Showing 42001 words to 45000 words out of 190707 words
ita yazo gaban gadon wani kalan kwantar da ita yayi ahankali yana kallon fuskanta kaman yanzu yafara ganinta, ahankali yasa bargo yarufa mata yawuce yafita da sauri bai jimaba yadawo rikeda abun duba temperature ganin temperature nata is too high zata iya fara convulsing at any moment yasa yaciro wayanshi dasauri, wani number yashiga daddannawa awayanshi sannan yashiga wajen text message yayi jim kaman mai tunanin tura sakon kafin chan yayi typing “Sick” yayi sending sannan ya ijiye wayan agefenshi sannan yasake juyowa yana kallon fuskanta, ayanda yake kallon fuskanta ko zaka dauka idan aka bashi paper zai zanata ne dan kallon kaman yaga abinda baitaba gani aduniya ba.
Wuraren 6 Dan yayi knocking dakin hakan yasa yakalli kofan baki yabude zaice come in saikuma yakalleta, tashi yayi ahankali yawuce wajen kofa bude kofan yayi ahankali hada idanu yayi dawani kyakkyawan matashi wanda kana ganinshi kaga mate na Maheer shima black beauty yana sanye da jumper na milk yadi Riga da wando hannunshi rikeda wata jaka fuskanshi daure tamau yana kallon Maheer din dashima yahade rai yakalli Dan yace “leave us alone” dasauri daga Dan har sauran guards din sukabar wajen dukansu suka tafi chan palour, akufule dayan guy din dake kallon Maheer din yace “akan me zakamin text bakada lafiya bayan lafiyanka kalau” wani mugun kallo Maheer yamai baice komiba, tsaki guy din yayi cikeda fushi yajuya fuuu zai tafi anatse Maheer yace “Hamad!” Chak guy din da Maheer yakira da Hamad ya tsaya batare daya juyoba, shiru Maheer yayi yaki magana hakan yasa ahankali Hamad yajuyo yazubamai idanunshi cikeda fada yace “who is sick”? Dan shiru Maheer yayi yana kallonshi kafin yadauke kai kaman wanda ke kunyan yjn maganan ahankali yabude kofan dakin murya chan kasa yace “she” sosai Hamad ke kallonshi kafin cikin tsananin fushi yace “sabida ka rainamin hankali nizaka kira nazo naduba matan nan” ahankali Maheer yace “not she” fuskanshi Hamad yakalla na kusan 5secs sannan yataho ahankali zuwa kofan da Maheer yabude yabi ta gefenshi yashiga ciki hakan yasa shima Maheer yabiyo shi ciki ya tsaya jikin kofa, kallon Yasmeen da kana ganinta kasan mugun zazzabi take sannan yakalli Maheer cikin wata kalan murya yace “kafara trafficking yaran mutane ne kuma yanzu Maheer” wani kalan matsiyacin kallo Maheer yamai yace “idan bazaka dubata ba kafadamin bance ka gayamin maganan banza ba” shiru Hamad yayi kafin chan yace “saikai excusing dina I can’t check patient agabanka” tsaki Maheer yayi yawuce yafita tareda rufo musu kofa hakan yasa Hamad dasauri yayi wajen gadon yabude jakanshi yaciro stethoscope ya makala a kunne ahankali with care yasa hannunshi zai dagota yace “baiwar Allah” firgigit Yasmeen ta tashi fashewa da kuka tayi zata koma baya cikeda lallabawa yace “no no no, wait ni Dr ne Maheer yakirani na dubaki, my name is Dr Hamad I will not hurt you okay” yanuna kanshi hakanan taji ta yarda dashi ahankali ta dagamai kai, cikin tattausan murya yace “can I do my work now”? Gyadamai kai tayi hakan yasa yace “good bani hannunki, and tell me meke miki ciwo” hannunta tabashi cikin muryanta dabaya fita sosai tace “cikina, kaina, duk ciwo suke inata