Showing 51001 words to 54000 words out of 121675 words
tasamu k'aututtukan dasukafi Na Azra tareda fatan alkairi, inda y'an saudia sukai murna, dukda sunyi burin zuwa Na d'aya suma.
Jikin Jiddah duk yay sanyi, azatonta ko ancire sunantane, sai tajiyo Ana kwala kiran sunan *Jiddah Zakari Yaro* *Najeriya* sosai jikinta yahau rawa, saida taimakon Ummusulaim dasuka zama k'awaye ta iya mik'ewa, tafiya take tamkar zata fad'i saboda sassarfa da idanun mutane, ga lalurarta ta tsoron kasancewa muhali d'aya da maza, danma Ubangiji ya sauk'ak'a lamarin..
Dak'yar ta iya k'arasawa garesu. Doguwar Addu'a da jinjina ga Jiddah da iyayenta da malamanta da k'asarta sosai akayi, kafin a damk'a Mata k'autar nasararta dakuma k'yaututtuka da malamai daban-daban wad'an suka fito a k'asashe daban-daban, da manyan attajiran da suka halarci wannan gagarumar Mubabaqa. Kuka kawai Jiddah ta sakamusu harda sheshsheka, inda mutane dayawa suke tayata musamman ma mu y'an Najeriya damuke cikin farinciki.
Aliyu dake murmushi yasaka handkerchief ya d'auke hawayen da suka cika masa idanu, hakama Uncle yahya, su malam mustafa malam Abdul-ra'uff, Sarkin musulmai da sauran malamai dasuka halarci taron y'an Nigeriya duk suna tare da tsantsar farinciki, Aunty Siyama jitake tamkar k'anwarta ciki d'aya, dad'i dukya lullu6eta.
Abubuwa sunciga da gudana kafin taro ya tashi lafiya, masu murna nayi masu kuka nayi.
A ranar su Jiddah suka baro birnin Riyadh zuwa Makkah.
Kowa saiji yake da Jiddah, sai nan-nan su malam Abdul-ra'uff sukeyo da Jiddah, yayinda dad'i ya cikata, gata ga Sarkin musulmai da manyan malamai Na k'asarta da takejin labarinsu kojin wa'azinsu a redio ko TV.
Saidai abinda yabata mamaki bataga malam Aliyu ba tun barowarsu Riyadh, dan badashi suka taho Makkah ba, batadai tambayi kowaba tayi shiru da bakinta, amma haka kawai taji tana kwad'ayin ganinsa kodan tamasa godiyar Handky daya bata ranar, dan dataji d'an Najeriya ne kuma d'an mutumin da zuciyarta take kauna da girmamawa sai dad'i ya kamata, ashema tana sauraren tafseer nasa sosai batasan shi baneba sai yanzu.
Uncle yahya kam fad'a muku irin farin cikin daya tsinci kansa ai 6ata lokacine ma.
Labari kuwa yakai Najeriya tuni, sai hotunan Jiddah ke yawo a jaridu da televisions.
Lokacin da zance yakai kunnen su Umma ai kuka kawai ta sanya Na dad'i, tuni labari yagama zagaye dangi, kowa burinsa Jiddah tadawo ya k'ara ganinta. (Saikace sun manta fuskarta??), sundake sai sayen jarida suke suk'ara ganinta, su Zarah ma har Umma suka sayomawa, aiko tasaka k'asan gado ta 6oye bayan sungama Karantawa, wai zata adana tarihi????. Zumud'in dawowar Jiddah garesu dukya cikasu.
Lokacin da aka nuna Jiddah a labarai Abba da Hajia Hindu suka gani Hajia Hindu rud'ewa tayi, shikansa Abba yau saiyaji wani iri, yarinyarsace a tsakkiyar manyan mut¨¤ne da duniyar musulinci ke ji dasu, duk surutan da Hajia Hindu kemasa baibi takantaba yatashi yashige d'akinsa saboda wani jiri dayakeji yana Neman kwasarsa.
hakance takuma kasancewa a gidan Alhaji Garba, dan gaddama suka kwaso suka dire akan ba Jiddah data zauna a gidan baceba, yayinda Ashir keta rantsuwa da ALLAH itace. Alhaji garba yace bai yardaba saiya bincika.
