Showing 75001 words to 78000 words out of 190707 words
"wh zanje nagayama
Ammi" dasauri ta mike tsaye hannayenta narawa har saida Sa'a ta lura hakan yasa yakama hannunta tajawota suka fito, tunda suka fito Maheer yadaura idanunshi kan Yasmeen da kanta ke kasa har suka shigo cikin falon Sa'a ta zaunar da ita kan 1sitter dake facing Maheer sannan tajuyo takalli Maheer akunyace itama tace "ina yini" dan murmushi yamata yace "Yaya Sa'adatu ina yini" wani kalan dadi Sa'a taji akunyace tace
"sannu da zuwa bari naje" Gyadamata kai yayi tajuya tafita daidai lokacin Farida na shigowa da wani hadadden tray da kayan kwalama ke kai taba zuwa wani stool tajawo tadaura akai sannan itama tafice daga dakin bayan tasaci kallon Yasmeen da kanta ke kasa sai wasa da gyalen jikinta take.
Kusan 20min dukansu suna zaune adakin babu wanda yay magana acikinsu.
For the first time in those 20'min yajaye idanunshi daga kanta yakalli tray da aka kawomai zobo ne mai sanyi a jug da cup sai dambun nama da cincin dago kanshi yayi yakalleta ahankali yace "zoki zubamin drink nasha" kaman bazata dago kanta ba ahankali tadago kanta takalleshi suka hada idanu for the first time tunda yazo faduwa gabanta yayi sosai so take ta dauke idanunta amman ina takasa yay locking eye contact nasu strictly yamata pointing abin gabanshi da yatsa alamun tazo ta zubamai, bataso tayi bamataso ta tashi daga inda take amman takasa musu tashi tayi ahankali tamike tsaye tana jajjan gyalen jikinta tana lullube ko'ina najikinta sabida vanda yake mata lafiyayyen kallo ko kunya bayaji saikace baitaba ganinta babu hijabi babu mayafi bama, karasowa gabanshi tayi ahankali ta tsugunna taki kallonshi jug din tadauka duk yana kallonta ta tsiyayamai zobo a glass cup sannan ta jiye juice din tadauki cup din ahankali tadan dago kanta kaman mai tsoron kallonshi tamikamai hada idanu sukayi dasauri tadauke kai murya chan kasa tace "ka amsa hannuna yagaji". Dan murmushi kadan yasaki yana kallonta kaman yau yafara ganinta he just wants to understand dalilin dayasa tunda yasan yarinyar nan yarasa peace of mind he's just chasing after her, for how many years now baitaba abandoning sana'an shi ba but sabida yarinyar nan yabar komi tsabagen yanda take kanshi yazo in disguise zai aureta, what kind of charm tamai?
What kind of black magic? He just hope idan ya aureta zai dainajin abinda yakeji yacigaba da rayuwanshi. "Ni kadaina kallona" tafadi tana dauke kai tana kallon gefe, dan kunya yaji baice komi ba yasa hannunshi yadaura kan kan nata yahada hannunta da cup din tare batare dava karbi cup din ba yarike wani kalan zabura Yasmeen tayi sabida shocking din dataji dabadan yarike hannun nata da cup din da kyau ba data zubar da kofin da zobon, kallonshi tayi tana zaro idanu takalli kofa gudun kar wani yashigo kaman zatai kuka tana kallon kofa tace "ka sakeni pls kar wani yashigo dan Allah, dan Allah kaji" "to kalleni" juyoda idanunta tayi tazubamai su dasukaji kwalli dan lumshe idanu yay yabudesu murya chan kasan makoshi yace "why are you so beautiful Fateema"? Ya tambayeta cikin cool husky voice dayasa gabanta yafadi itama ta tsareshi da idanu takasa magana, murya chan kasa yace "I want u to be smiling sabida kowa yadauka kina sona and also" tasake zaro idanu tana kallonshi kara make murya yayi yace
"idan an tambayeki kan aurenmu kice yes" Gyadamai kai tayi da sauri tace "toka saken mini hannun" gently yasaki hannunta tareda karbe glass cup din Gyadamai kai tayi da sauri tace "toka saken mini hannun" gently yasaki hannunta tareda karbe glass cup din dasauri tajuya takoma tazauna yabita da kallo everything about her is just too perfect, tamai kyau bana wasa ba kaman ba itaba everything about the outfit looks fabulous ajikinta, zama tayi daidai lokacin aka fara kiran sallan la'asar 3:45 dasauri takalleshi hada idanu sukayi yana rikeda cup na zobon data bashi dauke kanta tavi da sauri tareda ballamai harara tadan turo baki tace "kazo katafi Baba yace awa daya zakayi" dagakai yayi yakalli agogon dakin yace
