Showing 69001 words to 72000 words out of 190707 words
fitowa da kitchen rikeda kula tace “ba biyar zaki dawo ba incedai lafiya”? Murmushi ta kakalo tace “Ammi lecturer 4-5 wai bazata zo ba” Gyadamata kai Ammi tayi tace “to jeki rage kayan jikinki kizo kici abinci” murmushi tayi tawuce dakinsu su Farida ne kadai aciki jefar da jakanta tayi kasa tana kokarin cire hijabi chocholate din suka watso daga jakan dawani kalan sauri da Farida da Sa’a suka kwasa tareda daukan jakan, Farida tahau bude chocholate zatakai baki tace “waya baki hadaddun chocholates din nan Anty Yasmeen”? Dasauri Yasmeen dabama tasan Chocolate din sun watse ba kokarin cire kaya take takallesu dawani kalan sauri ta yarda rigan nata tazo wajensu ta fizge jakanta da chocholate dake hannun Farida tazuba ajakan back tarike jakan gam tace “wayace ki budemin jaka”? Dasauri Farida tace “laaaa Ya Sa’a dan Allah ba ita ta jefar da jaka ba suka zubo”? Dan dariya Sa’a tayi dan ita harta karanta wata yar karaman takardan ciki tace “wlh saurayi ne yabata ai harna karanta takardan saisa dukta tsure” dasauri Yasmeen takalli Sa’a ahankali tace “wace takarda?” Dariya Sa’a tayi tace “duba jakan ki” dasauri Yasmeen tabude jakan wata yar karaman takarda ne da note jiki da akayi da byro handwriting din so fine.
Take Care
MM❤️
Aka rubuta dawani kalan sauri taboye takardan abayanta daga Sa’a har Farida suka kwace da dariya ganin yanda tayi tana zaro ido, Sa’a tace “dalla chill bazamu fadama Baba ba mudai kibamu chocholate muci” hararan Sa’a tayi tace “baram bayarba” zata juya Sa’a ta fizge jakan tabude ta kwashi chocolate son ranta taraba biyu ta watsama Farida rabi tace “Allah sanya alheri first boyfriend din Yasmeen, her first love, nasan yanzu duk afirgice kike sabida Baba kika natsu kya bamu labarin shi ko Farida” kasa magana Faridan tayi tana danne dariyanta bakinta cikeda chocholate yarda jakan kawai Yasmeen tayi tajuya tafita daga dakin dan zuwa dakin Ammi cus she’s loosing her mind.
EPISODE 4️⃣7️⃣
Kusan atare dagashi har Hamad sukakai gida, Hamad yafara isowa sai shi daga baya, wucewa ciki yayi Dan biyeda shi, afalo yasami Baba da Hamad zaune suna magana, kafin ma yayi magana Baba yace “Maheer” anatse Maheer yace “Na’am Baba” “taho nan” dan juyowa Maheer yayi yakalli Dan da idanu yamai alamu yatafi sama yahuta wucewa wurin Baba yayi waje yasamu yazauna kusada Hamad yasauke kanshi kasa dan yasan maganan shi Hamad yama Baba, shiru dukansu sukayi chan Baba yace “kalleni Maheer” dago kanshi ahankali Maheer yayi yakalli Baba dake da bakin glass kaman Baba yanagani yace “Maheer zan maka tambayoyi biyu kagayamin tsakaninka da Allah dan Hamad yafada mini komi daga farko zuwa karshe, baka tabamini karyaba Maheer tunda kake yaro kawowa yau dan haka ka amsani tsakaninka ga Allah” Baba yadanyi shiru sai chan yace “kanaso ka auri yarinyar nan dan kaci mata mutunci ne ka wulakantata kodan ka kara tozarta mahaifinta sabida yataba kayanka??? Kaa gayamin gaskiya Maheer” shiru Maheer yayi kafin chan yace “a’a Baba” shiru Baba yayi tun yana karami Allah yabashi baiwan gane idan mutum yana karya ajikinshi kodan sabida shi makaho ne Allah yabashi baiwan oho, cikin kwantacciyan murya Baba yace “sai tambaya tabiyu kanason yarinyar ne Maheer”? Hakanan Maheer jiyayi gabanshi yafadi, wannan karan yakusan kai 5min yakasa amsa maganan kafin chan cikin murya mai taushin gaske tsakanin shi ga Allah dakuma zuciya daya yace “nima bansani ba Baba” dan shiru Baba yayi yana kallonshi sunnar da kanshi kasa Maheer yayi kusan 10min suka bata ahaka kafin Baba yasauke ijiyan zuciya yace “tashi katafi zan kira Malam Sani yau zaije yama Baban ta magana yaneman mana izini idan ya yarda cikin satin nan zamuje sai ayi magana kutashi kutafi” cute smile Maheer yasaki yatashi ahankali yawuce sama shikuma Hamad ya tsaya batare daya tashi dagakan wajen ba yana kallon Baba cikeda mamaki dan baiyi tunani Baba will accept maganan nan dawuri haka ba, dan murmushi Baba yasaki dan yasan Hamad na zaune awajen har yanzu, anatse yace “hanyar shiriya Maheer ya dauko Hamad I have to support him dudda nasan kalubale na gabanshi, akasin hakan zai iya jefashi yaje yayi wani babban kuskuren dayafi komi muni, tashi kaje soon u will understand abinda nayi dakuma abinda hukunci na ke nufi” harya tashi Baba yadauki wayanshi yamikamai yace “gashi kiramini Malam Sani, idan kaje sama ka karbi address na gidan su yarinyar saika turama Malam Sani ta wayanka” ijiyan zuciya Hamad yasauke yayi ma Baba dialing number sannan yawuce yatafi sama yana tunanin kiran telanshi dan dinkama Maheer manyan kaya dan bazasu neman aure yana sanye da kananun kaya ba.
