Showing 30001 words to 33000 words out of 190707 words

Chapter 11 - KYALKYALIN KAUNA HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

11 Oct 2024

9318

nashi ta hanyar daura kafa daya akan daya.


Wani kalan kamshi da tunda take arayuwanta bata tabajin kamshi mai kwatankwacin dadin nan bane yadaki hancinta dayasa tadaure tabude idanunta ahankali dan kadan takalli gabanta daidai shima yana dago kanshi dan kallon yaran for the first time suka hada idanu dudda idanunshi na cikin bakin glasses. Wani kalan faduwa gaban Yasmeen yayi dasauri tasauke kanta tareda sake maida idanun ta lumshe kallo daya tamai tagane shine Ogan sabida kalan zaman kadai dayayi akan kujeran, dauke kanshi yayi tareda dan girgiza kanshi kadan sabida yanda Nanah ke kuka yana shiga kanshi, he hates children and he hates kukansu, daurewa yayi ahankali yadaga hannunshi sama hakan yasa dasauri Dan yaciro kwalin cigar dinshi yaciro daya yasamai a hannu sannan yazo tagaban shi ya kunna lighter akan taban hakan yasa ahankali Maheer yakai taban bakinshi ya zuka kadan tareda dan runtse idanu jijiyoyin kanshi har mimmikewa suke sabida yanda kukan Nanah ke damun kwakwalwan shi, sake kai taban bakinshi yayi zai zuka kawai yakasa controlling kanshi yayi mugun loosing cool nashi cikin wani mahaukacin tsawa da saida dakin yawani amsa yace “Ke!” Ba Nana ba har Yasmeen da Farida dukansu saida suka firgita, cikeda bacin rai dakuma daka tsawa kaman dakin zai fashe yace “shut up!” Wani kalan zabura Nanah tayi tana kuka sosai kaman zata mutu ta kankame idanunta tana kwakume Yasmeen gamgam ta bayanta kaman zata barka mata riga irin yanda yara keyi din nan idan sunga wanda suke tsoro tace “Anty Yasmeen Ammi Ammiii” tana maganan tana makyarkyata tana sakin fitsari bin fitsarin fitsarin Maheer yayi da kallo datakeyi tana kuka cikin fushi yakalli Wike yace “why did you bring this child to my house bayan kasan how much I hate children haaaa, shoot her idan batai shiru ba!” Dawani kalan sauri Yasmeen tadago kanta takalleshi tana boye Nanah abayanta da kyau gabanta na bugawa ita bama tasan ko kallonta yake koba kallonta yakeba sabida glasses na idanunshi but dai fuskanshi na kan kallonsu ne, cikin wata kalan muryan dake cike da tsoro mai kuma mugun sanyi tace “she’s just a child that is very scared, idan da wacce zakasa a harba adakin nan should be me! Not my sisters” for the first time Maheer zubama Yasmeen manyan idanunshi yayi dudda ta cikin glass ne kasa jurewa tayi tadauke kai da sauri ta tsugunna tareda kallon Nana da idanunta ke kulle gamgam kaman na Farida ahankali tashafa kanta da fuskanta tace “kiyi shiru Nanah kinga Uncle bayason kukan yara, please Nanah zan kaiki wajen Ammi idan mungama kinji yi shiru to Nana na” gyadama Yasmeen kai tayi ahankali ta rungume Yasmeen da sauri, ahankali Yasmeen ta mike tsaye tareda sauke Nanah taboyeta abayanta sannan tasauke kanta akasa tana wasa da yatsunta kirjinta bugawa kawai yake kaman tashin aradu, da hannu Maheer yama Dan alamu yabasu wani takarda da Dan ke rikeda shi hakan yasa Dan yataho gabansu baya Yasmeen tayi dasauri a tsorace ganin wani ya nufota, Maheer duk yana zaune inda yake yana kallonsu, tsayawa daidai gabansu Dan yayi yana kallon fuskan Yasmeen din ganin kaman yataba ganinta amman yakasa tunawa yabata paper tana wani kalan nishi kaman zata shide ta amsa tana kallon paper, Dan yace “wannan sakone zuwa ga Baban ki da zaki karanta yanzun nan zan muku video idan zaki fara karantawa dazamu aika mishi, let’s hope he listens yasaki kayanmu muma musake ku” yay maganan yana komawa baya itakuma Yasmeen na kallon rubutun takardan da takasa gane komi ciki ko abin yahadu da she’s under stress da tsoro ne oho but word na farko kadai ma takasa karantawa ballantana sauran, waya Dan yaciro yakunna video yakalli Yasmeen din yace “kifara nafara video” gyadamai kai tayi ahankali takalli paper tana ware manya manyan idanunta dasuka kara haske tass sabida safiya ne kwaiduwan idanun sunyi gray sosai tana kokarin karanta word na farkon ma takasa, ahankali Maheer dake shan taba yadago kanshi yadaura mayun idanunshi akan fuskanta yana kallonta tundaga kan hannayenta data rike paper gamgam yatsunta na motsi sosai da dan tiny little red lallen daya rage a kumbunanta, zare hannunta daya tayi daga rikon datama paper takai yatsanta dasauri tadaura akan letters din kaman mai koyan ABCD tace “P……..Paaaaa……” tasake kakarewa dakin yay tsit ana kallonta, kafin takara daddagewa da duka karfinta hawaye na taruwa a idanunta tsabagen yanda take fama ta karanta tace “Paaaa……bu…bu….no….boooo…..” Daidai nan hawaye ya sauko daga idanunta dasauri takai bayan hannunta ta share kwallan tana kara ware manyan idanunta trying to read it by fire by force kowa na kallonta na dakin, ahankali Farida dake bayanta tafito gently tasa hannunta akan paper tareda kallon Yasmeen murya chan kasa tace “kawo na karanta Anty Yasmeen” gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali gwanin ban tausayi sannan tasakin mata paper karba Farida tayi tadan dagokai takallesu kasa kasa dan takasa kallon fuskan kowa kafin tasauke kanta dasauri cikeda tsoro tace “my sister nada matsalan hada baki so I will read” sosai Maheer ke kallon Yasmeen data tsaya gefen Farida innocently har lokacin kwayan idanunta na kyallin hawaye sabida hawaye dasuke ciki, anatse Farida tafara karanta takardan.