Yayinda wancan cakwakiyar ke faruwa a Najeriya Su Jiddah suna can suna gudar da Umrah a Makkah, tareda zagayen guraren tarihi domin k'arin ilimi, yayin da daga baya kuma suka tattarasukak nufi Birnin Madina.
Kwanansu bakwai a Madina Gari Mai tarin Ni'ima da dad'in zama, Wanda duk muminin daya shiga baya fatan yaga ya fita, kuka dai Jiddah ta shashi yayinda taganta gaban kabarin MANZON ALLAH (S.A.W) da ahalin gidansa.
Ranar jinta take wata iri daban tamkar ba itaba.
Duk inda yakamata suje wajen tarihi malam Abdul-ra'uff shine jagoransu, itadai Jiddah tana k'ara mamaki Ina Aliyu ya shiga?.
Gaba d'aya kwanakin su Jiddah ashirin Cif da tafiya suka juyo k'asarsu ta haihuwa Najeriya cikeda farin cikin d'umbin nasaarorin da suka k'unso.............???
*_Barkanmu da Juma'a sweet sister's??????????_*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/7/2019, 2:43 PM] ??Noorunnisa??: *_
[12/7/2019, 11:57 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[25?26]_*
............Saukar dare su Jiddah sukayi, hakanne yasaka masu tarbarsu suka kasance k'alilan, tana farin cikin dawowa ga ahalinta gefe kuma na zuciyarta na kewar k'asa mai tsarki, jin hawaye kawai tai suna gangarowa a kumatunta, wanda harga ALLAH batasan yaushene suka fara saukaba. Muryarsa Mai sanyin nan ta daki kunnenta.
"Yakamata a nad'aki sarauniyar kuka ta k'asarnan".
Gabantane ya fad'i, har abadan bazata mance wannan sassanyar muryarba, da sauri ta d'ago idanunta ta saukesu a kansa.
Janye idonsa yayi daga gareta tareda d'ora Mata handky d'in hannunsa saman trolley d'in gabanta ya wuce.
Da kallo kawai ta bisa tana sauke wani kasalallen numfashi a hankali, sanye yake cikin shadda ruwan gwaiduwar kwai, yazuba dukkan hanayensa a aljihu, dukda darene hakan bai hanata shaida k'yawun haibarsa ba, mamaki take dama ashe ya dawo Najeriya shiyyasa bata sake ganinsaba a can.........
"ALLAH ya tabbatar". 'Muryar aunty Siyama ta katsema Jiddah tunaninta'.
Janye idanunta tayi daga kan Sheikh Aliyu daya k'arasa suna gaisawa da Uncle yahya.
Jiddah ta share hawayenta tana murmushin yak'e, "Aunty addu'ar mi kikeyi?".
"Ta abin alkairin danaga yana Neman k'ulluwa mana Jiddah".
Jiddah bata fahimci inda Aunty Siyama ta dosaba, dan haka sai tai shiru. Itama Aunty Siyamar bata ja zancenba daga nan, saima haramar tafiya da sukeyi, dan dama sun tsaya jiran Malam ne dake gaisawa da mutane.
Har gida sukaima su Jiddah rakiya.
Su Umma suna zaune jiran isowar su Jiddah, dan Uncle yahya ya sanar musu ta waya, dan haka sunajin tsayuwar motoci suka fito cikeda d'oki.
Tuni farincikin ganin juna yasa sun manta da kowa, murmushi Aliyu yayi yana lumshe idonsa, ba k'aramin birgeshi wannan family sukaiba, hakama Malam sun matuk'ar birgeshi, Aunty Siyama kam tuni taji kewar mahaifiyarsu ta mamayeta.