As usual wuraren 6 na yamma Baba yadawo gidan saida yafara duba yaran dan yau babu islamiyya sannan yawuce daki, wanka yayi agurguje ya chanza kaya zuwa shadda yasa hula yafito dan tafiya masallaci atare suka fita da Baffa da Baba Karami dan suma sun dawo daga kasuwa.
Ana idar da salla andanyi jawabi suka fito suna gangarowa Baffa namusu magana kan kayan gonna da aka samu a gonan Baban su, wani magidancin mutum suka gani akofar gidansu tsaye jikin wata yar mota corolla tsaf tsaf dashi yaci manyan kaya harda Malum malum suna karasowa cikeda girmamawa yabasu hannu yace “Assalamu Alaykum barkanmu dai” dasauri Baffa dan yafisu raha yace “barkanmu bismillah naga kaman mu kake nema ko”? Atsanake yace “kwarai kuwa nazo naganku ne gaskiya kam ni ina matsayin kaman dan aike ne, wajen Malam Ibrahim nazo”
Yay magana yana kallon Baffa, Baba dashi kadaine babu wata fara’a akan fuskanshi bawai kuma ko wulakanci bane no he’s just a serious person, sanin halin Baba yasa dasauri Baffa yace “incedai bawata matsala bane, ga kanina nan shine Ibrahim Meya faru”? Dan dariyan dattawa mutumin yayi yace “to dafarko dai sunana Malam Sani nine babban aminin Malam Maheer Makaho wanda a gaskiya shiya aikoni nan na nemi izini wajenku” anatse Baba da sai alokacin yah magana yace “izinin mene”? Ahankali yace “Kunsan dayake makaho ne baya iya fita sosai ya aikoni ne nazo na nemi izini awajenku yanaso yazo axauna ya nemawa danshi Maheer izinin neman auren diyarku Fateema” wani kalan gyara tsayuwa Baba yayi dan maganan ta saukanmai kaman aradu, baki yabude zaiyi magana Baffa sanin halinshi yadagamai hannu yace “waye dan nashi a ina yasan Fateema? Sannan ita tasan shi”? Anatse Malam Sani yace “ehh to kusan zan iya cewa Fateema tasanshi amman bawai irin sannin dakuke tunani ba dan banjin wata magana ma yataba hadasu ba danshi Maheer lecturer ne a makarantan su yana koyar da English ma duka department dake makarantan, yasami Baban shi yau kan yanaso afara sanarda iyayenta idan sun bashi izini sai afara neman aurenta gaskiya banjin suntaba magana bama” kusan Baba zai iya cewa ya yarda dan wayanta akai akia yake bincika wa kuma da aka dauketa wayan all through na hannunshi ba’a taba kiranta daidai da 1 miss call ba” anatse Baba yace “ba yanzu zan aurar d……” tareshi Baffa yayi da sauri ta hanyar sakin ma Malam Sani murmushi yace “gobe juma’a zaku iya zuwa bayan juma’a dan bayan salla bama komawa kasuwa agida muke yini” murmushi Malam Sani yayi yace “Masha Allah to too Allah ya zabamana abinda yafi alkhairi, bari na barku ku shiga gida to saida safenku” yasake babbasu hannu suka gaisa, motanshi ya shiga yaja yabar wajen Baffa yakalli Baba da bacin rai dan dama baiwani huce sosai ba dudda Baba yabashi hakuri yace “kana kokarin gayamusu baka shirya aurar da Yasmeen ba kasan alamomin gidan mutunci kuwa”? Baffa yanuna motan mutumin daya wuce yace “gidan mutunci ne da yaron kwarai awannan zamanin zasuzo sufara tambayan izinin iyaye kafin dansu yama yima diyarka magana, kadaisan bazan taba bayarda Yasmeen banyi bincike ba kabar ganin