Showing 9001 words to 12000 words out of 190707 words

Chapter 4 - KYALKYALIN KAUNA HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

11 Oct 2024

9314

“ni”? Akufule Sa’a tace “a’a bakeba da gatari ake magana, kinga Farida kada ki kara sata a zancen mu ita ta sani tsoron Baba saiyasa kin kasa auruwa saisa har yau ko me babur baitaba cewa yana sonki ba” adan tsorace Farida dake kallon Yasmeen itama tace “kuma Anty Yasmeen duk kin fimu kyau wlh haka har yan unguwa ke cewa, wani kalan sweet skin gareki coffee coffee, butter butter dake” hararanta Yasmeen tayi ta tashi batare datace musu komiba tashiga cire kaya ta daura zani tafice wanka taje tayo sannan tadawo, gaban sip nasu taje taciro wata atampa mai kyau brown da aka mata dinkin doguwan riga saka sannan tadauki jakan zuwa aiki school nasu tadawo wajensu tazauna handout taciro tamikama Sa’a tace “dan Allah karanta mini page 10 Ya Sa’a mutumin yace shi baya fadin ranan test kuma kinga gobe Friday zani school” fizge handout din Sa’a tayi tace “ni kinaso na taimakeki amman ke baki taimako na” dan murmushi tayi daya karamata wani kalan kyau tace “to kiyakuri bazan karaba, ba Farida tace yazo bayan layi ba, ita saita miki gadi koda Baba yazo saita miki flashing koda wayan Mama ne” sai alokacin Sa’a tai murmushi sannan tabude page 10 din tashiga karanta mata tai shiru tana saurare anatse, daidai Sa’a tazo wani gaba da sauri Yasmeen tace “Ya Sa’a yimin spelling phe……ri…” dasauri Sa’a tace “peripherals wai?” Gyadamata kai Yasmeen tayi da sauri tana ciro wani byro daga jakanta, Sa’a tace “P, e, r, i,p,h,e,r,a,l,s” palm nata Yasmeen ta kalla data rubuta words din ahankali tashiga maimaitawa da baki kafin takulle idanu tana kokarin karanto spelling din. “P, E R E P E” ahankali Farida dake kallonta tace “P, H ne Anty Yasmeen kafin E din” ahankali Yasmeen tabude idanunta takalli tafin hannunta, ajiyan zuciya tasauke dayasa Farida taji idanunta sun kawo kwalla tashi tayi dasauri takwashi cups na kokon dasukasha kawai tafito daga dakin, Yasmeen nabata tausayi tun tana yarinya tana yar karama lokacin tana ganin yanda Ammi ke bugun Yasmeen idan ana koyamata homework agama fada mata ta manta har Ammi tagaji tadena dukanta, gashi Anty Yasmeen tun tana yarinya lokacin yarinya ce mai zuciyan so takoya babu wurin wanda bata zuwa agidan nan yakoya mata karatu but still, su Baba, su Baffa su yayinsu, hatta su Yaya da bama suyi makaranta ba suma sun koyar da Yasmeen ABCD but still, Yasmeen bata taba cewa sabida ta girmeta baratazo takoya mata ba, har yau so da dama zatazo tasameta tabata handout takaranta mata, yanda Yasmeen ke wahala da karatu abin na mata gwarama tadaina makarantan to dole ne karatun bayahuden gwara tacigaba da zuwa wajen Maman Intee koyan girke girke da Islamiyya abinta wannan bokon ba dole dan bakar wahala kawai Anty Yasmeen kesha. Wasu hawaye masu zafi guda biyu ta goge kafin ahankali tadauke bucket din tawuce bayi.


