Showing 6001 words to 9000 words out of 190707 words
akasuwa idan ana hiran nan nakan cemusu uhm’uh kada suce haka, inada kani da tunda yashiga aikin yan sanda yau kimanin shekaru kusan sha takwas kenan daidai da cin hancin naira biyar baitaba karba ba kuma ahankali ahankali anata karamai girma gashi yau za’a nadaka CP maiyafi haka? Nan gaba saidai muji an maidaka IG gabaki dayama” Baffa yadanyi shiru tareda daukan ruwa ya kurba sannan anatse yace “a kullum ina fadamaka kowani matsayi kasamu arayuwan nan kayi amfani dashi wajen magance matsalolin al’umma gabaki daya, wajen yaki da rashin gaskiya da kafa gaskiya, wajen taiwakama addinin musulunci, wajen tsare hakkin dan adam da saman da zaman lafiya adoron kasa, ta hanyar kawo karshe sata, kidnapping, shaye shaye, fyade, kisan kai da sauransu, Allah ubangiji yabaka sa’a yakuma tayaka ruko sannan kasani wannan position din amana ce, karkaci amanan sabon seat din nan kaji Ibrahim” anatse Baba yace “naji Baffa nagode sosai” dafashi kanninshi mai binshi yayi Baba Karami wanda shine mijin Hajjo yace “Allah yatayaka riko Yaya” murmushi yayi yace “Ameen” tashi Baffa yayi yace “to kumu tashi mutafi masallaci, kukuma matan sai kuyi naku sallan” dan juyawa Baba yayi yakalli Ammi dake kallonshi cikeda farin ciki dauke kai tayi dasauri ganin sun hada ido dan haushin shi takeji wani kalan murmushi yayi yabi su Baffa suka wuce mosque batare dayace mata komiba.
As usual daman gidan ana sallan isha’i kowa ke shigewa daki dan yara anje school angaji, weekends ne dama yaran gidan basu cika bacci da wuri ba dan ranan baaje boko ba, Ammi na idar da salla tadauki Nanah datai bacci asaman gadonta tafito waje tashigo dakin su Yasmeen tagansu duka sun kwanta dudda ba bacci Sa’a da Farida keyi ba amman Yasmeen tadade da bacci, kwantar da Nana tayi tareda su tana kallon Yasmeen tace “kin gaji ba dole kiyi bacci ba cikin dare kya tashi kiyi ishan kukuma baraku kashe wutan bane” dasauri Sa’a dakejan lullubi tace “Ammi dan Allah kikasha mana” dan hararansu tayi sannan takashe musu tajawo musu kofan tafito tashiga nata dakin, maida kofan falon tayi tarufe sanan tashiga uwar dakinsu, dan matsakaicin bayinsu da wanda kadai ake aciki ta shiga ta watsa ruwa sannan tafito ta shirya cikin kayan bacci ta fesa yan turarukanta ta kwanta.
Wuraren 10 su Baba suka shigo gidan, direct dakin yara yawuce, shikuma Baffa yana kulle gate, ahankali yatura kofansu yashiga wayan hannunshi ya kunna saida ya dudduba su ganin duk sunyi nisa abacci sannan yasake Tofa musu addu’a yafito tareda maida kofan nasu ya kulle sannan yama Baffa sallama duk kowa yashige dakinshi maida kofan dakinsu yayi yarufe sannan yawuce uwardaka, jallabiyan shi yashiga cirewa yana kallon Ammi dako sallaman shi bata amsaba kuma yasan ba bacci take ba, bayi yashiga bakinshi ya wanko tareda dauro alwala wanda wannan haka yake kullum sannan yafito ya kashe wuta taredayin bismillah yahau gadon, ahankali ya matsa kusada Ammi yakai hannunshi yana kokarin juyoda ita cikin wata kalan murya yace “juyo kimin Allah sanya alheri dan ke kadai ce kika rage baki samini albarka ba” kabarda hannunshi tayi cikin fushi da rashin son yin magana dashi tace “stop touching me” dan shiru yayi saikuma chan yace “kiyakuri to” kaman jira take wani kalan juyowa tayi saikuma ta tashi zaune cikeda masifa amman bamai karfi sosai ba gudun kar ajinsu tace “nagaji da hakurin dakeke bani kullum saikagama cimini mutunci agaban uban kowa sabida yara saika biyoni da daddare kana cemin nayakuri yau bazanyi ba kaji Ibrahim bazan yi ba” shiru Baba yayi jin takira sunanshi yau kai tsaye yasan ranta yabaci, cikin wani yanayi na nuna kunci tace “Ibrahim ka manta cewa nine mahaifiyar yaran nan, nine nadaukesu wata tara acikina, nine nai laulayinsu, haka kuma nine nan nikadai