Showing 96001 words to 99000 words out of 121675 words

Chapter 33 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17178

Saurin shan gabanta Amarya tayi.
"K ballagazar mace nutsu mana, minene kikeyi haka tamkar sabon kamu?".
Takaicine ya cika Hajia deluwa, ta ?aga hannu da nufin marin Hajia Bariki sai caraf aka ri?e hannun nata, Alhaji garbane yari?e, yayinda ?ayan hannunsa ya toshe hancinsa dan wani irin mugun warin dayafi na jiddah yaji tana masa".
"k shashasha, karki sake ?azamin hannunki ya hau kan matata". Ya ?are maganar tareda hanka?e hajia deluwa yakama amarya suka shige abinsu.
Tibiran Hajia deluwa tashiga hauka a cikin gidan, ta koma sashenta ta ?akko ta?arya tazo taita dukan ?ofar, su balki mai aiki da mai gadi da Abba dabai tafiba sunyi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH. Daga ?ofa hajia deluwa saita koma winduna taita fasa gilasan.
Dolefa Alhaji Garba ya sake fitowa, ?ya?y?yawan mari ya zubama Hajia deluwa.
hannunta dafe da hancinta. Cikin jin azabar shigar marin ta cakumi wuyan rigarsa, tunifa kokawa ta hargitse a tsakaninsu, ?arfi ba ?ayaba yahau jibgarta ganin zata zubar masa da mutunci gaban ma'aikatan gidan. Saida yay mata lilis tana kuka da zaginsa da jan ALLAH ya isa ya turata cikin sashenta ya kulle.
Su Ashir duk basa gida, shiyyasa Alhaji garba yasamu wannan damar.
Mota Abba ya shiga yafita yana she?a dariyar mugunta, aganinsa wannan tashin hankalin ka?ai ya ishi Alhaji garba mantawa da maganar ku?insa, indai hakane kam zaisa hindu taita tunzura Hajia deluwa dan ta ?auke hankalin Alhaji garba.


????maga yanda za'a kwashe to??¡â??.

???????????

Su Umma na zazzaune a tsakar gida tanashan labarin gidansu jiddah da su aunty hannatu ke basu Abba ya shigo fagan-fagan tamkar an jehoshi.
Saikuma yayi turus ganin duk ?a?ansa gasu Yaruwaiya kuma, gashi duksun watso masa idanu tamkar wani ojuju.
?auke kai Umma tayi tamkarma bata gansaba, sai yaranne suka shiga gaidashi, cikin sar?ewar harshe ya amsa musu da tambayarsu ya yara. Abin yabasu matu?ar mamaki.
Umma data fahimci tsorata yayi da ganinsu sai abin yabata dariya, dan alamunsa duk sun sunana bada arzi?i yazoba, ita dama tasan arzi?in bazai kawoshi a irin wannan lokacinba, ballema Jiddah ta tare bai saniba.
Gani kawai sukai yajuya yafita batareda yashiga cikiba, hakanne yasasu tunanin anya lafiya kuwa?, Yaruwaiya tayi murmushi dan itama ta fahimci ba arzi?i ya kawoshiba, ganinsune yasakashi tsorata shine yafita..

Daga nan gidan Abba gidan Uncle yahya yaje ya aika a kira masashi, danya kira wayarsa a kashe.
Amma koda ?an aiken ya fito saiyace ai Uncle yahya bayanan ma, ance yaje Adamawa.
"Adamawa kuma?" Abba yafa?a a fili cikin mamaki da al'ajabin uwarmi akeyi a adamawar kuma?.
Bashida mai bashi amsa, danhaka yabar anguwar da ?udirin ai gobema ranace ko, zai dawone.

????Abba kana ruwa gaskiya??.


???????????

*BAYAN KWANAKI UKU*

Abubuwa dayawa sun faru takowanne ?angare, dan hajia deluwa tana cikin jin azabar jin jiki su Ashir suka dawo suka sameta, hankalinsu tashe sukahau tambayarta miya faru, cikeda magagin azaba tafa?a musu abinda ya faru, takumace Alhaji Zakari ne da Amarya suka saka Alhaji garba dukanta.
Sosai Ashir da bala suka hasala, suka kuma kira babban wansu suka sanar masa abinda ya faru.
Ransa a matu?ar ?ace shima yazo gidan, sai dai kuma Alhaji garba ya?i fitowa, wannan ne yasaka su sakawa amusu bincike akan Abba.
Ita kuma suka kaita asibiti, kwananta uku cif tana jinya acan, yau da safe aka sallamosu, suna direta a gida kuma suka nufi gidan Abba da akai musu kwatance.


????????¡âAbba maza bisa kanka.


???????????

