Showing 9001 words to 12000 words out of 121675 words

Chapter 4 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17143

shiga take jiyo sautin muryar Abbansu Na magana a zafafe.... Batada ikon juyawa dan haka ta ida shiga. Umma Na zaune a kujera y'ar tsugunno, yayinda Abba ke bisa tabarma da Umma ta shinfid'a masa. Yaye nik'ab d'inta tayi tak'arasa gabansa ta durk'usa, cikin rawar murya tace, "Abbah ina yini?".
Harara yakuma zuba Mata, wadda dama tunda ta shigo yake mata ita. "Daga ina kike k?, nifa bazan d'auki wannan iskancin nakuba, wlhy duk wadda tajawo min magana saidai ya k'arema uwarku, ke ko kunya bak'yaji kiyita yawo gand'an-gand'an cikin anguwa domin kuji dad'in tozartani a dinga nunaku Ana y'ay'an Alhaji zakari ne ko? To lallai bazan lamunta ba, kodai ki fidda Mijin aure kokuma wlhy Na baki duk Wanda yaymin, itama Zarahn tazo ta fidda miji dan banga amfanin wannan karatunba, kuma da kukeyi bazai amfaneku da Komaiba balleni dake wahala daku".
Cikin share hawaye Jiddah tace, "Abbah kayi hak'uri, wlhy ba wani waje najeba, gidan Uncle yahaya naje Na duba Maman Sadiq batada lafiya".
"Wannan kuma ke kika sani, nidai nafad'a miki".
Umma na zaune tana saurarensu, duk k'ok'arinka baka isa gane yanayin da take cikiba, dan fuskarta gwanace wajen shanye damuwa da 6acin rai. Koda Jiddah ta tashi ta shige d'akinsu tana hawaye da kallo kawai Umma ta bita, bayan shigewarta ta d'auke idonta tana maidawa ga Abba.
"Alhaji nikam inason na tambayeka wani abu".
Banza yay bai tanka mataba, sai dai ya nuna alamun yana saurarenta.
Bata damuba itama ta cigaba da fad'in "Shin wani yata6a nuna maka illar abinda kakeyi a rayuwarka kuwa? Baka tsoron ranar da zakayi nadama akan wannan ak'idar taka ne? Kokuwa dan kaga dai ina maka shiru akan lamarin yarannan? Lallai Ubangiji adalin sarkine, domin adalcin mulkinsa ne yasa shi fidda rayayye a cikin matacce wlhy, lallai ina jiye maka ranar dana sani".
Umma Na gama fad'a ta tashi ta shige d'akinta. Cike da tsantsar takaici Abba ya bita da kallo, sai dai kuma ya had'iye abinsa ya mik'e domin bin bayanta.

Umma dake zaune a bakin gado tayi tagumi ta d'ago idanu ta kallesa kafin ta janye.
Zama yay kusa da ita a bakin gadon yana fad'in "ke dad'ina dake Yagana rashin fahimta, to miye Na yankamin wannan maganganun?".
Murmushi kawai Umma tayi, dan hakan da yayi yakuma tabbatar Mata da zarginta. Ta d'an kallesa a kaikaice, "Halan yau amarya ta murd'a kanbunta na doguwar tafiya? Shiyyasa aka taho ga juji?"......
Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki. "Nidai karkimin sharri, a yaushe na ta6a cemiki juji?".
Nanma murmishin Umma tai kawai ta d'auke kanta tana had'iye wani Abu mai d'aci. Lallai rayuwar wasu mazan wanan zamanin Na d'aure kanta, mace batada wani kima ko muhimmanci a garesu sai in zasu biya buk'atarsu. Takanyi wata bataga Abba a Idonta ba, badan tayi tsufan da bazata iya amfanar dashi ba, a'a sai dan kawai ita uwace ta y'ay'a Mata wad'anda ba sune tsarinsa ko ra'ayinsa ba, idan harka gansa yana yawan zuwa gidan to lallai yayi fad'ane da hindatu ko tayi wata tafiyar da bazai iya jurewaba shikuma, to lallai a wannan lokacin zai maida gidanta wajen zuwa, abinda ke 6ata ranta da zuwan nashi shine gushewar farin cikin yaranta, dan yata caccakarsu da jifansu da kalamai marasa dad'inji, badan sun masa laifin komaiba, sai dan kawai su ba abin sonsa baneba............
Katse mata tunani yay da jawota jikinsa, tai firgigit Na dawowa hayyacinta, sannan ta janye jikinta tana mik'ewa.
Fuskar Abbah a d'aure yace, "Amma kinsan hakan bakomai bane a gareki sai nemawa kai tsunuwar Ubangiji da mala'iku ko? Dan inada ikon nemanki a duk sanda Na gadama kuma nayi buk'ata.
Wani murmushi. Takaici Umma tayi tana had'iye hawayen dake Neman cika Mata idanu, da k'yar ta iya furta "Salla ake kira".
Tsaki yayi ya cire hular kansa ya ajiye a saman gadon sannan ya mik'e, babbar rigarsa ya ajiye itama kusada hular ya fita.
Umma ta share hawayen fuskarta da bakin zani kafin tabi bayansa zuwa tsakar gidan. Yana zaune gindin rijiya a kujerar da Umma ta tashi, k'arasowa tayi ta d'auraye butar k'arfe data d'akko a d'aki sannan ta zuba masa ruwa ta rissina gabansa ta ajiye.
Hakan yayi dai-dai da shigowar Zarah da Walida suna Y'ar dariya, amma ganin Abbansu Na alwala sai kowa tai azamar had'iye dariyarta, ko kad'an basu Lura da motarsa ba a waje su.
Kallo d'aya yay musu ya d'auke idonsa, yayinda sukuma suka durk'usa suna gaisheshi.
"Lafiya". Kawai yace yaci gaba da alwalarsa.
Jiki a sanyaye suka maida kallonsu ga Ummansu. "Umma barka da gida".
Murmushin kwantar da hankali ta sakar musu tana fad'in "y'an makaranta an dawo?".
"Eh Umma". Suka amsa murya na rawa, kafin su mik'e zuwa d'akinsu jiki a sanyaye.