amai” ahankali Hamad dake kallonta yace “kuma akwai mura ba”? Gyadamai kai tayi ahankali, anatse yana haska kwayan idanunta yace “are you on period”? Gyadamai kai tayi ahankali tana sauke idanunta, paper yadauko yana rubuce rubuce batare daya kallo fuskanta ba yace “yaushe yazo”? Ahankali tace “dazu” Gyadamata kai yayi yace “yanzu abinda nakeso shine zansa akawo miki wani abu kici sannan zan baki magani kisha okay ko kinaso namiki allura”? Girgizamai kai tayi tana goge hawayen datake da bayan hannu, murya chan kasa tace “ni banason komi gidanmu nakeso nakoma” yana kallonta yace “meyakawo ki nan dama”? Kallonshi tayi tace “they kidnap me and my sisters amman yace su yakomar dasu gida, nima dazaran Babana yabasu kayansu zaisa amaidani” takara fashewa da kuka sosai tana gogewa da bayan hannu, dan ijiyan zuciya yayi yace “zaki koma gida kinji” gyadamai kai tayi yace “bari naje nasa akawo miki abu kici before kisha magani nasa miki drip” gyadamai kai tayi hakan yasa yawuce yafita anan bakin kofa yaga Maheer tsaye yayi folding hannu akirji ba karamin mamaki abin yabashi ba, bude kofan dasauri Maheer yayi yashiga dakin hakan yasa tadago kanta danta dauka Dr ne yadawo, hada idanu sukayi da Maheer daya tsaya nan wajen kofa, wani kalan ballamai harara tayi da kumburarrun idanunta da saida abin yasa yadan zaro idanu din nan, sake ballamai wani hararan tayi danji take kaman tazo ta kashe shi, wani kalan gajeren murmushi ne ya kufce mai daga baki faduwa gabanta kawai yayi ganin murmushin shi dan ba karamin kyau smile yamai ba dasauri ta dauke kanta, shima fita yayi tareda rufo kofan yajuyo yakalli Hamad dake binshi da idanu
.EPISODE 2️⃣7️⃣
Follow my TIKTOK PAGE YI CATCH UP ON EPISODES DIN💃
https://www.tiktok.com/@mshakurr?_t=8d9o7ToAvDC&_r=1
Wani mugun kallo Hamad yamai yace “she needs abinci kafin nasata akan medication kaje kahada mata tea” dan zaro idanu Maheer yana kallon Hamad din yakasa magana, saikuma chan kaman bashiba ahankali yace “ya akeyi”? Sakeyin shiru Hamad yayi yana kallonshi yanzu da gaske yimata zaiyi? Maheer daya sani direct zaice bazaiyi ba koya kira wani yayi is something going on tsakanin yarinyar nan da Maheer ne ya tambayi kanshi, kafin akufule yace “take me to the kitchen” dasauri Maheer yayi gaba Hamad biyedashi abaya har zuwa kitchen suka shiga Maheer ya tsaya agefen kofa Hamad yawuce ciki yadauki kettle yana tara ruwa yazo yajona sannan yawuce yadauki mug da gwangwanin madara da milo yana kokarin deba yazuba a cup batare daya kalli Maheer ba yace “she’s on her period, kabata pad cus I don’t think she has any” dan zaro idanu Maheer yayi yana kallon Hamad din dake kiciniyan hada tea kaman bashi yayi magana ba, kaman dan yaro Maheer yace “a ina zanga pad”? Shiru Hamad yayi yadauki kettle na ruwan daya tafasa yana tsayaya ruwan zafin a mug na tea kafin yajuyo yakalleshi yace “you should’ve thought about that kafin kayi kidnapping yarinyar mutane” shiru Maheer yayi yana kallonshi baice komiba, juyawa Hamad yayi yadauki tea daya gama hadawa yadaura kan tray yadauka yataho yakalli Maheer dake tsaye kusada kofa still yace “kaje wajen Matar gidan ka nema idan kaga dama” yana maganan yawuce yafita daga kitchen din yayi hanyar corridor abinshi.
