Showing 87001 words to 90000 words out of 121675 words
da hankalinki, wlhy idan kika bamu dama bazata cika satiba a gidannan zata Kama gabanta, narasa mike damun kan Dady, yarasa wadda zai kwaso mana sai wannan tsohuwar karuwar, ALLAH garama yarinyar nan Jiddah, dama ita kika hak'ura muka zauna da Dady bai kwaso mana wannan motar hayarba ai".
Hararsa hajia deluwa tayi, "Kai dan Ubanka waya fad'a maka kishiya duk k'ank'antarta tanada sauk'i, dalla kuficemin anan kafin najuye muku takaicin dake kaina yanzunnan".
Kallon juna sukayi shi da bala suna ta6e baki, suka fice suka barta tana cigaba da borinta da zagi kwando-kwando ga Alhaji garba da amaryarsa.????
???????????
Sai 10:30pm Aliyu ya dawo gida, tunda magriba ya dawo anguwar amma bai shigoba yana massalaci, bayan sungama karatun dare yakuma barin anguwar, sai dai baiwani dad'eba yadawo, Kai tsaye gida ya shigo, tsitt kakeji tamkar babu mutane, leda d'aya ya d'auka yanufi sashen Maimuna, kwance ya isketa harma tayi barci, ganin magani a durowar gefen gado yabashi tabbacin batada lafiya, zama yay kusa da ita yajanye bargon datake ciki yana ta6a wuyanta zuwa goshi, jikinta ringim da zazza6i, tausayintane ya kamashi, bai tadata ba ya tofeta da addu'a ya maida mata bargon sannan yafito.
Kicin d'inta ya shiga yasaka Mata abin cikin ledar a firij sannan yadawo falo, tea d'insa da kayan fruits data gyara ya d'auka yafita yaja Mata k'ofar.
Saida Yakoma mota ya d'auki d'ayar ledar sannan yanufi sashen Jiddah itama.
Bai isketa a faloba, dan haka yawuce bedroom. Zaune take tana duba littafin Umdatul Ahkam, kanta ta d'ago tana amsa masa sallamar, ganinsa da kaya saita ajiye littafin tamik'e ta amshesa tana masa sannu.
"Yauwa Juddatulkhair, ya zaman shiru? Amin afuwa kinsan nid'in sai a hankaline".
Fusakarta d'auke da murmushi amma batace komaiba.
Zama yay kan k'aramin kafet d'in gaban gadon ysna kallonta, itakam takasa kallon nashi, tana k'ok'arin aje kayan gefe tace, "Aunty fa batada lafiya, amma tasha magani tun d'azu ta kwanta, zan kiraka amma ta hana".
"Eh naje wajenta kafin nashigo nan, Mata kuna k'ok'ari, tunda tasamu cikinan haka taketa fama, nikaina bansan adadin ledar ruwan data shaba ma".
Cikin tausayawa Jiddah tace, "ALLAH Sarki, ALLAH ya k'ara Mata lafiya, wlhy Na tausaya mata, dan d'azun daga cin abincin sai amai".
Shima duk fuskarsa ta Nuna alamun damuwa yana tausayama Maimunatu matuk'a.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Bayan sunsha fruits d'inda saida yasha fama da ita sannan yasa ta had'a masa Shayin, koda yace taci naman daya kawo catai ta k'oshi, bai takurataba ya kammala shan tea d'insa yamik'e yana fad'in tayi alwala kafin ya dawo".
Bai jira amsartaba ya fice, kwashe kayan tayi cike da tsarguwa tafito, tabud'e abinda tasan zai iya lalacewa dan batada firij.
Umarninsa tabi, bayan tayi shirin barci ta d'auro alwala, duk yanda su Yaruwaiya suka koyar da ita wajen saka k'amshi da tsaftace bakinta saida tayi, kafin tasaka hijjab ta zauna zaman jiransa.
Bai wani jimaba can sosai ya dawo cikin jallabiya ruwan k'asa.
Kallonta yay damata alamar ta tashi, itadai duk jikinta yayi sanyi, addu'a kawai takeyi a k'asan ranta ALLAH yasa ba zargin datake baneba.