"ban cinye time dina ba" juyowa tayi dasauri takalleshi gain baya tsoron Baba kaman ma Baba baya lissafi shi daidai
E3 lokacin Nanah tashigo dakin tana
kallonsu faduwa gaban Yasmeen yayi kar
Nana taganeshi murmushi Nana tayi tana kallon Maheer dan murmushi Maheer yasakin mata da sauri tai wajenshi zata shige jikinshi tace "Uncle" dan firgita kadan Maheer yayi dahar saida Yasmeen dake kallonsu ta lura, murmushi yama Nanah yace "how you"? Washe mai baki tayi tana kallonshi tace "Uncle kanada kyau sosai" murmushi shima yamata ganin yanda take kallonshi kaman tanaso ya dauketa ne yasa yakai hannu cikin aljihunshi yaciro dubu daya sabuwa fil yamika mata yace "gashi jeki sayi minti" dan kallon Yasmeen Nana tayi yace
"karbi kayanki kada ki kalli Anty Yasmeen" Aiko dasauri Nana ta karba tana murmushi tace "Allah amfana
Uncle" tajuva tafice daga dakin, mikewa tsaye yayi ahankali yakalli Yasmeen sannan yafara tafiya jin takunshi
Yasmeen take har zucivanta dasauri tamike tsave tana wasa da kasan gyalenta, wuceta yayi ya tsaya waien kofa yace "jeki gayama Ammi zan tafi" gyadamai kai tayi yafita daga dakin itama tafito ko kadan batasan yana wajen kofan ba saura kadan tafadi vatareta da hannu fizge jikinta tayi da gudu tana turamai baki yay murmushi tawuce dakin Yaya su Ammi duk suna waien tace "Ammi zai tafi wai yanaso yagaidaki" kallon su Yaya Ammi tavi dasauri tace "kie ku gaisa
E3 yakamata" hijabin Yaya Ammi takarba tasaka taja hannun Yasmeen din tace
"muje" fita tayi waje hangota yasa
Maheer dake tsaye gaban Dakinsu ya tsugunna kanshi akasa anatse yace "ina yini Ammi" cikeda kunya itama Ammi tace "dan Allah katashi Maheer, tashi tashi" girgiza kai yayi batare dayayi magana ba Yasmeen dake kallonshi tawani murguda baki, Ammi tai murmushi tace "Ya aiki Maheer? Allah yabaku sa'a, Allah kuma ya taimaka ka gaida Baban ka dan Allah" Gyadamata kai yayi yace "sai anima" cikeda murmushi Ammi tace
"mujima lafiya" wucewa yayi Ammi tanunama Yasmeen gate da hannu alamun tabishi ta makema Ammi kafada, fita yayi ko 10secs baiyi da fita ba wani almajiri yay sallama dawata yar jaka mai kyau ahannunshi yace "salamu alaikum ance nabawa Fatima wannan" yay maganan yana karasowa wajen su Ammi kallon ledan Ammi tavi tace "kai maida" dasauri yaron yace "yaja mota yatafi" hannu Ammi tasa ta amsa tareda bude yar jakan kayan zakine zalla su chocolates biscuit da sauransu ajiyan zuciya tayi ganin ba kudi bane tabama
Yasmeen tace "gashi jeki kaima su Yaya" daidai an bude gate hakan yasa dukansu suka kallo gate Baba ne yashigo, maida gate din yayi yarufe yajuyo yana kallon Yasmeen baima jira yakaraso cikin gidan ba daganan gate yakalli Ammi cikin fushi
E3 yace "why is this girl dress like this?"
Faduwa gaban Yasmeen yayi dana Ammi itama amman Ammi tadaure takalli
Yasmeen daga sama zuwa kasa kafin takalli Baba daya karaso gabansu tace
"ohhh kayan salla su nace tasaka saina bata gyalen da makotan mu suka bani tsaraban makka tas......
." "Akan mene zaki
sa Yasmeen tayafa gale sabida wani"
Baba yama Ammi wani kalan ihu da saida gidan ya dauka dasauri Yaya da Hajjo suka fito su Sa'a babu wanda ya iya yafito Yasmeen taboye bayan Ammi jikinta na rawa gain kaman Baba zai daketa, shiru Ammi tayi tana kallonshi batace komiba Baba fa kaman yadawo da bacin rai vanuna kanshi yace "wato ina miki magana kinmini banza ga shashasha namiki magana ko" anatse Ammi tace "to me kakeso nace nidai banga aibun wanna shigan datayi ba shigan mutunci ne full covered kaya da babban mayafi ma bawai karami ba naga kuma ba fita tayi ba tana nan da..