A gidan Sheikh Aliyu dai sai muce Alhmdllh, dan suna cikin aminci gwargwadon iko, bandama dai Maimuna dake fama da lalurar laulayi, wadda kuma Alhamdllh tana samun kulawa ga mijinta da Jiddah ma, dan ?iri-?iri Jiddah ke ?o?arin hanata wasu ayyukan, dukda itama Maimuna na hana jiddah, acewarta amaryace saita gama amarci sannan.
Amma sam Sai Jiddah ta?i bari. Hakanne yasaka Aliyu kuma samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, a gefe kuma yana addu'ar ALLAH yasa su ?ore hakan.
Shida Jiddah dai kam tun ranar bai kuma takurata ba, dan soyake takuma sakin jikinta tamkar yanda yaga ta fara, ?an wasanni dai kam yakanyi da ita, dan har yanzu a sashenta yake kwana saboda kwanakin da Maimuna ta ?ara musu, da safe Jiddah taita ?oye fuska batason su ha?a ido, shikam yata tsokanarta kenan yana dariya.

Yaukam tunda suka gama fira a sashen maimunatu ta dawo nata sashen, tana gama shirin barci saiga Aliyu ya shigo shima cikin nasa shirin.
Kallonsa ta?anyi tana amsa sallamar a saman la??anta, mamaki yabata, takula tunda yasha kunun kwakwar ?anzun yakoma wani shiru, firarma daina saka musu baki yayi, yabarta itada Maimuna kawai.
Cikin sauke numfashi tace, "Kobaka jin da?ine?".
Murmushi yay mata danya kula batasan dawan garinba, amma harga ALLAH tausayintama yakeji shi, dan yasan yau kam bazai iya juriyar binta a hankaliba tunda yasha kunun kwakwarnan............?????


*_Ya Sheikh masoyan jiddah fa sunce kabi a sannu dan ALLAH??????¡â_*

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)

????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*????????????



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/27/2019, 11:35 AM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[53?54]_*


