Showing 60001 words to 63000 words out of 121675 words
suka had'a Ido, saurin janyewa tayi ta maida kanta k'asa.
Murmushi yayi yana fad'in "Ahaka ake za6en miji dama?".
Kuma k'asa tayi da kanta jikinta na wata tsuma. Tsaf ya lura da halin da take ciki, sai tausayinta ya k'ara kamashi, har tunani yake Yaya zasu kwashe idan ya tuno matsalarta......
Tunaninsa ya katse sabodajin tarinta, Wanda da alama yawune ya sark'eta. Ruwan da walida ta zuba masa yasha rabi ya d'auki sauran da hanzari yamatso kusada ita yana jera mata sannu.
Ansa tayi Tasha, idanunta harsunyi jajir sun cika da kwalla, sai kuma jera Mata sannu yake tana d'aga masa kai, saida tarin yalafa sannan yakoma wajen zamansa ganin jikinta na rawa.
"Ki daure kina k'arfafa zuciyarki dan ALLAH".
Kanta tad'an d'aga tana share hawayen da suka cika Mata ido.
"Magana kuka, karatu kuka, Anya kuwa ked'in jarumace?".
Batareda ta saniba tad'an turo bakinta, dan taji haushin maganarsa.
"Yi hak'uri Malam, maida bakin nagani, Bari sai nan da kwana uku amma ba yanzuba".
Bata fahimci ina ya dosaba, amma hakan bai hanata jin kunyar maganarsaba.
Murmushi yasakeyi yana kallon agogonsa silver dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, "Bara nayi abinda ya kawoni, dan wannan hajiyar bata shan inuwa d'aya da jinsina. Malam Jiddah nasan zakiyi mamakin shigowar maganar aurenmu da wuri, gashi kuma maganar so bata had'ani dakeba, wannan hukuncine Na ALLAH dakuma cika burin mahaifina dayay tunkan aurenki na farko, cikin Amincin Ubangiji nima dana ganki sainaga kin cancanci zama matata, wannan yasaka iyayena suka shigo da zafi-zafi, dan hausawa kance da safe ake Kama Fara, anzo nema min izinin neman so a gareki saikuma akamace an bani, na jinjinama dattako da halin girma irin Na iyayenki, dan sun tabbatar mana sud'in iyayene nagari, yanzu dai fatan da zanyi shine ALLAH yasa Na kar6u, karna zama macen shige, Ku mata kunce bata kwarjini".
K'asa Jiddah tai da kanta takasa magana.
"Ki daure kice wani Abu, dan ayanzu kinada ikon za6arma kanki miji a matsayinki na wadda ta ta6a aure".
Nanma bata iya cemasa komaiba, amma yanayinta yabashi amsar tambayarsa.
Numfashi ya sauke, "To koba'a amsamin a bakiba nasamu sak'on zuciya, ALLAH yay miki albarka, kunya adone na d'iya mace, hakama jan aji mayafine Na kimarku, kin kuma tabbatarmin kinada banbanci da zawarawa na yanzu, wad'anda suke ganin sunsan komai idonsu abud'e yake akan namiji, Abu nabiyu shine inada Mata, kuma maganar gaskiya inasonta sosai, saboda tanada halaye Na kwarai da tarbiyya, sannan bata gazamin a komaiba Na rayuwar zamantakewa da hak'k'ok'ina na aure, hasalima har yanzu amarci muke dan aurenmu bazai gaza watanni shida ba zuwa bakwai, to ban saniba ko malama Jiddah zataso tsoho mai mata".
Kan jiddah a k'asa, ko kad'an kalamansa basu Sosa rantaba, dan duk jarumin namiji Na kwarai bazai tozarta uwargidansa agaban ta wajeba, hakannema yakuma saka Mata kwanciyar hankali akan aurensa, ko anan gaba bazataji shakkaba idan zai k'ara ta uku akan itama zai tozartata. Cikin sanyinta tace, "Duk namijin kwarai shike mutunta matarsa ga macen waje, halayen matarka sun birgeni, kuma ina addu'ar ALLAH yabani ikon yin koyi da ita, dakuma girmama ta amatsayin wadda take a gaba dani".
