Showing 45001 words to 48000 words out of 121675 words

Chapter 16 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17159

sassanyar Muryar Sheikh Aliyu cikin sallama. Gaba d'ayansu amsa masa sukayi suna d'agowa da kallonsa. Sanye yake cikin shadda boyal ruwan k'asa mai haske, sai hularsa itama ruwan k'asa amma tad'anyi duhu kad'an, hanunsa rik'e da waya da key d'in mota daya saya tun bayan aurensa da Maimunatu. Kallo d'aya zakai masa ka fahimci hankalinsa a kwance yake, yad'anyi k'iba kuma yay fayau dashi alamun akwai kwanciyar hankali da nutsuwa a duniyarsa.
'Daya bayan d'aya ya basu hannu suka gaisa bayan ya gaida malam dake kallonsa tamkar zaiga maganin warakar Jiddah a jikinsa.
Kallon malam Mustafa yay yana fad'in "Ashe kana nan?".
"Eh wlhy, tun bayan sallar la'asar nazo dama Na sanarma malam yarinyar da muka za6a".
"Masha ALLAH, to bara na shiga cikin gida Na gaidasu, idan kun gama Na dawo".
Harya mik'e malam ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunansa.
"Aliyu!".
"Na'am baba" ya amsa yana maida kallonsa garesa.
"Ku shiga kaida mustafa Falona akwai yarinya Mai lalura ka dubamin ita".
A sanyaye yace, "To Baba".
Malam Mustafa na gaba shi yana baya suka shiga, Jiddah Na kwance tayi ligif kamar matacciya, dan tunda su malam suka fita saita bar abinda takeyi ta nutsu, dama matsalarta maza ne kuma sun fita, amma su Malam Mustafa na shiga tahau fisge-fisge da kwalla k'arar datafi wadda takeyi a d'azun.
Hannu Aliyu yasa ya toshe kunnensa yana lumshe idanu danjin k'arar har cikin kwanyar kansa.
Ganin zata fice malam Mustafa yay saurin zungurinsa, idanunsa ya bud'e yana janye hannunsa daga kunnen, taku d'aya ya fisgo hijjabinta ya maidota baya ta fad'in yaraf tana wata irin jijjiga.
Tuni idonsa yayi jajur da 6acin rai (karku manta tunkan Aliyu yaje saudia yanada wajen saida magungunan musulinci dama), kallon Jiddah daketa faman takurewa a jikin bango tana k'yarma yayi, sai duk'unk'une fuskarta take a cikin hijjab. Yaja kujera ta roba dake gefe ya zauna d'an nesa da ita. Nuni yayma malam mustafa dake tsaye yana kallonsu da yabashi ruwa.
Malam mustafa ya mik'a masa ruwan daya d'ebo a Kofi, kar6a yay yafara tofa addu'a a ciki yana kallon Jiddah dahar yanzu take mutsu-mutsu, sai dai takasa yin k'arar sosai, dan ta k'udundune kanta a hijjab.
Ruwan Addu'ar daya watsa mata a jikine ya sakata zabura tana fasa wani kuka, bai sauraretaba ya cigaba, sai kuma mamuk'e bango take tamkar xata koma cikinsa.
Ransa a 6ace, amma hakan bai hana muryarsa fita da sanyiba yace, "Kai wane irin shaid'anine Mai taurin kai? Kana azabtuwa amma bazaka nunaba?".
Shiru Jiddah ko nace aljani bai maganaba, k'yalesa Aliyu yayi, ya d'auki Qur'an malam Mustafa ma haka suka Fara karatu cikin suratul bak'ara.
Karkarwa jikin jiddah ya cigaba dayi tana wata irin zufa maiban mamaki. "Babu inda zanje, bazan fitaba, nace bazan fitaba, ni kubar k'onani bazan fitaba......." wad'annan sune kalamun dake fitowa a bakin Jiddah tana kuka. Hakan kuma baisa su Aliyu dakatawaba, kusan mintuna talatin suna janyo ayoyin Ubangiji cikin surori daban-daban, sosai Jiddah ta jigata matuk'a, muryartama ko fita batayi, daga k'arshe kuma tama kwanta k'asa tamkar wata matacciya, cigaba da karatu su Aliyu sukayi, sai bayan kamar mintuna goma suka dakata saboda jin numfashin Jiddah ya daidaita.
Sassanyar ajiyar zuciya Sheikh Aly ya sauke yana rufe Qur'anin, ya kalli malam mustafa shima dake rufe nasa, "Mustafa wacece wannan d'in wai? Minene kuma matsalarta?".
Nisawa malam mustafa yayi fuskarsa da tsantsar damuwa yake fad'ama Aliyu komai game da Jiddah, harma yunk'urin had'ashi aure da malam yay da ita tun farko, amma suka iske mahaifinta yamata miji".
Shiru kawai Aliyu yayi yana kallon wani waje daban, shi mutumne mai tsananin tausayi da shiga damuwa akan damuwar wani, tuni hawaye harsun cika masa idanu, ya zari handkerchief daga aljihunsa yay saurin tsanesu. Batare daya yima malam mustafa maganaba yatashi ya fice.
Inda su malam suke zaune yad'an kalla kafin ya kauda idonsa gefe dan kar malam ya fahimci yayi kuka, "Baba ina zuwa su jirani".
"To saika dawo Ali" 'malam yafad'a cikin murmushi'.
Yana fita malam Mustafa ya fito, kallonsa malam yay "Mustafa miya farune?".
"Malam tasamu barcine, inaga zai had'o magungunane".
"To Alhamdllh, ALLAH kai mana maganin abinda yafi k'arfinmu, harma wanda muke gani munfi karfinsa".
Amin malam, suka fad'a gaba d'aya falon harsu Uncle.
cikin zolaya malam yakuma kallon mustafa yana cewa, "Halan abokinka yauma halin ya ta6a?".
Malam mustafa yay murmushi yana bama malam amsa, "Malam ai wannan wajib ne ga Aliyu, sai dai in Abu bai raunana zuciyarsa baneba".
"To ALLAH ya kiyaye, Yaro ya maida kansa kamar wani mace, Abu kad'an yafara zubda hawaye".
Duk murmusawa sukayi har su Uncle yahaya dake zaune suna saurarensu. Sosai Uncle yahaya yakumajin k'aunar Aliyu da samun nutsuwa akan maganar da suka gama da malam yanzu.

