Showing 24001 words to 27000 words out of 190707 words
wayan na gab da katsewa tadauka tace “yallabai congratulations naga karin girman da aka maka, nasan hala kana kirane dan kaji ko su dawo an gama musu interview ko, Farida zata iya dawowa ita sai 3:30 dama, Nana ko kawai kawuce da ita gida” Baba ji yayi magana na neman gagaranshi ga Ammi sai kira take yana shigowa as call waiting, da kyar Baba ya tattaro natsuwa shi yace “ban gane abinda kike fadi ba, ina sukaje Farida da Nanah?” Baki principal tasaki tace “a’a, dazun nan ba ka aiko wani dan sandaba yasa Uniform sunanshi Aliyu SS nagani a tag nashi wai kace yazo ya kawo maka Farida da Nanah station za‘amusu interview, namaso nakira ka yace kana meeting” Baba ji yayi kaman iska na dibanshi Aliyu natare dashi a station tun jiya har yanzu, yanzu da gaske an dauke yaranshi, katse wayan yayi dasauri daidai wayan Ammi nasake shigowa hakan yasa yadauka yakai wayan kunnenshi yay shiru yakasa magana, anatse Mama tace “Baban Nanah meke faruwa wai? My mind is telling me something, tun safe yau natashi gabana sai faduwa yake yanzu kuma yadadu meke faruwa?” Kasa magana Baba yayi saida Ammi tamai ihu. “Baban Nanah!” Firgigit ya farka daga nisan tunanin dayayi ahankali yace “don’t worry I will handle everything gani nan zuwa” baijira mezata ce ba ya katse wayan daidai Aliyu na fitowa duk yay zufa ganin Baba shikadai tsaye a filin station din rana na dukanshi zufa na ketomai yasa yay wajenshi da sauri yace “Yallabai lafiya ka tsaya kai daya arana haka” juyowa yayi yakalli Aliyu, kafin anatse yace “come with me”.
✨SPARKLES OF AFFECTION ✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣3️⃣
KINASON MAGANA DA NI M SHAKUR??? Click on this link and chat me up directly;
wa.me/+2347012181461
Office din IG suka wuce wannan karan baima jira secretary yabashi izinin shiga ba Baba ko kallonshi baiyiba yatura kofan kawai yabude yashiga cikin office din, IG natare da mutane but ayanda yaga fuskan Baba yasa yasallamesu yakalli Baba yace “CP lafiya kuwa? Why are you looking somehow”? Karasowa Baba yayi gabanshi ahankali yamikama IG wayan cikin wani kalan yanayi yace “y’ay’ana Oga” dasauri IG yaduba hoton yace “Innalillahi wa innailaihi raji’un, ya kwashe maka yara”? Dasauri Aliyu yataho leka hoton yayi sanan yakalli Baba, anatse IG yakalli Aliyu yace “daukomai ruwa daga fridge dina yasha” dasauri Aliyu yay wajen fridge dake office din yabude goran ruwa yadauka karami mai sanyi yakawo ma Baba tareda bude marfin, karba Baba yayi saida ya tada ruwan duka sannan ya ijiye goran, anatse IG yace “calm down” gyadamai kai kawai Baba yayi yay shiru shi kadai yasan yanda yakeji, IG yakalli Aliyu yace “yanzu a ina kuke any progress”? Anatse Aliyu yace “babu so far so good su karan kansu basusan waye Pablo ba i believe them, ire iren mutanen nan dama kananun workers irin direbobi haka basu sansu ba, sannan basu bamu address na inda zasukai kwayoyin nan ba, shikuma Pablo yaba CP dama awa daya dazu dasukai waya kan yasaki kayanshi da yaranshi inba hakaba zai aiko mai sako, I guess wannan ne sakon” ijiyan zuciya IG yasauke yakalli Baba dayay shiru kawai yana kallonsu yace “Ibrahim” ahankali Baba yadago kai yakalleshi, IG yace “kai kasan I have only kyaykyawan niyya akanka, nasan cewa daka kawomini case din nan nina baka go ahead akan eh go for it, banyi kuma bantaba tunanin cewa shi wannan Pablo Escobar din kwararren criminal bane dazai iya kidnapping family naka