Showing 15001 words to 18000 words out of 190707 words
kanshi dasauri yana hadiye abincin yasake gutsuro tuwon for the second time yakai bakin shi, abincin eatry din dama has always been nice saisa dudda wajen is not fancy bawai wani continental restaurant bane but he always choose abincin su but then again, tunda yake baitabacin abincin dayaji dandanon shi suit his palate and his stomach like this tuwo dake gabanshi ba, ijiye spoon din yayi ganin bayamai da kyau yasa hannunshi yashiga cin tuwon kaman bashiba within 5min yacinye duka uban tuwon nan tas da nama da kifin abin nabashi mamaki, kaman akaromai yakeji, zobon dake kan tray yakalla he hardly take zobo he don’t like it sabida kalan amman samin kanshi yayi da mika hannu yadauki goran bude sealed marfin yayi yakai bakinshi ya kurbi kadan kaman mai tsoron sha, lunshe idanunshi yayi dasauri Oh No! Kafin yadaga goran yakafa abaki saida ya shanye tassss sannan ya sauke goran dagakan bakinshi OMg roban zobon da takeaway ya kalla saikuma ahankali yakalli cikinshi yana mamaki shine yaci abinci haka yakuma sha zobo, it’s unbelievable.
✨KYALKYALIN KAUNA✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 7️⃣
Wuraren 3:30 daidai tafito daga shagon Maman Intee tana kalle kallen dan wajen gaban shagon dababu wani mota yanzu datafito ko kadan bataji komi ba keke data gani yazo zai wuce ta tare da sauri ta hanyar daga mishi hannu tashiga suka wuce radio Keken duk yacika mata kunne damai keken ya kunna, muryan Baba taji a radio kaman daga sama yana jawabi kaman jawabin dayayi ne bayan karin girman da akamai.
“Inama alumman mutanen nigeria gabaki daya alkawari cewa zanyi yaki da rashin gaskiya, zan kawo karshen barayi da yan shaye shaye, zan kawo karshen karban cin hanci da rashawa da akafi sanin polisawa da halin, zan kawo karshen miyagun abubuwa sannan zan tabbatar da tsaro da kuma gaskiya…..” wani kalan cute smile tasaki dayasa tai kaman wata Barbie doll sabida kyau tanajin wani irin farin ciki azuciyanta tana alfahari da Baba irin sosai din nan.
Har gaban gidansu Mai keken yakawota bayanshi tayi sanan tajuyo ganin motan Baba yasa tagane yana gida, ahankali tabude gate tashiga ciki da sallama su Nanah ne da Sa’a dakuma Farida ke tsakar gida kan tabarma ga abubuwa daban daban agabansu harda takalma suna gwadawa dasauri tayi cikin gidan Nanah naganinta tasaki takalminta taruga aguje ta rungumeta cikeda tsananin so dakuma shakewa tace “oyoyo Anty Yasmeen kinga Baba yasayo mana abubuwa da yawa naki nadaki wajen Ammi, itane tarike naki, nima kinga yasaya mini takalmin kwas kwas” wani kalan murmushi Yasmeen tayi tareda gyarama Nana kitson kalaban dake kanta dake lilo yana neman shiga idanunta tace “dagaske, sakeni kiga naje na amsa nima naga nawa takalmin kwas kwas din” tawuce ciki batare daya tsaya kallon nasu Farida ba, da sallama tashiga dakin Ammi, Ammi da Baba nazaune kan kujera suna magana akunyace tace “Baba sannu da zuwa” Ammi tace “sannu da zuwa, zo ga naki takalmin da