"Masha ALLAH, Alhamdllh, ALLAH yay miki albarka, yanzukam hankalina yasake kwanciya, ina kuma miki albishir da samun soyayya tsaftatacciya agareni inhar kika girmama zaman lafiya tsakaninki da matata insha ALLAH, sannan Zan kasance mai adalci a tsakaninku da yardar ALLAH, fatana muyi koyi da rayuwar aure irinta gidan MANZON ALLAH (S.A.W)".
"Insha ALLAHU".
"ALLAH yay muku albarka, bara na barki haka kije ki huta, inaga sai bayan an d'aura aure kuma insha ALLAH zaki kuma ganina saboda sabgogina yawane dasu, mikike da buk'ata na shagalin biki?".
"Bana buk'atar komai, dan babu abinda zanyi".
"Haba dai malama Jiddah, kod'an rawan coge d'innan Na Mata bazakuyi a cikin gidaba".
Dariya yabata wai coge, amma saita danne batayiba, sai murmushi datayi Wanda harya bayyana fararen hak'oranta a fili.
"Kin iya murmushi haka ashe amaryar Aliy? amma jan aji yasa ba'a ta6amin naganiba tunda muke had'uwa?"..
Da sauri Jiddah ta kudundune kanta a hijjab, shima ya mik'e yana fad'ad'a murmushinsa. "Tunda rowa akemin bara nayi gida matana tamin".
Ita dai Jiddah takasa d'agowa, takula yanada yawan tsokana, amma a fuska saikaga tamkar baya magana ma.
Kujerar dake d'an kusa da ita kad'an ya sake zama, addu'a yaymusu kafin ya kuma mik'ewa yana fad'in "Na barki lafiya".
Batare data d'agoba tace, "ALLAH ya tsare, ka gaidamin auntyna".
Yaji dad'in maganarta, dan haka ya amsa da amin ngd, auntynki kuma zataji, kafin ranar juma'a kuma kid'an canja dan ranar babu y'ar nesa-nesa..".
Ya k'are maganar ahankali bayan yad'an duk'o kusa da ita kad'an.
Sosai jikinta yake tsuma saboda jinsa kusa da ita, ga k'amshinsa yakuma mamaye hancinta, ta takure jikin kujera sosai har saida ya fita sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya".
???????????
A gidan Malam Aliyu kam da yamma saiga Aminatu k'anwarsa dasuke uba d'aya, d'iyar iya habi mai ruk'on Maimunatu, sai kuma yayar maimunatun Hassana.
Tarbar mutunci tai musu, bayan takawomusu ruwa ta zauna suka gaisa.
Aminatu ta kalli maimuna baki a ta6e tana fad'in "Miya samu idonki nagansa jajur kuma a kumbure?".
Dariyar yak'e maimuna tayi, sannan tace, "Babu komai Aunty Amina, kawai dai kinsan bajin dad'in jikin nakeba".
Kallon juna Amina da Hassana sukayi suka ta6e baki, Hassana ta maida kallonta kan maimuna, "To Uwar y'an zurfin ciki, auren na Mijin nakima 6oyewa zakiyi? To ai kin makaro, dan kowa yasani, yanzunan maimuna sabodake wawuyace zama kikai kina kwad'a kuka saboda za'ai miki kishiya?, kishiyarma bazawara, to wlhy idan zaki mik'e ki mik'e, kuka babu maganin ubanda zai miki, ni bammasan sanda zakiyi hankaliba kekam....."
"Ke wlhy da hankalinta, son mijine kawai, kinsanfa ita batason laifin Yaya Aliyu saboda shine autan maza". Amina takatse Hassana tana huci.
Maimuna ta share hawayen da suka zubo Mata, wad'anda dama suta yini yi, bayan fitar Aliyu dayace mata zaije wajen amaryane Yakuma tunzura kukanta, shinema suka iske tanayi, jin sallamarsu tai saurin zuwa ta wanke fuska ta shafo fauda, "Haba Aunty Amina yakikeson nayi, Zan hanashi yayi aurene?".
"Bakuwa zaki hanashiba wawuya kawai, yoke banda kin rako Mata duniya wata shida da aurenku kacal kizauna a dank'aro miki kishiya? Wato ya Danna miki ciki amfaninki yak'are shine zai auro wata ko? To wlhy kibud'e kunne kiji bayani, idan zaki mik'e kitada masa hankali ki haukace masa, duk yanda ya taroki kice bakisan zancenba....."