*********

Kusan mintuna talatin da fitar Sheikh Ali saigashi ya dawo d'auke da farar Leda madaidaiciya, zama yay yana bud'e ledar, dalla-dalla yayma Uncle yahaya bayanin yanda Jiddah zatayi amfani da magungunan, kafin ya d'ora da fad'in, "Ko kunada damar tura wani can gidan data baro yad'an mana wani bincike? Dan ina zargin kamar akwai abinda aka ajiye ko aka binne dake saka aljanin koda yatafi yake dawowa jikinta, abinda na lura dashi kuma kamar shine ke tsoratata inhar tasamu kusanci da namiji, alamun shine tushen sihirin jikinta, sai kuma mun samu rusa wancan kullin nasu da izinin ALLAH koda komai zai dai-daita, sadai insha ALLAH indai tacigaba da amfani da wad'annan magungunan sannan ta tsare yin azkar da salla akan lokaci, ta kiyaye yawo babu d'ankwali da yawo babu takalmi a tsakar gida, ta kiyaye sauraren wak'a ko shiga bayi batareda tayi addu'a ba, da yawaita kusanta kanta da Qur'ani, to muna fatan dacewa wajen samun sauk'i insha ALLAH".
Alhmdllh kowa ya shiga maimaitawa da fatan dacewa. Uncle yahaya ya d'ora da fad'in "Zamuga yanda za'ayi a bincika d'in insha ALLAH, mungode sosai ALLAH yak'ara girma da hak'urin taimakon bayin ALLAH"..
Amin duk suka amsa dashi, Aliyu daya amsa a la66ansa ya mik'e yana fad'in "Zaku iya tafiya da ita".
Sun amsa da to, shikuma yay yunk'urin shigewa cikin gida.
Da sauri Uncle yahaya yace, "Malam bakai maganar kud'i ba ai".
Murmushi Aliyu yayi, batare daya juyoba yace, "ALLAH yabata lafiya" kawai ya ida shigewa.
Uncle yahaya ya maido kallonsa ga Malam zaiyi magana. Murmushi malam yayi shima, "Malam yahaya wane maganar kud'i kuma? Tunda kaji yace haka bazai amsaba, kuma ai yima kainema, ALLAH yabata lafiya dai mu shine fatanmu".
"Amin malam, ALLAH ya saka da alkairi, ya albarkaci zuri'a, ALLAH ya k'ara girma".
Kowa ya amsa da amin.