Sai Uncle yahaya ne ya tsaya sukayi sallama da mutane, amma su Jiddah tuni sunyi ciki.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Barci dai yau sai 6arawone ya d'auki wannan ahali, washe garima da wannan farin ciki suka tashi, kafin kace mi gida ya d'inke da y'an taya murna, aunty Nafisa kam ai tunda farar safiya ta iso.
Haka wannan yini Yakuma kasance musu cikin kar6ar bak'i, ita Jiddah ma sai kunya takeji.
Dangin Umma ma sunata kiran waya, kawu Bunami (yayan Umma) yace Jiddah tafad'i komi take so indai baifi k'arfintaba zai Mata, dan d'ansa Banu da autar su Umman Balu suna nan zuwa Kano.
Rasama abinda Jiddah zata za6a tayi, dan haka tabashi za6in ya saya Mata komi yaga yamasa. Albarka dai tashata wajen wajen kakarsu.
Rana ta uku da dawowar su Jiddah saiga Abbah suna tsakar gida suna hira da innarsu Balu ya shigo, duk shiru sukai sai Balu d'ince dake murmushi. Shima saiya Saki fuskarsa yana fad'in "Ah ah yau Balu ce a kanonmu haka?".
"Aiko nice yayanmu, ai tunda nazo nake cigiyarka akace kayi tafiyane".
Cikin in ina yake fad'in "E...eh...eh ta..fiya nayi wlhy, jiya na dawo da daddare shiyyasa".
Su Zarah dake zaune kawunansu a k'asa duk saida suka d'ago suka d'an kallesa saboda jin k'aryar da ya sharo babba dashi.
Yayinda shikuma yad'an hararesu yacigaba da gaisawa da Balu.
Duk abinnan dake faruwa Umma na cikin kicin tana jinsu, amma ko tarima batayiba, saida taji shigarsa d'aki sannan ta fito tabi bayansa da ruwa d'auke a hannunta.
Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta gefe tana gaisheshi, jin a yanda ya amsa saita kuma kallonsa, harma ta kasa hak'uri saida tace, "Lafiya kuwa?".
"Lafiya lau, mi kika gani ne?".
"Babu komai". 'Umma ta fad'a tana mik'a masa ruwan'.
Soyake yay Mata murnar nasarar da Jiddah ta samu amma ya kasa, sai mulmula maganar yake a zuciyarsa. Tsaf Umma na lura dashi, amma sai tayi tamkar bata ganshiba. Daga k'arshe daya rasa ta inda zai kamo zance saiya maida akalar maganar kan zuwan Balu. Itadai Umma eh a'a shine amsarta dashi, harya k'araci zamansa yay mata sallama ya tafi.
Sosai hakan yayma Umma da Jiddah ciwo a zuciya, koba komai yakamata ya nuna murnarsa ga nasarar data samo, kodan ma darajar Addininta data samo nasarar a dalilinsa, amma saiyay k'ememe.
???????????
"Aliyu kasan miyasa na kiraka kuwa?".
"A'a baba".
Zama malam ya gyara sosai yana murmushi, "Wato Aliyu abari ya wuce shike kawo da rabon wani Na hango maka".
Kallon malam, Aliyu yayi dan bai fahimci inda zancen ya dosaba.
Malam yakumayin murmushi "Zancen yarinya Jiddah nake magana wadda mukaje saudia, wannanfa damace akaro Na biyu tazo mana, Na fahimci tun a saudia akwai wani Abu a ranka game da ita, amma sakaci irin naku da wautar k'uruciya yasaka yima lamarin rik'on talala Wanda lallai idan kayi wasa zaka ciji yatsa a daga baya. Zancen danake maka yanzu haka tun muna saudia naji Sarkin Musulmi yana waya da Mai d'akinsa akan sha'awar naimawa d'ansa auren Jiddar".
Da sauri Sheikh Aliyu ya kalli malam cikin waro fararen idanunsa.
"Ba ido zaka zarominba, kana sontane? Kokuwa hasashenane kawai nakeyi?".
K'asa Sheikh Aliyu ya maida kansa yana susar k'eya, fuskarsa d'auke da murmushi yace, "Inason na cika maka burinka natun farko Baba, sannan harga ALLAH yarinyar ta kwantamin arai".