Sheikh Aliy ya jasu salla raka biyu kafin suyi zaman addu'ar, yaja addu'a mai tsayo tafatan zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al'umar musulmi kafin su shafa ya juyo gareta.
Cikin tsareta da idanu ya jeho Mata tambaya..............???
*_Zan d'anyi jan hankalo anan please, wasu suna ganin maganar da Maimunatu tafad'a akan mutumin da ya turo sak'o tamkar da Aliyu take, a'a badashi takeba, sak'one aka turo masa kamar yanda ta fad'a, mun ta6o wannan ga6arne kuma saboda girmanta da yawautarta acikin al'umma, sannan masu gani shi Aliyu kamar baya iya Mata komai ba haka baneba, itadai tace yakan had'ama kwanaki hud'u bai nemetaba, sannan baya dogon zango tare da ita, (abinda nakeso mu fahinma anan shine yanada k'yau muringa kwatanta rayuwarmu ta zahiri a cikin novels, babu wani namiji da azahiri zaikai tsawon awoyi hud'u ko sama da haka tare dake, inkuwa hakane to lallai munshiga uku??????, idan kuwa har za'a samu irin wannan to basuda yawa gaskiya, nata6ajin wani likita Na fad'in yawan jima'i kullum-kullum yana ragema ma'aurata sha'awa da jindad'i harma suji abun yana fita Kansu basa wani shauk'in yinsa, sai dai suyi domin sabo kawai, sannan yana ragema mace d'and'ano awajen miji, abinda kuma zamu kalla bakowane namiji baneba a zahirima zai kasance dake a kullum, dan wani yaje aiki ya gaji, wani kuma damuwa tamasa yawa da sauransu, kuma ke kankima wlhy saikinji lamarin da takura dukda dai halittarmu kala-kala ce, akwai masu yawan buk'ata a mazan da matan, a dalilin karatun novels Mata da yawa sunama mazajensu kallon ragwaye, a buk akan saka namiji yayi awa uku tare da matarsa, maybe ma bai ishesaba, sannan da safe zai k'ara, idan yadawo aikima haka, tayaya ke a zahiri da ba'aima haka bazakiga gazawar naki mijinba?, wannan yasa lokuta da dama ake kalubalantarmu mu marubuta, dan mungaza fahimtar tasirin da alkalumanmu kedashi ga al'umma, badan nishad'i kawai ake rubutu ba, yakamata y'an uwana marubuta muringa saka hakan a ranmu, dan yanda zaki rubuta Abu Mara k'yau ALLAH ya tambayeki haka idan kika rubuta k'yak'yk'yawa zai baki lada, balle idan wani ya amfanu dashi Yasamu amfani kuma, idan awannan littafi kin saka yawan bukatar ma'aurata to Ya kamata acan kisaka k'asa-k'asa, awanima kisaka rauni sosai domin wasu su sami mafita daga matsalarsu Na gidajen aure, hakanne yasakani a farkon buk d'inann Na nuna Aliyu yanama da Matsala gaba d'aya, wadda kuma a sanadinta harya rasa matarsa da yake matuk'ar so da k'auna. Ina fatan kun fahimceni, nayi wannan maganarne domin murunga tafiya akan abinda ya dace, dan idan mun kauce kuke Fara k'alubalantar mu, alhalin kuke tunzura marubuta da yawa rubuta abinda zai burgeku a buks nasu, kuma koda ya kasance Mara tsari ga al'umma)_*.
_ALLAH yasa mudace_.??????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[12/21/2019, 1:15 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[47?48]_*
..............Muryarta na rawa kanta a k'asa tashiga amsa masa,
"Sharuddan alwala guda goma ne 1.Musulunci, 2. Hankali, 3.Wayo, 4.Niyya, tare da kyautata hukuncinta tare da niyyar ba zai yanke ta ba har sai ya kammala alwalar, 5.Daukewar abunda ke hana alwala (Jinin al'ada da jinin biki), 6. Istinja'u ko istijmaru, 7.Ruwan ya kasance mai tsarki, Ruwan ya kasance na halasta, 9.Gusar da abunda zai hana shigar ruwan fata, 10.Shigar lokaci ga wanda ke da hadasi a kowani lokaci.
