin gadon azuciye zai wuce yayi kofa hannunshi Hamad yarike yace “ina zaka muna magana”? Azuciye Maheer yajuyo cikin tsananin fushi yace “why are you asking me all this questions? Kasan menake going through? Kasan meke damuna? See Hamad I don’t believe in Marraige you know that but nima bansan meke damuna ba this girl has become like parasite tazo tashiga jinina she’s everywhere in me, the thought and everything is driving me mad, Hamad I see her in my dreams, I see her idan nabude idanu, I see her in everything danake, tunda tashigo rayuwana I can’t handle anything again, not me not my empire, what do you want me to do inba in aureta ba? Maybe if she’s close to me bazan dingajin abinda nakeji ba but why do you keep questioning me Hamad why why why”? Bakaramin baci ranshi yayi ba yayi shiru saikuma chan yanuna kanshi yace “kasanni sama da kowa d normal Maheer daka sani it will take me not less than 2hrs I will kidnap this girl nadauketa tadawo wajena har abada and nothing will happen but no banyi all this ba I want to marry her legally base on addini nasan tana taredani ne amatsayin matan aure not yarinyar danai kidnapping wrongly but why are you asking me all this questions is it because I come to you I can do this myself kasan dahaka ko”? Kafadanshi Hamad yakama anatse yace “calm down Maheer kaima kasan I will always support you, you are the only brother danake dashi aduniya uhmm tambayoyin danake maka is just to look out for u Maheer yanzu mekake so”? Lumshe idanu Maheer yayi Hamad yabishi da kallo wato idan Allah yatashi kamaka baya maka da kyau rana daya Allah ya jarabi Maheer da mahaukacin son yarinyar mutumin dakeson kaishi gidan yari. Bude idanunshi Maheer yayi ahankali yace “inaso karakani muje nama Baba maganan aje a nema mini aurenta sannan mu taushe any loophole dan nasan kafin ya bada auren yarinyar nan saiyay binciken sama da kasa” shiru Hamad yayi yana kallonshi anatse yace “yarinyar fa”? Ahankali Maheer yace “I will handle her ita” jimm Hamad yayi yana kallonshi saikuma yace “wacchan matar fa yazakai da ita” dan yatsine fuska Maheer yayi yace “batama cikin lissafi na she’s not relevant and she will never know” ahankali Hamad yace “Maheer” kallonshi Maheer yayi baice komiba, shiru Hamad yayi yana kallon idanun Maheer din all abinda yagani is sincerity da tsantsan so, gyadamai kai yayi yace “shikenan I will support you nadawo gida anjima sai muje muma Baba magana idan yaso shida Mallon Sani sai suje gidan su ko” gyadamai kai Maheer yayi kafin ahankali yasaki dan murmushi yajuya yafice daga office din Hamad yabishi da kallo har cikin ranshi yasan this is first step na shiryuwan Maheer, idan ta wannan sanadin Allah yakeso ya gyarashi to Allah ya tabbatar da Alkhairi yakara raba shi da matan nan dan she’s not Khair in his life.

✨KK✨


EPISODE 4️⃣5️⃣
44
https://www.instagram.com/p/CtwFCtXITwD/?igshid=YjgzMjc4YjcwZQ==




Yasmeen na zaune a shagon Maman Intee dan tunda tashigo tazauna Maman Intee nata mata hira, tana bata labarin yanda customers din nan nata suka daina zuwa yanzu bata ciniki sosai, bata iya magana kawai bin Maman Intee take da idanu da abinda ke damunta yafi karfin tunanin ta, harsaida Maman Intee tace “Kodai har yanzu bakiji sauki bane” tace a’a taji kanta kedan ciwo tasa hannu suka fara filling na samosas datakeyi.


