Showing 120001 words to 121675 words out of 121675 words

Chapter 41 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17140

kuka, hakama su Jiddah na tayata a gefe.

Kwanaki biyu da gama bikin Jiddah Mutuwar hajia deluwa ya baje gari, koda Jiddah taji sai da taimata Addu'ar samun rahmar ubangiji, Walida tace, "Tab, sannu yaya Jiddah, wlhy kinada zuciya mai ?yau, duk abinda tai miki amma kike mata wanan doguwar addu'ar haka?".
Murmushi kawai Jiddah tayi bata iya cewa komaiba.


???????????

Lokacin da cikin Jiddodon Uncle ya cika watanni goma cif ta haifo ?iyarta mace santaleliya, murna a wajen ya Sheikh da Maimuna ba'a magana, hakama su Umma da sauran dangi, ranar suna yarinya taci suna Maryam, akasha walima da daddare.
Washe gari Jiddah tadawo gida wanka cikeda kewar ?anta Muhammad da ya Sheikh ?inta da ?ar uwarta Maimunatu.
Sosai Umma ta tsaya akan kula da jiddah, yanda Abba ke nunama Maryam soyayya har mamaki take basu, ko yaushe yana mamu?e da ita, ko kukanta yaji yata fa?a kenan wai sakacin Umma da Jiddah ne, su dai su Umma sai dai kawai suyi dariya.
Ahaka Jiddah tagama wanka ta tattara ta koma ga ya Sheikh ?inta, aka ?ora soyayya daga inda aka tsaya, yayinda dukkan kulawar Maryam takoma wajen Maimuna itama.
Haka rayuwa tacigaba da shurawa cikin amincin ubangiji da rahamarsa, wataran aji da?i wataran ayi kuka.

*_BAYAN WASU SHEKARU_*

Rayuwa ta shura, gidan Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff maina yazama na ?a?a da al'umma, yanzu kam shine magajin malam ?in na gaske, dan ALLAH yayma malam rasuwa shekaru uku kenan da suka wuce, hakanne ya saka girman malma da hidimarsa ga al'umma duk ta dawo kan Aliyu.
A yanzu haka akwai ?a?a tara a gidansa, maimuna nada biyar. Muhammad, Ai'sha, Hauwa'u, Umar, Aliyu.
Jiddah nada hu?u, Maryam, Maimunatu, Abubakar, Usman.
Rayuwa mai cike da tarin farin cikice ke gudana a gidan ya Sheikh, ga girmama juna da sanin ha??in zaman tare, duk sun zama manyan mata, dan daga Maimuna har Jiddah sunyi ?iba tamkar ba suba, sun zama iyaye alamun girma duk ya bayyana a garesu. A yanzu haka suke ri?e da islamiyyar mata ta ?ofar gidansu, yayinda suma basu zauna hakaba, suna neman ilimi a wajen mijinsu ga kasuwancinsu na hijjabai da sukeyi da jallabiyoyi daga ?asar saudia, wanda Aliyu ne yay musu wanan hanyar.
Rayuwar gidan na tafiya dai-dai gwargwadon iko, ba wasu tarin ku?ine dasuba, babukuma talauci na an shiga uku an lalace.

************

?an gaten su Umma ma masha ALLAH, tuni Walida ma tayi aure, yanzu haka dagasu sai Munner daya zama saurayi, yanata karatunsa ?angaren shari'a, tsufa sosai ya kama Abba da Umma, musaman ma Abba da abin ya ha?a da lalurar rashin tafiya, dan har yanzu a Wheelchair yake yawo. Shida ?a?ansa kam sai sambarka, dan sune ke ri?e da gidan yanzu, cinsu shansu suturarsu shida Umma da karatun Munner du ?a?ansa matane keyi, bai nemi komai ya rasaba dai-dai gwargwadon iko.
Shiyyasa lokuta da dama yakan zauna yayta kuka idan ya tuna ta?argazar da yayi na butulcema ALLAH, duk sanda wani acikin ?a?ansa yazo gidan sai ya maimaita neman gafararsa, hakama Uncle yahya.
Shidai saidai yace masa dan ALLAH abar tuna abinda ya wuce, komai ya wuce ai yanzu.
Shima Uncle yahya yazama dattijo sosai, furfura dukta taso masa, yaransa sun girma sunata ?awainiya dashi harma da Abba, sanan sunata zuminci dasu Jiddah abin gwanin sha'awa.


