Showing 63001 words to 66000 words out of 190707 words
yace “banson shirme school zata ba gasan kwalliya ba” hannunta Ammi taja zuwa uwardaka tace “kai dama kafison kaga yaranka fuskokinsu kaman na maza basasa komi, Bakasan Yasmeen budurwa bace tana jami’a bata gayu ba saurayi” akunyace Yasmeen tace “Ammi” dungure mata kai Ammi tayi tace “dalla barni nai magana kunyan Baban naki kike ai dashi nake, sa’o’inki na gidan miji, ni wlh addu’a na ba dare ba rana Allah yafito miki da miji Allah baki miji nagari mai hankali” tai maganan tana daukan janbaki pink ta shafa mata a lips sannan tadauki brush ta gyara mata gashin giranta ita kanta Ammi saida tasake kallon Yasmeen din tace “ke kinganki Alhamdulillah, Allah kabani diyar yar kyakkyawa, yar budurwan Ammin ta iyyee” lokewa Yasmeen tayi akunyace daga falo Baba yace “let’s go Yasmeen shirmen mamanki yayi yawa” karban hijabinta Ammi tayi ta warware tasamata “wlh kinyi kyau Yasmeen” Ammi tafadi ahankali juyawa Yasmeen tayi tace “bye Ammi” Baba harya fice sallama Yasmeen tama su Yaya da Hajjo sannan tafice motan Baba tashiga Baba yatada motan yafara tafiya sundanyi nisa sannan yace “I don’t want kiyi paying attention to maganganun Mamanki, banson shirmen samari, kada kiyi kuskuren tsayawa kula samari awaje, inhar yaro nagari ne dayasan darajan iyaye idan kuma yana sonki da gaske kafin ma yakulaki zaizo yafara sanarda mu iyayenki mubashi izinin magana dake, inhar Allah yabaki miji bazan hanaki aure ba, amma dai concentrate on school okay banda wasa, kallon maza kokuma magana da maza am I clear”? Ahankali tace “eh Baba, naji” “kina bukatan wani abu”? Girgixa kai tayi tace “a’a” school sukakai Maheer na zaune a motanshi kaman a mafarki yaga Yasmeen tabude gaban wata mota datai parking gaban classes na department nasu tafito hakama Baba, wani kalan sanyi Maheer yaji ajikinshi yakara zuba mata ido yana kallonta tundaga kan takalmin datasa akafa zuwa saman hijabinta, zagayowa Baba yayi yazo ta inda take yana kallon fuskanta hannunshi yakai aljihunshi yazaro handky baiji kunyan kowa da dalibai dake zuwa wajen ba yace “wannan abin da mamanki tasamiki yay yawa” share janbakin yayi yarageshi sosai yarage kadan sannan yakalleta yamaida hannunshi aljihu yazaro dubu biyu yaciro jakanta ya karba yasa 2k ciki yace “ga transport naki idan kun tashi 5 zaki gama lectures yau ko”? Gyadama Baba kai tayi tace “eh Baba” karban jakan Yasmeen tayi Baba yakama hannunta yawuce da ita har ajinsu, class nasu yashiga sai kallonsu ake Yasmeen tasauke kanta akasa Baba nabin kowa na ajin da kallo just to makesure yarshi is safe wani kujera yakaita yace “take care kiyi karatu da kyau ki” gyadamai kai tayi duk kunya yacikata, kanta ya shafa kaman yar yarinya yajuya yafita daga ajin dalibai kowa na dariya kasa kasa wasu na cewa Daddy’s gurl, fitowa Baba yayi daga ajin duk Maheer na kallonshi jujjuyawa yayi yakalli ko’ina kaman mai duba wani abu sai chan Maheer yaga ya maida idanunshi wani bangare daban hakan yasa yakalli wajen dasauri Aliyu yagani Baba nama magana da ido, wani kalan murmushi yayi yace “CP if I want ur daughter ko security dubu kasa I will get her” dan dariya yayi yana kallon Baba daya wuce yatada motanshi yatafi, hakan yasa Maheer yace “let’s leave daganan kaini office dina”.