Abubuwanda ke wajabta alwala. Abunda ke wajabta shi ne samuwar hadasi.
Farillan arwala, Farillan alwala shida ne.1. Wanke fuska da baki da hanci wad'anda ke furkar. 2. Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu. 3. Shafar kai tare da kunne 4. Wanke kafafuwa. ALLAH madaukaki yace:
"Ya ku wad'anda sukayi Imani! Idan kun tashi za ku yi sallah, to sai ku wanke fuskokinku da hannaye zuwa gwiwar hannu, kuma ku shafi kawunanku da kafafuwa zuwa idon sawu" (Ma'idah: aya ta 5).
5. Jerantawa, domin ALLAH maigirma da d'aukaka ya sanya jerantawar hakan sai ya sanya shafa tsakanin wankewa. 6. Jerantawa kamar yadda ANNABI (S.A.W) ya aikata.
SUNNONIN ALWALA. Daga cikin sunnonin alwala akwai; 1. Asuwaki
2. Wanke tafin hannu sau uku. 3. Kurkurar baki da shaka ruwa.
4. Tsefe gemu mai yawa da yatsun hannu da kafafuwa. 5. Damantarwa. (fara gabatar da dama). Wanki na biyu da na uku. (idan na farko ya game).
7. Debo ruwa domin wanke kunne. 8. Addu'ah bayan alwala. 9. Sallar nafila raka'a biyu bayan ta.
Daga cikin makaruhan alwala. 1. Yin alwala a wurin da ba shi da tsarki, domin tsoron abinda ke iya taba jikinsa na najasa. 2. Kari akan wanki uku, domin abinda aka ruwaito lalle ANNABI ya yi alwala sau uku-uku ne, sai ya ce duk wanda ya yi kari hakika ya munana, kuma ya yi zalunci. (Nasa'i ne ya ruwaito).
3. Barna da ruwa wajan alwala, ka tuna lokacin da ANNABI (S.A.W) ya yi alwala da mudin Nabiyy, shi ne kuma kanfatar hannu. Barna abace da aka hana a komai. Barin sunnah daya ko fiye da haka, daga cikin sunnonin alwala, lalle kuma barinta rashin lada ne, kuma bai kamata baya bari lada ya wuce shi.
Abubuwanda ke warware alwala. Abubuwa masu warware alwala bakwai ne;
1. Abubuwan dake fitowa daga mafita biyu (ta gaba ko ta dubura).
2. Abinda ke fitowa daga sauran jiki.
3. Gushewar hankali ta hauka ko farfadiya ko maye. 4. Shafar azzakarin mutum ko shafar gaban mace ba tare da shamaki ba. 5.Namiji ya shafi mace domin jin sha'awah ko mace ta yi hakan. 6. Cin naman rakumi.
7. Duk abunda ke wajabta wanka yana wajabta alwala, kamar shiga musulunci da
fitowar maniyyi da makamancin haka, saidai mutuwa lalle shi yana wajabta wanka ne banda alwala.
WANKA: Ma'anar wanka; A yare da kuma wurin mallaman fikhu, Alghuslu ) ( da wasalin dumma ruwan da ake wanka da shi ne, amma da wasalin fataha ) ( aiki ne (wato yin wankan) da wasalin kasra ) ( kuma shi ne darasin mu, watau tsarkakewa. Ma'anar shi a shari'ah: shi ne zuba ruwa a dukkan jiki, daga tsakiyar kai har zuwa kasan diddige da ruwa mai tsarki akan sifa kebantacciya. Mace da namiji wajan siffar wankan su dayane, saidai ga mace a lokacin da take wankan daukewar jinin al'ada ko na biki, to yana kamata a gare ta da ta wanke alamar jinin domin tsarkaketa da kuma kauda warin jinin.
Abubuwan dake wajabta wanka. Abubuwan dake wajabta wanka guda shida ne:-
1. Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji.