Shiru Maheer yayi yakasa koda motsi kafin chan yajuya yafita stairs yayi yawuce sama direct dakin Hajiya yawuce, ahankali yabude kofan dakin tana kwance tana bacci ta lullube da bargo, wucewa yayi direct yabude kofa yashiga closet dinta, neme neme yafara yana zubar da komi yana dube dube inda zaiga pad, karan bude nan rufe chan zubar da chan yasa Hajiya ta farka daga bacci, bude idanuwanta tayi da kyau tana kallon kofar closet dinta dayake abude wanda daga cikinshi takejin kararraki dasauri ta mike zaune tana yaye bargo ta sauko daga gado tana tafiya ahankali tayi hanyar closet din ta tsaya agaban dakin ganin Maheer ne ke bincike yajuya closet nata up side down duk kayayyakinta akasa yasa tazaro idanu gabanta yafadi dasauri tace “Baby mekake nema haka”? Dan juyowa yayi yakalleta kafin yamaida kanshi yacigaba da neme neme murya chan kasa yace “pad” dasauri tace “wa…..wat! Pad? Pad dai dana sani na mata mezakayi da Pad din mata Pablo”? Batare daya kalleta ba yace “that girl” wani abu Hajiya taji ya soki kirjinta, cikin nuna rashin jin dadi tace “yanzu sabida yarinyar nan ne kazo ka juyamin closet up side down haka, inama ruwanka idan tana period kaine ka dauramata, wait when did all this even started? Pablo Kodai yarinyar nan tai charming naka ne? Dan banga dalilin dazaisa kazo kana nema mata pad ba kaman kaine ka haifeta kaika daura mata lalluran jini ajiki” juyowa yayi yamata wani matsiyacin kallo yace “kinadashi ko baki dashi?” Cikin wani kalan bakin kishi tace “rabon danai jini shekara daya kenan so bandashi” kayayyakinta dake hannunshi yawani kalan zubar akasa cikeda fushi yace “fine I will go and buy for her then” yana maganan yafito yabi ta gefenta yawuce yayi hanyar kofa tabishi da kallo daidai yasa hannu zai bude kofa dakin yafita tace “wait” dan dayaje yasiya mata gwara tabashi, tsayawa yayi chak batare daya juyoba, shiga cikin closet din tayi zuwa wajen wata locker tabude wasu lafiyayyun expensive tampons da pad na kasan waje ta kwaso tafito tawuto har inda yake daidai gefenshi ta tsaya tana kallon fuskanshi tace “gashi” kaman bazai juyoba juyowa yayi yasa hannu ya fizge batare daya kalli fuskanta ba yawuce yafita tabishi da kallo kaman ta kurma ihu takeji.
Tana zaune akan gadon hannunta rikeda cup na tea tana sha ahankali idanuwanta sun kumbura suntum da kyar ta sha maganin Hamad da yabata guda uku, shikuma Hamad na tsaye gaban gadon yana kokarin hada drip dazai sa mata aka bude kofa aka shigo hakan yasa dukansu suka kalli kofan, hada ido sukayi da faduwa gabanta yayi hakan yasa ta wankamai harara tadauke fuskanta cikeda tsiwa kaman ba mara lafiya ba tace “mutum ko sallama bai iyaba” shi kanshi Hamad dake kokarin fixing drip a karfen gadon saida yakalli Yasmeen dayaji tai maganan dan she looks so innocent tayi tsiwa haka bare kuma gogan Maheer daya jita sarai, hade giran sama yayi data kasa yazo dab da Hamad yabashi uban pads din daya riko a hannun yace “ga abinka” juyowa Hamad yayi yakalleshi azuciyanshi ya tambayi kanshi are this people lovers, hannu yasa ya karba ya ijiye akan gadon kafin yakalli Yasmeen din anatse yace “jeki shirya Yasmeen kafin nadawo nasamiki drip din” dadan sauri Maheer yakalli Hamad jin yanda yakira sunanta Yasmeen saikuma ya fuzar da iska yajuya fuuu yafita kaman ana turashi Hamad yabishi abaya yana mamakin to mekuma yafaru danya kira sunanta yay fushi ikon Allah, suna zuwa falo Maheer yakalli Dan rai abace yace “take those hijabs to her” yawuce ya zauna yay crossing kafa daya kan daya idanunshi akan tv dake aiki, duk Hamad na kallonshi kafin yaja wata kalan dogon tsaki yasami waje ya zauna, kaman jira yake Maheer yace “wa kake ma tsaki”? Kallonshi Hamad yayi cikin ido yace “wa inba kai ba” wani kalan kallo Maheer yama Hamad din kallon da su kadai sukasan fassaran shi sannan yadauke kai kawai yana yatsine fuska yasa hannu a aljihu yaciro kwalin taba yazaro daya yadauki lighter daya gani kan table ya kunna yahau sha yana