Kusan sau uku Sa’a takaranta mata page 10 din kafin tabata handout din tace “to hada bakin ki karanta naji, kinga kun kusan fara first semester exam gashi bakince malamai kusan 4 ke muku course din ba kuma kowanne da nashi Yasmeen yaya zakiyi wannan na mutum dayane cikinsu yanzu kike page 10, wannan page 10 din nan kadai zai iya daukanki 10days kafin ki gama iyawa ki gama gane spelling da komi wai karatun nan dole ne, ki hakura ki barshi, karatu is not for u Allah bai baki kwakwalwan bane ba kawai, ki sami Baba ki sanar dashi kada kiji tsoro wlh” mayun gray eyes nata Yasmeen tazuba ma Sa’a tanajin wani abu nataso mata daurewa tayi ahankali tace “nidai in karanta kiji mini”? Ijiyan zuciya Sa’a tasauke zuciyanta namata badadi sabida yanda taga Yasmeen na wahala da karatu tace “karanta naji to tunda ke Allah yamiki bakin zurfin ciki” anatse Yasmeen tafara karatun, yanda take hada words da kyar tana fadi zaka dauka yar primary 1 ce, layi biyu tayi masu kyau takakare at the 3rd line wajen kalman Jahillya period, tashi Sa’a kawai tayi tace “nima zanje nai wanka inada lectures 11 gwarake Baban ki yanzu zai wuce dake ya kaiki ni saidai nahau mota, better think about abinda nafada miki and meet Baba da maganan” binta da kallo Yasmeen tayi harta fice daga dakin kafin ahankali tadawo da kanta takalli littafin idanunta kan kalman data kasa fadi, yatsanta tadaura kan Ja din ahankali tace “ga…..no ja is JAAAA” tai shiru tana kallon Hi tace “Hi, kaman hi din hello kenan yauwa ai nasan hi” shiru tayi tana kallon LI, itafa duk words dazata gani ta iya karantawa to tazauna ta haddace spelling din ne tasan yanda ake kiran word din, irin su Apple, cup, house, happy, da sauran kalamai da makaranta yasa ta zauna ta koyi spelling din ta haddace other than that ko she yanzu karubuta mata inhar bata taba zama da takoyi kalman ta iya shi ba to kafin ta iya pronouncing she din nan aiki ne babba agareta.
Labulen dakin aka daga hakan yasa tajuyo dasauri Baba ne yayi wani irin kyau yasa goggagun uniform, yana kallonta yace “da hijabi mutafi” gyadamai kai tayi tamike tawuce sip wani pink gogaggen hijabi tadauka tasaka dake kaimata har kasa tadauki jakan zuwa aiki da flat takalminta najiya tasaka sanan tafito, su Ammi dake tsakar gida sukace “adawo lafiya” gyadamusu kai tayi Nana tabiyota har gate tace “Anty Yasmeen yauma ki kara kawomini tsaraba” wani kalan murmushi Yasmeen tayi sannan ta duko hancinta taja tace “Nanani na ta iya kwadayi ko shikenan zan kawomiki” washe baki Nana tayi tana tsalle tareda mata bye bye ta kwala ihu tace “Baba bye bye” bye Baba yamata yana murmushi shima.