???????????

Sheikh Aliyu maina kishin gi?e a falonsa yana kallon wani program a Sunnah tv, yayinda Maimuna da Jiddah ke gefensa suna tayasa hira da kallon program ?in suma, daka gansu zaka fahimci tsantsar soyaya da kwanciyar hankalin dake tattare dasu, zukatansu fayau suke babu nukufurcin kishi mara ma'ana, hakama adalin mijinsu kulawarsa tana akan kowaccensu. A gabansa juk ne na kunin aya da yake dorawa.????
yarone da bazai wuce shekara 8 ba, ya shigo da kuka hannunsa ri?e da litatafai, yana sanye da Uniform ruwan ganye masu haske.
Harya shigo ya koma da baya danya tuna baiyi sallama ba, daga Sheikh Aliy harsu Jiddah babu wanda yamasa magana, saida yakoma yayo sallama suka amsa aka bashi izinin shiga sanan ya shigo, har yanzu kukan yakeyi.
Kai tsaye wajen Maimuna ya nufa ya fa?a jikinta yana fa?in "Ummina kinga Yaya Umar yasaka yaya Muhammad ya dakeni".
Maimunatu tace, "Duka fa auta? A lallai yau babu maicin abinci a gidanan tunda aka dakarmin Auta, kai har Abbu bazamu yima maganaba shida Ammi".
Baki Jiddah ta ta?e tana mi?ewa da fa?in "Sai kukam ku?i ci Ummi, kema kinsan tsokanar Usman da hana bakin mutane zama shiru, aini yayama baimin dai-daiba dabai barka a ?ofar gida ka kwanaba ya kullo mana gidanmu". Ta ?are maganar da hararar Usman dake lafe jikin Maimuna.
Murmushi Aliyu yayi shidai, rayuwar matansa na birgeshi, baka isa banbance ?ayan gidan na wanenenba idan har ba'a fa?i makaba......
Sallamar Muhammad daya zama ?an saurayi dan kusan shekararsa 22 yanzu ta katsesu, daka gansa kaga cikakken Ustazu, ga tsananin kamanninsa da Aliyu sun fito ?aro-?aro. Jiddah ce ta amsa masa sallamar tareda bashi izinin shigowa, tunda ya shigo Maimuna ke dalla masa harara.
Murmushi yayi yana sunkuy da kai, cikin muryarsa mai sanyi da batada maraba data mahaifinsa yace, "Afuwa Ummi, wlhy autanki ne bayaji, ki dinga bashi ruwan al'awa kozai dai-daita, muna karatu amma sai tsokanar ?a?an jama'a yake....."
Jiddah ta katseshi da fi?in, "I shurunka yarona, itama ai tasan halin abunta, ni sonaima kabarsa can ?ofar gida ya kwana ai".
"Wai Ammi ashe yau Ummi zata hanani tuwo kenan a gidanan, gara dai mu lalla?a ko Abbu?".
Aliyu datun ?azun yake musu dariya ?asa-?asa yace, "Da gaskiyarka babban yaya, mu lalla?a dai Ammi, kar Ummi ta turamu bayan ?ofa akan wannan autan nata sarkin shagwa?a".
Maimuna tace, "dakun taimaki kanku kam".
Dariya duk suka ?anyi, Usman ya sakko daga cinyarta yakoma wajen Aliyu ya zauna jikinsa, "Abbu!".
Aliyu yace, "Na'am autan Ummi ta samune?".
"A'a Abbu bata samuba, zance maka dai nama ha?ura na daina kukan, shima yaya Umar ?in na yafe masa".
Rungumeshi Aliyu yayi tareda sumbayar goshinsa, "Yauwa autan Ummi mai halin manya, ai haka akeso, yanzu kaima kaje ka bama yaya Muhammad hakuri, kace bazaka sake rashinji a ajiba".
"To Abbu".
Gaban Muhammad Usman yaje ya durkusa, "Yayanmu kayi ha?uri kaji, kaga ALLAH yana tare da masu hakuri, indai nine zan dinga jin magana insha ALLAH, na daina tsokanar kowa a aji".
Muhammad ya ajiye littatafan hannunsa ya ?auki Usman ya ?aga sama yana nufar kofar fita da fa?in "yawwa Autanmu, ALLAH ya maka albarka kaji".
"Amin yayanmu" usaman ya fa?a shima suna gab da fita......
Da sauri Aliyu ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunan Muhammad, hakanne yasaka Muhammad amsawa ya juyo, "Na'am Abbu".
"Inasu Maryam suke? Banace kadaina shigowa gidaba sai kaga sun shigo?".
"Afuwan Abbu, na biyo Usman ne dama amm......"
Sallamar sauran yaran ta hanashi ?arasawa.
Maryam da Ai'sha kusan kansu ?aya, sun zama ?an mata masha ALLAH, sai Hauwa'u (Noor) da Maimoon (Amatallah) suma kansu ?aya, sai sauran yaran maza Umar, Abubakar, Aliyu, yaran gwanin sha'awa, atare suka durkusa suna gaida iyayensu, dan tasowarsu kenan daga makarantar dare dake a ?ofar gidansu.?????