"Alhamdllh Aliy, lallai nayi farin ciki, ALLAH yaymaka albarka. Tofa a wannan karon bazamuyi sanyaba, dan insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zanje musami mahaifinta da zancen, sonake ana gudanar da taronan da za'ayi washe gari a d'aura auranku"..
Acikin Zuciyaryarsa yace, "ALLAH dai ya tabbatar Baba".
¡ï¡ï¡ï¡ï
Tun a ranar malam baiyi sanyaba ya Kira Uncle Yahya sukayi maganar.
Wannan zance ba k'aramin farin ciki ya saka Uncle yahya ba, dan haka shima baiyi sanyaba ya doka waya zuwa Adamawa domin gayyato kawunansu guda uku suzo ayi dasu, dan baya son Abba ya sake basu Matsala a wannan karon. Sannan yakira Abba ya Sanar masa shima, da to kawai ya amsa saboda a time d'in suna tare da Hajia Hindu.
Washe Gari tunda asubahi su Kawu Safiyanu suka baro Adamawa kuwa, cikin amincin ALLAH saigasu sun iso da wuri, sun huta sannan sukaje suka gaida Umma da tayata murna, Albarka dai Jiddah dasu Zarah sunshata. Uncle Yahya dai bai fad'a Mata abinda ya kawosuba, dan yafison a kammala komai sannan.
Daga nan gidan ABBA suka d'unguma, dukkan Abinda za'a iya buk'ata Na tarbar bak'i saida Uncle yahya ya tanada daga gidansa suka tafi dashi, dan baya buk'atar abinda zai 6ata ransa a gidan Abba.
Abba yayi mamakin ganin su Kawu Surajo sosai, dan haka yayta bin Uncle yahya da kallon tuhuma, yayinda shikuma yay biris tamkar bai gansaba. Sunyi kusan zaman mintuna talatin kafin hajia Hindu ta shigo gaishesu tana wani yatsine-yatsine, babu Wanda yabi takanta, dan Uncle yahya ma ko kallo bata isheshiba.
Tunda ta fita take masifa wai Uncle yahya yakawo su Kawu Bliya maula, duk sunzo sun cika Mata gida da warin talauci.
Tun Uncle yahya da Abba na zuba idon ganin hajia Hindu ta kawo ruwa har suka fidda ransu, dan haka Uncle yahya yamik'e ya fita, mintuna kad'an yafara shigowa da kulolin abinci, dandanan ya cika tsakiyyar falon da kayan arzik'i, ko zama baiyiba daga ajiye Na k'arshe sukaji shigowar mota. Hakanne ya saka Abba had'iye tambayar dake ransa suka mik'e suka fita domin tarbo su malam.
Gaisuwa sukai cikin mutunta juna, kafin Kai tsaye malam da kansa yafara fad'in abinda ya kawosu, dan a ganinsa da zafi-zafi akan daki k'arfe.
Kafinma Abba ya tofa nashi tuni su Kawu Safiyanu sun bada Jiddah tareda addu'ar sanya alkairi.
Dad'i ya cika zuciyar malam, cikin fad'ad'a murmushinsa yace, "Muda mukazo Neman izinin Fara Neman so Kuma sai ace amma bamu?".
Kawu Surajo yay Y'ar dariyarsu ta manya, "Ai malam Kai ubane, kimarka tawuce kazo Neman izinin zance kawai ka tafi, dan kaima mai iya aurar da Hauwa'u ne ko bama a wajen, to balle kuma babban mutum irin Sheikh Aliyu yaga yarinyarmu yace yanaso harma a tsaya jan dogon zance, badan badan bama mu saimuce ama d'aura ka tafi da amaryar kawai".
Dariya suka sanya gaba d'aya suna musabaha, Malam yace, "Wlhy da hakan zata kasance danayi murna kuwa. Amm to indai hakane mizai hana indai bamuyi gaggawaba ranar juma'a ta sama kawai a d'aura".