Har gaban shagon Maman Intee ya ijiyeta sannan yaciro 1k a aljihun shi yabata yace “gashi idan kin tashi kikaga babu keke ki koma ki zauna call me da wayan Maman Intee zanzo na daukeki kada ki kara takowa daganan har gida is risky kinji” gyadamai kai tayi ahankali tace “to Baba” tasa hannu zata bude kofar kaman daga sama taji Baba yace “me da me kuke bukata”? Dasauri tajuyo ta kalleshi tana zaro manyan fararen idanunta masu bala’in kyau, maimaita tambayan Baba yayi yace “medame kuke bukata keda yan uwanki”? Ahankali tace “ai Baba munada komi kasaya mana last month” takalmin kafanta yakalla yace “baki bukatan takalmi” murmushi tayi akunyace tace “eh inaso Baba” ahankali yace “dame kuma” kanta tasauke akasa cikeda ladabi tace “inaso na dinga hijabi sabo wayan nan sun tsufa wasu iron ya konamin, Ya Sa’a kuma ita jakane da takalmi da turare, Farida ma haka, sai Nana ita ribbon takeso da dankunne” jinjina kai yayi yace “shikenan tafi” gyadamai kai tayi cikin cool voice nata tace “Baba Allah ya tsareka yakara daukakaka Allah bada sa’a yakawo rabo Mai albarka” murmushi yayi yace “Ameen diyar Baba kema Allah miki albarka” murmushi tayi sosai tace “Ameen” sannan tabude kofan motan ahankali tafice tawuce ciki, saida Baba yaga shiganta sannan yajuya motan yawuce tareda ciro numbershi yay dialing number Ammi, wayan na gab da katsewa tadauka, strictly yace “yaran nan sun tafi school”? Ahankali tace “Farida ta tafi” “Nanah fa” Baba yay maganan bawasa, bayabo ba fallasa Ammi tace “naga yau Thursday danace ne kawai abari monday sai takoma gabaki daya tunda bataje tun ranan monday ba” shiru yayi kaman bazaice komiba saikuma ahankali yace “banson kina mini ganganci da karatun yarana, sabida kinga ina rigasu fita shine zaki dinga barinsu bazasu makaranta ba, Allah kaimu gobe I will personally take them to school” cikin kunkuni Ammi tace “kanada lokaci ne ai saisa” cikin fushi Baba yace “me kikace” dasauri tace “ni bada kai nai magana ba” dan murmushi yayi, cikeda son su shirya danshi baiso yana fada da matarshi yace “inda dani kike dana juyo motar nan back nadawo gida nabaki hukunci mai kyau” kaman jira Ammi take tace “bani kama mugunta jiya ba” dan murmushi yayi yana shiga cikin police headquarter nasu da aka budemai gate yace “haka akema mata mai tsiwa” dan murmushi kadan Ammi tayi dayaji sautin murmushin hakan yasa yaji hankalinshi ya kwanta sosai ahankali yace “ina sonki sosai Maryam kinsan da haka ko”? Gyadamai kai Ammi tayi kaman yana gabanta jiki asanyaye tace “nasani” ahankali yace “haka kuma inason yaran dakika haifamin aduniyan nan sosai Maryam” murya chan kasa tace “I know” kashe motan Baba yayi yace “dan haka inaso kome kowani decision zan dauka akansu ne supporting me okay, banso muna fada akan yaran nan” ahankali tace “shikenan bazan karaba” murya chan kasa Baba yace “kada ki kara kiran Yasmeen da dakikiya” tasan maganan nan yafi komi tabama Baba rai hakan yasa tace “kuskurene I promise bazan karaba Baban Nanah” murya chan kasa yace “good! Kemin list na abubuwan dakukeso all ki aikamin tawaya, bari naje na zama CP Commissioner Ibrahim Ibrahim mijin Maryam koba hakaba” kwashewa da dariya Ammi tayi ta wayan tace “hakane bari naje na kunna news na kalla” dan dariya yayi yace “to na barki lafiya” ya katse wayan yana murmushi feeling so happy and at ease nothing beats a happy family, his whole entire family is his everything, he literally lives for them now he can go and collect stars nashi cus he know cewa he deserves it, he’s such a dedicated hardworker both in his field and in this house yay maganan yana fitowa daga cikin motanshi.

EXCLUSIVE IS 5k
GGM IS 1k
Kindly pay into 3107021073 Aisha Muhammad first bank
✨KYALKYALIN KAUNA✨