“Pablo Escobar yabaka 1hour kasaki his shipment da drivers nashi yasaki maka yaranka inba hakaba zaka tsinci gawawwakin yaranka ukun nan dakake gani akan video agaban police station dinku”.
Fashewa da kuka sosai Farida tayi cikin wani kalan muryan tsoro da tsantsan tashin hankali ganin sunce zasu kashesu tace “Baba dan Allah ka basu abunsu we are scared Baba” katse video Dan yayi yajuyo yakalli Maheer dake kallon Yasmeen har lokacin cikin glass nashi yace “it’s done Sir” gently Maheer yamike tsaye ganin zai juya yasa cikeda Yasmeen tace “kaine Ogansu ko”? Chak Maheer ya tsaya batare daya juyoba hakama yaranshi, Dan yakalli Yasmeen datai magana yace “ke are you okay kike tambayan sir ko shine Ogan mu” wani kalan kallo tama Dan adake cikeda damuwa dakuma jarumta tace “da Oganka nake magana bada kaiba” wani kalan juyowa Maheer yayi kaman zaki jin yanda yarinyar tai magana da saida Yasmeen din tai baya da sauri sannan ta tsaya takalli hayakin taban daya huro tasa hannu ta kakkabe kafin takalleshi tace “inaso kasaki kannena su koma gida ni ku barni anan har lokacin da Baba zai saki kayanku da direbobin ku dakuke so yasaki” sosai Maheer yake kallonta yanda takemai maganan kaman tana bashi command, ganin yanda yake kallonta yasa Dan yabude baki zaiyi magana yadagamai hannu alamun kar yayi, yadda karan taban hannunshi yayi akasa cikin wani kalan husky voice yace “are you commanding me”? Cikin yanayi na matukar bacin rai ganin yanda Ogansu keda rainin wayo yasa tace “I don’t know! All I know is kannina basuda lafiya, kabarsu sutafi niku rikeni bakada imani ne dazakai kidnapping 4yrs old little girl”? Hannun Yasmeen Farida takama cikin tsoro fizge hannunta Yasmeen tayi cikin zafin rai tai ihu tace “ki barni, yadauka tsoronshi akeji ne the worse zai iya shine ya harbeni namutu ko yadade baiyiba, baka da Imani ne”? Sosai abin yabashi mamaki tunda yake babu wacce ta taba kallonshi tamai magana kwatankwacin haka ballema rashin kunya irin na yarinyar nan, wani makirin murmushi yayi tareda shafa sajenshi yana kallonta still kafin cikin wani dan iskan takadirin murya yace “bani dashi ko kadan” yajuya mata baya tareda kallon Dan yace “take this lousy girl and lock her up a study” Maheer yay maganan azafafe tareda juyowa yana kallon fuskan Yasmeen din, zaro idanu tayi tana komawa baya tana kallon sauran mazan dakin dake dumfarowa inda take, Farida tafashe da kuka suna kankame ta, ganin da gaske suke dauketa zasuyi yasa dasauri Yasmeen tace “kayakuri dan Allah karka sa akaini wani waje daban da kannena please please please dan Allah” juyawa Maheer yayi fuuuu yafice daga dakin, Dan da Nas suka bishi abaya, su Farida suna ji suna gani daukanta akayi aka fita da ita daga dakin suna kuka sosai suna kururuwa itama Yasmeen na kuka sosai tana kururuwa aka kallesu itakuma aka wuce da ita wani waje.