2. 6oyewar kan azzkari a cikin farji. 3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, sai dai in shahidi ne. 4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda.
5. Jinin al'ada.
6. Jinin biki (wato jinin haihuwa).
Daga cikin wankan da suke anso ayisu a musulunci.
1. Wankan jumu'ah.
2. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah). 3. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka.
4. Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah) 5. Idan mutum ya farfad'o daga hauka ko farfad'iya 6. Wankan shiga Makkah.7. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rok'on ruwa. 8. Wanka na mai istiha a kowacce sallah.9. Ga kowanne jima'i an so a yi wanka.
SALLAH:- Hukunce-hukunce da suka rataya da sallah. Sallar jam'i, Sallar Kasru, (Sallar matafiya), Hada salloli biyu, Sujjadar rafkannuwa (Kabaliyya da Ba'adiyya), Sallar nafila, Sallar juma'a, Sallar Idi biyu, Sallar rok'an ruwa, Sallar kisfewar rana ko wata, Jana'iza da hukunce hukuncenta.
RUKUNI NA BIYU DAGA CIKIN RUKUNAN
MUSULUNCI: SHI NE SALLAH.
Ma'anarta a yaren Larabci da kuma Shari'ah, Sallah a yare:- ita ce addu'ah, Allah ta'ala ya
ce:
"Kuma ka yi musu addu'ah, lalle addu'ar ka natsuwa ce a gare su" {Taubah: aya ta 103}.
Sallah a Shari'ah:- ita ce 'zancene da ayukka ke6antattu, wacce ake bud'e ta da kabbara, kuma a rufeta da sallama tare da sharud'd'an ta ke6a66u, Tarihin Wajabta sallah. An farlanta sallah ne daren Isra'i kafin hijra, kuma da ya ce daga cikin rukunnan addinin musulunci, bayan imani da ALLAH da MANZONSA ita ce farko, domin ta kunshe su,
wacce MANZON ALLAH ya shardanta ta bayan Tauhidi, mai tsira da aminci ya ce:
"Kan dukkan al'amari shi ne musulunci, gimshikinsa kuma ita ce sallah, kuma kololon gimshi kuma shi ne jihadi domin daga Kalmar ALLAH.
{Tirmizi ya ruwaito}.
Hikimar Shar'anta ta. Sallah godiya ce ga ni'imomi masu girma, wace ALLAH ya ni'imata ga bayinsa, kamar
yadda take daga cikin ababan dake bayyana kad'aituwar ALLAH, ta yadda take bayyanar da fuskanta ga ALLAH mad'aukakin sarki da kusanci, k'ank'anta da kai a gaban shi, da kuma ganawa da shi mad'aukakin sarki, ta hanyar karatu, da zikiri, da addu'ah. Kamar yadda ta kasance hanyar da take hada bawa da Ubangijinsa, kamar yadda take daukaka shi akan wasu abubuwa na k'yalek'yali zuwa inda zai samu natsuwa a ransa da kwanciyar hankali, saboda haka duk wanda ya nitse wajen tunanin rayuwa mai d'aurewa to sallarsa ta kasance tabbatacciya ta hak'ik'a daga barin gafala daga ita. Hak'ik'a abindake nuni da akwai abun dake da girma fiye da wannan, ita rayuwa kuma bai kamata a tafiyar da ita akan wannan tsari ba, kuma tana juya mutum don yayi ruyuwa akan ta, amma yana shiga cikin wata rayuwa zuwa wata rayuwar.
Hukuncin sallah da adadinta. Sallah nau'i biyu ce; ta farilla da ta nafila. Amma farilla ta rabu kashi biyu: farali wanda ke kan kowa da farali wanda wasu na dauke wa wasu. Farali wanda ke kan kowa; shine wajibi akan kowanne musulmi mukallafi na miji ko mace. Sune kuma salloli biyar, ALLAH ta'ala ya ce:
"Lalle sallah ta kasance wajibi abun yiwa lokaci ga muminnai" (Nisa'i: aya ta 103).