*_ALHAMDULLAHI ALAH KULLI HALIN, GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI, WANDA SHINE YABANI DAMA DA LOKACIN RUBUTA WANAN ?AN LITTAFI NAWA, ABINDA NA FA?A DAI-DAI ALLAH YA BANI LADANSA DAKU BAKI ?AYA, WANDA NAYI KUSKURE ALLAH KA YAFE MANA DAKU BAKI ?AYA DA KUKA KASANCE DANI_*

_Babu abinda zance da masoya sai godiya, nagode ?warai da gaske da Comments naku, da addu'oinku a gareni da mahaifina??????, wanan ka?ai da kukamin kun biyani ?warai da gaske, dan mai ?aunarkane zai maka addu'a harma ya tuna da mahaifanka a ciki, ALLAH ya ha?amu a aljannarsa baki ?aya, ina kuma godiya irin trillions ?innan musamman

*_MUTUM DA DUNIYARSA GROUPS_*
*_MASARAUTAR BILYN ABDULL_*
*_TASKAR LITTATAFAN HAUSA_*
*_KUNDIN HASKE_*
*_HUGUMA CONVERSATION ROOM_*
*_ZAUREN BIEBEE ISA_*
*_BENEFICAL WRITERS ASSO..._*
*_ZAUREN HASKE WRITERS_*
*_ZAUREN KHADIJA CANDY_*
*_HOME OF NOVELS_*
*_ZAUREN SADEEYER NOVELS_*
*_ALFAHARI NOVELS ONLY_*
*_NI DA AMARYATA FANS_*
*_MANSHAT NOBELS_*
*_ZAFAFA PAID GROUPS_*
*_SAIFUL-ISLAM FANS_*
*_WUTSIYAR RA?UMI FANS_*
*_KAI MIN HALACCI FANS_*

Kunada yawa matu?a, ina godiya ga sauran wa?andama ban lissafoba, harma wa?anda ban saniba kuda admins naku gaba ?ata????????????????????????????????????????????



*_Daga ?arshe muna muku albishir da zuwan zafafa biyar insha ALLAHU a ranar 7 ga watan janaury nan da muka shiga, muna fatan wa?anda basu sayaba zasu garzayo kusa suma ayi dasu, dan har yanzu hajarmu abu?e take a gareku, shima wannan babban halaccine da zaku nuna mana wanda bazamu ta?a mantawa dashiba, zukatanmu sukuma yarda ku?in masoyane na gaske????????_*.


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)

????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*????????????



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login