✨KYALKYALIN KAUNA✨



✍🏻M SHAKUR



EPISODE 1️⃣8️⃣

For your original Egypt Abayas,home decor, Gold (new and used), shoes that are qualitative and unique at affordable price , siyen daya ko sari (wholesale and retail) contact +201123302418


Instagram @Shopper_topia
WhatsApp group *Maryam’s Egypt abaya *

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj



Ita bama tagane inda akai da itaba kokawa take sosai tana tutturjewa tana kokarin kwace hannunta tana kuka sosai tana waigawa tana kiran Farida da duka muryanta da Nana, batasan ta ina akabi da itaba wani babban mahaukacin falo suka shigo da ita akai wani corridor da ita sai chan aka bude wani kofa daganan bakin kofa aka jefata cikin dakin saida ta buge dan kwalin data rufa dashi ma fita yayi daga kanta bata damu da bamata bi ta dankwali ba tashi tayi da gudu tai kofan tana kuka sosai tashiga kiciniyar bude kofan amman arufe hakan yasa tafashe da kuka sosai tana bubbuga kofan tace “dan dan Allah, dan Allah ku budemini kofan, wlh Nanah da Farida zasuyita Kuka please please dan Allah kuji tausayina dasu Nana kubude mini” gajiya tayi da bubbuga kofan ahankali ta tsugunna jikin kofan tareda kife kanta akofan tana wani kalan kuka mai tsuma rai ashe tun jiya batai kuka bane sabida tana taredasu Farida tana ganinsu, yanzu da aka rabasu sai taji duniyan gabaki daya yamata zafi kawai Nanah kefadowa ranta da Farida ga tausayinsu da yanda zasuyi yanda batanan din nan takeji, tai kuka tai kuka harta godema Allah, takai kusan awa biyu awajen kofan kuka take once in a while tana roko abudeta, chan same kamshin turaren nan dataji dazun ne yadaki hancinta hakan yasa tamike tsaye dasauri tana wani kalan bubbuga kofan tana jijjiga kofan tana kuka. “Dan Allah kace su bude ni dan Allah, kayakuri please please please, Nanahhhhhh, Faridaaaa, Ammiiiii……. Dan Allah kayakuri baran karaba” bude kofan dataji anayi yasa tai shiru tashiga kallon kofan da sauri takoma baya, shigowa Maheer yayi dakin yana sanye dawani 3quater navy blue na Fendi sai off white t-shirt mai gajeren hannu dayamai wani kalan mahaukacin kyau dan kunnen diamond dake makale a kunnenshi yana wani kalan shinning yana sheki hannunshi rikeda wayanshi, kafafunshi sanye dawasu fararen crocs designers, yana zuba wani kalan kamshi kaman wanda yafito daga kogin turare, wavy gashin kanshi na kyalli da sajenshi, lips nashi sunyi pink sosai looking so moist and succulent, wannan karan baisaka bakin glasses ba hada idanu sukayi wani kalan faduwa gabanta yayi dasauri ta sauke kanta kasa ganin yanda yakeda dogayen gashin idanu kaman mace, takai bayan hannunta tana share fuskanta, dauke kai yayi yawuce cikin office din shikuma Dan dayake tsaye ata waje yarufo kofan dasauri tai wajen kofan tashiga bugawa tanajan kofan ganin ba’a budeba yasa takife kanta jikin kofan tafashe da kuka sosai kaman wata marainiya da aka kulle adaki tanaso tafita.