Jiddah dake kuka tun bayan tasowarta gaban Abbah ta mik'e da sauri jin maganar y'an uwanta, bata buk'atar su isketa tana kukan, dan haka tai azamar share Hawayenta.
Yayinda suka shigo da sallama saita tarbesu da fara'a, harda tsokanarsu.
"y'an matan gidanmu yau kun makara, dolene ayi muku bulalar makara gaskiya".
Duk yanda taso 6oye musu hakan bai hanasu fahimtar tayi kukaba, sai gani kawai tai Walida ta fad'o kanta ta fashe da kuka, itama zaran saita had'asu ta rungume tana sakin Nata kukan. Daman sunsan zuwan Abbansu gidan tamkar zuwan 6acin rai ne a garesu da Ummansu abar alfaharinsu da sonsu.

Umma data d'aga labulensu saboda Abba ya fita masallaci tace, "Kukuma minene haka? Nifa kunsan banason wannan shashancin, kufito kuyi alwala, k Zarah tunda ba salla zakiyiba maza fito ki d'aurayemin kulolin Abbanku Na abinci". Daga haka ta Saki labulen tabar wajen.
Suma sai suka saki juna kowacce Na share hawayrnta, sunsan ita kanta Umman nasu k'arfin hali kawai takeyi. Umarninta sukabi suka fito waje, walida da Jiddah suka d'auka butocin al'awala, Zarah kuma ta shiga kicin d'akko kulolin.................???








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[11/19/2019, 3:14 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[5......]_*


..............Gaba d'aya saisu Jiddah suka kasance cikin rashin sakewa, dan koda suka idar da salla basu fito tsakar gidaba, duk da zafin da ake zubawa yau. Itama Umma bata nemesu ba, dan tana idar da salla ta fito ta had'a abincin Abba takai falo, baiwar ALLAH harda kunna turaren wuta da maganin sauro. Tana kammalawa Ana kiran isha'i, dan haka bata nemesuba tawuce d'aki dan yin salla.
Ana idar da sallar isha'i Abba ya shigo gidan, babu batun sallama dama a tsarinsa sai gyaran murya, ada dasu Jiddah Na k'anana dasunji gyaran muryarsa suke guduwa su 6uya. (Humm ALLAH ya k'yauta??).
Babu kowa a tsakar gidan, dan haka ya wuce d'akin Umma, kulolin dake a tsakkiyar falon yake bi da kallo, kafin ya maida kallonsa ga Umma dake can wani d'an loko inda ta maida wajen ibadarta a tsakanin kujeru. Addu'a takeyi, dan haka baice komaiba ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu.