ba sai yanzu, kalleni da kyau Ibrahim” Baba yakalli IG, yace “yaranka are involve in this whole thing now, yaranka ma bawai anyhow yara ba ana maganan yara mata anan kuma kanana karaman chan ma banjin takai 5yrs ba dan haka inaso kasaki kayan nan da dirobobin nan yasakin maka yaranka kafin wani abu yazo yasamesu, tunda yanzu munsan waye Pablo Escobar din, munsan how he operate, munsan how notorious yake zamu shirya mishi da kyau kafin muce zamu kamashi ko jam’iyyan shi muyi case dasu” tunda yafara maganan Baba ke kallonshi baice tak ba, IG yace “your children are mine, I can’t imagine wani kasurgumin dan ta’adda ya sacemini kananun yarana yammata ko aure basuyi ba kasan risk na hakan kuwa Ibrahim? Kasan me this abun nan will do to their future idan duniya tasan Pablo Escobar ya kwashe maka yara, babu wanda zaiso yahada zuri’a da matan da Pablo Escobar yay kidnapping. No no no banmaso nayi wannan tunanin nan Allah ya tsare, dama this whole operation is black operation mu kadai ne muka san dashi muka san abinmu, ko mun sakesu babu abinda zai faru ko wani abu yafaru ma you have me, da sanina akayi komi I can stand for you, kayanshi da direbobin shi yakeso kabashi ka karbi yaranka, family before everything kada kasaka rayukan the only yaran da Allah yabaka aduniya in danger in the name of kanason ka kama Pablo Escobar kanajina Ibrahim, idan baka kamashi ba an kama criminals dubu kuma duka duk kauda mugun daga doron kasa ne” kusan minti daya Baba yayi yana kallon IG kafin ahankali yasauke ijiyan zuciya cikeda damuwa yace “naji yallabai amman ina neman alfarma wajenka” gyadamai kai IG yayi yace “ina jinka” shiru Baba yayi kaman mai tsoron abinda zai fadi kafin cikeda dakewan zuciya yace “dan Allah Yallabai kabarni nan handling this issue in my own way Dan Allah Yallabai kada kabada umurnin asaki kayan nan ko direbobin nan dakanka kabarni nayi decision din idan nagama tunani” baki IG yabude yana kallon Baba kawai, sai chan yace “shikenan Ibrahim daman shawara ce nabaka duk yanda kai handling case din is fine but remember family comes first karkace ban fadamaka ba” gyadamai kai Baba yayi sannan ahankali Baba yatashi yawuce yafita Aliyu yabishi abaya IG ya girgiza kai kawai Ibrahim nada taurin kai na gidi komadai menene Allah ubangiji ya karemai yaranshi.
Office Baba yakoma ya zauna ganin Ammi taki daina kira yasa ya kashe wayan gabaki daya, yakalli Aliyu yace “hoto kawai yatura mini baice wani abu game da hoton ba, na gwada kiran number da yakirani da ita dazu kaman number bata kan network” ahankali Aliyu yace “Yallabai can I say something?” Batare da Baba yakalli fuskanshi ba yace “you can” ijiyan zuciya yasauke, ahankali yace “abinda IG yafada gaskiya ne, yallabai koda ace yau bomabomai yake sakawa akasan nan bama kayan shaye shaye ba, gaskiya da kamashi gwara ka hakura ka bashi kayanshi yasaki yaran nan” cikeda masifa Baba yace “did you look at me kaman mai tsoron wani lowlife stupid drug kingpin eh? Bakasan dama wannan tsoron da shakkanshi shine dalilin dayasa ya kwashe su Yasmeen ba sabida na tsorata nasaki kayanshi da gudu, he can’t do anything to them jikina yabani hakan, he’s a druglord not girl trafficker, babu abinda zai sami yarana I am sure, yes yes” yanda Baba ke magana kaman ya zare hakan yasa Aliyu bai kara fadin komiba, tashi Baba yayi yakwashe duka wayoyin incase Pablo yakira sannan yadauki key motanshi yace “zanje masallaci daganan zanje gida” yawuce fuuu yafita.