hijabi da jakan Baban ku yasayo muku” dasauri takarasa gaban Ammi takarbi nata dasune suka rage a leda tana murmushi sosai sabida yanda taji dadi tace “Baba nagode Allah saka da alkhairi” juyawa tayi dasauri zata fita danta kosa taje itama tazauna kusadasu Farida tabude nata tagani kaman daga sama Baba yace “zonan” juyowa tayi da sauri tana zaro manyan idanunta masu shegen kyau da grayish kwallan idanun dake gareta, wani leda Baba yaciro daga jakan aikinshi daga ita har Ammi suka bishi da kallo dan itama Ammi batasan me aledan ba mikamata yar ledan yayi ahankali ta tsugunna ta ijiye ledan kayanta akasa sannan takarasa wajen da Baba kezaune tasa hannunta ahankali takarbi ledan jin kwaline Mai tauri tauri yasa Ammi tace “menene aciki bude mugani” kaman dama jira take Ammi tace haka dawani kalan sauri tabude ledan ganin kwalin waya na techno spark 3 yasa batasan lokacin datawani kalan kurma ihu ba tai wani uban tsalle su Farida suka shigo dagudu dan sun dauka bugunta Baba yayi, cikeda murna tace “Ammi waya, touch screen” saikuma kawai tafada jikin Ammi tafashe da kuka sosai ba kakkautawa, Ammi dariya ma abin yabata tace “kagamini shirme menene nakuka kuma, kaga kuka take Baban Nanah” juyoda kanshi Baba yayi yakalleta yanda tadaura kanta ajikin Ammi tana kuka yace “mena kuka kona karbi wayar ne”? girgiza kai tayi ahankali tana ciro kanta daga jikin Ammi takai hannunta tagoge fuskanta tass, takalli fuskan Baba dake kallonta kur batare daya kyafta idanu ba ahankali tace “Baba nagode sosai” murmushi yayi kawai tareda dauke kai, Ammi tace “tashi kije kisa a chaji, kasamata sim dinta aciki ne?” Ammi ta tambayi Baba dan karaman wayanta na hannunshi daya karba jiya, Gyadamata kai yayi hakan yasa Ammi tai murmushi sosai tace “imaza jekisa chaji to tunda ga nefa saiku shirya islamiyya kan ki dawo wayan tacika dam” murmushi tayi ta tashi tafito su Farida biyeda ita suka shiga dakin nan fa suka shiga tattaba wayan saida sukaji gyaran muryan Baba arude sukasa wayan achaji kowa yamike yashiga shirin islamiyya kafin suyi salla suwuce.
Sai bayan la’asar daya shigo gida Ammi tafito daga kitchen tazo tasameshi zaune akan gado a uwardaka yana kokarin boye bindigarshi akarkashin gado wanda daman anan yake boyewa sabida yara, ahankali tazauna kusadashi anatse tace “Baban Nanah yau ka kashe kudi dayawa, nadauka kudin da aka bakan nan na karin girma fili xaka saya muyi gini” girgixamata kai yayi yace “bazan taba barin gidan nan ba wannan gidan gidan gado ne, iyayenmu suka barmana, saidai nai gyaran gidan amman ba barinshi ba” shiru Ammi tayi hakan yasa Baba yace “gobe ki sayo musu atampopi da kudin dana baki da packet na audugan ku (pad)” gyadamai kai tayi tace “shikenan” yunkurawa tayi zata mike karaf yariketa zaro idanu tayi tana kallonshi tace “Haba babban Nanah, matan gidan nan duk suna nan fa, zan koma kitchen ne mucigaba da girki” murya chan kasa yace “nikuma bukatan ki nake su karasa girkin” bai kara bari tai wani magana ba yasata akan gado.