Su Jiddaha sunajin Abbansu na gyaran murya amma babu wanda yay koda gigin lek'owa waje.
Saima tagumi duk da suka rabga, kowa da irin kalar tunanin da yakeyi.
Jiddah ce tafara d'ago Kai ta kallesu, tausayin y'an uwan nata Yakuma kamata, cikin kauda tata damuwar ta zunguri walida dake kusa da ita. Kallonta Walidan tayi, Jiddah ta sakar Mata murmushi "Haba Autar Umma, irin wannan tagumi haka? Yau kin rik'e karatun islamiyya ko?".
Kasa magana Walida tayi, sai hawaye da suka fara zarya a kumatunta. Jiddah tad'an zaro ido waje tana kamo hannunta "Walida miya faru da kuka haka? Ko bakida lafiya ne?".
Kafin Walida tayi magana Zarah tace, "Yaya Jiddah kema kinsan Abbane".
"Abba kuma? To mi Abban yayi? Naga da kuka shigo baice daku komaiba ai?".
Shiru duk sukayi, Walida ta d'ora kanta bisa kafad'ar Jiddah tana cigaba da kukanta.
Kamata Jiddah tayi ta tayar zaune, "Kinga kukan ya isa haka to, yanzu dai idan anmuku k'ari kuzo muyi, idan kuma ba ai mukuba muci abinci nabaku wani labari, dan wannan kuka bazai canja komaiba y'an uwana, sai k'arin takaici da saka k'unar zuciya, mukasance masu godiyar ALLAH da samunsa a matsayin mahaifi, wani mahaifinma yafishi munin hali ai, amma masushi basu jefarba, to muma addu'a yakamata mu cigaba da masa kunji".
A tare suka amsa da to, kowa Na share hawayensa.
Qur'an suka d'akko suka karanto inda akai musu k'ari, Zarah ta fara karantowa, dan haka Jiddah taimata gyara dakuma maimaita mata har saida taji ya zauna a harshenta sannan takoma kan Walida, itama saida ya zauna sannan sukai Addu'a, Zarah ta fita d'ebo musu abinci.
Koda suka zauna zaman cin abincin sai duk suka kasa, sai kad'an sukad'an tsakura kowa yace ya k'oshi. Damma kad'an suka zuba.

Daga Umma har Abba suna jiyo sautin karatun su Jiddah daga falo, shi yanacin Abinci ita kuma tana zaune gefensa, dukda dai ba wata hira sukeyiba, garama shi akan kirashi a waya lokaci-lokaci, wani ya amsa wani ya share.
Itadai Umma ranta cike da farin cikin jin sautikan muryoyin y'ay'an nata Na karatun littafi mai tsarki, saitaji kaso mafi yawa Na damuwarta ma ya ragu.
(ALLAH sarki Umma??)

¡ï¡ï¡ï¡ï

Da asuba Umma da kanta ta fito ta hura gawayi, dan sanda Jiddah ta tashi harya ruru, lokacin anata kiran sallar farko.
Jiddah Ta fito tana fad'in "Umma kinga yau mun kusan makara wlhy".
Kallonta Umma tayi tana d'aura tukunya bisa garwashin, "Ai dama yanzu nake shirin zuwa na tadaku Jiddah, halan baku kwanta da wuribane?".
"Kusan haka kam Umma, yanzu mi Zan miki?".
"A'a jekiyi alwalanki kawai, suma su Zarah ki tadosu".
"To Umma".

Abba ya fito daga d'akin Umma fuska a d'aure, kai kace sak'on mutuwa aka aiko masa, Butar da Umma ta cika da ruwa ya d'auka domin yin alwala.
Su Zarah da Jiddah ta taso harsun lek'o kai zasu fito suka koma saboda ganin Abba atsakar gida, ciki suka koma, idan yagama ya fita sa fito.
Shikam baima San sunayi ba, yana kammala alwalarsa batareda yacema Umma komaiba yanufi hanyar soro, k'ofa ya bud'e ya fita.
Umma ta sauke ajiyar ziciya kafin ta kalli k'ofar d'akin su jiddah tana fad'in "Ku kuma Na la6e saiku fito ko". Ashe tana kallon su Walida sanda zasu fito suka koma.
Fitowa sukayi, walida ta d'auki butar alwala, Zarah kuma ta matso wajen Umma.
"Umma dan ALLAH nad'an d'iba ruwannan?".
Umma ta mik'e tana cewa "Ki d'iba mana, Amma ki k'aramin".
"To Umma Na gode".

Lokacin da Abba ya dawo su Walida duk suna tsakar gida, bayan sun idar da salla suka fito suna kimtsa gidan.
Umma ta dama kunu, sai Jiddah dake suyar fanke, Walida Na bakin rijiya tana wanke-wanke, Zarah kuma sharan tsakar gidan bayan ta gyaro d'akinsu.
Umma ma tana gyaro nata d'akin, dan inhar Abba Na gidan bata barin su Jiddah shiga mata d'aki.
Da gyaran murya ya shigo kamar kullum, dan haka su Walida duk suka nutsu, Dama bawani hira sukeyiba. Kowacce gaisheshi ta shigayi, ya amsa saud'aya yana harare-hararen Neman kuskuren dazai ci zarafinsu. Saidai kuma baiga komaiba, dan haka ya shige yana fad'in Zarah ta goge masa takalmansa.
Da to ta amsa muryarta Na rawa.
A d'arare su jiddah sukaita komai tamkar jiya da daddare, su Walida dai suka samu sukai shirin makaranta bayan sun cakuli abinci, dan yauma basuci Na kirkiba.
Lokacin da sukema Umma sallama Abba yanaji amma bai tankaba, sai Ummace taimusu addu'ar dawowa lafiya.