fuzar da hayakin agadarance duk Hamad na kallonshi. Agogo Hamad ya kalla na hannunshi ganin Kunsan 15min kenan da zamansu falo yasa yatashi daidai Hajiya na saukowa dagakan bene hada idanu yayi da ita ya watsar yawuce Hajiya itama tabishi da mugun kallo takalli Maheer data gani azaune yayi crossing leg yahade rai sosai yanashan taba hakan bakaramin dadi yamata ba ganinshi afalo waje tasamu kusada shi tazauna zata fara magana Hamad yaleko daga corridor yakalli Maheer yace “are u coming namaka bayanin magungunan ta ko u are not danni tafiya zanyi” Wani kalan kallon Hamad Hajiya take, tashi Maheer yayi ya ijiye karan taban akan ashtray nakan center table din yataho yabishi zuwa dakin, Yasmeen dahar bacci ya kwasheta Hamad ya nunnunamai magunguna zaimai bayanin yanda zata shasu saikuma yay shiru yakalli fuskan Maheer din anatse yace “maisa bakai mata treatment dakanka ba saida ka nemoni”? Hade giran sama da kasa yayi yace “ganin dama” jinjina kai Hamad yayi yace “Kaika sani ga magungunan kasan dosage din dan bazaka kara gani nan gidan nan naku ba, kaji tsoron Allah ka maida yarinyar nan gidansu nabarka lafiya” yana maganan yawuce yafita, fitowa falon yayi babu kowa hakan yasa yawuce yafita hango Hajiya yayi jikin motarshi jingine da kofar mazaunin direba hakan yasa yakara haderai tareda karasawa wajen anatse yace “excuse me” wani kallon tsana Hajiya tamai tace “badadan kaine mutumin dayan da Baby na yadauka amatsayin dan uwa ba dana dade da sa akasheka” rungume hannunshi Hamad yayi akirji yana kallonta, cikeda tsana Hajiya tace “nasan duk take taken ka Hamad kokari kake ka cusamai yarinyar nan yafara sonta ko to bari kaji nagaya maka Maheer nawane ni kadai har abada, shi karan kanshi baisan iya adadin soyayayan dayake mini ba, Maheer bazai taba so wata ba sama dani, nina raini kayana, tarbiyanane, nonuwan nan nawa kadai dayasha tun yana dan shekara takwas kawowa yau kosu kadai bazasu taba barinshi yaso wata ba sama dani, dan haka kome zakayi kayi Maheer is mine! Mine forever!” Dan murmushi Hamad yayi kadan yakalleta baiso yakulata ba amman yakasa daure wa, he needs to put this woman in her place, anatse yace “koma me kikama dan uwana trust me yana gab like gab da warwarewa, don’t think bansan cewa all this years you’ve been raping Maheer ba tun baisan komi ba kawowa yay, kin lalata rayuwan Mahee…..” dasauri Hajiya tace “criminal iyayenshi ne suka lalata rayuwanshi dama yaron da akai cikinshi agidan yari aka haifeshi agidan yari kazaci albarka zaiyi banda ni danazo rayuwanshi na ceceshi nai cireshi daga kangin kunci da bakin ciki da damuwa ban barshi yana binka kunakai makahon babanka bara kuna babiya Allah akan titi ba, I picked the boy from street akasan gada nabashi rayuwan mansion I educated him, na maidashi whatever he is today, my dear kada ka kara kuskuren fadin na lalata rayuwan Maheer iyayenshi suka fara lalatamai rayuwa kuma kagama munafincin ka da makirci da kulle kullen ka, ni kadaice macen dake rayuwan Maheer and so shall it be har ranan tashin alkiyama” kwashewa da dariya Hamad yayi yana mata wani kallon raini yace “ranan da Allah zai babbaka ki ba, for all ur sins, and let me tell u don’t think sabida tun Maheer na 8yrs yana yaro kike raping nashi kinaji kece kika budemai ido yasan mace sabida haka bazai taba so wata ba” yadanyi murmushi yace “get your bag of tissue close dan as it stand yanzu haka, Maheer is already in love with someone else” “Hamad!” Hajiya tai wani kalan ihu tadaga hannu zata daurama Hamad daya tsaya chak yana kallonta mari takasa kai marin, tana wani kalan sauke ijiyan zuciya tana kumfan baki tana nishi kaman zakanya, takalli hannunta data daga zata mareshi dashi tace “kaci darajan Maheer kaci darajan asalin kauna daya nunamin yana maka da wlh wlh wlh yau bazan barka ka kwana aduniya ba” tana maganan tawuce fuuuuuu tai cikin gida Hamad ya bita da kallo kafin ya tofar da yawu akasa yabude motanshi yashiga yatada yabar gidan.