Sunyi nisa sosai wayanshi na office yahau ringing, dan yanada normal waya na gida yanada waya na office wanda department nasu ne yabasu, ganin baya hayyacinshi yasa da kyar Ammi tace “ana kiran wayanka na aiki” kasa magana yayi ya kankameta yana kara sauri kafin chan yasaki kara sannan yakoma gefenta ya kwanta yana maida ijiyan zuciya yajanyo Ammi yadaurata akan kirjinshi yana shafa bayanta, da kyar ya iya mika hannu yadauki wayan yakai kunnenshi yace “speak” wani kalan yunkurawa yayi yatashi zaune harsaida Ammi ta firgita, yace “awajen wa kaji this information Aliyu”? Shiru yayi saikuma chan yamike tsaye yace “wat I want you to do now is trace the number dayay message din I believe is a whistle blower, but kayi komi lowkey dan most of our people anan station yariga yasayesu you will see me in the next 30mins” katse wayan yayi yajefar yawani kalan diro daga kan gado zaiyi bayi dasauri Ammi ta tashi zaune tace “meke faruwa”? Juyowa yayi yakalleta dan murmushi yayi yace “is work related” hmmm ajiyan zuciya ta sauke bata cika saka sa ido aharkan aikinshi ba but wannan dataji yana gayama Aliyu kada wani yasani she is worried, Aliyu yaronshi ne da dadewa, juyawa Baba yayi harzai shiga bayi Ammi tarikemai hannu tace “Baban Nanah I am worried and I don’t know why? I feel kaman you are about to get yourself in trouble” dan dariya Baba yayi kadan tace “why are you worried normal aikin dana saba zanyi, munsami wani tip kan Pablo Escobar ne da hakan zaisa komashi waye ya bayyana agareni nadade ina neman gayen nan and finally I think lokaci yayi da dubun shi zai cika, inamai tabbatar miki saina kawo karshenshi da karshen business na kwayoyin dayakeyi kodako su uban waye da waye ke bayanshi Alhamdulillah yanzu nazama CP I have my own power and I have my team now, yanzu dai barni nai wanka ana jirana” ahankali Ammi tasakeshi yawuce bayi itakuma tadawo bakin gado tazauna tana shafa kirjinta dataji yana bugawa sosai, bayau Baba yafara aikin police ba infact a police dinshi ma ta aureshi, yasha kama criminals dasuwaye da waye but hakanan yau yana amsa wayan nan taji kawai gabanta nafaduwa and she is not just at ease. Lumshe idanu tayi ahankali tace “Ya Allah ka kare kakuma tsaremini Ibrahim duk inda zaije duk inda kuma zai shiga dan Ibrahim is very very stubborn” ajiyan zuciya tasauke daidai yafito hakan yasa yace “jeki wanka kema” gyadamai kai tayi tashiga bayin kofin tafito harya gama shiryawa riga da wando yasaka na jeans ba uniform ba, bindigarshi yaciro daga kasan bed yabude yaduba bullet kafin ya maida yasake abayan wandonshi sannan yadauki car key nashi da wayoyinshi yakalli Ammi daketa kallonshi yace “natafi pray for me, nakama mutumin nan gwamnati ina mai tabbatar miki saita karamin girma, bye wifey yaran nan makesure sunci abinci sunyi salla kafin su bacci” gyadamai kai tayi tana binshi da idanu ganin kaman she is worried yasa yazo gabanta fuskanta yakama ya manna mata kiss agoshi ahankali yace “please cheer up kada kisamini damuwa dan as it is I am so very happy yanzu you have no idea what kama Pablo means to me and to the entire nation, yaran al’umma zasu rage shaye shaye that is in ma basu daina ba, are you not happy? This is good news” murmushin yake Ammi tamai tace “eh” kumatunta yashafa yace “bye ba lallai nadawo ba maybe gobe zaku ganni” baijira abinda zatace ba yawuce yafita dasauri sauri.
✨KYALKYALIN KAUNA✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 8️⃣
YOU CAN JOIN MY GROUP BY CLICKING ON THIS LINK;
https://chat.whatsapp.com/HyR79BijM7XFBaNPrFcBYn
Saida Baba yay magrib anan masallacin headquarter nasu sannan yafito yawuce ciki sai gaidashi ake direct yawuce wani lafiyayen office da aka rubuta CP ajiki yabude yashiga, office din yahadu daidai gwargwado, ko 1min baiyi da zama ba saiga wani matashi fari sol bafulatani da akalla bazai wuce 30yrs ba yashigo office din rikeda wasu takardu a hannunshi, Baba na ganinshi yace “yauwa Aliyu close the door kazo” maida kofar Aliyu yayi yakaraso tsakiyan office din akan table ya ijiye papers din yace “yallabai wannan ne sakon da aka turo” yabama Baba wata waya Baba yakarba dasauri yana duba sakon.
“Tonight da atsakiyan daren yau din nan motoci guda biyar na Pablo zasu shigo garin nan dauke da coke, da tramo dawasu kwayoyi da Nigeria bama tasan dasu ba. Sai abu na karshe kadama kuyi kokarin bincike kan layin nan dan mai wayan makaho ne dake bara atsakiyan kasuwan nyanya”.