Jiddah ma a gaggauce takuma kimtsa gidan tai shirin Islamiyya ta fito, dukda da sauran lokaci ta gwammace tabiya ta gidan Uncle yahaya ta cinye lokacin acan.
Kod¨¤ tazo yima Umma sallama bata hanata ba, dan tasan gudun zama suke a gidan.
Bayan duk sun fice Abba ya kalli Umma yana wani cika da batsewa yace "Yagana had'amin ruwan wanka".
Da "to" ta amsa tana mik'ewa ta fice. Babu dad'ewa ta dawo tace ta had'a.
Fitar Abba wanka babu jimawa wayarsa tahau ringing, Umma batako kalletaba balle tayi tunanin d'auka harta tsinke aka kuma Kira, nanma sharewa tai, ganin anyi kira Na hud'u ta nufi wayar danta duba.
*Matata*
Shine abinda taga an rubuta a jiki, dan haka ta maida ta ajiye masa kayarsa takoma wajen zamanta.


Daga can ba k'aramar harzuk'a hajia Hindu tayiba, dan jikinta ya bata yana gidan matarsa. Shanye damuwarta tayi, saboda tana cikin taron mutanene, k'awarta ce ke aurar da y'a a jigawa shine taje. Dalilin kiran nasa kuwa ta kira kalifa ne taji idan sun wuce makaranta shine yace Mata driver yace babu mai a mota, kuma Abbansu tun jiya da yamma daya fita bai dawoba. Shine ta kirashi taji ina yaje? amma har Kira hud'u babu amsa.
Tana cikin wannan tunanin Kira ya shigo wayarta. Abba ne daya fito daga wanka Umma ta fad'a masa an kirashi shine ya duba, ganin Hajia hindatu ce yay azamar kiranta yana shigewa bedroom yabar Umma a falo. Sai dai kuma har wayar ta tsinke bata d'agaba. Kuma kiranta yayi.
Hajia Hindu dake kallon wayar taja guntun tsaki sannan ta d'aga. Ko sallama babu tace, "Alhaji kana inane?".
Dukda tambayar tabashi haushi saiya danne, saikace wani yaronta. Amma a fili sai yace, "Haba Maman kalifa ko gaisuwa ma babu?".
Dogon tsaki taja, a harzuk'e tace, "Kaga malam nifa ba wannan ya sakani kiranka ba, yara suncemin tun jiya baka gida, gashi yau sun tashi motarsu ta zuwa makaranta babu mai........"
Cikin nuna damuwa da 6acin rai yace, "Amma driver d'innan d'an iskane, shine bazai kirani a waya ya sanarminba?, to lallai bazan yarda da wannan iya shegenba......"
Hajia Hindu ta katse masa magana da fad'in, "Aiba laifinsa bane shi kad'ai, inda jarabarka bata motsaba katafi wani waje ka kwana hakan zai faru? Kamayi duk yanda zakayi kakaimin yara makaranta kafin su makara".
Kafin yayi magana ta yanke wayar. Ya dafe kansa saboda takaicin yanda Hindu ke datsa masa magana tamkar boyi-boyinta. Da hanzari yahau shiryawa, dukda ba zaman gidan yakeba yanada kaya a gidan.

Lokacin daya fito Umma na k'ok'arin had'a masa shayi da kayan tea d'in da Nafisa ta kawo musu.
Ganin zai fice tayi saurin fad'in "Abban Nafisa ina kuma zakaje ga Karin kumallo ina had'a maka?".
"Kinga barshi Yagana, su kalifa zanje nakai makaranta karsu makara, motar da ake kaisu makaranta babu mai".
"To".
Kawai Umma tace masa taja bakinta tayi shiru. Shikuma ya ajiye dubu uku a hannun kujera yay ficewarsa batareda yayi bayaniba.
Ko motsi Umma kasawa tayi a wajen balle tasamu damar d'aukar kud'in. (Nace, "Humm"??).

???????????


Lokaci da Aliyu ya fito daga cikin gida malam ya shige falonsa da k'ofar ke a zaure Na biyu.
Sallama yayi ya amsa masa tare da bashi izinin shiga.
Malam dake kishingid'e bisa lallausar dardumar dake wani sashe Na falon ya d'ago ido yana kallon Aliyu bayan ya rufe littafin dake hannunsa. Zama Aliyu yayi a gefen dardumar, malam yaymasa alama daya matso kusa dashi. Matsawa yay yana guntun murmushi.
Saida suka nutsu malam yace, "Aliyu!".
Cikin sanyinsa yace, "Na'am baba".
"Aliyu ina muka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login