Tana cikin hada salad wayanta dake cikin jaka yahau ringing faduwa gabanta yayi takalli agogo dasauri this is just 2:15 na rana Baba ne ke kiranta amman normally yau 5 zata gama lectures sabida duniya dataji yamata zafi ne yasa tazo nan shagon Maman Intee kota manta damuwanta, dasauri tagoge hannunta tawuce wajen jakanta tabude wayan taciro takalli screen din, wata bakuwar number ke kiranta ba number Baba bane hakan yasa ahankali tace “waye wannan number kuma”? Maman Intee dake bama Intee nono tana jinta tace “ki dauka kiji ko waye” gyadama Maman Intee kai tayi ta danna wayan takai kunnenta cikin sassanyar muryanta tace “hello” har tsakiyan kanshi yaji dadin zakin muryanta, cikin wani irin cool romantic voice yace “inajin yunwa sosai Fateema, am outside shagon ku, bring food for m……” dawani kalan sauri Yasmeen tazare wayan daga kunnenta ta shiga daddanna screen din tana kokarin katse wayan harsaida Maman Intee tace “ke lafiya? Waye kika kashe wayan da gudu haka”? Rasa abinda zatace gabanta na faduwa sosai yasa tace “wa….wani mutumi ne” yanda tabada amsan zakasan tasan waye, dasauri Maman Intee tace “wani mutumi kuma”? Rasa abinda zatace tayi saitai shiru tana zaro manyan idanunta tana kallon Maman Intee tana maida wayan jaka da sauri, Maman Intee yar gari ce tasan whatsupp dan dariya tayi da shewa tace “yaushe kikai saurayi Yasmeen”? Zaro idanu Yasmeen tayi sosai tanuna kanta tace “ni” dariya sosai Maman Intee tayi ganin yanda tayi tace “kwarai kuwa ke, watanki nawa kina zuwa shagon nan inhar wayanki tai ringing kodai Baban ki ko Mamanki ne ke kira, bantabajin wani ya kiraki ba, yarinya har yarinya gaki kyakkyawan gaske black beauty abinki amman baki kula samari ni nasan duk sabida Baban ki ne yanzu dai waye wannan”? Rasa abinda Yasmeen zatace yasa tace “lecturer mu ne” wani kalan kecewa da shewa Maman Intee tayi tace “to meyake so”? Ahankali tace “uhmmmm cewa yayi yana waje wai yunwa yakeji” zaro idanu Maman Intee tayi tace “shine kika barshi tuntuni” hannu Maman Intee tasa tajawo Hijabi dagakan kofa tabata tace “maza saka kije ki shigo dashi nan” wani kalan miyau Yasmeen ta hadiye tana zaro idanu gabanta nafadi baki Maman Intee takama tace “ohh ni jama’a duk wanda yaganki yasan sabon shiga ce ke a harkan samari, idan tsoron Baban ki kike kinsan dai bazai taba kamaki anan ba ko menene amfanina idan bazanyi guiding naki ba, wuce jeki shigo dashi idan naganshi mai hankali ne dakaina zan kira Ammi ki namata wannan sanarwan, wuce kije kishigo dashi” Gyadamata kai Yasmeen tayi duk atsorace take ya akayi yasami number ta, ya akayi yayi tracing nata zuwa nan wannan wani kalan takadirin maye ne? Da gaske babu inda bazai iya samota ba, ahankali take tafiya kanta akasa har zuwa waje motan ita kadaice pake awajen hakan yasa takara hadiye wani kullutun abu awuya tawuce wajen motan kafin takai taga an bude kofar baya alamun nan zatazo hakan yasa takarasa wajen, ko cikin motan bata kalla ba kanta akasa tana wasa da dogayen yatsunta ahankali kaman yar yarinya tace “ance…….ance kashigo” tunda