11 suka fito daga lectures din, jakanta tadauka dan wucewa auditorium yin English, ahankali take tafiya ita kadai dan batada kawa bata iyama yan ajinsu magana kodan harda kowa jijji dakanshi yake as per new student oho, ita kunyan abinda Baba kemata ma yasa ko dagakai ta kalli wata ko wani a aljin bata iyayi, wucewa tayi tana tafiyan nan ahankali anatse zuwa auditorium ancika sosai abinka da yan different department anzo ayi english da kyar tasamu sit a tsakiya ta zauna tareda ciro handout nata na english tana dubawa sai hayaniya ake kaman gidan biki, all of a sudden taji ajin yay tsit kaman anyi ruwan sama an dauke hakanan taji feet nata sun mata wani irin sanyi saiga kamshin turaren da har yau gobe batajin zata manta da kalan kamshin nan ba dawani kalan sauri ta dago kanta ta jujjuya gefenta kaman wani abu take nema saikuma chan kaman ance ta kalli chan stage gaban aji ido da ido tayi da Maheer dake tsaye yasa wani dark blue suit idunshi sanye da glasses bakake amman tasan ita yake kallo, yayi mahaukacin kyau kaman ba dan Nigeria ba, gently yakai hannunshi yazare glasses na idanun nashi yana kallonta still faduwa gabanta ya mugunyi dasauri tadafa table, almost cikakkun 2mins yayi yana kallonta kafin yajaye idanunshi daga kanta yadan kalli student din tareda sakin little smile yace “good morning student I’m Maheer M Maheer your new English master” wani kalan tafi ajin yadauka dan he’s so charismatic kanajin yanda yake turenci kasan ba’a nigeria yay karatu ba ga kyau ga pink lips ga gayu ga tsayi, kowa kallonshi yake both maza da mata babu kyafta idanu.
Dan kallon Yasmeen yayi sannan yadauki marker yajuya to the board kawai yarubuta C.A dasauri ajin yadauki yan kananun magana kala kala.
“Write an Eassay about yourself” 15mins 20mark ya ijiye marker tareda juyowa yana kallon yan ajin da kowa yashiga yago paper banda Yasmeen dake kallonshi, yarinyar dake kusada ita ne ta taba Yasmeen firgigit Yasmeen ta kalleta yarinyar tace “ke bazakiyi test din bane 15min fa yabayar kin tsaya kina kallon sabon malamin kaman baki taba ganin namiji mai kyau irinshi ba” Gyadamata kai Yasmeen tayi tama rude tabude jakanta tadauko long note ta fallo ta ijiye tadauki pen sannan takalli allo tahada essay tafadi tasan me Essay zata iya amman spellings dinne, ahankali tafara rubutun tana tunani dan dago kanta tayi suka hada idanu yana kallonta sauke kanta tayi kasa dasauri tacigaba. 15mins daidai suka dauka yace “time up” hakan yasa kowa yadago ya kalleshi, anatse yace “at the end of the class zakuzo individually to my office kuyi submitting, now let’s talk about Essay” yashiga lecturing nasu kan Essay duk Yasmeen na kallonshi takasa yarda shine a school nasu tunda take tafara school din nan bata taba gane karatu kaman na yau ba, is as if yana bayanin yana bude kanta ne yana juyema ta yana shiga, 12:30 yagama dasu yawuce yafita, class rep yatashi yace “by 1 za’aje ayi submitting” kowa fito da nashi yayi yacigaba da yi wasu na gyare gyare 1 nayi aka fita kusan su 200 aka tafi office nashi classrep namusu jagora, Dan ke tsaye agaban office din dayake kulle yay dressing kaman wani dalibi, one by one ake submitting to Dan saiya kalla yace you can go, Yasmeen sai kallon Dan take saida yakarbi nata sannan yakalleta yace “what is this kika rubuta haka? Take jeki bama Sir da kanki” yay maganan yana bude office, kallon Dan tayi some mutanen yan department nasu dasuka santa sukahau dariya kasa kasa sabida sunsan yanda batada kokari, miyau tahadiye tareda sauke ijiyan zuciya gabanta na mugun faduwa ahankali tawuce tashiga office din Dan yamaida kofan yarufe office ne mai shegen kyau, akan table taga Maheer zaune yazuba mata idanu kaman he’s seeing her for the first time in life, daganan ta tsaya tareda mikamai paper kirjinta na bugawa, binta da kallo yayi zuwa paper datake bashi sannan ya sauko daga kan table din yafara takowa zuwa wajenta yana tafiya one one, kasa jure yanda takeji tayi dawani kalan sauri tajuya zatai kofa dagudu wani kalan fizgota yayi da bala’in karfi tajuyo tafado jikinshi adan zuciye ya mannata abango yana gabanta.