EPISODE 5️⃣


✍🏻M SHAKUR

Saukowa yayi daga stairs ranshi duk abace daidai gaban office dinshi ya tsaya batare dayama security wani kyakkyawan kallo ba yace “tell my driver to get the car ready zan fita yanzu” yana maganan yabude office nashi ya shiga, security daya yabiyoshi cikin office din, wasu keys yadauka a drawer da wayanshi yawuce akufule yace “get the coke let’s go” daukan cocaine nakan table dinshi security yayi yakashe wutan office din sannan yafito daga office din yabi bayan Maheer dake tafiya kaman sarki yashiga lift fita sukayi daga club din already wata arniyan bulletproof Chevrolet Suburbans jeep na kampanin Inkas baka na gaban entrance din danshi kwata kwata baya hawa motan daba bulletproof ba for security, ga wasu bodyguards dake sanye da suit su hudu tsaye gaban motan suna ganin Maheer budemai bayan motan akayi kaman wani gwamna yafito hakan yasa yashiga dasauri ya zauna aka maida kofan aka rufe shikuma security ya tsaya kikam yana jiran Maheer da coke a hannu, kusan 1min Maheer yadauka kafin asauke glass din bayan leko da kanshi Maheer yayi hannunshi rikeda Cuba Aliados cigar wanda kudin shi kadai ya ishi mutum yasai manyan filaye kusan guda goma dan irin tulikin designers taban nan ne da turawa kesha mai Aromas na creamy oak, leather, fresh brewed coffee, tobacco, earth and sweet bread emanate from the wrapper, along with a small amount of citrus peel buso da hayakin yayi awaje ahankali yace “you see those two guy over there” yama security pointing gaban wani Brabus jeep dawasu samari biyu ke tsaye suna magana yace “give it to them” cikeda girmamawa yace “yes sir” ahankali yakoma cikin motan tareda jinginar da bayanshi ajikin motan yana lumshe ido yana huro hayakin taban, almost 2min yayi ahaka kafin murya chan kasa yace “what says the time Dan”? PA dinshi dake gaba kusada direban ne shima yana sanye da bakin suit yakalli agogon hannunshi calmly yace “is 3:45AM Sir” ahankali yace “and what is my schedule”? Wani iPad bodyguard din yadauka tareda dannawa sannan Anatse yace “kanada meeting da wannan senator by 4:15AM” wani kalan gajeren tsaki yaja har lokacin bai bude idanunshi ba, kaman wanda magana kema wahala yace “then what”? Bodyguard dake kallon pad din yace “1hr dama kace zaka bashi, immediately after that kuma kanada zoom meeting da head na distribution department namu na Lagos dakuma Delta, sunce akwai shortage na staff dan yanzu end users sun soma yawa” kaman wanda zaiyi bacci yace “can I cancel the meeting Dan”? Dasauri bodyguard kuma PA din daya kirada Dan yace “no sir you can’t, meeting din is very important unless zakai flying gobe kaje duka state din kai magana dasu” yatsine fuska Maheer yayi yace “naaah I can’t” dan ijiyan zuciya yasauke yace “I guess I will take the meeting then, let’s go” yay maganan yana zaro taban daga bakinshi daya gamasha anan kasan mota ya yar ko ajikinshi idanunshi a lumshe kusan tafiyan 40minutes sukayi, sannan suka yanki wani daji almost 20min drive sukayi kafin su kai wani babban gida gari guda Mai bala’in kyau, gate wani soja yabude musu sukaja motan ciki, wasu motoci guda biyu wanda suke pake abangaren wajen parking na baki yasa yagane senator yazo.

Babban gida ne sosai da ta ko’ina security kawai kake gani da bindigogi a hannunsu suna zagaye babban compound din da akalla sunkai su 15, kashe motan driver yayi Dan yasauko dasauri yabudemai kofa saukowa yayi ahankali yakalli Dan yace “you know wat to do” dasauri yace “yes sir” hanyar main entrance Maheer yayi yashiga asalin babban flat na wajen, shikuma Dan yajuyo zuwa wani different flat dake opposite wanda Maheer yashiga, direct bude kofa yayi wani babban daki ne that’s more of office ga kujeru arnaye dakasan money lives here, wani mutum ne babba zaune kan kujera ga men dinshi tsaitsaye abayanshi tsayawa Dan yayi akanshi kaman Soja yace “nan bada jimawa ba Oga zai ganka” gyadamai kai senator yayi hakan yasa Dan yajuya yafita daga ciki.