............A matu?ar kasalance ya zauna a bakin gadon idonsa akan ?irjinta, hakan data fahimtane yasata yin?asa da kai da ?o?arin gyara ?aramin gyalen data ?aura akanta ya rufe mata ?irji sosai.
Sassanyan murmushi yayi yana lumshe ifanunsa da sauke ajiyar zuciya kafin yakuma bu?ewa a kanta yana mi?ewa tsaye, hanyar fita ya nufa, saida yaje ?ofar sanan yajuyo yana kallonta "Idan kingama abinda kike, Kisameni a ?akina".
Kamar zata fasa ihu tace, "to".
Bai kuma cewa komaiba ya fice abinsa.
Shiru jiddah tayi a tsaye, zuciyarta sai sa?awa da kwancewa take, tana mamakin miyasa yace taje can? Tunda tazo gidan bata ta?a shiga ?akinsaba, kullum shike zuwa ya sameta, taja wasu mintuna kafin ta matsa gaban madubi ta ?auki turare ta fesa da wasu sirrikan ?amshi na humra, sannan ta saka hijjab har ?asa ta fita.
Gidan tsitt babu wata hayaniya gashi babu nepa, rabonsu da wutarma tunda safe, saida aka tada gen ?in masallaci, kuma suna kammala karatu aka kashe, koda Aliyu ma yashigo gidan har an kashe.
Taja wasu adadin mintuna a bakin ?ofar falon kafin ta tura ta shiga da sallama. Babu kowa a falon, hasalima dun?um yake da duhu, fitilar wayarta ta haska falon dashi, komai yamata ?yau gwargwadon iko, kujeru da labuloli duk kalar ruwan siminti, sai ba?i ka?an, ?ofa ?aya dake rak a falon ta nufa, ta ?ora hannunta saman handle ?in, harzata mur?a saikuma ta fasa tayi tsaye tamkar mai fargabar shiga ?akin jarabawa.
Saida taja kusan mintuna biyu kafin ta mur?a ?ofar ta bu?e, da sallama ta shigo a bakinta kanta a ?asa.
Aliyu dake zaune a bakin gado laptop a gabansa yana dannawa ya ?ago ido yana kallonta da amsa mata, kafin ya ?auki kofin shayinsa yakai baki.
"Kosai na taso nayi tarbane Amarya?".
Kai Jiddah ta girgiza tana cigaba da takowa ciki da fa?in, "A'a nagode".
Murmushi yayi yacigaba da abinda yakeyi, "Bismillah ki zauna to".
Takowa tayi zuwa bakin gadon ?an nesa dashi ta zauna.
Kofin shayin ya mi?a mata. ta girgiza masa kai alamar a'a.
Baice mata komaiba ya cigaba da akinsa, itama saita jawo littafin *KITABUT TAUHID* daya ajiye tana dubawa.
Kusan mintuna hu?u suna a haka kafin ya ?ago yana kallonta, "Afuwa gimbiya ina?an rage sa?wannine, kozaki tayani?".
Murmushi tayi tana ri?e baki, "Wai inani ina wannan sa?wannin? Aina manyane".
?an murmusawa yay kawai yana cigaba da aikinsa, "Hakadai kikace, amma ai kuma bana wasa baneba Jiddatulkhair. Shin Kin haddace littafin nan ne?".
?agowa tai ta?an kallesa ta janye idonta "A'a ba dukaba, mun fara babu da?ewa na daina zuwa makarantar".
Sosai ya kalleta yace, "miyasa?".
da ?yar ta iya fisgo maganar tana inda-inda, tunda yata?a cemata bayason ya tuna ta ta?a aure, "lo lokacin wancan au..ren ne".
"Humyim" kawai yace yamaida kansa.
Kasa daurewa tai saida ta?an kallesa saboda yanda ya bata amsar, ganin yacigaba da aikinsa itama saita cigaba da duba littafin.
Minti kusan ashirin yanata aikinsa, kafin ya janye laptop ?in gefe yana fa?in "Alhamdulilahi, hajiyata basai kicemin na huta hakananba".
Cikin rufe fuska Jiddah tace, "Haba saikace wani aiki?".
"Aikine mana tunda nabar Matata ita ka?ai" yay maganar yana Matsowa jikinta.
Jitai duk kasala ta saukar mata, ta?an matse jikinta waje ?aya tana sinne kanta.
Sumbatar hannunta yay dake ri?e a nasa, "kinyi alwalar barci?".
"A'a" ta fa?a tana girgiza masa kai.
Batareda yace komaiba ya fara ?o?arin cire mata hijjabin, batayi jayayyaba ta barsa ya cire, kayan barcinta wando da riga kalar pink suka bayyana, sihirtaccen ?amshin da take zubawa ya sha?a yana lumshe idonsa, kansa ya ?aura bisa kafa?arta, gashin gemunsa dake ta?ata ya saka tsigar jikinta tashi, hancinsa yakai jikin wuyanta yana shinshina, tuni jikinta yakuma yin sanyi ?alau.
Ganin yana neman zurmawa tace, "Zanje nayi alwalan to".
A kasalance ya sauke numfashi kafin ya matsa daga jikinta yana nuna mata hanya alamar taje tayi.
Sum-sum tamkar munafuka ta wuce bayi ?auro alwalar barci. Bayinma yamata ?yau, gashi a tsaftace babu wani ?azanta, kodayake dama batai tunanin samunta daga gareshiba, dan ko farcen malam ka kalla ka?ai ya isa shaida maka shimai matu?ar tsaftane.
Ta?an jima sannan ta fito, yanda ta barshi haka tazo ta iskeshi yana duba littafin data ajiye. Ta gefen ido yake kallonta harta zo ta ?ayan gefen ta kwanta can ?arshen gadon.
Ruwa takeson zuwa tasha, amma kallon ?urullar da yake mata duk saita daburce. Shima lura da hakanne ya sakashi ?auke idonsa daga kanta yana fa?in, "Ko kina bu?atar wani abune?".
"Uhm zan sha ruwa ne"
jug ?in Ruwan dake ajiye a dirowar gefen gadon ya tsiyayo ya mi?o mata. Zaune ta tashi ta kar?a tanasha, shikuma ya mi?e yanufi bayi.
Lokacin daya fito Jiddah hartayi addu'ar barci tai luf.
Baice mata komaiba ya shinfi?a abin sallah domin yin shafa'i da wutiri kamar yanda ya saba. Duk abinda yake Jiddah na kallonsa, amma ta?iyin koda ?wa?w?waran motsi dazai tabbatar da hakan.
Ya?an jima yana addu'a kafin ya mi?e yay shirin barci, tunda Jiddah taga zai cire jallabiyar jikinsa saita rumtse idonta, shi baimasan tanayiba, duk zatonsa kotayi barcine mashi.
Harya hawo gadon ya kwanta da kashe fitilar tana jinsa, hannu yasa ya lalubota yana jawota jikinsa, "Haba Kairunnisaa, waya ce miki haka mata da miji ke kwanciya?".
Shiru tai takasa koda tari, saida taji yana hura mata iska a kunne ne tashiga sauke numfashi da ?yar, hakanne yasakashi fahimtar idonta biyu dama, sai kawai ya canja zuwa wani salon daban..........????¡â


???????????