✨KK✨
EPISODE 4️⃣3️⃣
43
https://www.instagram.com/p/CtvvsTiI0Px/?igshid=YjgzMjc4YjcwZQ==
Yamata rumfa wani kalan kankame idanunta tayi tana numfashi da sauri da sauri gabanta na faduwa dum dum dum kaman zai fashe ganin Pablo gabanta, ahankali ya lumshe idanunshi yanajin yanda numfashinta ke sauka akan kirjinshi yana karajin mugun shaukin dayakeji aranshi gently yabude idanunshi yadaurasu akan fuskanta yanabin dogayen eye lash nata da kallo, zuwa kan pink lips dinta da har yanzu janbaki kadan ke kansu dayasa takara wani kyau kaman ba itaba lokacin nan da akai kidnapping nata, murya chan kasa dakeda dan kauri yace “open your eyes and look up” dudda yanda kirjinta ke bugawa kasa musu tayi kaman yamata magani tabude idanun ahankali tareda dago su tazubamai su sai kyalli suke sunyi tartar kaman an wankesu da ruwan alam. Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin daya hallici yarinyar nan sannan ya hallici wayan nan idanuwan nata saura kadan Maheer ya shide yadai daure ya tsaya yana kallonta kaman yanda take kallonshi gabanta na faduwa sosai batare daya nuna mata yanda yakeji ba, da hannunshi yadaki gefen bangon datake jingine saida ta firgita cikin tsananin fushi danshi kanshi he’s angry with yanda yakeji akanta azafaffe yace “what have you done to me”? Kaman ta kurma ihu takeji but sabida tasan akwai dalibai awaje yasa ta rike bakinta tareda lumshe idanu da sauri, adan zafafe Maheer yace “nace ki kalleni” bude idanuwan tayi dasauri ta maidasu kanshi sun cika da kwalla sosai dake gab da zubowa, babu wasa akan fuskanshi yace “wani spell kikai casting akaina? Tell me!” Yadanyi ihu kadan still ba irin wanda za’ajisu a school ba, rawa bakinta yafara tama kasa magana kawai gabanta is hopelessly beating, fizge hannunta Maheer yayi yarike gam yakai kan kirjinshi dashima ke bugawa binbimbin yace “listen to my heart beat from the day dana fara ganinki beating dinshi ya chanza to this, koda yaushe tunanin ki nake, when am awake, when am asleep, nabude ido na ganki, na rufe ido na ganki, you are in my head, my body, my eyes, my thoughts, my eyes, my everything, look at me, look at what I’ve subjected myself into ni koyarwa in this I donno cottage school din naku all because of you tell me wani black magic kikamin hooon!” yasake dukan bango dayasa tafashe da kuka tana girgizamai kai tama rasa mezatayi tadaura hannunta akan baki sabida kar karan kukanta yafito tsayawa she’s just so scared, wannan mutumin yabiyota school yana cewa metamai, to metamai? Kuri Maheer yayi yana kallonta da tsoronta da kukanta da yanda yake goge hawayen da bayan hannu everything about her na burgeshi ji yake kaman he should hug her and tell her sorry, ahankali yasauke ijiyan zuciya yana kallonta still batare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace “i want you to become my wife!!!” Dum dum dum haka gaban Yasmeen yafadi shi karan kanshi Maheer din mamakin abinda yafito daga bakinshi yayi dan wlh wlh baisan ya akayi abin yafito ba, sakin hannunta yayi da sauri yawuce yazauna kan table yay crossing kafanshi daya kan daya yana kallonta yanda take kallonshi tana kuka tana goge hawayen da bayan hannu kaman tana kokarin kara gasgasata abinda yafadi, yakai kusan 5min yana kallonta yana tunanin abinda yace sannan ahankali yace “remember you are indebted to me dan haka…” yamike tsaye yawuce chan gaban tv office din ya tsaya tareda kulle hannunshi tabayanshi yana kallon tv yajuya mata baya awani irin hankali yace “Fateema Ibrahim