kanka kaine dan sanda kaine ka iya bincike kasan abubuwa nafika sanin rayuwa Ibrahim, kabari gobe suzo muga yaron idan natsuwanshi yayi zamu bashi izini ya nemi Yasmeen inyaso saina hada bikinta dana Sa’a dan iyayen yaron sunzo kasuwa sun samen, kuam iyayen yaron sun damen sunaso asa rana nan da wata daya kanajina” badan yasoba Baba yace “eh” Baffa yakalli Baba karami yace “koba hakaba” anatse yace “hakan yayi Yaya, Yasmeen ta isa aure ai” jinjina kai Baffa yayi jin ana kiran isha’i yace “mutafi muyi isha’i kawai gabadaya” duk suka juya suka wuce mosque, koda suka dawo sama sama Baba yaci abincin yawuce dakinsu Yasmeen dukansu na zaune adakin harda Nana suna hira suna dariya ganin Baba yasa sukai tsit, binsu yayi da kallo one bye one sannan yasaki labulen yawuce yashiga dakinsu, direct kan kujera yayi yazauna Ammi dake zaune ganinshi haka yasa tace “lafiya Baban Nanah kanka ciwo yake ne”? Girgixa mata kai yayi baice komi ba yawuce yatafi uwarka da kawai.
Har wajajen dayan dare Baba yakasa bacci juye juye yake hakan yasa cikeda damuwa Ammi ta kunna wutan dakin takalleshi shima kallonta yayi saikuma yatashi yazauna tareda folding hannu akirji cikeda damuwa Ammi tace “wai menene Baban Nanah am getting worried? Meke troubling naka haka ka kasa bacci sai juye juye kake” shiru yayi yana kallon Ammi kasa dannewa yayi yace “wani mutumi dazu yazo tambayan neman Auren Yasmeen shine Baffa yace suzo gobe” wani kalan murmushi Ammi tayi da abin harsaida yasa Baba sakin baki dasauri tace “waye shi”? Cikeda dan bacin rai Baba yace “nima bansani ba sai gobe idan sunzo amman ance yaron lecturer ne a school nasu” wani kalan murmushi Ammi tayi kaman anmata albishir da kujeran makka hannu ta daga sama tace “Ya Allah ka tabbatar da Alkhairi kabawa Yasmeen miji mai sonta sama da yanda Baban ta ke sona” dan tsaki Baba yayi kawai yakoma ya kwanta tareda juyamata baya dariya Ammi tayi da shewa tace “wlh Baffa Yamin daidai aka biyemaka bazaka taba aurar da yaran nan ba” kashe wutan tayi tadawo rungume Baba tayi tace “zonan wlh saikai farin ciki” daganan salon labarin ya chanza.
✨KK✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 4️⃣8️⃣
EPISODE 48
To Jama’a anan nakawo karshen FREE EPISODES na wannan littafin nawa Mai suna KYALKYALIN KAUNA wato SPARKLES OF AFFECTION✨
Wannan aure zai yu kuwa??
Yaya Baba zaiyi idan yagano Maheer shine Pablo Escobar??
Kuna ganin kafin aure ko bayan aure ne Baba zai gano gaskiya???
Hajiya zata taba barin Maheer da Yasmeen suyi zaman aure???
Hmmmm!!! Kubiyoni.
Idan kinason cigaba da karanta littafin nan all you have to do is pay ko 1k or 500 into 3107021073 Aisha Muhammad first bank.
Zakimin magana a WhatsApp wa.me/+7012181461 sainai adding naki a paid group.
Group na 1k is 2updates daily banda alhamis da juma’a.
Group na 500 is 1update daily banda alhamis da juma’a.
And inada EXCLUSIVE shi a Email nake musu update yanzu haka sun wuce ku is 5k.
4episode daily❤️
Please patronize my little work, and appreciate my talent, show me support ta hanyar subscribing ki shiga paid group.