Ahankali yazauna kan kujeranshi yaja system yabude ya kunna kafin gently yadago kanshi yadaura manyan idanunshi akanta yanabin tundaga gashin kanta dayake abude da kallo wanda wani shuku dayay tsufa ne akanta but baihana kaga silky black long hair nata ba, gashin ma sun zazzaro waje dan tanada tsantsin gashi gasu kuma so coily, ganin duka gidan nan babu mai imani ko tausayin Nanah karama ma dake kuka balle ita babba yasa tawani juyo da sauri karaf suka hada idanu yahade rai tamau ya tsuke fuska, wani kalan wankamai wani uban harara tayi tareda kai bayan hannunta tashare fuskanta tass tass tawuce wajen dan kwalinta datagani akasa ta dauka takai hancinta ta fyato majina, wani kalan yatsine fuska Maheer yayi shi karan kanshi baimasan yayi ba irin ewww din nan dirty girl, kaman taji ajikinta dago manyan idanunta tayi ganin yanda yayi da fuska yasa takara wankamai wani mugun harara kaman zata kasheshi da idanu dayasa ya zaro idanushi cikeda mamaki irin wat! Sake ballamai hararan tayi ciki ciki tace “mara imani kawai” cikin kakkausan murya yace “mekika ce”? Juyowa tayi takalleshi da sauri suka hada ido cikin tsantsan dakewa dan yanzu jitake dukma abinda zai faru yafaru tace “cewa nayi Allah yasa kada Babana ma yabaka abinda kakeso duk abinda zakayi kayi” tsayawa yayi chak yana kallonta abin looks really strange to him, dan tunda yake babu wacce tama isa tamai wani kalan kallo balle tamai rashin kunya haka wato she’s stubborn kaman babanta, kwallin taba yadauka yabude yazaro daya yakai bakinshi yadauki lighter zai kunna saikuma yakalleta anatse yace “idan Babanki bai bani kayan kwayoyi na ba saina kasheshi har lahira” zaro manyan idanunta dasuke jikeda ruwan hawaye tayi ta kalleshi kana ganinta kaga tsoro da fargaba dakuma shakkan shi aranta jin yanda yake kiran kisan kai kai tsaye, hakanan saiyaji yaji mugun dadin hakan, lighter yasa ya kunna taban sannan ya ijiye ya zuki taban ya fuzar ahankali yace “bashi kadai zan kasheba duk wani tsatso da jininshi daya bari aduniya sainabi na kashesu daya bayan daya” yakara zukan taban ya fuzar, yabita da kallo yanda yaga yan dogayen brown skin yatsunta ke rawa masu kyau dabasu da dark knuckles, gently yadauki wayanshi yabude yay dialing number Dan yasa a speaker yace “bari nafara da kannenki” dawani kalan sauri ta kalleshi dan bata gane takamaimen mene ze fara da kannenta ba, daukan wayan Dan yayi yace “yes sir” dan shiru yayi yakalleta yanda take zaro manya manyan idanunta tana kallonshi cikin wani kalan murya na asalin mugunta da isa yace “shoot those children Dan, ka kwashe gawawwakin su ka bama Kikito yaci don’t cut the call, execute the task ina kan wayan” dasauri Dan yace “Yes Sir” wani kalan mikewa tsaye Yasmeen tayi kanta har juyawa yake jikinta wani kalan bari bari yafara kaman wacce takeda farfadiya tana dumfaro shi tace “dan girman Allah, dan girman Allah malam kada ka kashe kannina, kill me, nika kasheni dan Allah let them be, ka kasheni, kayakuri dan Allah kaya kuri” tana tafiya tana hade hannayenta biyu tana rokonshi tana karasowa wajen dayake ta zagayo ta bayan table din kusada shi tafashe da kuka sosai tahade hannayenta biyu tana kallonshi yanda yakeshan katon lukutin taban abinshi ko kallonta bayayi daidai nan taji karan bude kofa tawayan saiga kukan Nanah kaman zai tsaga wayan, Dan yace “Sir gani nan na iso” zaro manyan idanunta tayi kirjinta na bugawa sosai tarushe da kuka tai kneeling gefenshi takai hannunta saman hannun kujeran dayake zauna tana kallonshi tana kallon wayan tace “dan Allah kada ka kashe kannina dan girman Allah dan ya Rasullullahi, bawan Allah kayakuri kada ka kashe min Farida da Nanah su kadai ne kannina dan Allah” daidai lokacin taji kukan Nanah da ihun Farida tana cewa “wayyo me kake nunani da bindiga” Yasmeen batasan lokacin data mike daga kneeling din datayi ba hannunta har rawa yake tawani kalan daukan wayanshi garin haka hannunta ya gogi nashi wani kalan shocking Maheer yaji dasauri yakalleta, bama tasan tayiba dasauri takai wayan kunnenta kaman ba a speaker wayan yake ba tana ihu sosai tace “dan Allah kada ka kashemin kan……” tuss tuss taji sau biyu wani kalan ware idanunta tayi kafin idanunta suwani kalan juye sama tai baya luuuuu zata zube kasa dawani kalan sauri Maheer yatarota hakan yasa tafado jikinshi a sandare.