nashiga labour room nasha nakudan yaran nan nahaifosu maisa kake treating dina kaman banson yarana kaine kadai ke sonsu why? Inda ba nine na haifesu ba sai ace eh dama banice mahaifiyar su ba but this girls are mine, nine mahaifiyar su, mesa kakemin abinda kakemin akansu eh Baban Nanah”? Shiru Baba yayi baice komiba baki Ammi tabude zatai magana sai kawai kuka ya kufce mata kawai tafashe da kuka sosai dan abinda yake mata na kona matarai ainun, wani kalan sanyi jikin Baba yayi ahankali yajawota zuwa jikinshi batai musu ba tashige bayanta yashiga shafawa cikeda lallashi yace “kiyakuri bazan karaba, I know you love our girls beside yaranmu ne nidake muka haifesu sometimes ina miki fadane sabida sakaci, Maryam yara mata muka haifa guda uku, hakki ne su akanmu nida ke we have to protect them, support them, musa idanu akan lamarin su, mu tarbiyantan dasu da kyau kinsan idan ka tarbiyantan da yara mata da kyau ka aurar dasu Allah zai bamu aljanna ranan gobe kiyama? Hadisai daban daban daga Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata agareshi inda yake nuna falalan da iyaye suke samu ranan gobe kiyama dasuka tarbiyantan da yara mata da kyau, Please understand me kidaina fushi dani, inaso kiyi tsayin daka kaman ni akansu that’s all stop crying matata, I am simply doing the right thing” yay maganan yana bubbuga bayanta, da kyar tai shiru ta dago daga jikinshi sannan takalleshi dudda cikin duhu ne tace “I understand abinda kake kokarin yi kan yaran nan perfectly well but is too much! You are overreacting, Yara mata garemu kana tareda yaran nan 247, kana yawo dasu kana rike musu hannu a anguwa, anguwan nan kap babu wanda baisan how protective you are towards this kids ba, wazai taba zuwa ya aure su kowa tsoron tinkaranka yake, Yasmeen dinmu is 20yrs kasan mates nata guda nawa sukai aure yanzu alayin nan kadai? Ita ko saurayi batadashi sabida kai, kowa yasan babanta dan sanda ne kuma bai bari akula yarshi” Haderai Baba yayi dasauri kaman bashi ba yace “nina gayamiki aurar da ita zanyi yanzu?” Dasauri itama Ammi dan yau kome zai faru yafaru daidai take dashi tace “to karatu kakeson tayi da kana gani dai she is not going anywhere akaratun”? Shiru Baba yayi yajuya kawai zai kwanta dasauri Ammi tarikemai hannun tace “Ibrahim listen to me ba lallai saikabi abinda nake fadi ba amman inaso kai nazari kan maganata, nagaji damaka shiru ne so I have to tell you abinda ke raina yau, Baban Nanah” Ammi tai maganan asanyaye tace “Yasmeeen tun tana yarinya bansan ko dan ita yar fari bace amman dai me and you munsan tun tana yarinya batada kokari, adaddafe a repeating da chanje chanjen makarantu daban daban sabida kai kanka kagaji da repeating da ake mata aka samu tagama sakandare at the age of 18, tai waec na farko duka f9, waec din daka biyamata tana 19yrs Allah ya taimaka taci shima Allah kadai yasan tayaya tai passing dan am sure kai karan kanka har yau u are still in shock ya yanda tai passing exam din, har yau har gobe bakomi Yasmeen ke iya gani takaranta tsaf ba wani zubin Farida nan kanwarta that is just 15yrs SS3 student ke taimakonta dasu Sa’a, dudda babu kalan lesson teachers da lessons dabaka sata ba, Yasmeen is just like that haka Allah yayo brain nata, I am sorry to say this banson nakira yarda na haifa dakikiya amman me and you munsan cewa kusan hakanne, ka kaita school of nursing tafara anayin weeding exam nasu aka koreta batai passing ba shima F tasamu, dudda lokaci yakuri ni nasan dayaya dayaya kasamu da kyar kasamo mata admission na FCE part term shima yanzu tafara an bata Islamic studies amman she’s not going anywhere with it, infact ni aganina ma FCE yafi bata wahala kan school of nursing, subject daya kusan malamai ashirin akai Baban Nanah kuma kowa da nashi abubuwan karatun ina kakeson yarinyar nan