Showing 105001 words to 108000 words out of 121675 words

Chapter 36 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17176

Washe gari da safe mai gyara yazo, sabon ?ori ya sakema Abba a ?ugu, suma kam Abba yayita babu adadi, su Zarah kuka kawai sukeyi, hakama Umma takasa daurewa, sosai takejin tausayin Uban ?a?an nata dukda tsiyatakun daya shuka mata.
An gama gyaran Abba ya samu barci na wahala, a lokacinne hindu tasamu zarafin tambayar Uncle yahya wayarta wai zata sanarma danginta.
"Wayoyinku suna cikin wata jakarki na zuba, tana nan inaga an taho da ita, amma ina Zulaiha itace kamar nabama jakar dazamu taho?".
aunty Zulai dake sharo ?akin Umma tace, "Eh Uncle tana nan ?akinta a jar jaka".
"yauwa to kinji tana nan, sauran kayanku suna gidan malam Alfah na ro?i alfarma aka kai can, saboda mu gidajen namu babu inda za'a iya lode wa?an nan kayan, kayan gado dai dasu kujeru duk an saidasu harma katufun, guda ukunan dakika gani ka?ai muka bari, acikin ku?inne ma akabama mai gyaranan ku?insa, dan wlhy nidai ku?in dake wajena sun ?are, a jiyama saida na ta?a ku?in sadakin jiddah dubu ashirin aka ?ako sauran kayanku, amma an maida mata yanzu haka, wanan daliline yasa muka matsa aka sallamoku daga asibiti, tunda bamuda ku?in cigaba da biyan ku?in gado da sauransu, yarannan kuma su Hannatu iya ?o?ari sunyi dagasu har mazajensu, koma nace suna cikinyi".
A ?age hajia hindu ta amsa da "Uhhum". Dan taji haushin saida musu kayan gado kuwa, amma babu komai aiga ku?inan.
Babu wanda yasakebi ta kanta, saboda amsar da tabama Uncle yahya ta Uhum kowa tabashi takaici.

Shidai Uncle yahya yay musu sallama yatafi gida danya ?an huta kafin Abba ya farka.

***********

Da rana akayi faten doya da wake da alayahu, ?iri-?iri su Hussain sukace bazasu ciba, babu wanda ya tanka musu sai Umma daketa musu nasiha da lallashinsu, amma ?iri da muzu suka?i saurarenta, saima rashin kunya da suka nemi yimata, aiko Aunty Hannatu dukda ha?urinta tai azamar taka musu birki.
Hakan saiya harzu?a hajia hindu tafara sakin magana, gashi tana ?ya?e waje ?aya tana fama da kanta.
Aunty Zulai zatai magana Umma ta hana, takumace kar wanda ya sake tankawa, daga yanzuma komi su Halifa zasuyi a gidan babu ruwansu, abinci dai idan andafa a basu, suci ko karsuci wanan yarage nasu ai.
Hajia hindu dai tanata neman ?ananun magana babu wanda ya kulata, ga takaicin neman kaninta da take a waya amma ta?i shiga, tamasa kira yafi hamsin sai dai ace mata Busy, tun tana ?aukar abin wasa har nutsuwa ta fara gagararta.


Hummm hajia Hindatu yaya dai??¡â???.


???????????

