Showing 72001 words to 75000 words out of 190707 words

Chapter 25 - KYALKYALIN KAUNA HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

11 Oct 2024

9323

ya damo fura dayawa for kowa na gidan Nana kadai yasayama zallan yoghurt dan ita bata iyashan yoghurt mai hade da furaba har yanzu sannan yadauko ledan yazo yabude motan yabama Yasmeen karba tayi yamaida kofan yarufe yazagayo yashiga yatada motan suka wuce gida suna kaiwa bai shiga gida ba yawuce mosque dan anfara salla a masallaci itakuma Yasmeen tawuce cikin gida, babu kowa a tsakar compound dan kowa na daki yana salla sallama tayi ta shiga dakin Ammi daidai Ammi na sallame Salla Nana agefenta jiye ledan yoghurt din tayi gaban Ammi tareda zare hijabin ta yar akasa ta kwanta tadaura kanta kan kafan Ammi dakekan dadduma tace "wasshhh Ammi nagaji wh, Nana kawomini abinci na naci" tashi Nana tai dasauri ta wuce tafita dan zuwa dakinsu tadauko kulan abincin Yasmeen fuskan Yasmeen Ammi tashafa tace "yau wasu mutane sunzo neman aurenki" wani kalan faduwa gaban Yasmeen yayi dasauri takalli fuskan Ammi tareda tashi zaune kirjinta nawani kalan rawa, dan dariya kadan Ammi tayi tace "to matsoraciya relax Babanki yagansu yace yaron yazo yaganki jibi lahadi, saikin ganshi kafin ayanke decision kinji" gyadama Ammi kai tayi ahankali daidai
Nana tashigo da kulan tace "Anty
Yasmeen gashi" karba tayi ahankali itama tajawo ledan yoghurt din tace "Baba yasayo mana fura" karba Ammi tayi ta shiga rarrabawa adaddafe Yasmeen taci abincinta duk yunwan datakeji kasaci tayi sosai takarbi fitan ta tafita daga dakin zuwa dakinsu ijiye komi tayi tafita tayi alwala tadawo salla tayi sanan tajuyo takalli su Sa'a da tunda tashigo suke kuskus ganin taki tajuyo yasa suka kwashe da dariya Sa'a tace "wayaga Yasmeen amarya, ni wl naji dadi sosai Allah sa ahada bikinmu tare" wani mugun harara Yasmeen tamata baki tabude zatai magana sai kuka baki daga Farida har Sa'a suka saki baki suna kallonta yanda hawaye ke sauko mata tana kai bayan hannu tana gogewa da sauri sunki tsayawa dudda ba kuka take da karfi ba, Farida dasauri ta rarrafo zuwa wajenta kaman itane babba ahankali cikeda so tace "Anty Yasmeen bakiso kiyi aure kibar gidan nan saisa kike kuka"?
Gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali dan bazata taba iya fadin abinda ke damunta ba dasauri Farida ta rungumeta tace "kidena kuka please kinji Anty
Yasmeen babu inda zaki nima banso kibarni wazai dinga dafa mana indomie da abinci mai dadi, wazai dinga kawomana su cake da zobo daga shago eh" itama Farida tahau kuka, tsaki Sa'a tasaki tace "wIh kunci kun koshi ne van iska to dan kuji dukanku har Nana saitayi aure wata rana tabar gidan nan" sake rushewa da kuka sukayi daga Yasmeen har Farida babu mai lallashin wani hakan yasa Sa'a tamike tace "wlh bani zakusa a trouble ba dan Baba yashigo yaganku kuna kuka kunga tafiyata wajen baabata' ficewa tayi daga dakin abinta, da kyar Farida tai shiru sannan tadago kanta fuskanta ta share tass sannan takalli
Yasmeen dake kuka, hannunta takai kan fuskanta ta sharemata hawayen tass tace"kidaina kuka, ba ance ran Sunday zaizo ba tunda bakison Auren saiki fadama Baba kinji" Gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali, Farida tace "tashi to muyi salla idan mun idar saikiyi raka'a biyu ta istikhara ki nemi zabin Allah" batai musu ba tashi tayi suka fice sukayi alwala sukai isha'i sannan tayi istikhara abinta tagama takwanta kan dadduma tai shiru tunani yamata yawa, she's thinking of Maheer kaman ba gobe, koyaya tai numfashi shine kawai takeji azuciyanta, she's afraid of him, tana tunanin yanda zata aureshi bayan tasan criminal ne, tana tunanin abinda Zaima su Baba da duka yan gidansu idan tafadi dan tasan zai iya tunda har ya iya kidnapping dinsu duka, yasan makarantan su yasan ajinta yasan wajen aikinta yasan number a number ta daga yan gidansu sai Maman Intee kedashi ya
akayi yasamu oho yasan gidansu ta
tsinke da lamarin shi yanda yace zai
kashe su baba zai iva data zama sanadin
da iyayenta zasu mutu gwara tazama
sanadin dazasu rayu all abinda tasani
shine idan har akeai next life bazata taba
bari Baba yazama police ba infact she
hates the job sabida kana haduwa da
criminals daban daban dazasu addabeka
da family ka gashi yanzu she's the only one day can save Baba da duka yan
gidansu, all this aside shi Maheer din ko
Pablo nema oho akwai wani iri datakeji
azuciyanta gane dashi first of all tanason
yanda yake kamshi bata tabajin kamshin
turare aduniya kai dadin nashi ba,
saikuma yanada bala'in kyau saisa
bataso tana kallonshi bata taba ganin
namiji Mai kalan kyanshi ba, manyan
idanunshi, digon hancinshi, bakinshi da
pink lips nashi, bakin cikakken giranshi
da gashin kanshi dana saje bala'in mata
kyau suke, tsayinshi na burgeta sosai,
saikuma everything about yanda yake magana da yanda yake share mutum da
yanda yake daukan lokaci kafin yabada
amsa da kuma muryanshi ita bama zata
iva lissafawa ba komi nashi na mutuwan
burgeta kara wayanta yayi dasauri
tabude idanubta lallabawa tayi ta mike
dagakan dadduma tawuce wajen jakanta
data rataye tabude taciro wayanta
message taga tanada shi dasauri tashiga bude messege din gain daga bakuwar number ne, wani kalan ijiyan zuciya ta sauke takara natsuwa kafin ta kalli sakon tana kara bude manvan idanunta danta karanta da kyau.
"Sw..." tadanyi shiru Farida dake rubutu akasa tana kwafe note tace "me kike kokarin karantawa nazo na karanta miki"?
For the first time in her entire life tai rejecting akaranta mata abu dasauri tace
"'a" kwanciya tayi da gudu kan gado taja bargo tarufe har kanta Farida takalleta saikuma tai murmushi tacigaba da rubutunta.
E3
Daga wayan Yasmeen tayi cikin bargo tana kallon sakon ahankali sabida kar muryanta yafito ma sosai tace "Swe.. saikuma dasauri tace "sweet! Eh sweet ne" kafin ta kalli next kalman tace
"d…..