5:45 AM
@
"akan me kike lalata mini tarbiyan yarana kina koyamusu shigan banza, sabida wani zaizo wajenta ne zakisa tasaka gyale eh, ke wace irin mahaifiya ce ina tarbiya kina batawa!" Sai anan Ammi taji ranta ya sosu, amman ta daure juyawa tayi takalli Yasmeen dake bayanta tana rawan jiki tana kuka tace "wuce kije dakin Yaya" juyawa Yasmeen tayi zata tafi Baba
E3 yace "koyama yarana rashin biyayya yanzu kike ga mahaifinsu ina magana zakice ta tafi" dasauri Yaya tace "dan
Allah Baban Nanah kayakuri abin baiyi zafi haka ba, Maman Nanah ke bashi hakuri magana ta mutu" Ammi da ranta yagama baci takalli fuskan Baba tace
"wIh bazan bashi hakuri ba duk abinda zaiyi yayi nagaji tunda so kake mu raba hali atsakar gida agaban yaranmu to muyi Baban Nanah, nagaji da halin nan naka, kuma idan yaron nan zai dawo gobe still gyale zansa tayafa kome zakayi kavi kaji" wani kalan kakkausan kallo Baba kema Ammi yace "ni kike gayama magana haka"? Daga murya Ammi tayi kaman yanda yayi tace "eh nagaji nagaji da halinka nadaga din ka zaci kai kadai ka iya ihu, an gayamaka yaran nan kai kadai ka haifesu ne, me dan na bata babban mayafin nan ta yafa? Sunna ne idan namiji yazo neman aurenka yaganka yasan wazai aura wanna sunnar annabi ce so l don't understand, kazaci tsoron ka akeji ne, tunda akazo neman Auren yarinyar nan samfari iri iri kake fitowa dashi idan bakaso tayi aure ne kafito kafada saika dauketa da ita da kanni ta kajika aruwa kash...
...." hannu Baba
yadaga zai mari Ammi Baffa daya shigo gidan yanzun nan yace "kul Ibrahim, karkasake kayi kuskuren nan" tsayar da hannunshi Baba yayi azuciye yana kallon
Ammi dake kallonshi cikeda mamaki itane yadaga hannu zai mara haka, wucewa tayi fuuuuu daki Baffa yakaraso wajen yarufe Baba da fada, ga mamakinsu gani sukayi Ammi ta fito da jaka dasauri kowa vace "Maman Nanah" itama Yasmeen dake kuka tasowa tayi da gudu tazo gaban Mamanta tarike akwatin tace "Ammi ina zaki"? Baffa yace "me haka Maman Nanah" Yaya ma tace
"Mehaka Maman Nanah dan Allah?"Baba ya tsaya chak yana kallonta gabanshi na faduwa sosai.
Jin ana tambayan Ammi ina zata da jaka yasa Farida da Nana dasukai tsuru tsuru adaki suka fito da gudu, ganin
Ammin su rike da Babban akwati kowa na gidan ya zagayeta banda Baba dake gefe tsaye yana kallonsu yasa sukai wajenta da gudu gain yanda Yasmeen ke kuka tarike jakan gam yasa yasa suma duk sukasa hannu suma suka rike suka fashe da kuka duk sukace "Ammi ina zaki"?