KINASON MAGANA DA NI M SHAKUR??? Click on this link and chat me up directly;
wa.me/+2347012181461
✨KYALKYALIN KAUNA✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣4️⃣
Saida yay sallan juma’a wanda shidai yasan yay salla ne amman baida natsuwa sanan yashiga mota yatuko kanshi zuwa gida, duk wanda zai kalli Baba yasan ba lafiya ba, yayi dialing number da Pablo yakirashi dashi yau da safe yafi sau dari but number bayama connecting kaman babu number a network, parking yayi a kofar gida yadade zaune a motan sannan yabude mota yafito yashiga cikin gida ahankali, Ammi yagani zaune atsakar gida idanunta sun jajir kaman kuka tagamayi gasu Kaka da Hajjo akanta da duka yaran gidan harda Sa’a kowa yay zuru zuru, ana ganin Baba Hajjo tace “yauwa ga Baban Nanan nan yadawo” dasauri Ammi ta mike tsaye jin ance ga Baba kafin ma yakarasa idasowa wajensu tayi wajenshi dasauri tace “ina suke, su Hassana kowa yadawo daga makaranta banda Farida da Nanah, naje makarantan principal tace ka aiko a daukesu amman kuma wai kasake kiranta kaman dawani matsala, and yanzu danaga fuskanka nasan da matsalan dagaske ina suke, ina Farida da Nanah?” Kallon fuskan Ammi yayi wato uwa uwace she is feeling something, jikinta yabata ba lafiya, daidai nan aka bude gate, Baffa ne dakuma Baba Karami suka shigo dan dama duk Friday bayan masallaci suna dawowa gida aci abinci kafin akara fita, ganin Baba yasa yace “Ibrahim meke faruwa Maman Sa’a takirani wai ba’aga su Farida ba” yay maganan yana karasowa gaban Baba, fuskan Baba kadai yagani yagane da wani abu babba ma ba karami ba, ganin Baba yayi shiru har lokacin yaki magana yasa Ammi dake kallon fuskan Baba all this while takai hannayenta tadaura saman kanta saikawai tafashe da kuka sosai tace “Baban Nanah ina yarana? Kayakuri ka taimaka kafadamini inda yarana suke zanje dakaina in dauko su, jikina nafadamini they’re in trouble, tunda natashi yau I’ve been feeling somehow ina yarana eh, kafadamini ina yaran……” “an kwashesu!” Baba yay maganan da ihu ranshi abace cikin wani kalan zafin zuciya, kowa na gidan tsayawa yayi kikam yana kallonshi babu wanda ya iya yay magana, Ammi daura duka hannayen ta tayi saman kirjinta dake wani kalan mahaukacin bugu, Baffa ne yay namijin kokarin iya magana yace “ban gane an kwashesu ba Ibrahima” dan lumshe idanu Baba yayi dan yakasa jure kallon da Ammi kemai kaman wacce ta zare, kafin ahankali yabude su cikin wata kalan raunanniyan murya yakalli Yayan shi yace “Yaya akwai wani case danakeyi da wannan dan kwayan Pablo Escobar….!” Ganin kalan kallon da Ammi kemai yasa yakalli Baffa yace “Yaya na kwace motan kayanshi dasuka shigo na kwayoyi guda biyar da direbobin shi nakama shine yay kidnapping, Nanah, Farida dakuma Yasme…….” luuuuuu kawai Ammi ta tafi a asume dayasa su Hajjo tareta, azafaffe Baba ya karbeta daga hannunsu yana kiran sunanta, Baffa yace “kwantar da ita akan tabarma kawo ruwa Sa’a” da gudu Sa’a tawuce randa tadebo ruwa takawo, yayyafamata Baba yayi a fuska wani kalan ijiyan zuciya Ammi ta sauke sanan ta bude idanu tabi kowa na wajen da kallo kafin ta sauke idanunta kan Baba, dawani kalan sauri ta yunkuro tana kama hannunshi kaman wacce ta zare tace “wasa kake