"Malam indai hakan yamaka tomu bamuda ja wlhy, tunda dai yarinyarnan ta ta6a aure, banga wani abun jan jikiba ma". Uncle yahya ne Mai maganar'.
Atake kowa yayi na'am da wannan magana, ganin haka shima Abba saiyabi ayarin masu amsawa cikin yak'en dariya. Take annan malam ya ajiye sadaki naira dubu d'ari biyu, amma sai su Kawu Bilya suka nemi a rage.
Malam yace, "Lah-lah bazamu rage ko sisiba, k'arawama yakamata muyi, wato abinda muka kasa fahimta da 6al6alcewar aurarrakinmu na wannan zamanin da sakaci Na yawan sakin aure to k'arancin Sadaki yana ciki, inda za'a ajiye dukkan bidi'oi dake gudana yanzu a shagalin bukukuwa aringa tsawwala sadaki ga masu aure to lallai sai ansamu sauk'i sake-saken aure. Yaro ya biya dubu hamsin ko talatin sadaki, da anyi aure taimasa ba dai-daiba saiya sauta, idan anyi magana yace ga matanan ledar ruwa tafisu wahala, to yasan daya samo y'ar dubunsa d'ari biyu ta Isa masa wani auren, inda ace ana saka musu sadakin Mai tsauri mahaifin yarinya yace baya buk'atar kowacce bidi'a amma sadakin y'arsa dubu d'ari biyu ko uku ko hud'u to wlhy saisunji shakkar sakin, dan sunsan kafin su tara wani sadakin sun jigata, sannan za'a canja tunaninsu ga wanann shaid'ancin Na fati-fati dasukeyi, kunga mutum da kud'in sadaki zaiji kokuwa da kud'in bidi'ar aure?. To ni yarinyata jiddah ma ta girmi sadaki dubu d'ari biyu wlhy, kaf yarana ban yarda abani k'arancin sadaki a kansuba, bankuma yarda mazan sukai mafi k'aranci ba suma, sannan bana biyama yaro sadakinsa, zandai taimakeka da wani abun, amma kud'in sadaki ka nemo kayanka. Wannanma Aliyun da kansa ya bada abinsa".
Kai su Kawu duk suka shiga jinjinawa cikeda gamsuwa da maganar malam d'ari bisa d'ari, dajin a ransu suma zasuyi aiki da wannan shawara Mai k'yau da nagarta gamai hankali.
Fita sukayi sukabar su malam suci abinci, Wanda saida uncle yahya yayta rok'onsu sannan suka amince.
???????????
Bayan tafiyarsu Malam su Kawu Surajo tasa Abba gaba sukayi zuwa gidan Umma, lokaci Zarah da Jiddah basannan sunje gidan Aunty Nafisa, walida da Umma ne kawai a gidan.
Mamaki sosai Umma tayi, ita tunaninta ma ko dama Abba ne yakai k'ararta itada Uncle yahya wajen su Kawu Safiyanu akan barin Jiddah taje Saudia. Amma da suka zauna sai taji jawabin nasu bai doshi canba, tuni farinciki ya lullu6eta, dan ita wlhy d'ari bisa d'ari ta amince da wannan zance, saidai tabisu da addu'ar ALLAH ya sanya alkairi kawai.
Abba dai tunda aka zauna baice Uffanba, hakan kuma bai damu Umma ba, Ana cikin maganarma saiga su Jiddah sun dawo. Da hanzari tayi niyyar komawa cikin rawar jiki, Uncle yahya yace, "Daure ki shigo kinji Jidodona, k'arfafa zuciyarki kinji Y'ar albarka duk iyayenkine".
Jikinta na tsuma Zarah ta kamo hannunta suka ida shigowa, tuni harta had'a zufa, muryarta na rawa ta gaishesu.
Kawu Surajo yace, "ALLAH ya yaye miki kinji Hauwa'u, ALLAH ya warware wannan k'ulli cikin hikimarsa da rahamarsa, Yakuma gaggauta saka miki".
Da amin duk suka amsa, sai dai banda Abba dayay shiru