"Hummm, aunty Hassana kenan, da hauka Na hana namiji k'aro aure da mata da yawa sun tsira daga kishiya, da asiri Na Hana maza aure da wasu matan ba'ai musuba, yakamata muringama kammu adalci kafin ai mana, idan mun hana mazajenmu aure yazamuyi da y'ay'an da muka Haifa?, Kituna yanzu haka mamanmu yara hud'e kannenmu Mata agabanta, idan munce mazanmu bazasu auro mana wasuba, su wanene zai auresu?, dukma ba wannanba, shin munada tabbacin kaiwa darene dahar mukeda kwarin gwiwar Hana abinda ALLAH ya halatta?, kuyi hak'uri inason mijina, kuma ina matuk'ar kishinsa, amma hakan bazaisakani bijire masaba Na lalata alak'ata da Ubangijina akan son zuciya, kishi gaskiyane amma bata mummunar hanya yakamata mu Mata mu jagoranceshiba, kamata yayi Ku koyamin yanda Zan kuma damk'e zuciyarsa, Na zama tauraruwa a garesa ba yanda Zan tsinke igiyar aurenaba, iyayenmu babu wadda bataje ta tadda kishiyaba, miyasa su iyayensu basu k'i aurar dasuba saboda zasu iske wata? Saimu da za'azo a iskene zamuce bazai yuwuba?.......".
"Kinga Amina taso mukama gabanmu kafin tace mana y'an wuta", Hassana tafad'a tana mik'ewa.
"Wa'iyazubillahi aunty Hassana, mak'iyinama bazan dangantashi da wutaba balle ku".
Basu tanka mataba suka fice, duk kiransu datake ta biyosu har gate basu sauraretaba.
Kuka tayi sosai akan hakan, a ganinta bai cancanci manya dasu su kawo mata rabuwar hankaliba.
Koda Aliyu ya dawo bata fad'a masaba, shima bai tambayeta ba dukda yakula ranta a 6ace yake, yanayinta kuma ya nuna masa tayi kuka. Kulawa yayta bata yanda hankalinta zai sake kwanciya da sake rarrashinta, dan tunda yaymata zancen aurennan duk sai ta susuce, dukda dai tana dannewa a gabansa.
Hakan saiya k'ara dasa masa k'aunarta da tausayinta, koba komai ya yarda da son da take masa mai nagartane, kamar yanda shima ayanzu yakejin sonta tun bayan aurensu, sokuma Na gaskiya mai gauraye da zallar k'auna.
???????????
A 6angaren Jiddah ma ranar kwana tai da tunanin Aliyu, hardasu mafarki.
Komai nasa yamata yanda take addu'a da fatan mijinta ya kasance, fatanta ALLAH yasa matarsa ba irin hajia Deluwa baceba.
???????????
*_RANA BATA K'ARYA_*
Yau take juma'atu babbar Rana, duk tarone Na maza kawai hakan bai hana su Maman Sadiq yin abinci ba dai-dai misali saboda y'an Adamawa maza su kusan goma da y'an barno biyar da sukazo d'aurin auren, a Mata kam gajiram da yaruwaiya ne kawai sukazo (Yayar Umma, da k'anwarsu wadda Balu ke bimawa).
Abba zakari dai baisan hidimar da akeba, amma har gida Uncle yahya yaje yacemasa yashiryo suje d'aurin auren wani yaron malam Abdul-ra'uff, da farko cayay akwai inda zaije, amma Hajia Hindu ta saka baki harya amince.
A babban masallacin juma'ar dake anguwar gwammaja sukaje sallah, mamaki ya Kama Abba ganin Kawunansa, Kawu Surajo da bashida 6oye-6oye yafito yasanarma Abba auren Jiddah za'a d'aura yau d'innan, kafin Abba yasamu zarafin magana tawagar malam Abdul-ra'uff data ango suka Iso.