Thank you I love you all❤️
https://vm.tiktok.com/ZM2U8NPMo/
Kusan duka yaran gidan babu wanda yasan akwai wani abu dazai faru yau Baffa dai yasa Baba karami yasayo drinks harda su Maltina da ruwan gora, matan gidan kuma harda Ammi aka hau girki yaran gidan kuma duk suka tafi school, Baba sabida haushi tun 6 yatafi aiki Baffa dai saida yakirashi ya jaddadamai biyu tamai agida, Yasmeen 9 ta tafi school abinta yau har 6 takeda lectures.
Ana idar da sallan juma’a Baba yadawo gida gidan an gyara yay kal kal an shimfida manya manyan tabarmai a compound kasan bishiya girgixa kai kawai yayi yawuce ciki wanka yayi ya shirya cikin babban kaya harda Malum Malum da hula ya fesa turare yafito waje daidai ana sallama Baffa ya kalleshi yace “muje mu shigo dasu” baiyi musu ba suka fita atare, Hamad ne ke tuki sai Maheer agefenshi Maheer yasaka wata faran shadda jumper da hulan Hamad akai wlh kaga Mageer zaka dauka ango ne, Malam Sani da Baba sai limamun anguwan su wanda yake abokin Baba ne sosai, duk suna tsaitsaye Baba yafara fitowa daga gidan kallo daya Maheer yamai yasauke kanshi kasa sabida yanda Baba yamai wani kalan kwarjini a ido gaisawa su Baba sukayi dasu Malam Sani hakan yasa Hamad yataho tareda dan jan Maheer daya kasa motsi Malam Sani yace “surukin naku akwai bala’in kunya, wannan shine yayan shi Hamad” yanuna Hamad dake bama Baffa hannu Baffa yakarba cikeda murmushi yace “ina gajiya” sannan yanuna Maheer da kanshi ke kasa yace “wannan shine Maheer” ahankali Maheer yabama Baba dake kallonshi hannu karban hannun Baba yayi murya chan kasa Maheer yace “ina yini” ba yabo ba fallasa Baba yace “lpy lau” tareda karbe hannunshi, Baffa yace “bismillan ku kushigo” shiga ciki sukayi Ammi dasu Yaya ta window suke lekawa kaman yara dukansu are so excited Ammi tace “waye surukin nawa naga samari biyu” Yaya tai pointing Maheer dake sunnar dakai tace “daga ganin mai kunyan chan shine mai neman Yasmeen” wani kalan murmushi Ammi tayi tace “surukina badai kyau ba kaman bakin balarabe Masha Allah tubarkallah” shewa sukayi, jin Baffa na kwala musu kira yasa duk suka saka hijaban su suka daddauki su drinks da ruwan gora suka fita dashi, anatse Baffa yace “ga iyayen Fateema nan” gaggaishe su sukayi Maheer yakasa dagokai suka wuce suka koma daki sannan Baffa yace “to bismillan ku”.
Gyaran murya Baba Makaho yayi yace “to godiya ya tabbata ga Allah ubangiji daya hallice mu ya raya mu sa’an nan ya nuna mana wannan rana, dafarko dai sunana Alhaji Maheer Makaho, haka aka haifeni da makanta, gaskiya dana taso iyayena basu da shi ahaka ahaka dai nasamu wata makauniya irina marigayiyi mukai aure Allah yamata rasuwa yanzu” atare kowa yace “Allah gafarta mata” ahankali yace “Ameen” sannan yace “bazan muku karyaba dalilin d’ana ne nazo gidan nan yau, yarana biyu da Hamad wanda shi likita ne saikuma Maheer pharmacy yakaranta amman bai sami aiki dashi ba Allah yabashi aikin koyarwa english kaman yanda nafadi, banda shi duka yaran nan nawa da scholarship sukai karatu akasan waje Alhamdulillah” Baba yasakeyin shiru kafin chan yace “yaran nan yarane dasuka taso na koya musu ladabi biyayya natsuwa da bin Allah ma’aiki, Maheer yasameni da maganan yaga wata daliba a makaranta sunanta Fateema yanaso soyayya irin ta aure bawai soyayyan da akeyi a zamanin nan ba, saidai yabukace ni dana fara ganawa da iyayenta amai izini yanemeta tukunna dan bai dace yatari yarinya a school yana mata magana ba karatu tazo yi a school ba soyayya ba” jinjina kai Baffa yayi maganan na shiganshi, cikeda dattaku Baba yace “to gani ga babban aminina da yarana gakuma Liman shima aminina ne kuma zai iya wakiltata