tasa kanta?” Ammi tai shiru tana kallon Baba ganin yaki magana yasa ahankali tace “nasan ka hadata dawata lecturer daka biya tana zuwa office nata ana kara maimaita mata komi sannan da kanka kadauketa ka kaita school na Maman Intee nakoyan su abinci, drinks da cakes which shine abu na farko danaga Yasmeen tasoma iyawa sharp sharp tunda na haifo yarinyan nan” Ammi tai shiru sai alokacin Baba yajuyo yakalleta yace “all lissafe lissafen nan what are you trying to say? Nagayamiki nagaji da kashe kudina akanta ne? Koko kintabaji nai korafi kan rashin gane karatun ta dawuri ne? Ai ni ke biya bakeba ko to ki barni da maganan nan please bansonji” girgiza kai Ammi tayi trying to make him understand her tace “Baban Nanah, abinda nake kokarin cewa shine you might thing abinda kakema Yasmeen shine the best thing any father zaima diyarshi but you are wrong yarinyar nan is going through a lot nine mahaifiyarta kwayan idanunta kadai nake gani nasani, karatun nan yamata yawa, sannan yanda ka tsaya tsayin dakan nan akan yaran nan baka basu breathing space karage, let this children be ko masamu wani yayi approaching Yasmeen da maganan aure, Yasmeeen tayi girma, she’s a very fine beautiful girl, give her space wannan kaita FCE dakake duk Saturday da sunday sannan ka koma ka daukota kabari, let her go on her own and mingle da dalibai irinta, allow Yasmeen kullum tadinga zuwa shagon Maman Intee da kanta, stop holding hannun Yasmeen a anguwa kowa nagani yes ansai kai babanta ne but stop treating this children kaman zaka maidasu cikinka u are being over protective and yaran da maza suka gani daddy’s girls ne tsoron approaching nasu ake barinma kai da u happen to be a police man uniform mutum, kar halin nan naka da tsayayyen uba yasa yarana su rasa mijin aure” wani kalan dogon tsaki Baba yaja yace “maganan banza maganan wofi” kawai ya kwanta tareda juyamata baya Ammi tadade tana kallonshi dama deep down tasan za’ai haka shifa indai kan yaranshi ne bayaji bayagani, abinda yayi shine always best akan yaranshi, tadade ahaka sannan takoma ahankali kawai ta kwanta itama tajuyamai baya kowa da abinda yake tunani, almost 20min suna ahaka sai kawai Baba yajuyo dudda yaso yabarta yahakura kasawa yayi cikeda masifa yace “bani hakki na, kuma wannan abun dana barki kikaje aka makala miki a hannu gobe karna dawo aiki naji shi a hannunki, nafasa dagamiki kafan haihuwa nakeso yara uku sunmin kadan” dukfa fitinanta mijinta yafita tanaji tana gani haka yashiga yin yanda yaga dama da ita kaman ma punishment yake bata, duk yanda takai ga jin haushin shi saida tashiga bashi hakuri sannan yasata ajikinshi Ya matse sosai yace “dagayau kada ki kara fadamin wata magana akan yarana, ni mahaifin su ne bazan taba cutar dasu ba, nafiki sanin abinda yadace akan yarana, inason yarana sama da rayuwata, inason yarana sama da zuciyata, my children are my entire life and reason for my existence, inhar kinason mu zauna lafiya ki koyi sonsu kaman yanda nake sonsu dan indai wannan abin dakike fadamin nayi aganinki shine so to kinyi kuskure ba so bane, idan abinda nake musu shine zaisa kada su sami miji to kada su samu din bangaji dasu ba ban gaji da ganinsu ba bazan taba gajiya da yaran da Allah yabani ba, sai maganata ta karshe kada ki kuskura ki kara kiramin yarinya da dakikiya Yasmeen ba dakikiya bace, my daughter is smart, ranan dana fara kaita makaranta aduniya ko A bata iyaba amman yau anwayi gari ta iya A har Z, ta iya 1234, tasan abubuwa da dama, kisan banbancin tsakanin wanda baya iya gane abu dawuri kokuma karanta abu da wuri da dakikiya, kada ki kara kwantata mini yarinya da mummunan kalman nan kinajina” gyadamai kai Ammi tayi dan sosai taga ranshi yabaci sakinta yayi yajuya mata baya yay bacci abinshi yabarta tana matsan hawayen tsantsan bakin ciki.