ko Baban Nanah, babu wanda yasace mini yara, Yasmeen na makaranta yau tanada test na Islamic Education wlh, kirata kaji tana makaranta, Yasmeen na makaranta wlh Baffa ni nasani” cikin wani kalan yanayi Baba ya lumshe idanu ganin Ammi na having panic attack surutai kawai take, cikin sambatu Ammi tace “Nanah autana yau batason taje school nasata taje, my little girl yaushe ta warke daga measles, ta gayamini idan tadawo shayi zata sha da buredi I promise, I promise her zan mata, ni nasan tana makaranta babu wanda zai sacemini yarinya she’s just 4, Faridah Sa’a ai Farida batai breakfast yau ta tafi school bako” Gyadamata kai Sa’a tayi idanunta nacika da kwalla sosai, Ammi tace “nasan she’s hungry yanzu bari natashi naje na musu girki dasauri wani abu ne yarike dukansu a school yanzun nan zasu dawo zaku gani, zakugani” arude Ammi ta yunkura tai hanyar kitchen Hajjo tabita da sauri, Baffa ya kalli Baba dayabi Ammi da kallo idanunta sunyi jazur yace “tell me everything” anatse Baba yaciro wayanshi ya kunna hoton ya nunamusu, salati Yaya tayi Sa’a kuma tafashe da kuka sosai koba komi tanason yan uwanta sosai wlh, adake Baffa yace “Ibrahim I know you but akanme zakai case da babban criminal haka idan yama yaran nan wani abu fa? Duk wanda zaiyi kidnapping har yarinya yar shekara hudu ai kasan baida imani yanzu ka kirashi”? Cikeda damuwa Baba yace “number daya kirani dashi batakan network, sai yagadama yakirani shine zan iya magana dashi” cikeda masifa Baffa yace “to meyakeso” ahankali Baba yace “direbobin shi da kayanshi inba hakaba bazai sakesu ba” cikin tsananin fushi Baffa yace “I don’t care about your work, mutumin nan harkan kwayoyi yake bawai dan boko haram bane, kasaki abubuwan shi yaran nan sudawo gida Ibrahim inba hakaba zan yi fushin daban tabayi dakai ba” lumshe idanu Baba yayi cikeda damuwa kaman zai saki kuka, cikeda damuwa sosai yace “Baffa bazan iya sakinsu without proof of life ba, I need to be sure yarana are fine kafin nasaki kayansu” cikeda damuwa Baffa yace “stay with phone zai kiraka, katashi ka koma wajen aiki duk yanda zakayi kayi yaran nan sufito sannan kafita harkan duk wanda ke kokarin illata maka iyali Ibrahim, kaje zan zauna agida mukula da Maman Nanah, if akwai wani abu I will call u just go and handle this issue” tashi Baba yayi kaman wanda kayan cikinshi suka mutu, Yaya tace “Allah ubangiji yafishe yaran nan, Yasmeen da Farida dasuke yammata Ya ubangijin sammai da kassai ka tsaresu ka kare mutuncin su na yara mata ya Allahu, wayyo Allah na mun shiga uku mun lalace wannan wace kalan kaddara ce, yo wayan nan yan fashin ne ko kidnappers kuka kirasu idan sukama yaran nan wani abu fa, yammata Farida sha shida, Yasmeen ashirin na shiga uku na, nan nan faram faram Yasmeen tazo tamin sallama da safen nan har ina bata naira hamsin, Ya Allah ka tsaremini Yasmeen da Farida da Nanah ka karemini mutuncin su” Yaya tafashe da kuka sosai tace “ga Maman Nanah chan kaman zarewa ma tayi yo ba dole ba, yaranta kakap uku wasu chan kattan maza su dauke sabida aikin ubansu” juyawa Baba yayi yafice yashiga mota ya kifa kai yana tunani kafin chan yadago kanshi yatada motan yabar unguwa babu abinda ke ranshi irin yaranshi.