....dr..." dasauri tace "dreams" ahankali tace "sweet dreams. MM" wani sweet smile tasaki ta manna hancinta kan wayan akunyace mistakenly tai dialing number kawai duu duuu taji alamun ringing, dawani irin sauri tazare wayan dagakan fuskanta ahaukace ta yaye bargon tafito tace "Wayyoo Allah" tashiga daddanna call din tana katse kiran Farida tasaki baki tana kallonta, wurgar wayan tayi chan gefe bayan takatse kaman ta fashe da kuka, daidai kira na shigowa wayan zaro idanu tayi kaman zasu fado kasa. Maheer dake kan couch adakin Hamad ne yadan lumshe idanu kafin yasaci kallon Hamad dake gefenshi yana aiki a system, tashi yayi ahankali yazura slippers yawuce yafita daga dakin Hamad yabishi da kallo kafin ahankali yace "munafikin miskili kawai your MM doesn't just stand for Maheer Maheer, harda Munafikin Miskili" last room din dake corridor Maheer yawuce yashiga, dakin a gyare tsaf kashe wutan akin yayi ya kunna AC dakin yawuce yahau kan gadon ya kwanta daidai Yasmeen nacewa "Hello, waye"? Ita adole so take ta nunamai bata gane waye ba, dan murmushi yasaki kadan kafin cikin wani soft calm voice yace "idanunki ne" dudda yadan gaban Yasmeen ke dari dari amman saida maganan yasa tasaki dan murmushi tana kara satan kallon Farida dake rubutun ta abinta taga ko tana kallonta, murguda baki tayi cikin murya yar karama chan kasa ta yanda ko Farida dake dakin barataji metake cewa ba tace
"me kake kirana ni"? Dan murmushi kadan Maheer yayi jin vanda takemai tsiwa cikeda son shima yakara tunzurata yace "ai ke kika kirani" jitayi kaman zata nitse akasa takasa magana, murya chan kasa yace "why are you feeling bad?" Dan shiru yayi kafin cikin murya mai bala'in dadi yace "zaki iya kirana anytime afterall very soon zan zama mitinki" hararanshi tayi kaman yana gabanta cikeda kulewa tace "ni bazan aureka ba"
"nikuma zan aureki Fateema!" Faduwa
gabanta yayi sosai tarasa mesa duk idan
yakirata sai gabanta yafadi hakan yasa
takasa magana hawaye ya fito daga
idanunta dasauri tasharesu da bayan
hannu. "Mesaki kuka yanzu"? Yay
tambayan ahankali bin dakin tayi da kallo ko yasa camera ne yake ganinta dasauri
tace "kasa camera ne adakin muma
yanzu?" Dan murmushi kadan yayi yace
"idan naso zan iva sawa but no bansa
ba" adan hankali tace "to ya kayi kasan
ina kuka"? Shiru yayi baice komiba
harsaida tacire wayan daga kunnenta
takalli screen di ganin yanakai still yasa
ta maida wayan kunnnenta tace "hello"
cikin tattausiyan mura batare daya amsa
hellon taba yace "my soul is connected
to yours saisa nasan u were crying" shiru
tayi batasake cewa komiba, murya chan
kasa yace "ina mai kukan nan kaman ke
Nana Aisha?" At this point tafara tunani
mavbe aliani ne mutumin nan vasan duka
sunansu na gaskiya, shiru tayi saikuma
tace "meruwanka da ita" murya chan kasa yace "she's now my sister in law,
itada Farida da Sa'adatu, Fateema kuma
itace matata" shiru kawai tayi tana
saurarinshi tana lumshe idanu wh kaman
karya daina magana muryanshi dadi
sosai, turo baki tayi tace "nidai saida
safe" cikin dan kakkausan murya babu
alamun wasa yace "nasallameki ne"? ahankali tace "a'a" dan shiru yayi kusan
1min baice komiba ahankali vace "have u had ur dinner?" Ahankali tace "eh"
"mekikaci"?Kwanciya tayi ahankali daidai zata bada amsan taji muryan Baba yana magana da
Baffa zai shigo dakin atsorace tace