Uncle yahaya yakai Jiddah dabatasan mi akeba mota, har k'ofar gidan malam da Malam Mustafa suka rakosu, suna niyyar tafiya Aliyu ya fito, hannu kawai ya d'aga musu ya wuce domin haramar d'aura alwalar magriba dake gabatowa.


???????????


Su Umma na zaune zugum-zugum itadasu walida da Maman Sadiq da Aunty Nafisa wadda tazo sake duba jikin Jiddah ta iske kuma basanan saita tsaya.
Alkubus d'inma da Jiddah ke k'ok'arin d'aurawa sai Aunty Nafisar ce ta k'arasa, dan Umma ma takasa ta6uka komai tunda aka fita da Jiddah.
Su Zarah kam tunda suka dawo makaranta sukaji halinda Y'ar uwarsu ke ciki sai suka hau kuka, alkubus d'inma tunda aka gamashi babu Wanda yako kallesa.
Jin tsayuwar mota ya sakasu mik'ewa a tare suka lek'a.
Sune suka shigo da jiddah wadda take barci har yanzu. Uncle yahaya ya biyo bayansu da ledar maganin bayan yayima malam alfah godiya sosai.
Shima yana ajiye ledar fita yay massalaci, dan ankira sallar magriba.
Jiddah kam d'akin Umma aka kaita aka kwantar da ita, suma suka fito dan suyi haramar sallar magriba, koba komai hankalinsu yad'an kwanta..............???



*_??jiya kwace kodai Abba zakarine ya biya bashin da ake binsa dani????, wani uzirine ya tasomin batareda Na shirya masaba??, messages d'in PC ma sai yanzu zanje Na amsa mukusu tun kusan Na kwana uku??¡â, wad'anda suka turo kumin afuwa yanzu Zan amsa insha ALLAH.??_*

Ina fata duk kuna lafiya?.







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*??????
[12/5/2019, 8:58 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[21?22]_*


..............Bayan Uncle yahaya yadawo daga salla suka zauna tattauna maganar Jiddah, bayani yay musu akan dukkan abinda ya faru, kafin ya d'ora da batun malam Aliyu na bincike a gidan Alhaji Garba.
Kowa ya jinjina maganar, domin wannan abune mai matuk'ar wahala agaresu, dama can babu wata alak'ar dangantaka a tsakaninsu, gakuma wannan batun na Jiddah daya gitta, Abba kam sunsan bama zai basu had'in kaiba, k'ilama idan sun masa bayani ya rusa komai, Hindu kam da ace abokiyar zamace ta kwarai dasai ta taimakesu tunda ita gidan zuwantane.
Sunta tattauna mafita amma basu samuba, duk hanyar da suka k'ulla saisuga bazata 6illeba. Dole dai suka ajiye zancen akan sai sunyi tunani.
Sund'an samu kowa yaci abinci, amma zukatansu dank'are da neman mafita suke.


???????????