Su Kawu Surajo basubi takansaba suka shiga hidimar tarbarsu, babu yanda ya iya dole yabi ayari dan karyaji kunya, dan manyan malaman sun cika masa idanu, amma daka gansa kasan a birkice yake gaba d'aya, kuma hankainsa baya jikinsa.
Ana idar da sallar juma'a wadda su malam sukayi anan suma aka d'aura Auren *Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina da Jiddah Zakari Yaro* akan sadaki dubu d'ari biyu ciff????..............???
*_Munga idi, ya za'ayi da Abba zakari da Alhaji Garba kenan???????._*
*_??¡â??kayana a shirye suke nayin hijira walla, kad'an daga aikin Abba ya lallasa gayu??????_*
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*zaku iya samun Raina Kama a audio ta wannan link d'in na sama sisters, Abban dausayi YouTube channel tv??????_*
*_Ubangiji yabama d'an uwan momin khairi malam Adamu lafiya, bisaga had'arin mota da yayi, muna barar addu'arku. Dama dukkan y'an uwa musulmi dake kwance sanadin ciyo??????_*.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
[12/12/2019, 12:13 AM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[31?32]_*
............Can na hango muku ango Sheikh Aliy shar cikin d'anyar shadda gizna ruwan toka mai haske, sai zabga k'amshi yake yana gaisuwa da jama'a da suketa masa ALLAH ya sanya alkairi, yau d'imma dai baka isa shaida yanayinsa ba tamkar lokacin aurensa da maimuna.
Yazo ya gaida su Abba da gaba d'aya jinsa ya barsa, sama-sama yakejin hayaniyar mutane, koda Aliyu na gaisheshi saida Kalla ya zunguresa sannan ya amsa cikin alamun baya a hayyacinsa.
Shidai Aliyu ya gaidashi cikin mutuntawa tareda masa godiya ya mik'e
Aliyu Na barin wajen Abba ya fisgi hannun Uncle yahya sukai baya inda babu jama'a.
"Yaya wai miya farune kaketa jana? ina zaka kainine?".
Banza Abba yay masa bai tankaba, kuma bai Saki hannunsaba. Sai da suka Isa can bayan k'aramin d'akin da Gen......take Na masallacin, Sannan ya sakeshi tare hankad'a Uncle yahya jikin bango ya shak'eshi. Da farko Uncle yahya ya tsayane yaga iya gudun ruwan Abba, amma ganinfa da gaske yake saiya shiga k'ok'arin rik'e hannunsa domin kare kansa, amma Sam Abba yak'i sakinsa, sai kuma k'ok'arin shak'arsama yakeyi, tuni kiciniya ta 6arke a tsakaninsu.
Kawu Surajo dayaga fisgar da Abba yayma Uncle yahya ne yaji zuciyarsa takasa nutsuwa, dan haka yabiyo bayansu...
"Subahanallahi, Zakariyya! Kanada hankali kuwa? 'Dan uwan naka zaka kashe? Miyaymaka?". 'Kawu Surajo yay maganar yana kiciniyar kwace Uncle yahya daga hannun Abba'.
Uncle yahya ya k'yale Abbane kawai amma badan yafi k'arfinsaba, Abba dai bai Saki Uncle yahya ba saida Kawu Surajo ya maresa, saurin sakin Uncle yahya yay yana kalon Kawu Surajo dake huci (dan shima akwai zuciya dam) hannunsa dafe da kuncinsa yace,
"Kawu shine zaka mareni?".
"An mareka d'in kozaka Rama? Waishin Zakariyya mikakeson zama kaikam a rayuwarka? A ina ka gado wannan halinne? Wlhy mahaifinka bashida wannan bak'ar halayyar taka, hakama Mahaifiyarku, girma kake kullum amma halin yara da rashin sanin yakamata yakasa barinka, kanason gamawa da duniya lafiya kuwa?".
Cikin harzuk'owa Abba yace, "Yaza'a dakeni sannan a hanani kuka? Yazaku zauna Ku k'ulla munafuncin aurarmin da yarinya sannan ace bazanyi maganaba?, Jiddah dai nina haifi abata bawani ya haifarminba, wlhy yahya kayi maza ka saka ya sakarmin yarinya, bashi nai niyar bawaba kuma bazan bashiba, inko ba hakaba wlhy saina maka rashin mutuncin dabaka ta6a tunaniba".