tafito yake kallonta hartazo wajen, hannayen ta datake wasa dasu ya kalla kafin yasaki dan murmushi softly yace “wayace in shigo”? Dan dagokai kaman barauniya tayi danta kallai karaf suka hada ido dasauri tasauke kanta kasa, murya chan kasa kaman mai shirin fashewa da kuka tace “Maman Intee” tana maganan tajuya da sauri tawuce ciki yabita da kallo wani irin sweet smile yasaki ganin dukya kara firgitata ganinshi datayi yazo nan kuma yakira number ta, ga mamakin Dan saukowa yayi daga motan tareda gyara zaman suit nashi ya da bakin glass na idanunshi yafara tafiya ahankali yawuce cikin shagon tana tsaye chan wajen kanta, kujerun dake wajen tanunamai da yatsa ahankali tace “kazauna” murya chan kasa yace “okay Wifey” dasauri takalleshi shima ita yake kalla tareda zare glasses na idanunshi daidai Maman Intee tafito tace “laaaa shine tabarka bata baka ruwa ba kaga shirmen Yasmeen ko” tajuya takalli Yasmeen dake rakube awajen kanta tace “wuce kije ki dauko ruwa sai kizo ki tambayeshi mai zaici yafito daga aiki keda kikasan harka da dalibai da wuya imaza” juyawa tayi tashige ciki itakuma Maman Intee takaraso wajen kan Maheer akasa kaman bashi ba yace “Ina yini Hajiya” washe baki Maman Intee tayi tace “ina Hajiya ai kirani da Maman Intee na ai yanzu an dawo daya, to ina gaji? Ya aiki? Yakuma fama da dalibai? Tacemini kai lecturer sune, Allah ubangiji ya taimaka” dan murmushi yayi kadan batare dayay magana ba ganin yanada kunya yasa tajuya takalli kofan ta kwala kara tace “ina ruwan zama kikai aciki” tajuyo takalli Maheer tace “Yasmeen fa akwai shirme abinka da yar fari, kuma yarinya ce she’s just 20yrs, FCE ma banjin tacika 2months da farawa ba dan Allah asamata ido dan gaskiya na yaba da natsuwa ka kaine saurayinta na farko wlh wlh aduniya, yaya sunanka”? Ahankali Maheer yace “Maheer” murmushi Maman Intee tayi daidai Yasmeen nakawo ruwan gora mai sanyi a tray ba zobo bakomi Maman Intee tasaki baki saikuma tace “bari naje ciki ni, Yasmeen yafada miki kome zaici idan ma babu saikizo ki dafamai kinji” Gyadamata kai tayi batai magana ba Maman Intee tawuce ciki itakuma Yasmeen ta ijiye ruwan akan table tajuya dasauri zata wuce karaf taji yarike kasan hijabinta amman irin rikewan dabazaka taba gane shine yarike ba dasauri tajuyo kaman zatai kuka ta tsaya tareda dauke kai, lumshe idanu yayi yabude su asanyaye, murya chan kasa yace “baraki tambayeni mezanci ba” batare data kalleshi ba makemai kafada tayi tahaderai tace “ka saken” dan juya mata idanu yayi yace “naki” dasauri takalleshi, wani cute smile yasakin mata dasauri tasauke kanta kirjinta na bugawa murmushi namai mugun mugun kyau, murya chan ciki kaman baiso wani yajisu yace “I want tuwo da miyan kuka da zobo” dan turo baki tayi batare data kalleshi ba tace “toni ka sakeni” ahankali yana kallonta yace “toni ki kalleni” juyowa tayi dasauri suka hada ido jin yanda yay magana kaman ita, faduwa gabanta yayi ganin yanda kwayan idanunshi kewani irin kallonta kaman zai hadiyeta dasauri ta fizge hijabinta da karfi tawuce tai ciki yabita da kallo.
✨Kk✨