"Baba yazo bye" tura wayan karkashin pillow tayi ta runtse idanunta tai lamo daidai Baba yay sallama yashigo Farida tace "Baba sannu da zuwa" karasawa gaban Farida yayi yace "yauwa Farida ya akayi bakiyi note a school ba" adan tsorace gain yanda ya kafeta da ido tace "Baba kaine na ciwo ne lokacin a class" dan sassauta mura yayi yace
"dakika dawo kin fadama Mamanki kanki na ciwo kinsha magani"? Gyadamai kai tayi ahankali tace "nasha" hannunshi yakai yataba goshinta kafin yakai wuyanta jin ba zafi yace "idan yasake damunki gobe lemme know zan kaiku hospital kiga Dr" anatse tace "to Baba" tashi yayi yakalli Yasmeen datai lamo itama Farida faduwa gabanta yake dan kada yakamata karasawa gaban gadon yayi yakalleta ganin kaman tai nisa abacci yasa yajuyo yakalli Farida yace "Ina Sa'adatu"? "Tana wajen Yaya" Gyadamata kai Baba yay cikeda gamsuwa Yasmeen yakara kallo yabi dakin da kallo kaman nai neman wani abu sannan yajuya yafita yace "saida safe kiyi addu'a kafin ki kwanta" "to Baba" Farida Farida tafadi ahankali tareda sauke jjiyan zuciya ganin yafita takalli Yasmeen tace "Allah yasoki bai kamaki kina waya ba hope dai kin katse wayan"? Dasauri Yasmeen tasa hannu taciro wayan daga kasan pillow ga mamakinta Maheer nakan layin dasauri takai wayan kan kunnenta tace "daman ban kasheba kai mesa baka kasheba" ahankali yace "ban sallameki ba" "to me kakeso?" Yasmeen tai maganan tana kallon kofan su jin antaba gain Sa'a ne tashigo yasa tasauke ijiyan zuciya, jin shiru baice komiba yasa ta turo baki cikin kunkunai tace "ni zanyi bacci" almost 10secs baice komiba kafin chan yace
"bakida kunya ko" dan dariya kadan tayi mara sauti tace "toka barni na kwanta baccin" yanda taja baccin saida yaji aranshi, anatse yasauke ijiyan zuciya cikin tattausan murya yace "good night Fateema" kasa magana tayi tai shiru tama rasa takamaimen metakeji danji tayi inama baice good night ba, anatse yace
"zanzo ranan Sunday by 3, 4 zan tafi" cikeda tsiwa tace "karka sake kazo gidan mu ni, kuma bara'a aureka ba din, bye"
dip ta katse wayan.

Ta tura wayan karkashin pillow dasauri tareda lumshe idanu wh batasan mesa ba bala'in dadin wayan dasukeyi takeji har aranta itadai tabani meke damunta ne haka, fuskanshi tafara gani ahaka daga baya bacci yay awon gaba da ita. Yau tunda ta tashi gabanta faduwa yake ita tunda take bata taba shiga irin wannan vanayin arayuwanta ba, wani bangare na zucianta na toron mutumin nan da shakkan shi sabida tasan criminal ne, koba komai ya gwada mata kadan daga halinshi, wani bangare na zucianta najin wani iri game dashi tun ranan Friday dasukai waya basu kara ba sotake yasake kiranta suyi magana taji muryanshi, tabude message nashi takaranta yafi sai dari na Sweet dreams din nan, tabude number shi takalla harta haddace akanta tsabagen yanda take tunaninshi she's just dying to hear from him, kewanashi infact babu abinda bamataji game dashi, wani bangaren na zucianta bayaso yazo gidansu yau amman har kasan ranta wh wl takosa taganshi, tarasa mezatai tunani to idan yazo su Farida suka ganeshi fa suka fadi koda yake Farida tace ita bata iya ta kalli fuskanshi ba Nana wannan daman
kuka take batasan shi ba
harsuka dawo daga hadda wuraren 1 tarasa meke mata dadi mix feeling takeji sosai daman gashi sunyi test
bata iya tayi komiba. Wuraren 1 aka bude labulen kofanta dasauri ta dago kanta Baba tagani yana sanye da manyan kaya dasauri ta tashi ta zauna tana jawo dankwalinta dan rufe kanta, Baba dake kallonta ganin tamai wani iri yace "kinyi salla"?