Ibrahim!” Faduwan da gaban Yasmeen yayi this time around saida ta daura duka hannayenta kan kirjinta tana kallon bayanshi dan yabata baya, anatse Maheer yace “i hate marriages but for the first time I think shine solution dina and how to end all this problems” yasake shiru kafin chan yace “listen and listen very well, there’s an envelope akan table dina jeki dauka ki bude” share fuskanta Yasmeen tayi ahankali kaman bazataba tawuce table nashi tadauko wani envelope data gani takoma inda take tsaye da, budewa tayi yawanci hotunan Baba ne dashi da wani dan saurayi daya kamo yana kalle kalle yasa a mota, sai wani gida, sai Baba da kayan yan sanda, Baba yafito daga masallaci, Baba dasu Baffan ta suna magana gaban mosque” juyowa Maheer yayi yakalleta yace “I know kinsan waye a hotunan nan dan mahaifinki ne d other mutumin dakika gani is one of my drivers” dan murmushi kadan Maheer yayi yace “Baban ki is secretly trying yakamani at all cost, all the four drivers ranan da aka sakesu suka bar garin wannan ma mamanshi ke rashin lafiya abinda yahanashi tafiya kenan but Babanki yakamoshi secretly yakaishi wanchan secret gidan yana ganamai azaba just sabida yasami information akaina wanda trust me driver chan gwara yamutu daya fadi anything” yadanyi shiru yace “what he don’t know is babu abin Babanki da bansani ba I have men dake binshi 2,4,7 sabida I know mutum kaman mahaifinki bazai taba barina mutumin dayakama yaranshi ba that easily he will do duk abinda zai iya dan kamani, yanzu haka naso sniper na ya harbe mahaifinki 1mins is too much” sosai Yasmeen ke kallonshi dan bata taba ganin cruel, ruthless dan ta’adda irin mutumin nan ba, dan murmushi kadan Maheer yasakin mata yakarasa zuwa gaban table dinshi yadauki kwalin taba yazaro daya yakai bakinshi yadau lighter zai kunna yaga tadan yatsine fuska hakan yasa gently yacire daga bakinshi ya ijiye danji yayi bazai iya sha agabanta ba, yakalleta yace “akwai wani al’ada damu yan mafia kedashi” yadanyi murmushi kadan yace “idan kanada enemy daya addabeka the best way kuyi ending na kiyayyan shine ta hanyar kulla auratayya, idan akai aure kasan bazaka taba iya taba gidan wane ba dan diyarka na ciki, haka kaima baraka taba gidan wane ba dan yarsu kake aure, zan aureki for only 2 reasons Fateema!” Yanuna mata yatsunshi guda biyu yace “one sabida yanda nakasa cireki daga zuciyana kinyi bewitching Pablo Escobar and secondly sabida mahaifinki daya addabeni” sosai take kallonshi kirjinta na faduwa, maida hannunshi kasa yayi yace “idan ban aureki na tabbata zanma mahaifinki abinda bazanso namai ba” tasowa yayi yazo gabanta dab da ita yana kallonta kasa jurewa tayi tasauke idanunta kasa awani kalan hankali yace “I will be sending my father his friends and my brother to gidanku azo atambayi aurenki” dan dukawa yayi yakai bakinshi saitin kunnenta ta saman hijab kaman mai whispering yace “if you dare koda wasa kika fadi cewa nine nake neman aurenki I will first kill that little girl ta gidanku mai shegen kukan nan like you” dasauri Yasmeen tajuyo da fuskanta takalleshi numfashinta dake fita fast fast na sauka kan fuskanshi hakan yasa shima yakalleta in the eyes irin tantirin nan yace “followed by yayarta, then your Mom…” yay dan murmushi irin na mugunta dinnan yace “then ur sweet caring father sannan kuma I will still marry you duk inda kika shiga kuma saikin zauna dani” hawaye ne masu zafi suka zubo mata daga idanu dasauri yadauke kai yace “you can go zamuzo” ya nuna mata kofa da hannu.