✨KK✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣5️⃣
For your original Egypt Abayas,home decor, Gold (new and used), shoes that are qualitative and unique at affordable price , siyen daya ko sari (wholesale and retail) contact +201123302418
Instagram @Shopper_topia
WhatsApp group *Maryam’s Egypt abaya *
Ahankali idanunta ke rawa rawa kafin gently tabude idanun nata dasukai wani kalan jaaaa suna kadawa suna juyawa tanabin kitson kalaban datagani nakan Nanah na lilo da kallo kafin tawani kalan lumshe idanu sannan tasake budesu tadaurasu kan fuskan Nanah dake kallonta tana wani kalan kuka bakinta abude majina har saman kan hancinta tana zaune akan kujera hannunta adaure kafafunta adaure, sosai take kallon Nanah da jajayen idanun nata dake juyawa tana ganin yanda take kuka amman batajin sound ko guda daya kunnenta yadaina aiki, lumshe idanunta tasakeyi tareda wani irin sauke ijiyan zuciya kaman daga sama taji. “Anty Yasmeen, Anty Yasmeen” wani kalan nesa nesa takejin sunanta ana kira hakan yasa tasake bude idanuwan nata kadan tai stretching idanun kaman wacce keson taga abu by fire by force, Farida tagani da Nanah ke tsakaninsu itama idanunta sunyi jajir ga hawaye shame shame asaman fuskanta azaune tana kallon Yasmeen din tace “Anty Yasmeen dan Allah kitashi kada ki kara kulle idanunki, Anty Yasmeen kalleni nine Farida ne, ga Nanah nan, an sacemu an daukemu anyi kidnapping namu bamusan ina ne nan ba, maza daban daban dasuka rufe fuskokinsu sai shigowa nan suke, Nanah tayi fitsari ajikinta, kitashi and do something, Anty Yasmeen!!!” Farida takirata dawani kalan karfi dayasa jikinta yawani kalan rawa, tasake lumshe idanunta kafin ahankali tabudesu babu abinda takeji banda karan kukan Nanah, Nanah nawani kalan kuka kaman ana yankata, sai alokacin abinda suka shakamata yasoma sakinta, tundaga kan hannuwanta dake jikin kujera a daure dawani belt dake attached to kujeran tabida kallo zuwa kan hannun Nanah dake kusada ita zuwa na Farida da duk suke kallonta Farida na kuka itama sosai tana kallon Yasmeen din dataga har yanzu bata dawo daidai ba kawai juya idanuwanta dake layi take, tabi kafafuwansu suma dake kulle da belt na kujeran tundaga kan na Farida har zuwa nata kafin ahankali ta daga kanta dake layi tabi saman dakin da kallo tana kallon fankan dake juyawa asama karan kukan Nanah na ratsa mata kai, tana mamakin inda take haka kafin kaman daga sama komi yasoma dawo mata ta tuna tana cikin Keke hanyar makaranta suka kusan samin hatsari sai wani yazo zai bata handky yasa a hancinta daganan bata sake sanin abinda ke faruwa ba, kaman wacce aka ciro daga rijiya wani kalan ijiyan zuciya tasauke mai kara tareda yunkurowa ta zauna da kyau takalli Nanah dake kuka dasauri, Farida dake kallonta sai alokacin tafashe dawani kalan kuka lafiyayye tace “Anty Yasmeen kin farfado”? Dasauri Yasmeen data rude cikin muryanta da baya fita da kyau takalli Nanah tace “Nana, Nana kalleni nan” cikin kuka Nanah takalleta tace “Anty Yasmeen ki kwance mini hannu da kafafu mutafi gidan mu ina ne nan” cikeda damuwa sosai, Yasmeen takalli Farida da itama ke kuka girgiza mata idanu tayi tareda nuna mata Nana da baki alamun tadaina kuka sabida Nanah tai shiru hakan yasa Farida tai shiru, Yasmeen takalli Nanah tace “daina kuka to zan kwance ki kinji, stop crying, zamu tafi gida wajen Ammi nan bada jimawa ba Auta” gyadamata kai Nanah tayi ahankali, dasauri Yasmeen taduka tadaura bakinta kan hannunta tana kokarin kwance belt din da bakinta da duka karfinta ganin haka yasa itama Farida tafara haka, bude kofan dakin akayi aka wani bugo kofan hakan yasa dukansu suka dago kansu Nanah takara fashewa da kuka sabida yanda bude kofan ya firgitata, Wike ne yashigo dawasu maza guda biyu da duk sun rufe fuskansu da hulan fuska ga ledoji a hannunsu dakuma bindiga, kallo daya Farida tamusu takulle idanunta tareda fashewa da kuka tashiga sambatu, jikinta narawa sosai, tasan Baba nada bindiga dan dansanda ne amman bata taba ganin bindigan shi ba sai yau take ganin manya manyan bindigogi haka ana yawo dasu agabanta, itama Yasmeen kallo daya tamusu tawani kalan runtse idanu tunda aka haifeta bata tabajin tsoron dataji tanaji yanzu ba, sace su akayi yanzu to mesukayi? Su waye mutanen nan? Mesuke nema awajen su? Hannunta tadaura akan hannun Nanah takama gam gam tarike tana karanto duk wani addu’a data iya azuciyanta.
Binsu gabaki daya Wike da shi kadaine baisa face mask ba da kallo kwashewa da dariya sosai yayi ganin duk yanda suke a tsorace sunyi zuru zuru kaman sunga mala’ikan mutuwa, kafin yakalli Nanah dayaga tana kara sakin wani