Jiddah na zaune a falo bayan tayi sallar la'asar tana duba littafin *Ahdhari* Aliyu ya shigo da sallama, ?ago idonta da sukai alamun tayi kuka tayi ta kallesa tana amsawa, ya tsaya a ?ofa tareda bu?e mata hannayensa alamar tazo gareshi.
Murmushi tayi tami?e jiki a sanyaye, dan yariga ya shaida mata hakan dokane acikin tsarinsa, kuma koba komai tana bu?atar jin ?uminsa a halin yanzun da zuciyarta ta wuni a ?untacennan.
Shigewa tayi ajikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
shima numfashi ya sauke, yace, "Nayi kewarki Jiddah na".
Ahankali ta furta "Nayi kewarka sosai nima".
Babu shiri yay azamar ?ago kanta, dan maganarta tabashi matu?ar mamaki, baiyi zaton hakan agareta ba nan kusa. Lumshe idanunta tayi tana murmushi, dan batason su ha?a ido.
"Jiddatulkhair da gaske koda wasa?".
Fuska ta?an shagwa?e tana tura masa baki, "Da gaske mana". Ta kare maganar da maida kanta a kirjinsa.
"Masha ALLAH, Alhmdllh Adaratul ainy (Turaren zuciyata) ya kuma rungumeta yanajin sonta nakuma tasiri a ransa".
Bayan sun zauna taje ta kawo masa ruwa. Yana sha idonsa a kanta, dan ya kula tana tare da damuwa kamar yanda maimuna ta sanar masa, saboda sashenta yafara zuwa, itama ya isketa cikin damuwa, ya tsareta da tambaya shine ta sanar masa abinda su Hassana sukazo sukayi, ransa ya ?aci sosai. Amma sanin halin Maimuna bazata ta?a sakasu suma Jiddah hakanba sai itama ya lallasheta akan karta damu, shi yasan bazata sakasu suyiba hakanba ga jiddah, sunyine kawai dan ra?in kansu, amma zai taka musu birki insha ALLAH.
hakan sai ya saka zuciyar Maimuna ?an samun nutsuwa, amma damuwarta kuma halin da jiddah take a ciki.
Aliyu ya ?auki aniyar gwada Jiddah yagani kozata masa maganar abinda su Aminar sukazo sukayi.
"?ammatana mike faruwa? Na ganki wani sukuku, ga idonkifa kamar kinyi kuka"......
Murmushi jiddah tayi tana danne abinda ya tokare ranta, "Babu komai, kumani ba kuka nayiba, kawai kewar Ummana nakeyi".
Idanu ya tsura mata zuciyarsa na tunanin ita takeson sanarma kenan? To amma dataso hakan ai da tayi tunda ga waya a hannunta, saurin kauda wanan tunanin yayima daga ransa, ya ajiye kofin da yasha ruwan yakamo hannunta cikin nasa idonsa akan fuskarta, "Haba tawan, anya kuwa kewar su Ummace kawai? Kodai Auntynki ce?".
"lah A'a wlhy, ni aunty tsakanina da ita sai sambarka, kawai dai kewar su Ummance".
"Shikenan, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zan kaiki, yanzuma tashi ki shirya danayi wanka zamuje mu gaida su malam, kinga baki ta?a zuwa gidanba tunda kikazo.
Da?ine sosai ya kama jiddah, harga ALLAH tana ?aunar dattakon tsohon, tuni taji nauyin da zuciyarta yayi kaso mafi yawa ya ragu.
tace, "To abincifa?"
"Naci abinci a office din mustafa, shiyyasa na kira auntynki nace karkuyi dani".
Murmushi tayi, dukda batasan anyi hakanba, kuma girkin Maimuna ne har rana, sai yanzu da yammarnan ita zata karbesa, batareda tace komaiba ta mike, harta nufi ?ofar fita Aliyu ya kirata, juyowa tayi ta kallesa, yace,
"Ina zakije kuma?".
"Zan ha?a maka ruwan wankane".
"Karki damu zoki ha?amin a bayinki kawai".
Kanta ta jinjina masa ta dawo da baya zuwa bedroom nata. Binta yayi da kallo harta shige, ya ?an sauke numfashi yana jingina kansa da kujera, a zuciyarsa yana tunanin miyasa ta?i fa?a masa abinda akai matan? Zai sake gwadata dai ya gani, harga ALLAH yana mamakin yanda wasu lokutan halayyar Jiddah da Maimuna suke kamanceceniya da juna, kodan dukansu sunada ilimin addinine da tarbiyya, kuma Alhmdllh suna aiki da sanin da ALLAH yay musu, sarai yasan salon kishin kowacce amma hakan bai hanasu ?yautata zamantakewar dake tsakaninsuba..........
Jiddah ta katse masa tinani, idanunsa ya bu?e, ya kama hannunta yana fa?in "Zomuje ki tayani wankan to".
Sosai ta zaro idanu da fa?in "Wankafa?".
Tabashi dariya data zaro idon, ya ran?wafo kanta yana jan hancinta, "Malama ba?yason koyi da sunnar MANZON ALLAH ne? ANNABI yana wanka da Matansa har hannayensu na gogayya a cikin ruwa, ba?yason samun wanan ?atotuwar ladar tawajena".
Hannu ta saka ta rufe fuskarta tana ?aramar dariya, shima yay dariyar yana jan hannunta sukai ciki....

???????

Gabda magriba suka fito da nufin barin gidan, dan Aliyu soyake yay sallah a masallacin ?ofar gidansu, Kasancewar Jiddah ce da girki maimuna tace ya shiga gaba, amma sai ta?i tace, "A'a wlhy Aunty ke zaki shiga, ba girki zaki dubaba, kimarki ta matsayin babba a gareni".
Daga Maimunatu har Aliyu binta sukai da kallo harta shige baya, sanan suka kalli juna sukai murmushi, kowannensu yanajin ?aunarta da kimarta a ransa, yayinda itama hakanne daga gareta.
Sun isa anata hada-hadar shiga sallar magriba, Jiddah da Maimuna suka shige cikin gidan, shikuma Aliyu yashiga masallaci..........???


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)

????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*????????????