EPISODE 4️⃣
Around 4:30 na asuba tabude idanunta tana kallon saman dakinsu kafin ahankali takaranto addu’an tashi daga bacci, kallon yanda Nanah ta cukuikuyeta tayi taredayin murmushi sannan gently tarabata da jikinta ta tashi zaune tana kallon Farida da Sa’a dahar munshari sukeja, lallabawa tayi tasauka daga gadon nasu ahankali wucewa tayi tabude kofan dakinsu ahankali tafito tsakar gidan wucewa tayi bayi dan ko’ina akwai wuta tayo tsarki tafito tadauro alwala tadawo daki ta shimfida dadduma tahau kai tayi sallan isha’i sannan ta tashi tadauko jakan school nata handouts nata taciro tabude babu randa bata karatu aduniya da safe amman bata ganewa dukta yanda zaka mata bata ganewa sannan karanta abu na bata wahala bakowani word ta iya karantawa ba ko rubutawa dudda Islamic studies take abubuwan da ake musu wasu ta sansu a islamiyya but she can’t still write it down, wani zubin fa zatai karatu, zata haddace sannan tazo ta haddace spelling din, amman abu kadan ne zai faru yasa ta manta tass ga FCE dinsu course daya arabashi kusan gida bakwai har gwara datana nursing ma mutum daya na daukan course daya bataso akoreta a FCE, batasan yaya zata kalli Baba ba dudda bai taba fushi dan akorota a school ba kokuma dan batai kokari ba amman tasan babu dadi itane lesson teacher menene menene babu abinda baya daukomata, yanzu haka akwai wata lecturer daya biya a FCE duk ranan Friday take zuwa 4 zuwa 5:30 take mata karatu tana kara koyamata abubuwan da aka musu amman still bata ganewa kota gane mantawa take sai kuma karatu na bata wuta, wani zubin tasan abu but spelling da rubuta abun down kesa tafadi dudda harda spelling lecturer ke koya mata, kuma Sa’a da Farida ma suna koyamata wani zubin ma suke karanta mata handout dinta.
Ajiyan zuciya ta sauke tabude page 10 a handout din na Islamiclaw tafara karantawa tanasa yatsu kaman mai koyan ABCD bill hakki take hadawa take karantawa tayi nisa akaratun kojin bude kofan Baba batayi ba, Baba yadade tsaye bakin kofan yana kallonta kana ganin yanda take karantun kasan she wants to learn it at all cost amman yana bata wuya, babu kalan means da addu’a da basu mata kawai saurin iya abu da ilimin boko ne kawai Allah bai bata ba dudda abin na damun Baba amman bai wani damuba sabida a islamiyya she’s doing very okay dudda nan ma su Farida sun fita ilimi amman still ta iya, ta iya karatun Al Qur’ani ta iya hada baki kawai she is naturally a slow learner, idan Farida da Sa’a zasu iya sura daya a rana daya ita zata iya suran arana biyu ko biyu da rabi saisa ko a Islamiyya ma Farida kanwarta tafita aji.
Dan gyaran murya Baba yayi hakan yasa firgigit tadago kanta tareda ijiye handout din agefe tace “Baba ina kwana” dan murmushi yamata yace “kin tashi kinyi sallan isha’i”? Gyadamai kai tayi da sauri, jinjina kai yayi yace “tashi su Sa’adatu kuyi sallan asubahi to” tashi tayi dagakan dadduman tace “too Baba” shikuma Baba yafice shida su Baffa suka fita daga gidan dan zuwa masallaci.