Almost 20min Maheer yayi aciki sannan yasauko cikin wata beige cotton suit na Cesare Attolini one of the world most expensive suit brand
mai shegen kyau yana zuba wani kalan kamshi dasaika lumshe idanu, yasa wasu covershoe dake kyalli na tomford hannunshi daure da wristwatch na damier graphite race na LV, Dan na tsaye acikin falon dawasu security guda uku ganin yasauko yasa sukai gaba yana biyedasu abaya suka fita tareda budemai kofa, fitowa yayi yana gaba suna biye dashi daga dakin zuwa dayan bangaren, budemai kofa sukayi hakan yasa senator yadago kanshi da sauri yakalli kofan cikin wani isa da cika idanu Maheer yashigo yana tafiyan nan kaman king, kallo daya yama senator Ya watsar yawuce direct zuwa kujeran dake gaban table dake cikin office din yazauna tareda daura kafa daya kan daya sannan gently yajuyo yazubama senator idanu batare dayace kala ba, Sosai senator ke kallonshi dama Pablo Pablo dayaji kowa nafadi bawani babba bane yaro ne matashi dake ganiyan samartaka but still jibi yanda yacikamai idanu, yaron dakowa shakkan shi yake babu wani hukuma data isa ta taba kayanshi, da hannu yama Men nashi magana kan su fita, saida suka fita sannan su Dan suma suka fita daga dakin tareda maida kofan suka rufe sannan Senator yajuyo yakalli Maheer yace “yau gani ga the African famous Pablo Escobar, I heard a lot about you bazanyi karyaba ganinka yamafi jink……..” hannu Maheer yadagamai no chills kawai no nonsense kai tsaye yace “you’ve been bugging my management for the past 3months kenan kanason ganina amaka arranging meeting, so can you skip the talk and get to the chess you have just 15min left in one hour dana baka” durun uwa! Senator yafadi aranshi cikeda mamaki, idan haihuwa ne zai iya cewa ya haifi Maheer dan yanada yaro dake 40yrs amman jibi yanda wannan yaron dabazai wuce 30something ba idan yay wuta yabashi 35 ke mishi magana, he sha must give him this yaron is damn charismatic kana ganinshi kasan yasan abinda yakeyi, ga shegen kwarjini which dudda ya haifeshi but still bakaramin kwarjini yamai ba, dan murmushin yake yayi hakanan yaji kawai gabanshi nafaduwa wani shakkan Maheer na tsiro aranshi, washe baki yayi yana kallon Maheer din daya kafeshi da idanu yana kallon kwayar idanunshi bayako kyaftawa yace “inaso na shigo harkan nan ne, naga shine harkan dayafi komi kawo kudi yanzu aduniya kakap, da power dakuma matsayi, amman inaso na kafa tawa fadar a Chadi ne, da Cameron dan basu da abubuwa, abinda yasa nazo wajenka naji kayi suna awajen supplying kaya masu kyau da inganci sannan kwata kwata ba’a samin matsalan shipment dakai duk garin dakaso kai kaya kayanka na shiga saidai in bakaso ba to shine nakeson naji yaya za’ayi” tunda yake maganan Maheer ke kallonshi saida yagama maganan tsaf ido cikin ido Maheer yace “zaka iya business dani”? Dasauri Senator yace “kaman ya zan iya business dakai? Ba son aiki dakai yasa harnazo wajen ka ba” tsareshi Maheer yayi da mayun thug eyes nashi, irin kallon real criminal din nan yakemai yace “I said zaka iya business dani”? Wani kalan shakka Senator yaji ya diran mishi arai na Maheer, cikinshi nawani kalan hadewa kaman zawayi na shirin kamashi tsabagen yanda gabanshi kefadi, baki yabude zaiyi magana yaji muryanshi ta dishashe, gyaran murya yayi dasauri yana kallon Maheer still kafin ahankali yace “zan iya aiki dakai Pablo, I assure you bazaka taba samin matsala daga wajena ba, koda wani abu zai faru to dagata sama bakada matsala” lumshe idanu Maheer yayi yabude, kafin ahankali yamika hannunshi yadauki kwalin cigar dinshi dake kan table din yabude yazaro kuttubi guda daya yasa abaki sannan yadauki lighter ya kunna kafin ya ijiye lighter ya zuko tabar tareda cireta abakinshi yakalli Senator in the eyes sannan ya bursar da hayakin taban saitinshi a natse yace “for you to join my organization kadai akwai sum of money dazaka biya na registration which a Euros € zaka biya, all products dazaka saya you have to pay kafin mubaka payments are being done in dollars bana harka da nigeria dollars, saikuma bayan nabaka kaya ka saya duk wani profit dazakai making from my product zaka dinga bani 5%, sai last but not least i kill duk wanda yay betraying dina kodako kaine, I will waste your life and that of your family down to your great grand kids that’s if akwai, idan ka shirya my assistance and lawyers will put you through everything kuyi signing papers, nagama dakai you can excuse me” Maheer yay maganan yana nunamai kofa kallonshi Senator yayi yadauka kodan hannu Maheer zai bashi su gaisa amman ina, ashe dai duk labaran dayaji hakane, yaron akwai wulakanci da rashin mutunci sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login