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/30/2019, 1:58 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[59?60]_*


............Duk da agidan Maimunatu ta girma, kuma akwai mari?iyarta Iya Habi, hakan baisakata kaisu canba itada Jiddah, saita nufi ?akin hajia bah-bah uwargidan Malam.
Sosai Hajia bah-bah taimusu tarbar mutunci, hakama Na'ima tafito fuskarta aji?e da alamar alwala tayo tana musu oyoyo.
Harara Maimuna ta zuba mata tana fa?in "An?i a amsa ?in, aini yarinya mun ?ata".
"Haba-haba Uwar ukunmu, yi ha?uri, nasan nayi laifi amma wlhy tafiya nayi tun bayan bikin yaya Ali, kuma tambaya bah-bah kiji. Aunty Amarya sannu dazuwa kinji".
Murmushi Jiddah tayi tana amsawa.
Hajia bah-bah ta katse musu jancen da fa?in, "Da wannam surutun da kika tsaresu dashi da alwala kika kaisu sukayi ga Aliyu can zai tada salla".
"To bah-bah. Kunga kumuje to".
?akin Na'ima suka koma, domin yin sallar acan.

Bayan an idar da sallah Aliyu na gaisuwa da mutane wayarsa tayi ring, cirota yay daga aljihu ya duba, ganin Uncle yahya saiya fa?a?a murmushinsa, bai ?agaba saida ta tsinke sannan shi ya kirashi da kansa.
Daga can shima Uncle yahya murmushin yayi ya ?aga, cikin girmama juna suka gaisa, Uncle yahya yama Aliyu bayanin halin da Abba ke ciki kusan kwana uku.
Sosai hankalin Aliyu ya tashi, yace, "Uncle aida an sanar mana, babu wata damuwa, ko yau aka kaita washe gari hakan ta faru ai dolene tafito, kuma koni aida nazo dubashi. Insha ALLAH gamunan zuwa bayan isha'i".
"ALLAH ya kawoku, nagode a gaida min malam".
"Zaiji insha ALLAH".
Sosai lamarin ya zauna a zuciyar Aliyu, duk zuciyarsa taimasa babu da?i, tausayin Abba sosai ya ?arsu a ransa. Matsawa yay kusada malam dake zaune yana duba al?ur'ani ya sanar masa da abinda ke faruwa.
"Ya Salam, ALLAH yabashi lafiya, yasa kaffarane a gareshi, insha ALLAH zanje na dubashi nima".
"Amin baba, to ALLAH ya bada iko, suma tare muke dasu sunzo gaisheku, daga nan zamu wuce mu dubashi insha ALLAH".
"To masha ALLAH, hakanma yayi".
Bayan an idar da salla malam yasaka Abba a cikin doguwar addu'a, wadda ta saka Aliyu jin da?i sosai.

A cikin gida kuwa su Jiddah suna idar da salla sukazo suka gaida hajia bah-bah, cikin fara'a ta amsa musu tareda sanya musu albarka. Sanan tace suje su gaida su Gwaggo.
Sun fara zuwa sashen gwaggo amarya, itama ta tarbesu da fara'a, basu baro sashenba saida za'a kabbara sallar isha'i, sashen iya habi suka shiga, itama ta tarbesu da barkwancinta, tareda jin da?in ganin Maimunatu ta bata cikin damuwa, saitaji Jiddah ta kwanta mata arai, nanma sun?an jima dan saida sukai sallar isha'i, suka koma sashen Hajia bah-bah saboda kiransu da Na'ima tayi suzo suci tuwo.