44
https://www.instagram.com/p/CtwFCtXITwD/?igshid=YjgzMjc4YjcwZQ==
EPISODE 4️⃣4️⃣
Juyawa Yasmeen tayi ahankali zata tafi saikuma ta tsaya chak kafin dasauri tajuyo takalleshi kaman yanda yake kallonta bai motsa daga inda yakeba, dakewa tayi takai bayan hannunta ta share fuskanta tace “ko kaine the only namijin daya rage aduniya bazan taba aurenka ba, kuma kuma baka isa ka kashe su Baba ba sai lokacin su yay…..” wani kalan kallo yamata dayasa maganan ya makale awuyanta ahankali yace “are you underestimating me? Ni?” Faduwa gabanta yayi tana kallonshi tana kara kallonshi mutumin daya sa akayi kidnapping ita da Nana da Farida babu abinda bazai iyaba, baki tabude zatai magana saikawai kuka yacita takasa magana irin kukan rasa mezakayi dinnan kariga kasan anfi karfinka, kukan tsaka mai wuya, tasowa yayi ahankali ya tsaya agabanta he feels kaman yay hugging nata, handky yaciro yamika mata makemai kafada tayi taki karba hakan yasa yakai hannunshi yakama hannunta yasa mata kafin yay folding hannunshi a kirji yace “destiny family ki lies on your hand, bazaki iya sadaukar da rayuwanki ma iyayenki ba, inhar kin aureni har abada babu abinda zai sami yan uwanki da iyayenki idan bakiyi ba I will take revenge dan ayanzu Babanki ya nemi tsokanata an kashe case yakama direbana again and you know I don’t forgive! Stop crying” yafadi ahankali hakan yasa ta tsayar da kukan, ahankali kaman mai lallashi yace “will you marry me”? Hararanshi tayi tareda turomai baki tace “babu abinda zanyi da criminal irinka dan Mafia” dan murmushi yayi ganin tanamai tsiwa kafin murya chan kasa kaman dan baby yana kallon fuskanta yace “I’m hungry” har cikin jikinta taji kalman saikuma tajuya tawuce tafita daga office din yabita da kallo ko kallon Dan batayi ba tawuce masallacin school nasu, zama tayi wajen alwalan mata takifa kanta a guiwa what kind of life is this? Wannan wani kalan tsaka kai wuya tashiga, wazata gayamawa, mutumin nan babu abinda bai saniba game da Baba dasu yaranshi harda su Baffa, idan yakashe Baba fa da Ammi da Nana da Farida fa dasu Baffa wazai rage mata aduniya? Amman idan ta yarda ta aureshi bazai musu komi ba kuma ta yarda bazai musu ba dan kaman yana sticking to alkawari, ijiyan zuciya tasauke ta dago tai tagumi tai shiru tana kallon waje daya all this while tanaji azuciyanta tanaso ta ganshi deep down she misses him har kuka take idan ta tunashi amman yau daga ganinishi saitaji inama bata ganshi ba, lectures din dabata koma kenan ba sai wajajen 3 ta nufi gate hakan yasa Aliyu shima yatafi ganin ta tafi dan Baba yace karyabari tasan yana binta, Keke ta tare ta shiga shagon Maman Intee tasa akaita dudda bama tasan dalilin dayasa tace chan ba.
Clinic da Hamad ke aiki yasa Dan yakaishi, suna shiga parking Dan yayi saukowa yayi glasses nashi akan idanunshi babban hospital ne ahankali yake tafiya harya shiga ciki, direct wani office yawuce budewa yayi yashiga kai tsaye daidai Hamad na duba BP wani tsoho dake zaune kan kujera yana sanye da lab coat hakan yasa ya tsaya jikin kofa shiba karaso ciki ba yana kallon Hamad, dasauri Hamad yay murmushi yace “Baba kaje pharmacy zan aika musu da magungunan da za’a baka” godiya tsohon yayi yatashi yazo yafice hakan yasa Hamad yace “kaikuma meya kawoka wajen aiki na”? Maida kofan Maheer yayi yarufe bayan tsohon yafita sannan yakaraso ciki yana kallon Hamad dake kallonshi, instead of yazauna kan chair wajen observation bed na office din yayi yahau yazauna wayanshi yaciro yana dubawa Hamad duk yana kallonshi yadade baiga miskili kaman Maheer ba ganin baida niyyan magana yasa yazauna yashiga tura magungunan da za’a bama tsohon daya fita