EPISODE 4️⃣6️⃣




Bata wani jima da shiga ciki ba Maman Intee taleko tana murmushi tace “tace tuwo kake so ko wlh bamu cikayin tuwo akasa ba amman yanzun nan zata maka dan Yasmeen makes the best tuwo da miyan kuka a shagon nan” adan kunyace ya gyadamata kai ciki Maman Intee takoma ganin Yasmeen kikam atsaye bata fara komiba yasa Maman Intee tashiga salati tareda kama baki tace “yau ina ganin bakin hali, yanzu baraki daura miya awuta ba nina tayaki yin tuwon ba kin tsaya kikam kaman gunki anan, ke bakiji dadi Allah yabaki mutumin arziki haka ba yaro gashi matashi ga kyau ga aikin yi abinshi, ga uwa uba kunya ke kinsan yanda mijin aure ke wuya kuwa, je daura miya kafin na makeki” wucewa tayi tana turo baki tahau daura miyan kukan itakuma Maman Intee ta tayata daura ruwa, Maman Intee tajuyo ganin tahada sawa yasa tace “to hadamai juice na pineapples da banana da kwakwa tunda bamu da zobo yau” batai musu ba tawuce tashiga hadawa tanayi tana gamawa tasa a fridge dan yay sanyi.


Cikin 15min sun hada tuwo da miya Maman Intee tasa tahada komi a tray ga man shanu abin yayi kyau daukowa tayi tafito daga kitchen din, dago kanshi Maheer yayi yana kallonta kaman yazo ya karbe tray a hannunta but baiso yataso tsoro yasa ta kabar hakan yasa bai tasoba har wajen tazo ahankali ta ijiye tray zata juya dasauri yarike hijabinta karaf hakan yasa takasa motsi tajuyo takalleshi murya chan kasa Maheer yace “sit down” duk yanda taso tamai musu kasawa tayi ahankali sabida yanda ya tsareta da idanu tazauna tasauke kanta kasa, tuwon yakalla dake tiriri da zafinshi saikuma yakalleta murya chan kasan makoshi yace “thanks” kin kallonshi tayi still, spoon yadauka yana kallonta yanda maroon hijabin yamata kyau, gashin giranta sun kwanta sosai, yakai spoon din cikin tuwo ya gutsuro ya dangwala amiya shi wlh yamanta tuwon da zafi yakai bakinshi wani kalan konamai lips da harshe tuwon yayi baisan lokacin dayasaki spoon din kasa ba yace “auuuchhhhh!” da sauri Yasmeen takalleshi jin faduwan spoon akasa, hannunshi yakai wajen bakinshi yabude mouth dinshi yana fifita da hannunshi yana hura bakinshi daya kasa hadiye tuwon dake tafarfasamai harshe, he looks super cute and innocent and so sweet yanda yakeyi mantawa tayi dakomi dasauri tasa hannunta tadauki glass cup da cold pineapple juice datamai keciki tabashi batare datai magana ba tsabagen yanda yakejin zafi cup din yakarba hannunshi ya gogi nata dasauri yakai bakinshi yahausha da sauri da sauri wani kalan mugun dariya abin yabata, murmushi tayi tareda daukekai zuwa one side cikin kukkuni chan kasa tace “rago kawai” “me kikace?” Taji muryanshi ahankali yay maganan dasauri takalleshi suka hada ido har lips nashi sun kara pink sabida yanda tuwon ya konasu, dan hararanshi kadan tayi cikeda tsiwa tace “ni badakai nake ba” dan murmushi kadan yayi yasauke cup din kasa yakalleta yace “ni kika cema rago”? Sake dauke kanta tayi cikin kunkuni tace “kunne kaman na maciji” “nine maciji”? Juyowa tayi tadan kalleshi tana zaro idanu takasa magana idanunta yabi da kallo dasukaji kwallin Ammi batare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace “you have the most beautiful eyes I’ve ever seen in my entire life Fateema” dasauri Yasmeen tasauke kanta gabanta nafaduwa yatsunta tashiga wasa dashi bata kara dago kanta ba, tass yacinye abincin ya shanye juice din tareda lumshe idanu wlh yakoshi kaman cikinshi zai fashe, wannan tuwon yamafi na rannan daya sayo dadi, she is such a talented cook, duk yawace yawacen dayayi aduniya bai tabacin abinci Mai dadin abincinta ba.
Zaro kudi yayi daga aljihunshi 20k ya ijiye a gefen tray din kafin yamike tsaye ahankali yana kallonta, yace “kicema Anty natafi” dagokai tayi anoke ta kalleshi, glasses na idanunshi yamaida kan idanunshi anatse yace “by 4 kibar nan and go back home banson ki kai 5” dan juyamai idanu tayi azuciyanta tace “sannu ubana” anatse yawuce yafita daga shagon adan sace tabishi da kallo kaman tace yadawo batamasan mesa ba, sai alokacin taga kudin daya ajiye dasauri tadauka duka duka abincin dayaci 7k ne wannan plenty money fa, daidai nan Maman Intee tafito ganin kudi yasa da sauri takarba tace “badai kudin abincin yabiya ba akan mene yana surukina to be” turo baki Yasmeen tayi ta kwashi tray tawuce ciki abinta.
Karasa taya Maman Intee ayyukanta tayi jin ana kiran la’asar haka nan maganan shi yafado mata arai, dudda tana gayama kanta bazatabi umarnin shi ba samin kanta tayi da saka hijabi tama Maman Intee sallama kan zata tafi tatafi, tana fita Keke tagani already pake agaban shagon, Mai keke yace “Hajiya kece Yasmeen ko wani bawan Allah yabiyani na ijiyeki agida yabani ledan nan kuma nabaki” Keken yajuya yadauko wani cute leda mai kyau daga bayan keken yamikama Yasmeen dake tsaye tana kallonshi, ledan ta kalla takasa amsa mai keken yace “amshi mana Hajiya” ahankali tasa hannu ta amsa, Mai keke yace “yauwa to shigo mutafi” kalle kalle tashigayi awajen saikuma ahankali tai bismillah tashiga tariga ta sadakar ita wannan mutumin tasan ko kasheta yay niyyan yi yanzu zai iya gwara tabishi ahankali kawai surabu lpy Baba ya tsokano shi.
Saida taga hanyar da akebi aje anguwansu akabi hankalinta yadan kwanta, ahankali tabude ledan dake hannunta chocholates ne ciki dayawa irin expensive cute chocolates din nan dasauri ta maida ledan tarufe tacigaba da kallon hanya, nunamai har anguwansu tayi har kofar gidansu mai keken yakaita sai alokacin tasauke ijiyan zuciya tasauka mai keken yatada kekenshi yatafi abinshi itakuma tabude jakanta ta wurga ledan chocholate din sannan ta rataya jakanta tai sallama tashiga gidansu daidai Ammi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login