Kawu Surajo zaiyi magana Uncle yahya ya dakatar dashi ta hanyar fad'in kaga "Kawu barshi, nima Zan bashi amsa dai-dai dashi, domin Yaya bai cancsnci kowacce irin girmamawa ba agareni yanzun. Yaya a wannan Karon bazan maka shiruba kamar yanda Na Saba, kaimin dukkan abinda zuciyarka ta fad'a maka dai-dai, sai dai kuma kasani Wannan auren yayi k'ulluwar da insha ALLAHU mutuwace kawai zata rabashi, duk kuma abinda kaga zakamin ga fili gamai doki nan, ko kunyar ALLAH bakaji ka saida yarinya akan kud'i kadawo kana hura hancin y'arkace, dan wannan wlhy saidawane, tunda batasan kaje kaci bashinkaba, k'ilama ko sisi bataci a cikiba....."
Duka Abba yakaima Uncle yahya amma sai Kawu surajo ya janye Uncle yahyan yana fad'in "Kaga yahya barsa muje kawai, wannanma kad'ai ta isheshi, yaje ya nemawa masu kud'i kud'insu".
K'iri-k'iri Abba yashiga mulmulo ashariya yana nakama Uncle yahya da tabbatar masa saiyayi dana sani, kuma aurene saiya rabashi.
Badan wajen babu kowaba kam dasun tara y'an kallo bana wasaba.
???????????
A gida kam Jiddah duk sai tayi wani sukuku, duk tsokanar dasu Aunty Nafisa kemata bata kulaba, dayake ba taro za'ayiba batayi wani kwalliyaba, tadaiyi wanka ta saka sabon d'inkinta. Zaune take a d'akinsu ta zuba tagumi tana tunanin rayuwa, wai itace aka d'aurama Aure sau biyu cikin shekara d'aya, rayuwa kenan, mai tafiya da jarabawa.
Dukda ba taro za'ayiba gidan nasu yad'an cika da makwafta, koda y'an d'aurin aurema suka dawo sai akaita bud'e-bud'e, wad'andama basu shigoma suka shishshigo sunama Umma ALLAH ya sanya alkairi.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Bayan su Uncle yahya sungama cin abinci suka shiga tattauna batun Abba da yanda zasu 6ullo masa.
Ana cikin wannan magana saiga y'an sanda sunzo tafiya da Uncle yahya Abba yakai k'ararsa akan ya aurar masa da yarinya batare da saninshiba.
Wannan lamari kam ya girgiza kawunnansu sosai, batareda an Bari su Umma dake cikin gida sun saniba Uncle yahya dasu Kawu Bilya sukabi y'an sanda station.
Acan ma suka iske Abba a Office d'in d.p.o .
Jin da d.p.o yayi zancene Na family saiyay nufin sulhuntasu a office d'insa, amma sai Abba yace Sam bai aminceba, shidai kawai akira sheikh Aliyu yanzunnan ya sakar masa y'arsa.
Su Kawu Surajo kuma sukace bai isaba yayi kad'an. Nanfa rikici ya hark'ume sosai, babu Wanda Abba yake hara sai Uncle yahya, yayinda kuma yake datsama Su Kawu dukkan maganar datazo a bakinsa, har dare suna station ana abu d'aya, su kamsu police d'in yau dukkan aikinsu ya tsaya rikicin su Abba ya d'auke hankalin kowa.
Shi d.p.o jin Mijin da yarinyar ta aura yasakashi k'in goyama Abba baya, dan aganinsa babu wani mutumin kirki dazaice baya buk'atar had'a jini da Malam Abdul-ra'uff maina a k'asarnan, musamman ma ace d'ansa Sheikh Aliyu ne Mijin. Shiyyasama yak'i amincewa akira sheikh Aliyun, dan aganinsa zubar da kimane ga Abban.
Dadai d.p.o yaga kansa na Neman d'aukar zafi sai kawai yayma yaronsa inkiya da ya nemo masa maganin barci a lemo ko ruwa, babu dad'ewa kuwa yakawo lemo. Abba kawai akaba, ganin hakan yasaka Abba kuma yin fad'i irin shi an girmamasa, dandanan yafara zuk'ar