https://www.tiktok.com/@mshakurr?_t=8d9o7ToAvDC&_r=1
✨KYALKYALIN KAUNA✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣8️⃣
For your original Egypt Abayas,home decor, Gold (new and used), shoes that are qualitative and unique at affordable price , siyen daya ko sari (wholesale and retail) contact +201123302418
Instagram @Shopper_topia
WhatsApp group *Maryam’s Egypt abaya *
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
Saida Hamad yarufo kofan sannan Maheer yajuyo dasauri yakalleta kaman jira yake dama Hamad yatafi, yanda take baccin tana numfashi dake fitowa da kyar a hancinta sabida nose block nata ya kalla, ahankali yatako zuwa gaban gadon yana kallonta kafin yadaga kanshi yakalli ruwan da ake kara mata ganin ruwan baya tafiya at all yasa yakalli hannunta dasauri ta dunkule hannun cikin bacci, gently kaman wanda baiso yadan duko da kanshi wajen gadon yana kallon hannun nata data dunkule ahankali yakai hannunshi zai taba hannunta saikuma ya tsaya kaman mai tunanin wani abu kafin yakalli fuskanta yanda take bacci chan kasan makoshin shi yace “what have you done to me”? Lumshe idanunshi yayi gently yadaura hannunshi kan nata wani irin sanyi yaji ajikinshi daga taba hannun nata, itama kaman tajishi dan saida tai motsi hakan yasa dasauri yakalleta, ijiyan zuciya tasauke cikin baccin takara komawa hakan yasa ahankali ya bude hannun nata data dunkule tafin hannunta ya jike kaman tazuba ruwa and so soft kaman hannun baby, baitaba sanin hannun mace can be this soft ba sai yau, sake dago idanunshi yayi yakalli fuskanta hannunshi still yana cikin nata daidai nan aka bude kofan dakin da karfi aka shigo hakan yasa yajuyo dakanshi yakalli kofan da aka bude batare daya raba hannunsu ba, wani kalan mutuwan tsaye Hajiya tayi ganin Pablo tareda yarinyar dake bacci yakama hannunta gam gam yarike, yanda kirjinta yafara bugawa zaka dauka heart attack ke shirin kamata, kallo daya Maheer yamata yadauke kai yajuya yacigaba da abinda yake, awani kalan hankali yabude tafin hannun Yasmeen da kyau ya kwantar da hannun ahankali tareda zare nashi yadago kai yakalli drip din ganin yana tafiya yasa yamike tsaye yana kallonta sake dukawa yayi yaja bargon yana rufamata ajiki da kyau Hajiya tasake bude baki tana kallonshi da kyar ta danne zuciyanta tace “Pablo” juyowa yayi yakalleta saikuma ya maida kanshi kan Yasmeen yana karajan bargon har zuwa shoulder nata yana kallon yanda gashin goshinta suka kwanta sukai lubb tai wani kalan kyau kafin yadago, Hajiya tace “I want to talk to you” juyowa yayi yakalleta zai sake juyawa yakalli Yasmeen tace “now!” Tabude kofan tajuya tafita fuuu, kallon Yasmeen yayi sannan yajuya yafita tsayawa yayi yarufo kofan nata yaciro key yasaka sannan yazare key yasa a aljihun shi yawuce yafita daga corridor ganin Hajiya bata falo yasa yay dan tsaki yayi stairs yawuce sama direct dakinta yayi yana zuwa yabude kofa yashiga tsaye yaganta atsakiyan daki idanunta sunyi jajir maida kofan tayi yarufe yakalleta yace “what? Gani” kaman jira take zuwa tayi dasauri gabanshi cikeda wani kalan bakin kishi tace “what are you doing with that girl”? Wani kalan kallo yamata danshi baima gane ba to be honest, cikeda daga murya dudda she’s controlling herself kartamai ihu dan ba’a dagamai murya idan anamai magana tace “why are you being so nice towards that girl Baby? Mehadinka da ita? Meruwanka da ciwonta what is your business with h……” “lower your voice!” Maheer yafadi cikin kakkausan murya dayasa tai wani kalan shiru tana kallonshi, saikuma ahankali tarage muryanta sosai tana kallonshi kaman yanda yake kallonta tace “why are you caring for that girl Baby”? Cikin muryan ko ajikinshi yace “she’s sick baki gani ne” cikin sauri kaman wacce ke shirin samin tabin hankali tace “idan she’s sick so many people can take care of