ako’ina munzo mu nemama danmu iznin neman auren diyarku idan babu kowa, idan suka daidaita nan bada jimawa ba ayi aure da izinin Allah to mekuka ce”? Shifa Baffa yasan halin kaninshi to bazai taba bari yakori mutanen arziki da mutunci haka bane dake neman Yasmeen ba, anatse Baffa yay gyaran murya yace “a gaskiya naji dadin wanna halin karamcin irin naku da sannin amfanin iyaye, sannan babu wani wanda ke neman aure Yasmeen wato Fateema dan haka nabashi izinin nemanta idan har komi ya daidaita saimu hada bikinsu taredana yayarta Sa’adatu da za’ayi nan da wata daya In sha Allahu” murmushi kowa yayi ana Alhamdulillah, Baba da tunda suka zauna Maheer yake kallo atsanake yace “Fateema is AS genotype dinta, menene genotype dinka”? Kowa bin Baba yayi da kallo Baffa kaman ya make Baba dan baisan what’s all this ba yanzu aka fara magana za’azo kan genotype nan gaba, dan dagokai Maheer yayi yakalli Baba kafin ya sunnar da kanshi kasa dasauri, cikeda kamala yace “ni AA ne Abba” hamdala Baffa yayi hakanan yaji yanason Maheer wlh dan yaron ga kunya ga sanyi ga rashin magana, daukansu Baba bazaice komiba yace “I need general blood test naka from a well known hospital saikuma” yadanyi shiru bai damu da yanda kowa ke kallonshi ba Baba yace “ban yarda ka taremini yarinya a titi ko a school ba ban yarda ba, Fateema karatu nakeso tayi banson tai loosing focus, ranan lahadi zan iya baka kadinga zuwa har nan daki a falon mahaifiyarta ka ganta kuyi magana na tsawon awa daya” gyadamai kai Maheer yayi ahankali, Baba yace “banson yawan kira, kira once in a day ya isa” sake gyadamai yayi” Baba zai kara magana Baffa yatareshi da sauri ta hanyar cewa “to Masha Allah, yanzu dai in sha Allahu tunda yau juma’a ranan lahadi saiyazo shida yarinya su zanta zamu kira yarinyar mu tambayeta idan tai na’am dashi zamu danyi yan binciken mu kafin mukiraku mu sanar daku kuzo asa rana da izinin Allah” dasauri Baba yace “zata cigaba da karatu” wannan karan Baba Makaho bai bari Maheer ya amsaba dan kafin yay magana yace “In sha Allah ai ilimi gatan bawa ne, ilim adon diya mace Fateema zata cigaba da karatu harsaitaji ya isheta” Baba zai kara magana Baffa yace “to bismillan ku muci abinci” badan Baba yaso ba ya kalli Baffa sannan yadauke kai.
Sosai su Baba Makaho suka saki jiki sukaci abinci Hamad ma vaci dan abincin gidan dadi Maheer nedai vakasaci sai wasa yake da spoon har aka gama, gaggaisawa akayi Baffa bai kara bama Baba room to talk ba suka shishigayin sallama Baffa na karban nambobin wayansu dakuma adreshin gidansu, sannan Baffa yakalli Maheer daketa sussunar dakai yace "muna jiranka ranan lahadi" gyadamai kai ahankali Maheer yayi sannan suka fiffice suka tafi.Koda suka dawo gida Baffa bai karabi takan Baba ba, Baba yatafi office kawai dan baiso abinda Baffa yamaiba kawai babu yanda ya iyane dan bazai iya ja dashi ba.6 dot suka fito daga lectures fitowa tayi daga class ga mamakinta Baba tagani gaban ajinsu yana kallonta kuri, ahankali tace "Baba, ina yini" dan murmushi yasakin mata yasa hannu yakarbi jakan nata tareda kama hannunta kaman yar yarinya yace "mutafi" awani kalan kunyace ta gyadamai kai tareda binshi har zuwa inda yay parking sai kallonsu ake, budemata mota yayi tashiga ta zauna yasamata jakan ajiki yarufe yazagaya ta dayan side din yazauna yaja motan, sundanyi nisa suna tafiya kaman daga sama yace "wani yataba miki magana a school din nan kan soyayya"?
Dasauri takalli Baba gain hankalin shi nakan tuki vasa ahankali tace "a'a Baba" bai karace mata komiba agaban wani shagon abubuwan Habib yoghurt ya tsaya fita yayi yace "kijirani" kusan 13k ya kashe a shagon