Gyadamai kai tayi ahankali, Baba dake kallonta ganin duktai wani iri yace
"baki da lafiva ne?" Baki tabude zatai magana saiga hawaye sharrr sun zubo dasauri Baba yasaki labulen yawuce yashiga dakin, abakin gadon su yazauna yana kallonta baice komiba itama kallonshi tayi kaman tafadamai abun da ya tsayamata awuya amman bazata ivaba batason tazama sanadin dazaisa akashe mata iyaye hannayenta kawai tadaura kan fuskanta tafashe da kuka sosai, Baba yakai cikakken 1min yana kallonta bai hanata kuka ba chan yace "Yasmeen" cikin kuka tace "naam Baba" hannunshi yakai saman fuskanta yazare hannayen taredakai bayan hannunshi yashare fuskanta tsaf yace "meke damunki"? Dan yasan kukan damuwa takeyi bana ciwo ba, vanda Baba ya tsareta da ido yasa ahankali cikin murya Mai balain rauni tace
"muni test a hadda ko daya ban iyaba
Baba, zasu karamin repeating ko halama nan gaba Nana tazo tafini aji, Baba maisa banda ilimi maisa har yanzu bana iya rubuta kowani kalan baki, nasan amsan tambayan but ban iya narubuta ba banda kokar...."
" kuka vakaracin kartinta dasauri
Baba yasata ajikinshi kankameshi tavi bayanta ya bubbuga yace "shiti kada ki kara cewa bakida kokari, kinada kokari kini bari akwai wata Malama da akamin maganan ta zan daukota tadinga zuwa gida tana miki all abubuwan kinji now stop crying" kara sosuwa zuciyanta yayi all Baba ever did was to support her daidai da sau daya Baba baitaba complaining cewa batada kokari ba dudda kowa na gidan nan yayi, baya gajiya da nema mata ilimi, baya gajiya da sata a makaranta daban daban, tayaya itama yanzu lokaci yayi bazatama mahaifinta hallaci ba, ta ceceshi koda mutuwa zatayi ta hanyar haka daya taba iyayenta gwara ta aureshin kome zaiyi yayi da ita idanma kasheni zaiyi yayi amman ya kale Baba yasa adaina binshi ya kyale yan uwanta. Sallama Ammi tayi tashigo ganin Baba dakin saida abin yabata mamaki baki tasaki tana kallon Yasmeen dataga idanunta sunyi ja dasauri itama tazo wajen tace "Yasmeen meya sameki"?
Takai hannunta tana cirota daga jikin
Baba, ahankali tace "muni test ban rubuta komi ba Ammi" Ammi jitayi zuciyanta ya sos dasauri ta rungumeta tana kallon fuskan Baba dake kallonta tace "stop crying a karatu the most important thing shine kanka yarike and Alhamdulillah kanki yarike was dan haka ki barma Allah komi watarana sai labari kinji saisa gara kiyi aurenki kihuta da wannan bakar wahalan dakike a makarantu" wani mugun harara Baba yama Ammi itama ta maida mishi hararan back, tashi yay yakalli Ammi yace "nafita idan yaron yazo kada yawuce awa daya agidana dan haka ku kiyaye" yay maganan da kakkausan murya yawuce yafice Ammi tabishi da kallo baki sake kafin tasauke jiyan zuciya tace "kaji dashi" tadago Yasmeen tace "ke dalla chan yau saurayinki zaizo duk kinbi kin kuka jibi idanunki, tashi kije kiyi wanka kizo dakina ina jiranki" makema Ammi wuya tayi cikin muryanta dakeda gobe na kuka tace "ni bazanyi wanka ba" haba Ammi takama tace "au yau shagwaban yatashi ne ahhh lallai Aiko mangareki zanyi anan niba Babanki bane dazai tsaya lallashinki ba, tashi muje ma abayin nawa zaki wanka" badan taso ba Ammi ta tasata agaba suka tafi dakinta wanka tasata tayi sannan tafito mata dawata sabuwar atampa superwax gal wanda na salla Baba ya dinka musu dan dazaran yasami kudi yake abubuwa da wuri duk a ijiye, kayan Ammi tanuna mata tace