Baba yakaranta sakon kusan sau uku sannan yakalli Aliyu yace “kayi mini tracking number”? Takardun ya kwasa yabama Baba yace “nayi gashinan yana nyanya dagaske, saikuma nambobin nanne sub target nashi, wanda duka nakira babu wani info dana samu dagaske mutumin makaho ne dat knows nothing” pen Baba yadauka yakai bakinshi kaman mai tunanin want abu chan yace “koma waye shi dole mu bincika shi dan what is suspicious shine maisa sai yaune da aka maidani CP za’a turomini sako daga wayan da gwamnati tai allocating to office na CP? Dan haka I want you to send some of your boys aje azomini da makahon for questioning, sannan gather the team zamu fita operation but in disguise, duk wani kofa da hanya na shigowa nan cikin garin Abuja zan rabaku zakuje wajen, get all communication devices ready, I want this operation to be a success, for the first time inaso nai confiscating kayan pablo hakan zai bayyana mana da Pablo duk ma a inda yake zai fito, sannan I want you to grab all the 5 drivers arresting nasu zaisa musami an insight kan wannan ghost organization na harkan kwayoyin nan, now go and get the teams ready gani nan fitowa zan magana da IG” saramai Aliyu yayi yace “yes sir” sannan yajuya yafita daga office din Baba yabishi da kallo, ahankali yasa hannu yadauki wayan yana kallon sakon da aka turo, wani kalan murmushi Baba yayi yana kallo again kafin ahankali yamike tsaye yawuce zuwa wajen wani allo dake jikin bangon office din, marker dayake jikin allon yadauka tareda bude marfin kafin ahankakali yakai marker kan board din yarubuta PABLO??? Da question mark guda uku abayan sunan sannan yay murmushi yajuya zuwa table yakwashe takardun da wayan yafito daga office nashi ya kulle yasauka yafito wani seprate building yawuce direct office na IG yawuce yasa secretary ya sanar dashi shine, kusan 10min yabata awajen sannan akace yashigo.
Cikeda fara’a IG yace “Oga CP daga kama office yau yau din nan harkazo nemana da zafi zafi haka incedai lafiya, I thought zaka huta zai gobe zaka fara aiki” murmushi Baba yayi sannan ya ijiye wayan agaban IG, hakan yasa IG yadauki wayan dasauri yace “ohh okay” yashiga karanta sakon kafin yakalli Baba yace “brief me” anatse Baba yashiga briefing nashi yafadimai komi yace “abinda yasa nazo gareka direct banje wajen deputy IG, ko Asst. IG ba is because I don’t trust them sir” jinjina kai IG yayi cikeda son aiki dakuma gaskiyan Baba yace “yanzu mekake so Ibrahim”? Anatse Baba yace “goyon bayanka” dasauri IG yace “I support you Ibrahim dari bisa dari, na yarda dakai nakuma yarda da amananka saisa nai tsayin daka aka saka awannan position din nan dan kap department namu banga wanda ya chanchanci seat din nan ba saikai dan haka nabaka goyon baya, but always report to me and keep me posted who ever is this devil ko evil nema zan kirashi, Pablo ko? Wannan Pablo Escobar din nan daya dami kasamu da kayayyakin maye I want him found, I want him to face the punishment base on rules and regulations da kasarmu ta tanadarwa masu sana’an dayake, I want yaron nan da sanadinshi yaranmu dubu duk sun lalace da shaye shaye found, arrest all drivers nashi and ku kwace duka products din, sai bayan ka kawo su nan mungama binciken dazamuyi before nai inviting NDLEA suma suzo suyi nasu abubuwan daya kamata, for now the mission should be a black mission just me you da yaranka, you have my full support Ibrahim so go do what you do best” “yes sir!” Baba yafadi tareda sarama IG sannan ya tattara abubuwan yafito yawuce kasa wani private daki yawuce yasami team dinshi of about 24 men, wanda shine yay training nasu tun suna police academy, so he trust him, shiyay putting request abarmai su dan da za’a chanza mishi su ne da aka maidashi CP, addressing nasu yayi sanna aka dauko map na Abuja yanuna ma kowa spot dayakeso su tsaya, sannan yasa kowa yatafi shikuma yabi team nasu Aliyu aka wuce.
Wannan kenan.