Salla sukayi sannan kowa ya dauki Al Qur’ani suka shiga karantawa kafin gari yay haske suka fiffito dan zuwa kitchen taya iyayensu aiki, Yasmeen Ammi takalla data gaida tana kallon wani katon pimple guda daya rak daya fito mata atsakiyan goshi tace “zonan” zuwa wajen Ammi tayi dasauri tana murmushi dake bayyana white teeth nata, Ammi dake kallon fuskanta tace “kagan mini shirmammiyan yarinya” Hajjo dake zuzzuba koko akufunan da suka kakkawo tace “hala yau ta tashi da shirmen yan farin ne”? Turo baki Yasmeen tayi ashagwabe tace “Ammi kinga Mama Hajjo ko” murmushi Ammi tayi tana taba pimple din tace “yau idan zaki shagon Maman Intee kidauki pad ki saka ajaka kinajina”? Gyadama Ammi kai tayi akunyace tadan juyo takalli su Hajjo ganin hankalinsu baya kansu yasa takalli Ammi cikin sassayar zakakkiyar yar muryanta tace “Ammi kinada bread ni banson Kokon nan da kosai” tai maganan tana yatsine fuska dan koko bacci yake sata bana wasaba, murmushi Ammi tayi tace “je inada shi ki dauka saiki maza kiyi wanka Babanki ya saukeki a shagon Maman Intee kinsan yau za’amai karin girma kada ku sashi latti” cikeda murna Yasmeen tace “karin girma Ammi”? Ammi tace “ohh uwar bacci natuna jiya dayana fadi kinyi nisa a jam’iyanna naki” kyalkyacewa da dariya tayi kana ganin yanda yake kasan tana bala’in son Mamanta hararanta Ammi tayi tace “za’amaida Babanki CP saiki tayashi da addu’a kina dariya awajen” tsalle tayi tace “Alhamdulillah naji dadi Allah taya Baba riko” cikeda farinciki tafito daga kitchen din tawuce falon Maman su inda Baba yake zaune yana duba jarida sallaman ta yasa yadago kanshi yakalleta hakan yasa takarasa wajen kujeran dayake tsugunnawa tayi adan kunyace tace “Baba Allah sanya alheri” murmushi yamata tareda maida kanshi kan jaridan dayake hannunshi itakuma tawuce tadauki bread din da Ammi tasa tazo tadauka, bin bread din Baba yayi da kallo ahankali yace “zai isheki”? Gyadamai kai tayi dasauri tace “eh Baba” wucewa tayi tafito daga dakin zuwa dakinsu inda taga Sa’a da Farida nashan koko da kosai da aka soya, zama tayi gefen Sa’a dake watsa mata harara saikuma kaman wacce ta tuna wani abu tace “Yasmeen kinsan Fahad yace yau zamu hadu narasa a ina zance muhadu wlh tsoron Baba nake” zaro idanu daga Farida har Yasmeeen sukayi suna kallonta, da sauri Yasmeen dan ita bata kaunar fada ko masifan Baba saisa har tsoro take tayi laifi tace “nidai baruwana kema kinsan Baba yahana muyi tadi bayace idan wani nasonka kace yazo gida ba” wani kalan mugun harara Sa’a tamata tace “ni saisa wlh nafison Farida dudda she’s just 15 amman tafiki hankali da mutunci da rufama yar uwanta asiri, sokike Fahad yazo Baba yakoramini shi yaro dan masu kudi Baban ku daya iya firgita mutane Allah yasawake wlh ko zan bari yazo yaga su Baba saina tabbatar yagama fadawa soyayyata yanda kome Baba zaimai ba gudu baja da baya shidai yanasona” tai shiru sannan takalli Farida dake kallonsu tace “Farida kinji bani shawara” kaman jira Farida take dan ita arayuwan ta tanason taji ana hira da zancen samari dasauri tace “ba yau za’ama Baba karin girma ba, bazai dawo da wuri ba, kibari yazo amman saiku tsaya tabayan layi ko Anty Yasmeen”? Dasauri Yasmeen takalli kanta saikuma ta nuna kanta ita hiran kadaima tsoro yake bata tace