Anatse Baffa dake kallon yaran yace
"please Maman Nana calm down kodan sabida yara matan nan uku dake kuka agabanki dan Allah kinji" dago kanta ahankali Ammi tayi duk yanda taso hawayen datakeji takasa fashewa tayi da kuka tace "Baffa nagaji, for 20yrs yanzu kullum cikin jure cin mutuncin Baban Nanah nake kala kala kan yaran nan amman yau for the first time yazagi character na, yazagi tarbiyana ace ina lalata mai vara zan bata mishi Yasmeen tafara Iskanci abinda yake nufi kenan, i will not take that, nahakura da aurenshi, yaran ma na barmai tunda shine the perfect father and mother ma duka yaran nan wh wIh na barmai karyaji komi"tai maganan tareda kallon su Yasmeen da Nana da suka rirrike akwatin ta suna kuka tace "ku saki akwatin nan"
cikin kuka Yasmeen tace "Ammi dan
Allah kiyakuri" Farida tace "Ammi dan
Allah kada kitafi kibarmu" Nanah tace
"Ammi idan zaki tafi to saidai kitafi damu duka ko Anty Yasmeen baramu zauna da Baba mai mana fada ba harda ke ko Anty Yasmeen"
Gyadamata kai Yasmeen tayi tana kuka, sakin musu akwatin Ammi tayi tabi ta gefensu tawuce dasauri suka bita suna kuka zasu riketa ta daka musu tsawan da saida kowa ya firgita agidan tanuna Baba da hannunta dake tsaye kallonta kawai yake tace
"kuwuce kutafi waien Baban ku wlh duk wacce ta tabini saina gaura mata mari harke Nana" duk wanda yaga
Ammi yasan tai fushi yau bana wasaba, tsayawa yaran sukayi juyawa tayi tawuce Farida da Nanah suka rungume Yasmeen suna kuka sosai ganin da gaske Ammi take tafiya zatayi tabarsu,
daidai Ammi tasa hannu zata bude gate duka yan gidan babu wanda yasan lokacin da Baba yamaje wajen hannunshi yasa yarike hannunta yacire daga gate din yajuya yasa all d sakata na gate din sannan ya tsaya jikin gate din yakalleta cikin fushi soyayya yace
"tunda fushi kike aani ai nina bata miki rai ko vent it out on me amman bazaki tafi kibar yarana suna kuka ba wh, kome zakimini kimin" sosai Ammi takalli Baba kaman yanda yake kallonta shifa mai hali bazai taba chanzawa bane, yanzu bai tsayarda ita dan kanshi ba saidan yaranshi, idanunta sunyi jazur tana kallonshi da takaici tace "Ibrahim tashin mini daga jikin gate" "cikeda dakewa dakuma taurin kai Baba yace "bazan tashiba"
cikin fushi Ammi tace "nace katashi idan nai loosing temper na zan iya abinda zanyi nadama daga baya" anatse Baba yace "do your worst amman dai baraki tafi ki barmini yara in agony ba kin haifesu zaki zauna mucigaba da basu tarbiya tare har zuwa ranan da Allah zai karbi rayukan mu" fashewa da kuka kawai Ammi tayi tashiga kaima Baba duka akirji tace
"nace ka matsamin nafita nabar gidanka ka matsa katashi nace, nagaji nagaji nagaji nagaji dakai Ibrahim" batare da Baba yahanata ba yace
"nikuma nan gaji dakeba zama dake yanzu nafara" gain haka yasa Baffa yakalli kowa yace "ku wuce dakin Yaya ku harsu zasu daidaita" dukansu dakin
Yaya suka shiga harda su Yasmeen
Baffa yamaida kofan yarufe yasa sakata.
Duk ta inda Ammi tasamu kaimai duka take tana kuka rungumeta Baba yayi tsamtsam ajikinshi gain babu kowa ahankali yace "dan Allah kiyakuri kiyafemini I am sorry please, haba wife ni zaki toxarta kice zaki tafi ki barni tayaya zanyi rayuwa babu ke Dan Allah ki yakuri" ina Ammi bata jinshi dan ranta yabaci, daukanta yay da karfi da yaji yatafi da ita dakinsu ya maida kofan yarufe yasa sakata yajuyo zatai magana yakama bakinta yawuce da ita uwardaka duk gardaman Ammi saida Baba ya wanke laifinshi tass azuciyanta sukai wanka yafito da jallabiya dan zuwa masallaci, dakinsu Yasmeen yabude yagansu zugum suna zaune idanunsu jazur gwanin ban tausayi kaman was marayu, ahankali yace "kutashi kuje kuyi salla" dasauri Yasmeen tace "Baba Ammi ta tafi" kafin Baba yabada amsa Farida tace
"Baba kayakuri" dasauri Nanah cikin tsiwan yarinta tace "Baba kadainama
Ammin mu fada, munason Ammin mu sosai ko Anty Yasmeen" kasa amsawa Yasmeen tayi Baba yadade yana kallonsu kafin anatse yace "Ammi bazata ko'ina ba, nabata hakuri and I promise bazan karama Ammin ku fada ba dagayau Baba yay kuskure Ammi tayafemai, kuje kuga Ammin ku" dasauri dukansu ukun suka tashi ta gefenshi suka fita suka wuce dakinta daidai Baffa vafito wani kalan mugun kallo yama Baba dasauri Baba yace "Baff..." Hannu Baffa yadagamai yace "I don't have anything to say to you duk wannan abubuwan dakake sabida bakason Yasmeen tayi aure ne ko, to bari kaji Ibrahim muna dawowa daga sallan nan zan kira Yasmeen inhar ta aminta tana sonshi zan aika amin binciken yaron inhar yasami shaidan kirki aura da
Yasmeen zany bana bukatan ko sisin ka mara mutunci kawai agabana kadaga hannu zaka kaiwa matarka mari kai son yara haukan ne metayi da bayida kyau?