Kuma
ya kara cewa; "Kuma ba a numurce su da komai sai don su bauta wa ALLAH, suna masu tsarkake addini gareshi, kuma suna masu karkata zuwa ga addinin gaskiya su tsaida sallah kuma su bada zakkah, wannan shine addini tsayayye" {Bayyana: aya ta 5 }.
MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce: "An gina musulunci akan abubuwa biyar ne: Shaidawa babu abin bauta wa da cancanta sai ALLAH, kuma ANNABI MUHAMMADU bawansa ne kuma MANZONSA ne, da tsaida sallah da bada zakka". {Bukhari da Muslim, suka ruwaito}.
Nafi'u dan Azrak ya ce Dan Abbas shin ana
samu sallah biyar a Akur'ani kuwa sai ya ce: "Eh", sa'annan sai ya karanta fadin ALLAH madaukakin sarki:
"Tsarki ya tabbata ga ALLAH da maraice da kuma safiya, godiya ta tabbata a gareshi a cikin sammai da kassai lokacin dare da rana" {Rum: aya ta 15-16}.
Haka hadisin wani balaraben kauye, wanda ya zo wurin MANZON ALLAH ya ce masa: Menene ALLAH ya wajabta mini na sallah?. Sai yace: Salloli biyar". Sai ya ce; Ko akai wasu a kaina bayansu?, sai Ma'aikin ALLAH ya ce: A'a, saidai idan nafila ka yi". {Bukhari da Muslim}.
Yaushe ake umurtar yara da sallah?.
Ana umurtasu da sallah idan suka kai shekara bakwai, ana kuma bugun su game da kin yin sallah idan sun kai shekara goma, amma duka mara karfi, saboda Hadisi mai cewa:
"Ku umurci yaran ku da yin sallah idan sun kai shekara bakwai, kuma ku buge su akanta idan sun kai shekara goma, ku raba musu wurin kwanciya". [Abu Dauwd da Tirmizi suka ruwaito}.
Hukuncin wanda ya musunta wajabcin sallah:- Duk wanda ya musunta wajibcin sallah to kafiri ne, idan ya kasance cikin wadanda ba sa jahiltar sallar kuma kuma ko da ya yi sallar, domin ya zama wanda ya karyata ALLAH da MANZONSA da kuma ijma'in al'umma. Haka kuma wanda ya barta kawaida don
wulakantar da ita ko kawai saboda kasala, ko da ya tabbatar da wajibcin ta, domin fadin ALLAH ta'ala:
"To ku yaki mushirikai a duk inda kuka samesu". Har zuwa inda ALLAH ya ce: "To idan suka tuba, kuma suka tsaida sallah suka bada zakka to ku sakar musu hanya".
{Tauba: aya ta 5}.
Kuma an ruwaito daga Jabir ya ce: MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce:
"(Abinda ke) Tsakanin mutam da shirka da kuma kafirci (to shi ne) barin sallah" {Muslim ne ya ruwaito shi}.
Rukunan sallah:- Rukunan sallah goma sha biyar ne, ba'a barin su dagangan ko da mantuwa ko da jahilci.
1. Tsayuwa cur a sallar farilla ga mai iko. 2. Kabbarar harama, ita ce kuma: "Allahu Akbar". babu wani lafazin sai wannan.
3. Karatun fatiha.
4. Ruku'u.
5. Dagowa daga ruku'u da daidaituwa a tsaye 6.Sujjada.
7. Dagowa daga sujjada.
8. Zama tsakanin sujjada biyu. 9. Natsuwa, ita ce kuma kamewa.10. Tahiyar karshe.11. Zama domin tahiyar karshe. 2. Salati ga ANNABI (S.A.W)
13.Sallama.
Ita ce kuma mutum ya fada sau biyu,
"Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah". Ta farko kar ya kara da "Wabarakatuhu". Domin hadisin Abdullahi dan Mas'ud, lalle Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi ya kasance yana sallama daga damansa, "Asalamu alaikum Wa Ramatullah". Daga hagu kuma: Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah". {Muslim ne ya ruwaito shi}.14. Jerantawa tsakanin rukunnai.