"imaza saka kizo kigani" Ammi tasauke wani babban akwatinta tunna aure taciro wani gyale chantily milk sabo a leda tace
"kinga tsaraban gyalen da makociyar mu
Hajiya Mariya tabani yau ga amfaninshi"
Yasmeen dake jan zip na skirt din datasaka takalli Ammi cikeda rigima tace
"waye zai da gyale Ammi"? Hararanta Ammi tayi tace "wale tunda kaina nake cirowa gyalen" kaman Yasmeen zatai kuka tace "Ammi ni hiabi zan saka" akwatin Ammi tadauka tamaida sama tace "uku saura kwata fa kike shirmen nan wh Yasmeen nadade banga fitinanniyan yarinya irinki ba bari kiga naje nakira miki Sa'adatu da Farida" juyawa Ammi tayi tafita dakin Yaya tawuce Sa'adatu na zaune da Farida afalon da Yaya da Hajjo suna hira shigowa Ammi tayi ciki tace "Yaya yarinyar chan na sani ciwon kai wh, Sa'a keda Farida kuje ku mata kwalliya naciro mata gyale dan gidansu shi zata saka" tashi sukayi suka fita da sauri Yaya tace
"ai Yasmeen ni bantaba gani yarinya baiwar Allah irinta ba, Allah dai ya tabbatar da Alhairi" atare duk sukace Ameen. Yasmeen duk yanda take rigima bataso bataso saida Sa'a tamata kwalliya
53|
lafiyayye mai kyau tasamata jan baki tamata dauri daya fito da jelan gashinta ta daurin yay wani kyau Sa'a ta yafamata gyalen awuya daidai nan aka sallama cewa yazo Yayacw ta leko tace "ace yashigo" tunda Yasmeen taji haka gabanta ke faduwa sosai da Sa'a da
Farida suka kwashe da dariya Sa'a tace
"wlh yanda kikeyi kaman wata amarya
Yasmeen that means randa zaa kaiki gidan miji ba karamin kuka zakiyi ba" daidai nan Maheer yashigo cikin gidan, yana sanye dawata milk yadi anmai dinkin jumper dayamai kyau ga hula akanshi Ya Allah! Zaka dauka wani kalan angon e tundaga gate kamshin shi yacika ko'ina Farida ne tafito daga dakinsu takalleshi yana tsaye wajen gate aranta tace wow wanna kyakkyawan ne mutumin Innalillahi karasawa tayi har inda yake akunyace tace "ina yini Yayan mu"
Maheer yadade yana kallon Faridan, she's just like Yasmeen amman Yasmeen tafita kyau nesa ba kusa ba, murmushi yasakin mata mai sanyaya zuciya yace
"Anty Faridan mu" wani kalan kashe
Farida yayi da dadi tace "zo muje na
Kaika daki ance kashigo" anatse yace
"ok" tana tafiya yana biveda ita abayin gidan tsaf tsaf dudda ba gidan masu kudi ba amman ko datti daya bai gani ba, dakin Ammi tashiga tajuyo takalleshi tace
"bismillah" cikin dakin ya kalla kafin anatse yace "Assalamu Alaykum" yashiga ciki Farida ta amsa kuiera tanunamai tace
"kazauna wata one sitter yazauna akai sannan tashiga ciki cikin whispering tace
"Innalillahi Ya Sa'a kinga yanda saurayin
Anty Yasmeen keda kyau kuwa kuje ku gaishe shi bari naje dakin Yaya na kwasomai ruwa" fitowa falon tayi akunyace yawuce tafita Sa'a takalli
Yasmeen dava zauna tai kuri kaman jira take ace kule tafashe da kuka tace
"tashi muje" makemata kafada tayi hakan yasa Sa'a tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login