Lokacin da Aliyu ya shigo gidan ya iskesu sunacin tuwo a falon hajia bah-bah. Bayan sun gaisa da bah-bah Na'ima ma ta gaisheshi, bisa kuskure Jiddah ta ?ago kai suka ha?a ido, gira ya?an ?aga mata yana nuna mata tuwon da ido.
Murmushi ta masa ha?e da ?aramin gwalo, ya murmusa shima yana mi?ewa domin zuwa gaida sauran matan gidan.
"Aliyu ka zauna a kawo maka tuwo".
"A'a Bah-bah, Alhmdllh, kinsan ni ba cin abincin darenma nakeba kwata-kwata".
Cikin hangame baki tace, "Wai wanan halin naka har yanzu baka barshiba Ali? Randa baka yini agidaba shikenan bazakaci abincin iyalinka ba?".
"Bah-bah ai inacin na safe, rashin cin abinci dare abune mai ?yau, yana ?ara lafiya inhar mutum zai iya jurewa".
"A'a wlhy badaniba kam, yoni idan banci tuwo da darebama jinake tamkar banida lafiya a gidan nan".
Dariya su Jiddah saukayi ka?an, kujifa hajia bah-bah da wani batu, saikace wadda batayi salla ba.
Shidai Aliyu fita yay yana mata dariya. Bai da?e sosai ba ya dawo yana fa?in, "Kumuje ku gaida malam akwai inda zamuje insha ALLAH".
Maimuna da Jiddah suka mi?e, dan dama sungama cin abincin, harma sun wanko hannunsu da baki. Sallama sukaima Hajia bah-bah, suka koma ?akunan su gwaggo suma sukai musu sallama, harda ?ar tsarabarsu ta kuka da ?anyen ku?ewa da daddawa suka samo.
Saida sukai sallama a ?ofar falo aka basu izinin shiga sanan suka shiga, sun iske malam da Aliyu zaune suna magana, idan ka gansu dolene su baka sha'awa, harsun tsuguna daga farkon falon malam yace, "A'a ?a?ana ku shigo mana ciki".
Duk a kunyace suka koma gabansu sosai, kansu a ?asa suka gaidashi, ya amsa musu cikin fara'a tareda tambayarsu gidan da rayuwar yau da kullum, sanan ya ?ora da nasiha a garesu su duka ukun mai ratsa jiki, yakuma sanya musu albarka tareda fatan alkairi a zamansu.
Suko kansu na ?asa sunata amsawa da amin, yayinda ?aunar tsohon da girmansa na ?ara yalwatuwa a ransu.
Baija zancen yayi tsawoba yace, "Aliy tashi kuje dare nayi, dan ALLAH ka gaidamin shi, ga wanan kabashi kafin nazo".
Tashi Maimuna da Jiddah sukayi suka fita, dukda basu fahimci zancenba sunga yadace su basu waje ko akwai abinda zasu tattauna.
Bayan fitarsu Aliyu yace, "Zaiji insha ALLAH baba, amma kabar ku?inka zan bashi injika insha ALLAH".
"A'a kar?i wanan ai tsakanina dashine, kuma nima ina bu?atar ladan sarkin wayo" ya?are maganar da tsokana.
Murmushi Aliyu yayi ya kar?i ku?in, sanan sukai sallama da malam ya fito. Ya iske harsu Maimuna sun shiga mota, sai Na'ima dake tsaye ajikin motar suna magana.
Cikin samarin dake gefe ?aya yazo ya bu?e masa motar da addu'ar sauka lafiya, dama sunzo suka gaida su Jiddah cikin mutuntawa.
Koda suka tafi a hanya bai musu bayanin inda zasujeba.
Ita kuma Jiddah gaba ?aya hankalinta ma bakan hanya yakeba, game kawai take a waya tana sauraren hirarsu jefi-jefi suma, saida har suka shigo cikin anguwar sosai ne Jiddah ta ?ago kanta donson ganin inama suka dosane?.
Ta?an waro idanu da fa?in "Ai nan anguwarmune".
Dariya Maimuna tayi ta juyo tana kallonta, "Wai da gaske dan ALLAH?".
"Wlhy kuwa aunty".
Aliyu na jinsu amma ya?i tanka musu, a ?ofar gidansu Jiddah yay fakin sannan ya juyo yana kallon Jiddah.
"Ku shiga, zan shigo daga baya nima".
Jikin Jiddah kuma sai yayi sanyi, cikin langa?ar da kai tace, "Basai gobe idan ALLAH ya kaimu kaceminba?".
Ganin Maimuna ta fita saiya shafa kumatun Jiddah, shima cikin kwantar da murya yace, "Haka naje, insha ALLAHU zan kawoki gobenma kinji".
Ha?iye ?wallan daya cika idonta tayi, ta sauke ajiyar zuciya sanan ta fita. Har suka shiga gidan idonsa na kansu, saida suka ?acema ganinsa ne ya sauke ajiyar zuciya da ?aukar waya domin kiran Uncle yahya.

??????.

Su Umma duk suna tsakar gida zagaye da Abba da Uncle yahya ke bama Abinci.
Hakanne yasaka Jiddah yin turus tana binsu da kallo, dama ?an uwanta basu tafiba? Idonta ta sauke akan Abba dake kwance ?a??aure da karan ?ori, sai Hajia Hindu dake gefe zaune ?a?anta zagaye da ita itama.
"Lah yaya Jiddah kece?" 'Cewar walida data fito daga ?akin Abba ?auke da kwanon magani'.
Sauranma duk sai suka maido kallonsu ga ?ofar, Zarah tazo ta rungume Jiddah suka saki kuka tare, dan Jiddah ta fahimci gidansu babu lafiya.
Aunty Hanantu data hangi Maimuna ce ta mi?e tana fa?in "Ashe tare kuke? Shigo mana Maimunatu".
Gwiwar Maimuna a sanyaye itama ta shiga ciki, dan alamu dai sun nuna babu lafiya kam.
Uncle yahya yayma Jiddah da Zarah magana sanan suka saki juna, Jiddah tazo gaban Abba ta dur?usa tana hawaye, "Abbanmu miya sameka?".
Dukda haushinta da yakeji dan shi duk akanta yadora laifin, data zauna gidan Alhaji garba wanan bala'in da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login