Tunda suka idar da Sallar Magriba sai yayma malam sallama yanufi gida, dan yasan d'alibai nacan na jiransa, fatansa sallar isha'i ta riskesa acan.
Kamar yanda yay fata kam saiya dace, duk da bawani nisabane tsakanin gidansa dana malam d'in, ya iske ana kiran sallar isha'i.
Alwala ya sake ya shiga masallaci. Bayan an idar sukai zaman karatu. Bai samu shiga gidaba sai kusan goma saura.
Cikin Sassanyar muryarsa yay sallama, Maimuna dake kwance cikin kujera tana kallon Sunna tv ta amsa tana tashi zaune, tsaf take cikin kwalliya tanata k'amshi, murmushi suka sakarma juna, yayinda Aliyu ya bud'e mata hannayensa alamar tazo.
Ahankali tataso ta shige jikinsa tana fad'in "Nayi kewarka Annur".
"Nima haka habibati". Malam Aliyu yafad'a a hankali cikin kunnenta.
Fuskarta d'auke da murmushi har yanzu ta d'ago ta kallesa, goshinta ya sumbata da la66anta, kafin a hankali yace, "Mikika tanadarmin sarauniya?".
Cikin kashe ido da murya tace, "Komaima Na tanada maka harda abinda malam ya hana fad'a".
Dariya sukayi a tare, Aliyu yaja hannunta yana fad'in "Zomuje ki fad'amin, ai bazan fad'ama malam kin fad'aba".
"Yaya Ali kacika wayo wlhy".
"Aunty Maimoon kin cika wayo kema al". 'Aliyu yay mahanar suna ida shigewa'.
Da taimakonta yay wanka sannan suka dawo falon, kullum dare fruits sune abincin Aliyu, gab da zai kwanta kuma yasha had'ad'd'en shayi irin Na larabawa Kofi d'aya, dan haka Maimunatu take k'ok'arin ganin tamusu nutsatstsan yanka.
Sosai ya maida hankalinsa ga Tafseer d'in da akeyi a Sunnah tv Wanda ya tarar Maimuna na kallo, harta gama ajiye dukkan abinda zai buk'ata hankalinsa naga tv.
"Yaya Aliyu". 'Maimuna tafad'a ashagwa6e'.
Juyowa yay ya kalleta batare da ya amsaba, da ido ta nuna masa kayan gabansa. Ajiyar zuciya yad'an sauke kafin ya sauka k'asa saman kafet ya zauna, itama zama tayi, sunashan kayan marmarinsu suna kallon tafseer, lokaci-lokaci sukan jefi junansu da murmushi dakuma magana idan ta kama.


???????????

Jiddah bata farkaba sai kusan k'arfe goma, lokacin Mijin Aunty Nafisa yazo ya d'auketa, su Uncle yahaya ma suna shirin tafiya, amma farkawar tata saita dakatar dasu.
Alhmdllh normal ta farka, dukda tanata ra6e-ra6e saboda ganin Uncle yahaya.
Zarah ce data had'a Mata ruwan wanka ta taimaka Mata zuwa ban d'aki, bayan ta shiga ta dawo waje zaman jiranta, bata wani dad'eba ta fito ta d'aura alwala sannan ta koma d'aki, bata shafa maiba sai kayan da Walida ta ajiye mata ta canja tahau ramuwar sallolin da bata samu yiba.
Su Uncle yahaya basubar gidanba saida sukaga taci abinci da fara amfani da wasu magungunan ta koma ta kwanta saboda jikinta duk babu k'wari.
Sallama sukaima su Umma suka wuce gida.


¡ï¡ï¡ï

Washe gari normal Jiddah ta tashi, wandama bai saniba bazaice tashiga wani haliba jiya, koda Uncle yahaya yazo dubata d'aki ta shige ta 6uya, bai damuba shidai, dan yasan bawai yin kanta baneba. Sallama yay musu ya wuce kasuwa.
Da d'an k'arfin gwiwa su Zarama sukai shirin makaranta suka tafi.