Tsirara kazo kaga Yasmeen dazaka fara haukan nan" Baki Baba yabude zai bama
Baffa hakuri kawai yawuce abinshi. Ammi na zaune afalo duk su Yasmeen suka shigo duk suka tsaitsaya wajen kofa kallonsu tayi jitayi she's feeling guilty saisa bata taba biyema Baban su tayi fada dashi agabansu dan fada na affecting yara sosai, hannu tabude musu da sauri sukai jikinta, Yasmeen tace
"Ammi dan Allah kiyakuri kinji kidaina barin maganganun Baba na tabaki yana sonki sosai he didn't meant maganan dayayi wlh kinji Ammi"? Gyadama Yasmeen kai tayi sannan tai murmushi tace "yanzu enough of fadana da Baban mu mun shirya dan haka ya isa kuje kuyi salla" dukansu murmushi sukayi suka juva suka fice aga dakin tabisu da kallo.
Tana zaune awajen Baffa yayi sallama daga waje anatse tace "shigo Baffa" shigowa Baffa yayi shi kadaine yasami kujera yazauna yace "Maman Nanah babu wacce nake yabo agidan nan akan hakuri kaman ke nasan halin kanina sarai akanme zaki biyemishi kuyi fada gaban yara da kowa" ahankali Ammi tace "Baffa kavakuri bazan karaba" murmushi yayi yace
"Allah yamiki albarka" anatse Ammi tace "Ameen" kafin ahankali tace
"Baffa dan Allah ka tsaya akan lamarin auren nan da kanka, soyayyan da
Baban Nanah kema yaran nan yana neman rufemai ido wlh aurar da
Yasmeen ne bavaso yayi kwata kwata
Baffa to idan bai aurar da ita ba mezaiyi Bokon bata ganewa gwarama Islamiya dasauki amman shima wajen rubutu duk abu daya, dazu bakaga kukan datayi da rana ba kan bata rubut komi a test din dasukayi ba, Baffa to tunda Allah yafito mata da miji yaro natsasse yanada aikin yi dazai rufamus asiri ya iya ciyar da ita to me wannan abubuwan dayakeyi eh Baffa" jinjina kai Baffa yayi yace "hakane, kada kidamu komi na hannuna anima zan kira Yasmeen wajena ni kadai tabani amsa zan aika shakikai na tareda Baba karami aje ayimin bincike idan komi lafiya lau zan kirasu ne Azo ada rana duk taurin kan Ibrahim bai isa yahanani abinda nasi yiba" gyadamai kai Ammi tayi tace Back
"nagode Baffa" tashi yayi jin ana kiran
Isha'i dan musamman sabida ita yau bai tsaya yaji karatun Umdatul Ahkam da akeyi a mosque dinba yabarki su Baba can yazo tabata hakuri yanata sallama yatafi.
Wuraren 10 Baffa ya aika Yaya data kiramai Yasmeen, Yasmeen dahar sun kwanta gyangyadi yasoma kwasanta dan tuni Baba yazo yamusu sallama
Yaya tabude kofansu dawuri dukkansu suka kalleta, Yasmeen takalla tace
"kizo Baffan ki na kiranki" ahankali ta sauka daga gado, hijabinta tadauka tasaka sannan tabi bayan Yaya suka I fito waje, anan waje Yaya takamo hannunta cikin whispering tace
"Yasmeen dan Allah Baffan ki ya tambayeki kice eh ki aure abinki kihuta. yaro kyakkyawa ga mota ga aikin yi me kikeso? Ba gwara aure ba da bakin masifan Baban ki da takuranshi, muje muje" binta abaya
Yasmeen tayi kirjinta na bugawa dim
dim dim da sallama tashiga dakin,
Baffa ne kadai zaune kan kujera yana kallonta Yaya tawuce ta zauna kusada shi, zama tayi ahankali akasa tace
"Baffa gani" murmushi Baffa yayi yana kallonta cikeda so yace "nakiraki ne namiki tambayoyi kan mutumin dayazo wajenki yau"
yadanyi shiru yace "ance malamin kune a FCE?" Ahankali ta gadama Baffa kai tace "eh Baffa" shiru Baffa yayi kafin chan yace "inaso ki natsu ki bani amsa mai kyau dan koba komi at least ke kin had da Maheer din countless time amakarantan ku koda bai taba miki magana a school ba,