✨SPARKLES OF AFFECTION✨



✍🏻M SHAKUR


EPISODE 1️⃣9️⃣

Anty kene ba warwaro, ba dan kunne ba sarka haba dan Allah, Oya Oya shiga group din nan kije ki kwashi sarkoki da dankunnaye akan kudi dan kankani.
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JGCK4a99vpjGLtepWcYwrn


Wani kalan sanyi yaji ajikinshi a asalin cikin bargon kashin jikinshi da tunda yake koda yay zaman Russian ma da Alaska baiji kalan irin sanyin nan acikin jikinshi ba, in his entire life banda Hajiya Maryam this is the second lady dayataba rikewa ko ta taba shiga jikinshi, tundaga kan guntayen hawayen dake gefen idanunta yake kallo harzuwa kan small yar doguwan fuskanta da brown skin nata kewani shinning kaman butter da aka narka, dan karamin bakinta yakara ja kaman wacce zazzabi ke shirin kamawa, goshinta da gashi yacika sun kwanta ga uban zufan daya ketomata agoshi sai sukai lub lub hakan yay mata wani kalan kyau idanunshi ya daura akan katon pimple guda daya daya fito mata a in between giranta guda biyu dayasa tai wani kalan kyau zuwa gudu ukun dasuka fito mata a kumatu dasuka mata bala’in kyau yasake maida idanunshi kan dan karamin pink lips nata dasukai so moist kaman ta shafa vaseline, wani kalan lumshe idanu yayi da bala’in sauri dan abin is somehow ko Hajiya Maryam baijin yataba tsayawa yamata wannan cikakken kallon dayama yarinyar nan ba kuma baimasan mesa yakemata kallan kallon nan ba, abu yaji yanamai yawo aciki kaman tafiyan butterfly dasauri ya runtse idanu saikuma yabude idanunshi da sauri yakai hannunshi kan goran ruwan shi dake kan table din yabude goran dasauri yakai duka ruwan saman fuskanta yana kallon fuskan yadaga goran yashiga juyemata ruwan, wani kalan nishi Yasmeen tayi dan ruwan akwai sanyi sosai hakan yasa ya tsayar da kwarara mata ruwan yamaida goran ya ijiye kan table yana kallon fuskanta still batare daya saki shoulder nata ba, ahankali take bude idanuwanta dasuka mata dishi dishi bamata gani da kyau idanunta na sauka kan wani kalan kyakkywan mutum dakenan kaman bakin balarabe ga lips dinshi jazur yana kallonta shima, cikin yanayi na asalin wacce bata gama farfadowa sosai ba tabude lips nata, saikuma kawai tafashe dawani kalan soft kuka tana karasa bude idanunta tass tana kallonshi still, yanda take kuka kaman irin karaman yarinyar nan dabata dawani hope daya rage mata aduniya hawaye na bulbulowa ta gefen idanunta, wani abu ne yaji yatabamai zuciya ganin yanda take kukan, dawani kalan sauri yadauke kanshi cikin kakkausan murya dake nan a bit calm ba kara sosai yace “tashi daga jikina” makemai kafada Yasmeen tayi batare datayi ko motsi ba, hakan yasa dasauri yajuyo da kanshi ya kalleta kaman yanda take kallonshi shi baitaba ganin karfin hali haka ba, tana kuka sosai mara kara tana kallonshi hade giran sama da kasa yayi yakoma sak Pablo dinshi yace “tashi daga jikina” makemai kafada tayi tana kallonshi cikin idanu kyur batako kyaftawa, kwayar idanunta yakalla yanda yay gray

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login