Tundaga wannan lokaci abubuwa sukaima Jiddah sassauci, dukda har yanzu batasan namiji a kusa da ita, amma bata firgita ko fita hayyacinta danta samu kusanci dasu, magani kuma da ruwan addu'oi daya k'are ake aiko mata wani daga gidan malam, malam mustafa da kansa yazo yaymata maganar komawa makaranta saboda sunason sudai taje Saudia d'in, dan tunda sukaji batada aure sai suka ajiye batun waccen da suka za6a suka maida burunsu akan Jiddahn.
Y'an ajinsu sunyi farin cikin dawowarta, musamman ma Madina.
Kuma himma sukai wajen Trining d'in Jiddah yanda zata kuma samun gogewar ilimi sosai dabin k'a'idojin gasar, kuma tana k'ok'arin maida hankalinta sosai, dukda duk lokacin da malami zai shigo musu karatu Jiddah batada sauran nutsuwa harya fice, amma haka take dakewa da yawan Addu'ar samun kwarin gwiwa harya fice.
Duk dokokin da Aliyu yace ta kiyaye Alhmdllh tana iyakar k'ok'arinta, dama can ita bamai wasa da irin abubuwan nan baceba, zaman sihiri jikinta kawai k'addarace daga ubangji Mai jarabtar Bawa aduk sanda yaso, akuma lokacin fayaso.

???????????

Shirye-shiryen tafiya gasarsu ya kankama, dukda duk wannan hidimar da akeyi Abba bai saniba, rabonshi da zuwa gidan kusan watanni hud'u kenan, kuma yana zaune a garin babu inda yaje.
Ganin yarage saura kwana biyu su Jiddah su tafi Uncle yahaya yaje har gida ya sameshi da maganar.
A harabar gidan ya iske su kalifa na ball, kallo d'aya sukai masa suka d'auke Kansu tareda cigaba da kwallonsu.
Murmushi Uncle yahaya yayi kawai shi yana k'arasawa garesu da fad'in "yarana kuna lafiya?".
Cike da rashin kulawa suka amsa suna cigaba da harkar gabansu. "To ALLAH ya k'yauta" uncle yahaya yafad'a yana kamo hannun kalifa domin tambayarsa. Amma sai yaron yay azamar janye hannunsa yana wani 6ata fuska. Uncle yahaya baice komaiba sai tambayarsu Abba nanan da yay. Muneer kawai ya amsa da eh, amma Hassan da Hussain da kalifa tunima sun koma kan hayaniya akan cin Ball.
Haka Uncle yahaya ya k'arasa ciki yana tausayin yayansa akan wad'annan yaran marasa tarbiyya, acikinma Hajia Hindu yatsine-yatsine taita masa, tana shirin cewa Abba baya gida saigashi ya fito saboda jin muryar d'an uwansa.
Zama yay suka gaisa Uncle Yahaya ya fad'a masa abinda ya kawoshi.
Kallonsa Abba yay rai a 6ace, "Yahaya kace min dama wannan shine dalilin dayasa kuka kashe Mata aure?".
Uncle yahaya yay murmushin takaici yana gyara zamansa. "Yaya ba wannan maganar bace ta kawoni please, nidai yanzu amincewarka kawai da addu'arka muke buk'ata".
"Yo inda amincewarsa ake buk'ata Aida tini amfad'a masa basaida lokaci ya k'ureba". 'Hajia Hindu tai maganar tana gatsine-gatsine'.
Murtike fuska Uncle yahaya yayi yana watsa mata wata muguwar harara, "Kinji na sakoki a cikin zancena Maman kalifa? To ki Kama kanki wannan ba huruminki baneba, kibari idan mungama Na wuce saikiyi keda shi".
Harara ta watsa masa tabar falon tana jan tsaki. Shima Uncle yahaya tsakin yayi ya mik'e.
Abba yace, "Ni wlhy ina mamakin yanda kokad'an kaida Hindu bakwa zama inuwa d'aya, nasan dai yagana ce kawai ke rura wutar k'iyayya a tsakaninku kullum tamkar kuna ganin hanjin juna".
Baki Uncle yahaya ya ta6e kawai, "Yaya nawuce ni".

Uncle yahaya bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login