Ba?i dai duk sunyi ?aura, hatta dasu balu duk sun tafi, sai umma taji gidan duk babu da?i, yayinda kewar jiddah ta dawo musu sabuwa fil a zuciya.
Koda Uncle yahya yazo ?azunma da safe haka yaytajin babu da?i da baiga jiddah ba. Yazone sun tattauna akan batun sauran ku?in sadakin Jiddah daya rage a wajensa, shinema har yake sanar mata Abba yaje nemansa ranar, amma sai ya cema yaron yace yaje Adamawa, kuma yana gida babu inda yaje.
Murmushi Umma tayi tana fa?a masa suma dayazo nan bai zaunaba ya fice abinsa.
"To ALLAH ya ?yauta, insha ALLAH idan ya huce zanje nabashi ha?uri, dan nasan da gaske ba a ?yauta masaba ?in, amma bamuda wata mafitane sai wannan ?in".
Murmushi kawai Umma tayi, dan tasan ko ma?iyi bazaice yahya baiyiba, mutumin kirkine dayasan ha??in ?an adam da darajar zuminci. a wannan zamanin irinsu ?alilanne a cikin al'umma.


???????????

Su Ashir harsun kama hanyar gidan Abba sai yayansu ya dakatar dasu bayan zuciyarsa tamasa wani tunani.
Canja hanya yayi zuwa police station.
Bala yace, "Wai ina kuma zaka kaimune yaya?".
"Station zamuje Bala, ?aukar hukunci a hannunmu bai daceba, ai dama da ji?a??iyar ku?i a tsakani, kunga daganan saimu wuce kotu".
A fusace Ashir yace, "Amma yaya kabarmu mu?an sassafashi mana, kaga daga yanzu baya sake munafincin zuga waniba ai".
"cooldown ?anina, abinda zamuyi masa yanzu saiyafi duka zafi ai".
Shiru duk sukayi badan sun soba, a station duk abinda ya dace sun yishi, atake akaje kamo Abba.

Abba yana kasuwa hankalinsa kwance, dan sosai yakejin da?i ganin a kwana ukunan babu sammacin da Alhaji garba yace za'a kawo masa na kotu, shi kansa Alhaji garban ma baya zuwa kasuwa gaba ?aya.......
Yana tsaka da wannan tunaninne ?an sanda suka iso shagon bisa kwatancen dasu Ashir sukai musu.
Sosai gaban Abba ya fa?i, amma saiya fuske yana mazurai, ?an sanda dai bayani sukai masa na bu?atar ganinsa a ofishinsu. Kamar Abba zai musa saikuma ya fasa ganin idanun mutane yadawo kansa gaba ?aya.

Tunda aka baro kasuwa da Abba ?ananun magana ke tashi, kowane baki da abinda yake fa?a akan wannan tafiya da ?an sanda sukayi dashi.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï.

Hajia hindu da yara tun suna tsumayen shigowar Abba har suka bari, gashi yau yamusu al?awarin sayo musu kayan da?i idan zai dawo kasuwa, hakanne ya saka yaran zumu?in dawowarsa, amma har goma na dare tsit kakeji babu amo babu labari.
?osawar dasu kalifa sukaice tasakasu fara tsaki, itako hajia hindu takaicinta da tunaninta yanakan cewa Abba yana gidan Ummane jarabarsa ta kaisa, hakanne yasakata ?aukar masifaffen fushi, tacika tayi fam dan kumbura, sai ka?a ?afafu take na tsumuwar bala'i.
Wasa-wasa dai har shabiyun dare, tuni ta kora yaran ?aki sunje sun kwanta, itakam tana zaune tana shiryama Abba shika-shikan bala'in da zata ?arar masa idan yadawo gidan. Dataga lokaci ya jane taje ta kwanta itama.


Hummm????


???????????

Iya tantance tsakanin aya da tsakuwa jiddah tayi a daren jiya kam, shikansa ya Sheikh yasan yabu?e ?wanji da yawa, kuka dai hajjaju jiddah an shasa har an godema ALLAH, sai taji ranar ashe wasan yara akayima, yau ?inne ta tabbatar da menene daren farkon.
Tana zaune bisa abin salla ya dawo masallaci, kanta a ?asa ta amsa masa sallamar.
Muskarsa shinfi?e da murmushi ya zauna a bakin gadon yana kallonta, cikin rawar murya tace, "Ina kwana".
"Ba irin wannan gaisuwar akema mijiba ai kairunnisaa".
Batareda ta shiryaba ta?an ?ago ta kallesa tai saurin janye idonta gefe.
"Ya kika fasa kallon nawa Hauwa-Jiddah?".
Shiru tayi takasa bashi amsa, tasowa yayi da kansa ya kamata ya mi?ar tsaye, dukda tagaza kallonsa bai damuba, ya cire mata hijjabin tareda sumbatar goshinta da la??anta, cikin kuma sanyaya muryarsa yace, "ALLAH yay miki albarka kinji, yabama su Ummi ladan tarbiyar da suka baku".
Hawayen da take ma?alewa suka silalo, a zuciyarta ta amsa da amin.
"Kukandai bazai ?areba Jiddatulkhair?". Yay maganar yana share mata hawayen.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login