Zaune yake kan gadonshi dagashi sai wata yar gajeren towel a waist dinshi da karamin white soft towel a hannunshi yana tsane black wavy gashin kanshi dakeda ruwa, dakin gabaki daya kamshi yake na sabulan wankanshi gefenshi kuma wayanshi ne dake a speaker muryan mace na magana.
“Nan da 2days ko 3days zamuyi finalizing deal din nadawo, I miss you badly my little handsome babyboy” dan yatsine fuska yayi ya ijiye karamin towel din yamika hannunshi yadauki wani cream kaman badashi ake wayaba.
Hajiya tace “shipment dinmu ya iso ranan kacemin kaman zai iso yau ko”? Kaman bazaiyi magana sai chan yace “yau” dasauri tace “wow yau zai iso” murmushi tayi sosai da saida yaji sautin murmushin tawaya, dan tunda takirashi dazu kafin yashiga wanka take magana bai kulata ba haryabar wayan kan gado yaje yadawo still bai kulata ba sai yanzu ne yay magana cikeda lallabawa kaman tana magana da sarkin duka nigeria tace “dan Allah muyi video call naganka, nasan kai baruwanka da social media baka WhatsApp, baka Facebook, baka IG, baka tiktok bamaka anything but atleast muyi FaceTime tunda iPhone to iPhone ne kaji King dina” dan gajeren tsaki yaja baice komiba wanda tasan tsakin simply implies bayaso, chan yace “I hate VC” shiru tayi sai chan tace “shikenan yanda kakeso haka za’ayi” kallon wayan yayi yace “I have meeting talk later” bai jira amsanta ba batare daya katse wayan ba yawuce closet, ita tasan dayace talk to you later to yagama wayan ne saidai ke kikashe wayan, katse wayan tayi tajefar da wayan akan lafiyayyen gadon datake kai takifa kanta akan katifar cikeda tsananin kunci, ahankali wani mutum dake dakin tuntuni da akalla shima zasuyi age mate da hajiyar yadaura hannu abayanta yace “narasa mesa kikeson yaron nan, yaron dake wulakantaki haka, nasan ada sai yanda kikai dashi dan lokacin dakika samoshi he was just 8 baimasan miye duniya ba but yanzu yasan duniya yasan rayuwa, yasan ciwon kansa, you have to understand that, babu wanda baki koraba sabida yaron nan Maryam, baki taba aure ba sabida yaron nan Maryam, look at me menene banfishi dashi ba, narasa meyamiki ni I believe wlh asiri yamiki stupid arrogant matsiyac……” “Adamu!” Hajiya takirashi da mugun karfi tana tashi zaune idanunta sunyi jajir tanunashi da yatsa tace “don’t you dare insult Maheer, babu uban abinda yashafeka da abinda yakemin, kaganni nan nasan Maheer sama da kowa aduniyan nan, abinda kaga yanamin bawai wulakanci bane haka yake ne, haka Allah yayishi, is his nature, akwai yarinyar da Maheer ta isa ma ya kalleta balle yay magana da ita harya kulata ya saurareta yama lallasheta irina? Maheer na sona son da shi kanshi baisan iyakan shi ba, kasan dalilin dayasa nai tafiyan nan dakai kawai sabida karagemin zafi ne, which biya ka nake idan kuma kagaji ne yanzun nan 1 call zanyi ansama maka ticket ka koma nigeria banson shirme kada ka kuskara ka zagin mini Maheer ko a mafarki, ka zagi Maheer nika zaga, Pablo yafika akomi da komi, a ilimi, a sura, a hikima, a kwarjini, a kyau, a gayu, akuma gamsar da mace, harna mutu ni nariga nasan bazan kara samun namiji kaman Maheer ba saisa nagodema Allah daya banishi tun yana yaro na more shi tun baisan komi ba, na more kuruciyanshi, inamai tabbatar maka haka kuma zan cigaba da moreshi har tsufan shi dan haka kakiyaye” ja idanun Adamu sukayi, maganganun ta sun tabashi sosai, kuma yay alkawari duk yanda zaiyi duk inda zai shiga saiya shiga ya tabbatar cewa tarasa Maheer din nan har abada sai yaga idan bazata